Showing 63001 words to 66000 words out of 154870 words

Chapter 22 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1121

dan ban adireshinka mana na kawo maka hira?

Tsohon ya dube shi da kyau ya kalli kudin hannunsa, sai kuma ya yi shiru, can ya ce" yanzu yaro, tsakani da Allah dan ka bani wannan zaka biyo ni ka yi kudin kaina? Kudin kaina mana yaro, da ganninka ai ba.a ga yannayin mutumen kirki ba ko?

BS kam gannin wannan mutumen komai ma yana iya fada kai tsaye idan ya so kowace wace ya saka shi saurin dage kafarsa ya bi bayan motar da kallo ya dauki number motar dan walahi sai ya tarda shi ya ci masa abinda ba za.a fadi ba, gashi kiri kiri zai hada masa masifa da wannan mutumen

Ya jima yana shawagi dan ba zai shiga kai tsaye su hade da Abdul ba, dan kuwa ya ga alamar ya gode din nan yana iya yi masa komai

Abdul kam na shiga, bai zame ko.ina ba sai dakinsa,

Ya jima cikin ruwa masu dumi, ya lumshe idannuwansa ya afka duniyar tunani,
Waye ta ganni? Yaya sifarsa take? Yaya aka yi ya san da wannan abin da zai same shi? Sihiri ne, wannan magannin makarin sihiri ne ba na poison ba, ko likita bai ga guba a cikin bakin jinnin da ya fitar,
Waye kuma ya neme shi da sihiri? Wanda ya fadi makarin a gabansa aka yi ko yaya aka yi ya sani har ya bada makari?

Sai da ya kusan kwashe minti ashirin yana gasa jikinsa, sannan ya wanke jikinsa sosai da sosai ya fito ya zauna bakin gadonsa,

Dakin ya bi da kallo, daga nan aka fitar da shi ko daga ina? A halin summa, yanzu da ya zama marigayi kennan?

Murmushi ya yi kafin ya daga kansa sama yana shafar gemun fuskarsa,
Ni.ima, Ni.ima toh wace irin mace ce? Tana ina? Idan tana zayanno irin son da take masa har mamakinta yake, aman shi baya gannin kulawa irin ta son? Bata taba nuna yi masa girki ba, bata taba idan sun gama abinda suke ta gyara shinfidarsu ba, ita dai barta da yarinta,
Shi yasa yake zaune da niyar aure aure idan komai ya lafa,
Sai ya auri hudu, ya jera su daki daki, tsala tsala, su ringa yi masa juyi suna kashe masa ido, ya wuni a daki abinsa (yanzu marar lafiar ne?=?3?)

Haka ya yi ta zancen zuci, har aka yi kiran magarib nan ya ajiye komai ya mike ya nemi sallah

Bayan sallar magariba, sai a lokacin BS ya nufi ainahin bangaren nasu,
A lokacin da ya karaso Abdul har ya shige daka wanda ya gama zance da Muhammad da mahaifin Muhammad din a waya

A lokacin da ya hangota tsaye sai da gabansa ya fadi, ita da Hasana ne tsaye a kofar dakin Abdul sai bodyguard din Ni.ima rigar sojan da ya amsa ya kara ja ya gyara a jikinsa kafin ya karasa inda suke tsatsaye,

Dubansa ya kai wajen Hasana cikin daurewar fuska ya ce" ki yi abinda na saka ki yanzu, tsalan kwado kai ka irga mata

Fuska hade ya juya ya nemi dakinsu shi da abokin aikinsa ya watsa ruwa , har zai fito ya tsaya ya dauro alwallah sannan ya saka wasu kayan ya dauki salayar abokin aikinsa ya shinfida ya hau ya yi tsaye yana mai kallon alkibla, rabonsa da sallah har ya manta ranar (wa.iyazubillah) , haka ya gabatar da sallar magariba ya yi nafila sannan ya mike ya fice yana tunanin karbar adu.o.im shiriya=?O?
Abdul bai nemi sakewa da kowa ba har sai da ya kara kwana biyu ya warware sosai ya kara samun lafia

A yamacin yau ya fito da wandonsa wanda tsayinsa ba zai fi gwuiwarsa ba sai riga mai hannu kananu fuskarsa dauke da gilashi

A lokacin da ya fito du suka shiga hada hadar shirin fita, inda Hafsat da Hasana suka take masa baya,

Sai da ya fito tsakar gidan ya tsaya ya shaki iskar yamar dake kadawa, sannan ya juya cikin nutsuwa abinsa ya nufi bangaren ruwan dake gidan inda ruu suka kuma biyo shi su hudu harda BS

A lokacin da ya zo wajen ruwan ya yi tsaye, can ya hango runfarsa ta shanawa, wace a nan yake holewa da yan matansa,
Kansa ya girgiza yana murmushi ya kai dubansa wajen Hafsat dake kallon yanda ruwan ke garairai da shi sai daukan hankalinta yake, ya ce" shiga mana,

Ta san da ita yake, ta share shi ta kawar da dubanta daga wajen ruwan

Hakan ya saka shi juyawa ya koma wajen kujera ya zauna, su kuwa suka tsaya a bayansa wato Hafsat da Hasana

Kaffafiwansa ya daga ya fora saman kujerar sannan ya dago fuskarsa ya tsura mata ido ta cikin gilashi wanda hakan da ya yi ya saka ta kawar da fuskarta inda hasana kuwa ta kale shi ta kauda kanta dan kar ya ga ta kura masa ido,

Rigar jikin nasa fara ce mai digo digo blue sannan mai boturai, boturan saman du sun bude har uku hakan ya saka gashin kirjinsa bayana kadan, harda pecto dinsa na gefen hagu ana iya hanga idan aka kure shi da kallo

Harshen larabci ya dauko, da sak irin larabcin larabawa wanda idan ba kwarewa ka yi sosai din nan ba ba zaka gane komai ba ya ce" na yi marmarin gannin gashin kanki kauriyata, ya aka yi kika tsori yafa dan kwali kamar wace akai maki aure? Ko a summar da na yi kafin na dawo akai maki aure?

Du abinda yake fada tana jinsa, tana kuma biye da dukan kalmominsa, aman yannayin da ta nuna sai ka rantse da Allah da ba da ita ake ba, koma bata jin yaren da ake yi,

Kansa ya gyada ya ci gaba da fadin" kin san rayuwa ashe abu ce mai mahinmanci? Hafsat Malan ina son na rayu mai dan tsayi, kin ga na yi aure aure du na masu ciki abina!


Ikon Allah, shi ne abinda ta fada a ranta, ashe dai bai yi sauki ba? Ta kara fada aman kuma bata nuna da ta san yanai ba koda kuwa ta gane ya kama sunnanta da na malan ne dan ta kula magangannunsa

Abdul dake lure da ita ya ci gaba da fadin" ashe dai kauriyata banda zama kauriya harda magannin karya sihiri ta samu? To dan kwatanta min sak fuskar macecin nawa mana?

Sai a lokacin Hafsat ta juyo da dubanta ta dube shi da kyau, sak fuskar tata tamkar ta balarabiyar dan kwalin da ta yane kanta da shi yay mata das masha Allah

Yaren da bata taba yi ya ji ba, wace sai da ya mike zaune da ta fara dan walahi shi baima yarda da ba yarenta bane wai koya ta yi, wato larabci wace ta saka hasana juyowa itama da mamaki tana kallonta harda sakin baki, inda hafsat ta gyara tsayuwarta da harshen larabci ta ce" *Rayuwa, lumfashi, shakar iska zan iya ce maka mun fi jin dadinsu da komai, to ai dole ne Abdul, mutun ba zai san darajarsu ba sai a lokacin da ciwo ko wani abin ya tunkaro shi, yah Abdul*

Bata damu da irin kallon da suke mata ba ta juyar da kanta, gefe ta kara rage muryarta ta ce " *Abdullah*

Hannayensa ya dora gaba daya ya rungume a kirjinsa yana dubanta yana kuma sauraronta,
Hafsat ta numfasa ta juyo wannan karron ta saka idannuwanta cikin nasa ta dan rage tsayinta tamkar zata afka saman kujerar da yake zaune ta ce" *Abdel*

Idannuwansa ya lumshe daga kallon cikin idannuwanta yana tunanin me take son fada da mahinmanci haka? Sai sunnayen da ta kiraye shi da su, wato Abdullah, da kuma Abdel

Katse shi ta yi da fadin" *bayan tafiarta bayan korar ta da kakanin ka suka yi, ta yaya ka samu labarin ta haihu? Menene tabacinka na namiji ta haifa? Wanda yake yayanka ko yayarka, shin zumunci kake yi da su ko taimaka masu kake da wani abin? Ka san inda suke a duniya? Ko baka taba nemansu ba? Suna da bukata ko sun fi karfin hakan? Abdel........ina suke?*

Sai da Abdul ya zauna da kyau saman kujerar da a da kwonce yake yana dubanta,
Idan ya gane tana son sannin wani abu dangance da labarin da ya bata na rayuwarsa cewar yana da dan uwa ko? Aman me ya sa? Menene dalilinta?

Ya jima da zama, tamkarma ba zai amsata ba, ya kai dubanda wajen su BS dake shawahi sunna aikinsu, ya kuma duban bakuwar Bodyguard dinsa mai nacin kallo wato Hasana da ta yi kuri so take dole sai ta gane me suke fada ko meye? Kafin ya maida dubansa wajen Hafsat da ta yi shiru tana kallonsa, kallon fuskarsa sak take tana sauraronsa dan ta san a yanda ya kasance mutun mai taka tsan tsan ba zai yarda kamar sakarai ba a yi masa tambaya irin wannan ta fice ba tare da ya bada amsa ko ya ji dalili ba,
Fuskarsa ya hade kafin ya ce""""
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 7??



Fuskarsa ya hade sosai kafin ya ce" wa kike magana kanta?

Hafsat ta sauke lumfashi, ta dube shi da kyau, ta san fa ya gane wanda take nufi aman zai wani tambayeta!
Dan haka ta ce" mai aiki mana

Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" ki ce dai budurwar ubana!

Ido ta zaro tare da dora hannunta saman bakinta tana dubansa, bata san lokacin da ta ce" Abdul!

Idannuwansa ya bude daga lumshen ya kalleta da su kafin ya mike gaba dayansa ya shiga kokarin bin hanyar cikin gidan

Bayansa suke bi daidai da takun tafiarsa,

Bata gajiya ba a lokacin da zai shiga dakinsa ta yi saurin fadin sunnansa ta hanyar kafe shi da ido

Tsayawa ya yi yana dubanta , ido cikin ido suke kallon juna sai kuma ya yi kasa da idannuwansa ya mayar wajen lebenta da shi baima san nan ya kurawa ido ba a hankali ya ce " Hafsat, sunna zan raya, kin san bata jira dai ko?

Da sauri ta rintse idannuwanta sanadiyar kunyar abinda ya fada, gashi ya fada ne da yaren da kowa zai iya ganewa ga Hasana itama a kusa da su take sosai dan kuwa ita zata shiga ta gyara dakinsa kamar yanda aka saba,

Juyawa ta yi gaba dayanta ta koma gefe ta tsaya, ta kasa daga idannuwanta bale har ta yi ido hudu da daya a cikinsu, gaba dayansu kunyarsu ta ji ta mamayeta a haka har bata san lokacin da ya shige ba, sai takun takalman sarauniya ya shaida mata har ta karaso,

A hankali ta dago da dubanta ta sauke saman Ni.ima,.ta sha wani danyen lesh mai ruwan madara, ta sha kwaliya fuskarta tamkar ka saceta ka gudu,
Ni.ima ba ramama bace, sam bata da rama, sannan ba sakaken jiki ne da ita ba gashi ya hadu da kulawa dan akoyta kwaliya sosai, budurwa ce mai zamani wace dubai ke son malaka a wannan karni

Yannayin takunta ke tafiar da isarta, Ni.ima ta jiki, jika irin ta naira, dan kuwa bata nema ta rasa ba, ga kuma daidai gwargwado iyayenta sun bata tarbiya, so ne kawai ya sakata sangarta da shiga sabgar Abdul

Kanta ta sada dan kuwa du macen dake wajen a tsaye sai da Ni.ima ta kwasheta da kallo ta yarfata kasa da idannuwanta sannan ta tsayar da masu bin bayanta da hannunta ta juya ta buda dakin Abdul ta shige abinta ba tare da damuwar komai ba a fuskarta

Tana shiga gabanta ya fadi, dan kuwa ta san abinda ya kawota dakin, wai ita, yaushe zai zauna ya yi hira da ita irin na soyaya? Yaushe xai dubeta da duba na darajanta dan adam a matsayinta na matarsa?

Inda yake zaune ta je, tana zuwa ta haye saman cinyarsa ta zauna tana kallon yanda yake lunshe ido

Abdul dake binta da kallo ta kasan idannuwansa ya saka hannayensa ya janyota a hankali jikinsa sosai sannan ya shiga kokarin sarafata dan samun nutsuwar damuwar dake damunsa

Binsa kawai take, du yanda ya jirgata sai ta bi ba tare da ta nuna wani yannayi na shauki ko murafin hakan ba,
Tun yana yi da nuni a yannayinsa na muradin gannin shaukinta har ya cire a ransa ya shiga kokarin zuwa duniyar ma.aurata

Da sauri ta rike damtsen hannunsa wanda du girman hannunta sai ya kasance ko rabin damtsen bata cika ba bale har ta cike wajen da hannun nata,
Muryarta na rawa ta ce" ka...ka bari na birgeka mana?
Yakan ce da ita birge ni, a duk ranar da baya son zuwa waje mai kakant din , takan yi ta fama kafin ta samu ya samu kansa, har bata son yace da ita ta birge shi dan haushi take ji lamarin na wahalar da ita, sai gashi yanzu da kanta ta nemi ta birge shi?

Tsai ya yi da niyar shigar nata ya tsurawa yannayinta ido,
Tabas bata cikin ra.ayin hakan, sam babu muradin hakan a tatare da ita,
Aman rabonsa da ita fa yau 2 days, shi ne batama daukinsa?

A hankali ya janye hannayensa ya rage nauyinsa a jikinta sannan ya mike gaba dayansa,

Maimakun ta ga ya juyo ya bata damar birge shin sai ta ga ya nufi bayi

Da sauri ta mike zaune tana raraba ido, gabanta ne ke ta faduwa lokaci guda kuma ta ji wani haushin kanta wanda har ya hadasa mata zubar da hawaye, ya salam, ya yi fushi? Fushi ya yi ko me?

Nan take zaune tana ta sharar hawaye har Abdul ya fito da tawul yana goge jikinsa

Turus ya ja ya tsaya da mamaki yana kallonta tana kuka,
Yana son ya budi baki ya tambayeta abinda ke damunta aman bai san me yasa yake da nauyin baki a kan lamarin mata ba, shi dai zai maki surutu ne idan ya yi niyar dizga ki, shi banda Kauriyama wace mace ce yake sakewa ya yi ta surutu da ita?

Kallonta da yake ya sakata mikewa gaba dayanta ta nufo inda yake tsaye ta mika hannu zata taba shi ta ce" dan Allah ka yi hakuri kar ka yi fuahi da ni

Abdul ya dan ja baya yana dubanta kafin ya fahimci inda ta nufa,

Wajen ajiye tawul din ya nufa ya sarkafe shi ya juyo inda take tsaye ya ce" bana takurawa mace dan zuwa duniyarnan, ina son koda yaushe duniyar nan ta zama a kawace, ba fushi na yi ba, ki saka kayanki kinje ki tsaftace jikinki

Yana gama fada ya bude wajen suturunsa ya kurawa wajen ido,
Kaya ne kala daban daban, na manyan manyan kudade sannan masu kyan gaske,
Du a cikinsu ya janyo wata riga fara ya zura ba tare da ya saka komai ba ya dawo saman bed din ya zauna,
Har ta fice a dakin, da kuma kuka ta fita,
Bakinsa ya tabe yana mai kallon wajen windows din da ba damar ya shaki iskan wajen an rufe ruf

Karamar wayarsa ya mika hannu ya dauko ya kunnata,

Kara wayar ya yi a kunnensa bayan ya danna kira a wata bakuwar number

Bai jima yana wayar ba ya ajiye ya mike ya shiga shiryawa sannan ya saka akaiwa masu tsaron kofa maganar zai yi bako a bar shi ya shigo

A lokacin da bakon ya zo , Abdul ya nemi Hafsat da ta shigo wajen da zai gana da bakonsa dan ta kula da lafiarsa,

Bakon wani mutun ne da ba za.a kiraye shi yaro ba, magidanci ne ya kwana biyu sosai sai dai ba tsoho bane,

Irin mutanen nan ne wayayu, masu shegen wayo da son da bakinsu su sayi du wani gara,
Suna siyen kuwa dan idan ka yi wasa lokacin da zasu tafi da kai kai kanka sai ka laluba ka ga babu kai

Tunda ya zauna suka gaisa Hafsat ke tsaye gefe tana aikinta ba tare da ta bada hankalinta kansu ba

Tambayar da Abdul ya jefa masa ne ya sakata maido hankalinta inda suke zaune ta raja.a dukan wani nutsuwarta a kansu da rataunawar tasu, sannan sai a lokacin ta gane ya saka ta shigo ne dan wannan dalilin

Mutumen ne ya dago hannunsa na dama ya shafi gaban goshinsa kafin ya maida hannuj bayan keyarsa ya dan sosa sau biyu ya ce" eh Elhaj, tabas marabina da su na ga dan nata , sosai saurayi ne kakarfa sai dai sam baya kama da kai, kuma shi fari ne,

Abdul dake kallonsa ya ce" kuma yaya sunnansa ne? Yanzu a ina suke ne? Ko nace marabinka da su a ina?

Dan zakutowa mutumen ya yi ya saka hannayensa ya ja rigarsa ta kara yin sama hakan ya baiwa dogon wandon rigar damar kara bayanuwa,
Agogon hannunsa ya murza da babar yatsarsa, ya zagaye ya kuma zagayewa, sai da ya rintse ido na sakonni sannan ya budi baki ya shiga bada labarin marabinsa da matar da kakaninsa suka koreta da cikin mahaifinsa, wanda ya tabatar masa cewa namiji ta haifa harma ya ga mutumen da idannuwansa, ya tabatar masa cewa makudan kudadan da kakaninsa suka bata dan ta kula da rayuwar dan da zata haifa sun isheta rayuwa suna cikin wadata suna rayuwa cikin jin dadi,

Abdul ya sauke kafa daya daga saman cinyarsa ya ce" ta musulunta ne?

Sai da ya kurawa Abdul ido sannan ya ce" ae, eh

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login