Showing 108001 words to 111000 words out of 154870 words

Chapter 37 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1124

ja baya tana kallon sa

Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" wanki kike ne? Ina mai wankin ki?

Kin bashi amsa ta yi , saima juyawa da ta yi ta dauko wata shanyar zata shanya

Kara matsawa kusa da ita ya yi ya ce " wai fushi ake da ni ne?

Hafsat ta tsaya da shanyar tana kallonsa,
Abdul ya saki murmushi ya ce" yi min murmushi kin ji?

Hafsat ta zabga masa harara tana kallonsa sannan ta shanya kayanta

Zuwa ta yi ta dauki bokicin karfen ta zubar da dan sauran ruwan cikin bokicin sannan ta juyo da niyar tafiarta

Da sauri ya kama kunnayensa ya ce" na tuba, dan Allah ki min magana ko daya ce Hafsat

Hafsat ta kale shi sama da kasa sannan ta juya ta yi shigewarta cikin dakinta

Ji yayi gaba daya hankalinsa ya tashi, a hankali ya lalubi kofar ya fita ya shiga motarsa ya ja,

Tukin dai kawai yake, aman gaba daya kunnayensa sun rikice, bukatarsu shi ne su ji muryarta, idannuwansa kuwa su ga murmushinta,

Hannun nasa da ya mareta da su ya kara kallo, sai kawai ya kai yatsarsa guda wajen bakinsa da niyar cizawa
Ko me ya tuna, ya fasa ya ci gaba da wani irin tuki har ya karasa gida

Yana shiga gidan wayarsa ya dauka a cikin motar ya shiga kiranta,
Tun yana kirga kiran da yake mata tana reject har ya daina irgawa ya zauna kawai bakin bed dinsa ya cire belt din wandonsa ya bale mabalin rigar ya dan sasauta wandon kasa ya dafe gaban goshinsa da hannunsa yana kara gwada kiranta hankalinsa a kanta gaba daya

Can ta daga, cikin wata irin murya mai cike da kasala da sangarta ta ce" Abdul, ka barni na yi hira da mijina mana, yaya ina waya da shi kana kirana sai titit yake ya kasa jina yanda yake so

Idannuwansa ne ya lumshe, a hankali yake jin maganar na girmama a zuciyarsa, kamar da wasa ya ringa jin maganar tamkar ta zagi mahaifiyarsa , wani irin dacin maganar yake ji,
A kasan ransa ya maimaita" *tana hira da mijinta?*

Zuciyarsa ce ya ji ta wani irin bugawa, a hankali ya ce" ki yi hakuri kin ji? Ki daina fushi da ni Hafsana

Ita kanta yannayin yanda muryarsa ta fito sai da ta ji gabanta ya fadi, a hankali ta janye wayar a kunnenta ta duba shi dai ne,
Mayar da wayar ta yi a kunnenta ta yi shiru tana sauraronsa, sai wata irin ajiyar zuciya take saukewa wace ke sauka da lumfashinta tana dirar masa har kahon zuciyarsa

Ji ya yi idannuwansa sun yi masa wani irin nauyi, a hankali ya ce" ba zan kuma marinki ba, kar ki hora ni da fushin ki Hafsat

Sai da ta ja numfashi kamar wanda ya toshe mata lumfashin nata ta ce" ba dukan da ka yi min ya tsorata ni da kai ba Abdul

Abdul ya yi saurin cewa" menene?

Hafsat ta ce" irin yanda ka nuna rashin damuwarka a halin da zan shiga da kuma mamana bayan na fada maka bana jin dadin hakan,
Abdallah, ka san girman matsayinka a wajena? Kai yayana ne, abokin sirina, aminina, Abokina,
Abdallah ina jinka a raina sosai, ni ba zan yarda na saka ka a damuwa ba, aman kai sai ka saka ni ka yi tafiarka, ka san halin da nake ciki a gidanmu ne?

Ji yake harta gaban jikinsa sun yi masa nauyi, du wani furuci nata sai ya kayar masa da gaba, wai me ya sa ne ta kasance mai karfin ruguza shi, sannan mai karfin saka shi risinawa? Shin me ya sa take da madaukakin iko a kan muradinsa da akasinsa?

A hankali ya buda bakinsa ya ce........




Hapoy sallah yan uwana,

Allah ya karbi ibadun mu, ya maimaita mana



>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?


>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 9??



A hankali ya kuma iya daga bakinsa ya ce" Hafsat... ..


Wani irin jan sunnan ya yi, ya karasa shi da ajiyar zuciya wanda ya hakan ya saka Hafsat rungume fillow din dake kusa da ita ta lumshe idannuwanta baki daya ta shiga neman saisaita lumfashinta, domin gagarar buda bakinta bale har ta iya amsawa ta yi

A hankali ya ce" bani da uwa, mahaifina yana jin kunyata da ba zai iya kuma rayuwa tare da ni ba,
Na tara dukiyar da ni kaina ban san adadinta ba,
Ina kwana da sannin ni ba kowa bane dare daya mala.ikan mutuwa zai zare raina na zama gawa

Shiru ya yi kafin ya ce" a da na zauna zaman ni sai na ga mace an min asiri, ko wata rana sai na ga wani kalar tsiraicin daban bayan na kwana da sannin mai kallon tsiraici baya tsufa da ido, tun a gidan duniya bare irin girman hukuncin da zan tarar aman haka nake tafe watara na hadu da yarinyar da na haifa da cikina, wata rana na hadu da wace ta haife ni da cikinta aman da yake aikin shedan ne haka zan zauna na bita da kallo har ta gama karanta min karatun nata na zubar da najasar tawa a kasa kusa da abin wankana!
Hafsat, sai da kika zo rayuwata na fara fahimtar eh lale idan da asirima to ni kaina na baiwa abin gaskiya,
Hafsat ke ce ta biyu bayan mahaifiyata da nake jin kunyar ki kama ni ko ki san irin halin da nake ciki daga bakin lokacin da na fahimci kina tare da ni da zuciya daya da niyar gama aikin ki lafia ki yi gaba abinki
Hafsat ba irin kalar iskancin da ban nuna maki ba aman sai ki juya abinki ko idan abin ya yi maki tsauri take kike wanke ni tas bakya raga min harma ki zubar da hawayenki dan takaicina
Ina sane, ina sane da dukan motsin ki,
Hafsat, ba zan iya hadiye abu a kanki ba, ba zan iya kawar da kai a dukan wani wanda zai cutar da ke ba,
Ban san dalili ba, har ji nake lumfashina zai tsaya idan na ji ki a damuwa,
Abin haushinma sai kawai kike son canzawa daga matakin mai kare yancin kanta ki koma wata mau tsoron mutun, ban kai hanuna fuskarki ba sai tukukin haushin kin kirayi kanki da muguwar kalma, Hafsat, koda a ce haka kike ina nufin kalmar nan ke din ita ce ta haramta ga kowani mutun ya fade ta, ina iya soya masa idannuwa dan ubansa!

Wani irin tsam tsam tsam ta ringa ji a gaba daya jikinta, lale ta yarda da maganar nan cewa a duniya ka ji a damu da kai ba karamin jin dadi bane bare ka gani da idannuwanka,

A hankali ta ce" kai mafadaci ne Abdallah

Murmushi ya yi, wanda bai yi shirin yinsa ba, wai Hafsat ce ke cewa wani yana da fada

Sai da ya gama murmushin ya ce" takura maki ake a gidan nan ko? Me suke maki ne? Wa da wa ke maki?

Ta so sakin baki dan fada masa , sai dai a likaci daya kwakwaluwarta ta tina mata wanene shi, da kuma magangannunsa ba cika baki bane yana iya aiwatar da alkawarinsa ko furucinsa,
Dan haka sai kawai ta ce da shi" ba wani abu ni dai ka taya ni da adu.a samun saukin rayuwa

Haka suka yi ta tautaunawa har kusan raba dare, sai da ya ji yannayin saukar numfashinta ya canza, a hankali ya ce" baci ki ka yi?

Shirun da ya ji ne ya saka shi sakin murmushi a fili ya kai dubansa agogo, karfe biyu har da rabi, adu.ar baci ya yi mata wato ta tsari daga wayar da niyar Allah ya kai mata domin suna tsakar hirar bacin ya yi awon gaba da ita ta gaji ainun gashi ya tsareta har wannan lokacin


Da duku duku, da duhu duhu kamar yanda ya saba jiransa har ya karaso yau har tarbo shi ya yi

Tun da ya hango shi ya tabata akoy abinda ke faruwa dan kuwa mahaifinsa nasa na kiyaye a ganshi tare da shi ko dan kar a san a yanda ya same shi ya jaza masa matsala a ma.aikatarsa

Motarsa ya bude ya shiga , kafinma ya gaishe shi sai ya ji ya balbale shi da fada kamar haka" lale lale Bashir kana wasa da wuta! Tun lokacin da ka je yi masa aiki na gargadeka cewa wannan mutumin da kake gani basaja yake dan kar a gane meye asalin aikinsa, na bayana maka ko waye shi mai gidan mai gidanka kuma ubanka ne shi! Aman da yake cikin kwakwaluwarka majina ne cike shine har kake son sako shi a lamarinka? Har ya kasance shi zai yi bincike kan yarinyar da kake so kuma? Yaushe zaka daina zuwa gidajen yan mata kana nuna kana so ? Nawa ka saka har muka je tambaya ka dawo ka fasa? Nan yarinyar nan har ciki kuka zubar kuna soyaya daga baya ka watsar da ita da ka gama samun abinda kake so, shine yanzu tsautsayin tozarci ya kai ka ga afkawa wajen da zaka tonawa kanka asiri ka tona min? Waima yar gidan wa ka je ka saka kanka a ciki da har ya saka shi tasowa da kansa da niyar yin bincike a kanka?


Haushi, takaici hadi da kishin lamarin abdul ne ya turnike BS, haka kuma haushin mahaifinsa ya kama shi, shi ya san du abinda ya saka babansa a taro a taro din nan dan baya so duniya ta san ya haifi dan gaba da fatiya ne, aman ba komai zai nuna masa shi din ya iya iskanci

A dake ya ce" yarinyar nan ce da ka kawo daga prison *KUTKALE* na horata ta zama bodyguard

Da sauri ya kale shi,
Kansa ya girgiza sannan ya ce" lale a mahaukatanma kai baba ne, ka san da shugaban kasar nan ya yi kira cewa a kurce sunnanta a matsayin mai laifi ko mai bashin kasa a kanta? Yarinyar da ta gagari yan ta.adar Kutkale? Yarinyar da ta fito lafia daga kutkale? Ta zo nan ta zama zakararsu? Yarinyar da ta tsare mutuncin kanta take adu.ar Allah ya tsareta?

BS ya ce" wannan abinda take nuna mana kennan! Ni kaina da farko na dauka hakan ne, aman daga bakin lokacin da ta fara yiwa Abdul aiki na gane cewa itama watsatsar ce sai dai bata haraka sai da manya, yarinyar da ta bi Abdul kuma ta kare da abokinsa? Idan ba aikinta ba ta ya ta gane shi ne mai neman rayuwar Abdallah? Idan ba kwaratanta ba ta yaya muka tarda ita a yannayin da muka tarda ita? Ta raina arzikina ne, bata san ba wanda ta gama watsewar da shi ba aurentan zai yi ba! Eh na je gidansu, kuma ina son aurenta dan haka a aura min ita ba ruwan kowa

Ikon Allah kawai yake kallo kafin ya ce" ka sani, ni kaina mai tsayawa shara.a da kai ne idan ka cutar da rayuwar yarinyar nan, bare na tabata ba za.a rasa mai iya wujijiga namanka ba, dan ka sani *yar kamilin datijo yar kuma baban gida ce*, yanzu fice min a motar nan tun kafin ka hadasa min wani ciwo!


Bakinsa ya tabe, sannan ya fice a motar, yana kallo babansa ya shige cikin gidan horon da motarsa sannan ya kara tabe baki a fili ya ce" idanma iskanci ne ai gado na yi, kuma yan mata yanzu na fara haye ruwan cikin du wanda ta dagan buje! Itama wancen tunda na lura ba zan samu dan arzikina ba zan aureta na haye ruwan cikinta na ga meye banbancin sa da na sauran da har ake min iskanci a kansa, dama dama ni na zubar da cikin ban bari ta haifo min dan ba! Kai da ka haife nin sai na saka ka a uku!

A haka ya gama magangannunsa na rashin kunya sannan ya aro fuskar jarumin namijin ya kutsa kansa cikin wajen da yana shiga du suka shiga bashi girma suna kauce masa har ya isa inda zai hori yaren


Bangaren Hafsat bata ga wani canji daga wajen BS ba, yakan kirayeta su sha hirarsu, hirar soyaya, bai taba kauce hanya wajen yi mata hira ba, yakan nuna mata soyayarsa tsakani da Allah ne, tsantsar tausayinta da nuna mata so ya saka ta ita kanta fara shakuwa da shi,
A haka har ya yi sauran kwana uku a kwanakin da Malan ya diban masa kan ya turo da magabatansa su zo neman aurenta da komai sai dai shiru ba.a irin daya daga cikin manyansa ya zo dan jin karin haske a batun

Abdul kuwa, ya zamewa dangin Hasfat tashin hankali, bashi da lokacin shiga gidan malan, kowani lokaci ta raya masa zai zo gidan malan ne ya dauki kujeru ya ajiye kasan katon dalbejiyar gidan mai sanyin ni.ima wace da yawancin lokuta matan sukan zauna a nan aman kirikiri wajen ya haramta wa su sai dai su hade a daki hajia uwar gudan malan su yi abinda suke yi a labe, abin na basu mamaki, na basu takaici irin yanda malan ko yayan cikinsa bai sake masun da zasu ringa shiga gidansa a lokacin da suka yi ra.ayi ba ko dan yayansa mata aman sai gashi wani garjejen kato dan kawai hannunsa na rike da hatimin nasara ya mayar masa da gida wajen zama sannan ya saka wannan tsaura idon a gaba har ka ringa hango hakoranta tana washkala dariya , dariyar da ba.a san me yake ce da ita ba, duda rabonta da ta yi wata shiga ta ba daidai ba tun da ta dawo aman ai ba daga shigar mutun abin yake ba!

Fitowa ta yi daga dakinta cikin nutsuwa ta shiga dakin mahaifiyarta,
Yayarta ce zaune tana ninke kayan da aka wanke kafin a kaisu guga , yaronta kuwa yana can cikin kuryar dakin da mahaifiyarsu tana neman kaeanfanin da ta saka aka siyo mata mai yawa ta raba biyu fan baiwa yarinyar nata rabi dan anfaninta sai wasansa yake ita kuwa tana taro shi

Da murmushi ta karasa kusa da yayar tata ta zauna itana ta dauka ta kade ta shiga ninkewa,

Kallonta yayar tata ta yi tana murmushi ta ce" amarya amarya

Itama kallonta ta yi, ta kawar da kanta a hankali ta ce" aunty gabana na yawon faduwa a duk lokacin da kika kirayeni da wannan sunnan, wai dama nima zan yi aure? Na auri mai sona haka? Harma na yi tunanin samun yanci?

Murmushi ta yi, ta ce" bawa baya cire rai da rahamar Allah, koda ace zaman kanki kikai kika hayayafa Allah zai baki malamuncinki bale yanda kowace y'a take haka kike? Ina so a kaiki gidanki da raina da lafiata auta, zan so na ga takun rayuwae aurenki na tafia cikin salama

Murmushi ta yi har hakoranta suka bayana fili , sai kuma ta sada kanta irin ta ji kunyar nan

Shigarta yayar tata ta kala, sabuwar abaya ce mai ruwan ja mai duhu ta yane kanta da dan kwalin abayar, ta yi kyau karshen kyau a haka bata shafa komai ba koda kwali ne

Tana shirin yi mata magana sai ga mahaifiyar tasu ta fito, kallonsu ta yi kafin a hankali ta ce" Anmih, yaya haka? Wancen bawan Allahn ba ke yake jiraba?

Bakinta ta dan cuno gaba ta ce" mama, fada fa mukai da shi jiya a eaya shine yau zai wani zo min haka kawai mutun sai neman fitina bayan na fada masa ya fita a harkar yan gidanmu, cewa fa ya yi zai zane yaya fa, kuma a gabansa da gaban hajia, kuma ya fadawa Aba cewa wai shi ya girmi yaya aman ya shigo gida bai gaishe shi ba shi zai xane shi idan ya ci gaba da yi masa rashin kunya, yanzu mama tsakani da Allah abdallahh ba zai shiryu ba? Yayanmu mu duka gidan zai zane? To mu mu shiga ina da ranmu? Baya gudun rigima sam, sai kace gidansu wai ya shigo gida bai gaishe shi ba
Ta karashe tana turo baki

Dariya auntynta ta saka sosai har

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login