Showing 93001 words to 96000 words out of 154870 words

Chapter 32 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1136

da ta gani a daidai kofar dakin da aka saka Abdul ya sakata nufar wajen har tana hardewa , muryarta ta buda ta ce" *ABANA*

Da sauri ya saki kofar da ya buda da jiyar shiga domin likita ya ce ana iya shiga Abdul ya farka ya juyo inda ya ji muryar

Ita ce tsaye gabansa
A hankali ya furta" Alhamdulilah.... *UWATA*

AI kuwa Hafsat ta fashe da kuka sannan ta arta a guje , tana zuwa ba wata wata ta fada jikin mahaifinta ta kankame hannunsa tana wani irin kuka , bata wani damu da tunawa ya hana su fadawa jikinsa ba, ko jikin wani namijin haka kawai ba, shi kansa sai da ya ji kwala ta cika idannuwansa sannan ya yi mamakin yanda mamansa ta girma a dan lokacin nan fuskarta ta nuna alamun ta nutsu.

A hankali ya cirata a jikinsa yana kallonta ya ce" ya isa haka ko Uwata?

Tana haki da komai ta ce" Aba, ba guduwa na yi ba Abana, Abana ka min auren da du wanda ka zaba min na maka alkawarin da zauna da shi koda kuwa yankan naman jikina yake, Abana ka yafe min, ina mamana? Abana ka san inda aka kai ni? Ka san me aka min? Abana gidan yarin *KUTKALE* aka kai ni a matsayin wace ta yi laifi na zama budurwar dan ta.ada, Abana daga nan aka kai ni .....

*UWATA* ya fada cikin nutsuwa yana kallonta,

Hannunsa ya saka ya share hawayenta sannan ya ce" Abdallah ya je ya fada min,

Shiru ta yi tana kallonsa, sai a lokacin mamaki ya kamata na jin wai Abdallah ya je wajen mahaifinya ya fada masa wannan maganar,
Ikon Allah, sai yanzu tunanin me ya zo yi asibitin ya dirar mata,

Dubanta ta kai cikin dakin marar lafiar nan ta hango Abdul kuri su yake kallo
Gabanta ne ta ji ya yanke ya fadi lokaci daya kuma ta damki hannun mahaifinta a hankali ta ce" Abana, ya farka

Malan ya kai dubansa wajen Abdul din, ya ga gaba daya hankalinsa a kansu dan haka ya ja hannunta da niyar shiga da ita, sai dai ga mamakinsa hannun ne ya fara rawa ta kasa motsawa harma ta iya furta cewa" Aba

Tsayawa ya kuma yi da mamaki ya kalli yannayinta, a hankali ya cika hannun nata sannan ya juya ya shiga dakin , sai dai ya kasa rufe kofar dan du ji yake idan ya rufe ba zai bude ya kuma ganninta a wajen ba

BS ne ya zo ya yi mata magana fuskarsa a tamke hakan ya sakata bin bayansa suka je suka tsaya nesa da dakin, bai ce da ita komai ba sai dai shirun da ya yi shima yana kallon waje daya kamar yanda ya ga hankalinta ya raja.a dakin da mahaifinta da kuma Abdul ke ciki

Tun da malan ya shiga ya nemi waje ya zauna, ba abinda yake karantawa Abdul sai girman hakuri mahinmancinsa da sakamakon da ake samu mai kyau idan an yi shi,
Jarabawar da ya shiga mai girma da duhu ya ringa bashi baki da musalai da kuma ribar da zai samu idan ya yi hakuri da ita a hakan,

Shiru ya yi yana kallon yanda Abdul ke kallon kasa bai ce da shi komai ba
Ci gaba ya yi da bashi baki, da nuna masa kar ya dauki maganar cewa zai dauki fansa shima, hakan ba zai kai shi ga ci ba, ba zai samu wata nasara ba

Abdul ya dago idannuwansa da suka yi jajajir da mugun nauyin da sukai masa ya sauke a kan malan
Sai da ya hadiyi yawu mai daci da kuma yauki a hankali ya ce" ba komai *ABA, ALLAH YA JIKAN DU WA.INDA SUKA MUTU*
Sai da ya ji zuciyarsa ta girgiza, ba komai fa yace? Tabas yana iya karbar abin aman ba komai din na lokaci daya ya bashi mamaki, ko dan yana cikin hali na rashin dadin yannayi shi sai ya ce kamar yau baya cikin yan magana ma,

Ajiyar zuciya ya sauke ya mike da niyar fita, sai dai muryar Abdul ta dawo da shi cewa" Aba,
Dama amini na zama makiyi? Aba dama alkhairi na jazawa mutun kiyaya? Aba, shin a gabanan zan iya yarda da wani dan adam komai kusancina da shi kuwa?

Aba ashe aminina ya kashe min kanwata? Ya kashe min mahaifiyata? Ya kashe mutanen dake tare da ni? Du dan ya kai ni ga ciwon hauka kafin na bar duniya? Aba........zuciyata sai nake jin tamkar ba zata kuma gannin haske ba, ji nake tamkar na gama da farin ciki, idannuwana na gannin kowa da fuska biyu, *ABA, shin me zai saka na yarda da kai kanka?*





Halin rudani na rudar da zukatanmu a likacin da wani lamari ya dake mu=??, sauki na Allah ne
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 2??


A hankali malan ya koma ya zauna ,
Sai da ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" da baka yi magana irin haka ba, da na bar wajenka cike da tsoro da tunani dan kuwa idan ba mahaukaci ba sai mai kishirwar ramuwa zai hadiye irin wannan lamari lokaci daya
Abdallah , imani da Allah da yarda cewa a cikin mutane akoy masu cuta akoy masu tsoron Allah,

Imani, hakuri ne kawai zasu saka ka yarda da wani mahalukin a nan duniya
Zan so ka kasance mai hakuri ka cinye jarabawar nan Abdallah

Kansa ya sada yana mai jin yanda zuciyarsa take cinkushe bata da wani yannayi na wanda zai iya samun nutsuwa,

Kansa ya kuma dagowa ya kalli malan ya ce" da idona, da kunnena na jiyo shawarar aminan mahaifina na zasu hada ni da bin mata, duda bata fadi komai ba idannuwanta sun karantar min komai
Zan so a ce ba daga bakinta haka ya fito ba ko na samu damar musawa har na fuskanci dan uwana

Malan ya kara matsa kujerarsa kusa da gadon yana kallonsa ya ce" ka rage zurfafa kauna , haka kuma ka rage zurfafa kiyaya
Tsananin kaunar da kake masa da yardar da ka bashi dari bisa dari ne ya rufe maka ido ka kasa gannin ainahin wanene shi, sannan wacece ta fada maka? Kar ka yarda ka hau kan abu ba da kwakwaran shaida ba

Idannuwansa ya dago yana kallon Malan,
Sai da gabansa ya yanke ya fadi, a lokaci daya kuma irin yannayin da ya tarda ta ya fado a idannuwansa,
Shikenan, ta dalilinsa rayuwarta ta bace ko me? Anfani ya ringa yi da ita? Shi kam me ya yiwa Muhammadu a duniyar nan? Me ya yi masa da zafi haka? Da sauri ya kali malan, tausayin malan da na Hafsat ne ya ji sun mamaye zuciyarsa, ta jure gwagwarmayar rayuwar nan, ta shiga Kutkale ta fito lafia, t??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????a shiga gidan horon maza ta fito lafia, du bata rasa mutuncinta ba sai a dalilin bashi tsaro? Bashi tsaroma ya dace ya mayar da ita tun harbin da akai mata aman ya kasa hakan ya riketa a wajensa gashi ya jaza mata wannan balaki?

Muryar malan ce ta dawo da shi daga dogon tunanin da ya saka shi mayar da ido ya rintse dan jin wani irin kyankyamin Aminin nasa,
Bai taba jin kyankyamin zina, kallon matan wasu ba irin na yau....sai a wannan lokacin ya ringa hasko dubunnan matan da ya ganni tsirara dan kawai ya samu biyan bukatarsa,
Sai a lokacin ya yi tunanin wa.innan mutanen fa y'ayan wasu ne, iyayen wasu ne, yayun wasu ne, kuma kannun wasu ne, duda su suka kawo masa kansu aman shi dan rashin tsoron Allah da rashin kunya ya mike ya mika masu abinda ya fi sirri a jikinsa suka lumda suka bashi nutsuwa ta hanyoyi daban daban....sai gashi shi ya ki ya haihu dan kar a yiwa abinda ya haifan aman cikin ikon Allah,
Allah ya saka masa muguwar shakuwa da yarinyar da basu hada komai ba, shekarunsu ba daya ba , fatarsu ba daya ba, shakuwa irin ta yan uwantaka wace yake jinta har cikin jinninsa, yake yi mata so daya da ba hadi... an yi mata abinda yake gudun a yiwa yayan nasa? Dama ba.a isa a zagaye ikon Allah ko a yiwa Allah dabara ba ko? Dama lokaci Allah ya ara masa na ya gama zagaye zagayensa kafin ya rike shi?
Kai, ya san ba zai iya ja da amininsa kan maganar kisan kan da ya ringa yi....wannan Allah zai saka masa! Cin amanar aminta da ya yi ..shima ba zai wani hukunta shi ba,
Aman baya jin zuciyarsa zata iya amince masa ya hadu da mutumen da ya tsaga jikin Hafsansa ba tare da igiyar aure ba dan kawai cin mutunci da wulakanci ba tare da ya gile shegiyar da ta kai shi aikata hakan ba, tabas sai ya yi masa kaciya da faratunansa zai tsinke abinda ya kasa rikewa a wandonsa sai da ya ketawa Hafsat hadi!

Shiru Malan ya yi gannin wasu guntayen hawaye na biyowa gefen fuskarsa , carbinsa ya ci gaba da ja yana mai dubansa a kasan zuciyarsa kuwa yana nema masa sauki a wajen ubangiji

A haka BS ya shiga dakin ya ja ya tsaya,

Ya jima a yannayin da yake na sarawa Abdul na kallonsa kafin ya iya daga masa hannu ya sauke hannunsa

Yana saukewa a hankali ya ce" takarda ce daga saudiya, suna bukatar a mika masu mai laifi dan an karanta masu komai an kuma tura masu dukan hujoji ta hanyar computer shine suka turo da sakon a mika masu shi can

Kafarsa dake ajiye yana karkadawa a hankali ya ce" idan aka basu shi me zasu iya yi masa?

BS ya yi shiru domin ya tabata tambayar ba ta neman amsa bace

Abdul ya dago jajayen idannuwansa ya ce" zasu saka masq fararan tufafi ne, su dauko shi su shigo tsakiyar gari da shi, su saka masa bakin yadi su rufe masa fuskarsa su dauki doguwar takarda su karanto laifinsa sannan su saka doguwar wuka sun gile kansa.....

Sai da ya tsaida idannuwansa cikin na BS ya ce" an bashi mutuwa mai sauki, bai ga duniya ba an tafi da shi lahira.....


Malan dake kallonsa sai da ya ji dar din Abdul din, dan kuwa gaba dayansa ya mike zaune ya kara kallonsa da kyau ya ce" ka bani wayoyina

Da sauri ya juya ya yafito su Hafsat dake tsatsaye

Suna shigowa ya karbi wayoyin Abdul din dake hannun su Hafsat ya mika masa su kuwa du suka juya suka layu daga kan Bs Har su Hafsat din kusan garu inda malan ya bi Hafsat da kallo dan kuwa yanzu ba hijab din a jikinta cikin damararta na aiki da ta saba

Abdul kam mikewa ya yi tsaye kan kafafuwansa da kayan asibiti a jikinsa ya danna kira,

Ana dagawa ya canza harshe ya shiga magana cikin yannayin zafi zafi , yana yaran larabawa wanda Hafsat da Malan suna fahimtar duka kaf abinda yake fada

Cikin yannayin tsoronsa ta kafe shi da dara daran idannuwanta, dan kuwa ya fito sak a baban mutun ma.aikaci mai zaman kansa mai iko da kansa wanda ya san hakokinsa da wa.inda ba.a isa a take masa ba

Maganar da ya karasa da uta shi ne" *in dai ba za.a sake shi a saki amininsa a fili a basu damar kashe kansu ba, to fa ba.a isa a tura shi saudiya ba, a barshi a Minna su yanke masa hukunci....a kai shi Niger a saka shi a cikin gidan kason KUTKALE*

Yana gama fada ya ajiye wayar ya daga manyan damatsunansa ya cusa hannayen nasa a cikin gashin kansa

Ya jima a haka ba wanda ya ce komai a cikinsu har ya yi niya da kansa kuma ya juyo a hankali

Yana juyowa ya kurawa Hafsat dake kusa da BS ido,
A hankali ya kai dubansa wajen BS din, da kuma Hasana....
Haka kawai ya tsinci zuciyarsa na cewa" ba abinda basu gani ba

Rigar asibitin ya shiga cirewa hakan ya saka Hafsat saurin sada kanta daga dubansa da take, ba ita daya ba du wanda ke wajenma sai ya kawar da dubansa a kansa , wasu na mamakin shi bashi da kunyar cire kaya ne? Wa.inda suka san ko shi waye kuwa basu wani yi mamaki ba

Wando da riga ya saka bakake lut, sannan ya saka gilas a fuskar tasa ya juyo wajen Malan dake tsaye,

Zuwa ya yi sosai kusa da shi sannan ya duka har kasa, a hankali ya ce" na gode da mutuntani, da adu.o.i da nasihohi, in sha Allah zaka juya da Hafsat a yau yau.....zan zo nima domin zaman kasar nan ya fice min a rai

Malan kam kansa kawai yake gyadawa yana kallonsa, haka ya mike ya fice inda suka mara masa baya gaba dayansu

Suna fita daga asibitin ya mikawa BS waya,

BS na gama sauraron maganar ya kalli Hafsat da sauri, sannan ya kali Abdul,

Ganni ya yi Abdul din ba wani alamar fara.a a tare da shi, dan haka ya mika masa wayar ya je kusa da Hafsat ya yi mata bayanin abinda aka ce

Ji ta yi kamar tsokanarta yake, dan haka da wani irin gudu ta karasa inda Abdul yake tsaye,

Haki ne ya hanata magana sai nuni da take masa,

Abdul ya lumshe idannuwansa yana mai jin nauyinta har cikin ransa ya ce" ki je

Hawayen idannuwanta ne suka bale, cikin yannayin kuka ta ce" kana nufin..shikenan? Kana nufin na zama mai cikeken yanci? A yanzu ta waya ka saka aka sake ni daga kason da na shiga? Kana nufin zan ga mahaifiyata

Dariyar da take ua saka shi tsurawa fuskarta ido,

Hannunsa ya dago a hankali, hakan ya saka hannun nasa dake bari bari ya dora yar yatsarsa a gurbin kumcinta da ya lotsa sosai , sannan ya kama dan mayafin nata da ya fadi a kafadunta ya dora saman gashin kanta sosai ya rufe,
Idannuwansa ne ya sauke saman kirjinta, lokaci daya gabansa ya buga da mugun karfi, lokaci daya kuma ya rintse idannuwansa a hankali ya ce" *zan waiwaye ki*

Suna tsaye suna kallo ya shige wata mahaukaciyar bakar mota ya tayar ya harba bakin titi inda su hasana suka mara masa baya

Gaba daya jikinta ne ya mace mata, bata son tafia ta barshi du irin zumudin gannin wannan ranar,
Gata dai ga mahaifinta, sannan an tabatar mata da ta bi mahaifinta ta je gida ta huta ba tare da an tsara mata tsarin rayuwarta ba,
Sai dai kash, yau ta tabata sabo tirken wawa ne, ita kuwa ta yaya zata iya sabawa da rashinsa bayan ya saba mata da shi a ko wani motsi nata?

Dubanta ta kai wajen BD dake tsaye yana yi mata murmushi, sai a lokacin ta waiwaya sai ta ga mahaifinta baya nan,

Da sauri ta ce" ina Abih?

BS ya saki murmushi yana kallonta ya ce" sun tafi da Abdul, daga can za.a kai shi aeroport ne, akoy abinda zasu yi, mu je a can zamu hadu

Ajiyar zuciya ta sauke ta daga kafarta ta shiga motar da ya nuna mata ya tayar suka kama hanya

Ko a hanya hira ne BS ya cikata da shi, wanda dadaya take tsinta sai dai ta yi masa murmushi

Cikin nutsuwa ya ce" kin taka sa.a, babar sa.ar rayuwa, wace ba kowa ke samun irinta ba,
A yau na ga abubuwa da yawa, na ga ribar zuciya daya da girman adu.a, tabas a baya na yi sake da na ringa wasa da Sallah, ashe dai wanda ya rike Allah ba zai ji kunya ko ya wualakanta ba?

Hafsat ta sakar masa murmushi tana mai kallon gari, itafa walahi har wata iska mai sanyi ce take ji tana ratsa gabanta.....

Muryar BS ce ta tsinke tunaninta a lokacin da ya ce" *me zai hana ki cika min nawa burin nima? 1ki karbi tayin soyayata ki so ni tamkar yanda nake son ki Uman Malan?*

Tsurawa fuskarsa ido ta yi tana kallonsa,
Menene aibunsa? Dama sallah ce, a yanzu yana yin sallah tun karfinsa,
Idan ta kai warhaka da karfinta a sha.anin kutakale tabas harda taimakon BS

Yana biye da ita ne dan yana matsanancin son ta,
Ita kuwa isan bata so shi wa zata so? Mutun ne shi mai daraja da daukaka, ya kasance mai kaunarta tun bata zama Bodyguard ba, ya kasance mai kawar da kai a irin halayanta na yau da kulun, ya jure iskancinta kala kala, baya hukunta ta, baya sakata kwana cikin maza.......yana kishinta, to ita kuwa wa zata samu ya yi mata irin wannan son?

Kanta ta sada cikin yannayin kunya, abinda bata taba nuna masa ba a hankali ta budi bakinta ta ce"........
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login