Showing 132001 words to 135000 words out of 154870 words

Chapter 45 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1129

doctern da kawai yake binta da kallo

Sai da ya dan sosa kansa sannan ya shiga yi mata tambayoyin da suka shafi aikinta ko karatu, shekarunta, shekarunta nawa da aure,

Tambayarta ya yi cewa, shin kafin ta yi aure ta ringa shan maganin hana daukan ciki? Jin cewa auren nata gaba daya bai fi wata biyu ba

Ido ta tsura masa, cike da mamaki,
Kanta ta girgiza

Ajiye biron hannunsa ya yi ya ce" look, zan so ki bani gamsashiyar amsar da zata bani damar dora ki abinda ya dace, mararki na cinkushe ne da maganin hana daukan ciki, na.urar da muka yi anfani da ita ta bamu damar fahimtar hakan

Ajiyar zuciya ta sauke, a ha?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 nkali ta ce" ban taba sannin kalarsa ba

Docter ya dubeta da yannayin mamaki, aikinsa ne ya zama wajibi ya bi didigi, dan haka ya ce" ko dai kin sayi magani a bakin titi na mura ko wani abin a rashin sani an baki wannan?
Shi kansa sai da ya fadi hakan ya ga abin wani baibai, a bakin titi?

Hafsat ta dago da dubanta, zuwa lokacin hankalinta ya fara tashi,
Idannuwanta ta saka cikin na docter ta ce" bana shan magani na fi kaunar a min allura da na hadiyi magani! Rabona da na hadiyi magani na kusan shekara hudu! Bana sha, bana bukatar shan magani docter!

Kansa ya daure, dan haka ya ce" magani ne mai hatsari kika ringa sha, ba sai kin sha shi a gudajinsa zai tarun maki a mara ba, koda a narke kike shan sa idan ya fi karfin ki zai je ya tarun maki ya zame maki matsala, magani ne mai narkar da sperm, muna samun irin cas din nan sosai, bamu bata a hakan, aikina ne fannin mata, yanzu haka zamu dauki fitsarinki dan mu ko ahigar cikin kika samu yake faman barewa ya saka haka?

Hannayenta gaba daya biyun ta dora saman table din, a hankali ta dora su saman yalwatacen gashin kanta dake fitar da ni.imtacen kamshi
Gabanta ne ke faduwa, lokaci daya rigimarsu ta baya son haihuwa ba zai daina baiwa matarsa maganin rashin daukan ciki ba ta shiga fado mata a rai, tun tana matsayin bodyguard dinsa, tun a lokacin da yake yi mata maganar matsalarsa a ranar da ta yi fushi ta shige dakinta ya bi bayanta yake mata bayani, har ta yi masa nunin yana tunanin ya isa ya zagaye abinda Allah ya hukunta a kansa?

Da sauri ta dago da dubanta ta ce" docter, ko a cikin abinci, ko a jus ana iya narkar da shi?

Docter ya bata amsar kwarai kuwa

Gabanta ne ya kara faduwa, lokaci daya kuma ta samu ta mike daga zaunen da take,
Lale yau ta yarda cewa rayuwar da suke da shi ana yinta ne bisa tafarkin sha.awar jikinta, ta sani mace bata daraja a wajen Abdul, rashin nuna mata soyayarsa bai dameta ba gannin suna zaman lafia, sai dai a yau ta gane yana zaune da ita ne da zuciya biyu, suna zaune gida daya karkashin innuwa daya suna wasa da dariya suna raba shinfida daya yana tatalinta yana rungumeta ba dan so ba sai dan albarkatun jikinta, ita kuwa me ya rufe idannuwanta har haka? Me ya yi mata dadi haka? A yau a duniya ba zata iya zama da mutumen da baya tsoron Allah har haka! Da ta mutu fa? Da ta samu mugun ciwo fa? Yanzu haka wa ya san me ya samu mahaifarta? Sam, bata ma fara yi masa son da idannuwanta zasu rufe ta zauna da shi yana bata maganin da zai cutar da ita a duniya sannan ta je ta tarda Allah, yo ita wani dadi ta ji na duniya da har zata ki mararin samun dan jaririn da zai debe mata kewa? Namiji? Zara yi ta zama da shi kulun a dadi zuma ne? Watarana sai ya nuna mata halin, wata rana sai ya yi mata abin, idan ya mayar mata da wuninta tamkar tana prison din KUTKALE wani sanyin idanniya zata kalla ta ji sanyi? Yau du wanfa baya son haihuwa da kai baya son ka, koda mutuwa ce zai maka fata

Likitan ne ke kiran madame, ji mana? Nurse din ma ta biyo bayanta sai dai ina, gashin kanta ya yi mata male male a jikinta, rigar ta mugun karbarta du kuwa da jigatar da ta yi ta fito a dakin

Abdul dake tsaye yana kallon kofar dakin urgence din ya tako da sauri yana kallonta da mamakin har ta mike likitan bai fito ya kiraye ahi ba??

Hannunsa ya mika wajen fuskarta, murna, mamaki, da fargaba ya dan dago habarta yana kallonta, a hankali ya ce" Kauriyata, kin tashi? Ni na san sai kin fi karfin wannan ciwon! Me aka ce ke damun ki? Mu koma na ji bayanin likitan

A hankali ta saka hannunta ta cire nasa daga habarta,
Idannuwanta da suka canza mata ta dago ta saka cikin nasa cikin wani irin kallo na kakausa,

A hankali ta ce" Abdul, dama haka ne rayuwa? Ashe ki ba zai tana zama so ba? Abdul na godewa Allah da bana jin ko digon son ka a raina!

Gabansa ne ya kwonci kwonci ya fadi, da sauri ya kara buda idannuwansa yana kallonta, a hankali ya ce" Hafsat, kwakwaluwarki ta tabu ko.me? Me aka baki a cikin dakin can???

Hafsat ta yi murmushi tana kallonsa, a hankali ta ce" Alhamdulilah, ban haukace ba, hasalima na fi kowani lokaci nutsuwa, Abdul dan Allah na roke ka, ka je gida ko ka tsaya a hanya ka rubuto min takardata, na hakura zama da kai!

Da karfi ya ce" *KE*

Hafsat ma ta ce" *KAI!*
Na tsane ka Abdul! Na tsane ka! Ka sake ni, in sha Allah koda ka bata min mahaifa ba zan rasa mai kwasana a haka ba!


Hannunta da ya rike ba da karfi ba ta fizge daga rikon ta juya da sauri ta fice a haka

Summar seconni ne Abdul ya yi a tsaye sakamakon jin cewa ta farga da abinda ya ringa bata cikin jus ko abinci,
Kalamanta suka kasance ruwan farfadowarsa,

Lokaci daya ya daga kafarsa da gudu ya bi bayanta,

Har ya kusan fita ya dawo doctern dake tsaye ya ciro baje dinsa ya nuna masa, a gagauce, murya cike da jaraba da tashin hankali ya ce" walahi sai na tagayaraka! Na rantse ba zan barka haka ba!


Doctern ya bi rubutun da kallo lokaci daya kuma Abdul ya fice daga wajen, Doctern ya kalli nurse din itama shi take kallo,

Muryarta na rawa ta ce" docter dama ana haka? Ba aikin ka ka yi ba???


Doctern ya juya da sauri ya shige Office yana danna wayarsa

Abdul da ya fito a kafarsa da mugun gudu, sai dai me...adaidaita ya hangi ta dauki Hafsat har sun falfala da gudu

Wani irin ihu ya saki a wajen ya ce" Hafsat! HAFSAT!
Burbudin hayakin adaidaitar kawai ya bade shi, lokaci daya ya ringa jin duniyar ta yi masa zafi,
Hankalinsa ne ya ringa jin ya gama tashi, a hankali ya ringa jin numfashinsa tamkar na mai ciwon huka sai sama yake yana kasa,
Hafsat ce zata bar shi?
Hafsat din sa ce zata bar shi?
Ky din motarsa ya laaluba ya ji baya jikinsa,
Ya tataba ita ta lalube dan kar ya bi ta da gagawa!

A hankali ya ce" Hafsat, kar ki bar ni....na tuba

Idannuwansa ya rintse yana jiran wani adaidaitan, dan ya san kawai gidan malan zata je, zai kai kansa da kansa , a yi masa du hukuncin da ya dace aman walahi ba mai raba shi da matarsa!

A lokacin daa Adaidaitan ya tsaya ya shiga, sunnan anguwar kaawai ya fada masa, bai damu da yau ya taba shiga adaidaita ba, hankalinsa a tashe kawai yake!
A hankali ya kuma fadin" ko hijab babu a jikin ki Hafsat, na san darajar du wata halita taki Hafsat, yaya zaki fita cikin garin dake cike da kuraye a haka? Hafsat, ina *Kishin ki=??*, ..............






=?)?=?)?=?)?=?)?=?)?=?)?=??=??=??=??=??=??
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 1??



Direct bakin makaranta Abdul ya nufa, dan ya tabatar cewa Hafsat ba zata koma gidansa ba, sai dai ta yi gidan su

Sosai malan ya yi mamakin ganninsa an sauke shi a adaidaita sahu,
Bai gama mamakin ba wani mamakin ya sake kama shi jin Abdul ya bukaci da a biya mai adaidaitan

Shi dai malan cirewa ya yi ya biya sannan suka zauna tare da almajirai ana ta karatu

Abdul ya yi tsuru tsuru yana bin malan da kallo, shi kuwa malan ya maida hankali tun bayan da suka gama gaisawa da Abdul din kan dalibansa

Sai da ya gama yiwa wa.inda zai yiwa kari, ya kuma karbi harda wajen wa.inda zasu kawo sannan ya takaita dogon zaman karantun ya yi masu salama

A hankali suke takawa shi da malan har suka samu wata sansanyar innuwa suka zauna

Malan ya fuskanci Abdul, sai da ya dan kara kallon yannayin shigarsa, lale mutun ne mai son saka jalabiya, sai dai shirin abin kallo ne

A hankali ya ce" Abdallah, yannayinka bai kwontar da hankalina ba

Abdul dake ta kale kale ya dubi malan, a hankali ya sauke boyayiyar ajiyar zuciya sannan ya ce" Malan, a gafarta min, ni din mai laifi ne

Malan ya kara fuskantarsa da kyau, a hankali ya ce" me ke faruwa ne??

Abdul ya sada kansa da kyau, can ya ce" dama ta taba nuna min bata son irin haka tun a lokacin da muka yi zaman aiki da ita, tsoron irin rayuwar da na gani, na kuma aikata a da can baya kafin na shiryu ya kasa barin zuciyata har nake daukan mataki, hakan ne ya hasalata har ta min fushi da munanan kalamai, Malan har cewa ta yi wai ta tsane ni

Malan dake sauraronsa ya dube shi da kyau, duda bai fahinci laifin da ya aikata ba, domin kuwa Abdul din sam bai fadi laifin nasa ba, sai dai ya ji mamakin mugun furucin da ta yiwa mijinta, miji fa? Miji mai daraja? Ashe du irin nasiha da gargadin da ya bata lokaci mai tsayi yanai mata a banza ne? Bai taba jin ya mugun ji haushin mamansa irin na yau ba, ashe ba zata saduda da duniya ta gane ba gidan zama bace
Malan bai iya cewa Abdul komai ba, sai da ya sauke ajiyar zuciya na bacin ya fi a kirga sannan ya ce" a ina take ne maman??

Abdul dake sasada kai cike da kunya ya dan dago jin kamar ton din voice din malan ya canza , a hankali ya ce" na san ta zo gidan ne dan ranta a bace ta shiga adaidaita

Malan ya gyada kansa, nan ya kara tabatarwa kansa cewa lale bata san ciwon kanta da na mahaifiyarta ba, yanzu ko dan gudun gorin yan gidansu ba zata yi hakuri ta zauna gidan mijinta ba? Mutumen da shi bai gujeta ba , a irin yanda aka so wulakanta ta, ya dauka ya ce shi a daura da shi, shine zata furtawa ta tsane shi,
Sai.ma ya ringa jin haushin Abdul din kansa dan ya nuna muguwar damuwa da shi, a nan take kuma ya shiga tambayar kansa....shin ya mugun sangartata ne ya saka ta irin wannan lamari ko me?
Bai iya cewa komai ba sai shiru da ya yi da bakinsa ya mike ya yi gaba

Abdul ya mike da sauri yana dan sosa kansa ya bi bayan malan

Wajen mitar suka nufa malan ya masa bismillah, wato yana nufin ua shiga

Abdul ya bude ya shiga motar ya yi shiru yana kallon waje guda

Sai da Malan ya tayar da motar ya fara tafia kadan kadan sai kuma ya take birkin, kallon Abdul ya yi ya ce" kai, dan me ka zuba mata ido ta yi maka rashin kunya baka lakada mata duka ba? Kai zaka bari ta ringa haka ne? Mamana fa idan ta samu haka ba zata taba jin magana ba, mamana ce, ni na haifi abina, na san wacece ita !


Abdul ya tsurawa malan kawai ido, duka, wai ya daki Hafsat, hm

Malan ya kuma tayar da motar ya dauki hanyar gidan

Abdul na lure da yannayinsa, kamar ransa ya baci sosai, sai dai ya kasa yin wani abin yana dai biye da shi

Malan na zuwa ya ja ya tsaya kofar gidan

Sauka ya yi ya nufi cikin gidan bayan ya umarci Abdul da ya tsaya

Bai jima da shiga ba ya fito,
Tsaye ya yi yana kallon yannayin garin,
Hankalinsa ne ya fara tashi bata gidan, bata zo ba
Juyawa ya yi ya karbi waya a hannun baban yaronsa ya lalubo number yayarsu

Amsar da ta bashi bai ji dadinta ba, domin rabonta da Hafsat tun da suka rakata gidanta wai

A haka ya ringa kiran yayan nasa har ya fada kan Mariama

Inda infa ta fara a lokacin da ya tambayeta Hafsat,

Kashe kiran kawai ya yi, ko hular kansa bai cire ba ya koma motar ya tayar

Tun da yake bai taba zuwa gidan yar tasa ba, bai taba zuwa ba ko da wasa, ko bata da lafia yana jira har ta zo da kanta sannan sai gashi yau bai jira an yi masa iso ba bai sanar da zai zo ba ya yiwa gidan tsinke bayan ya umarci sirikin nasa da ya biyo bayansa su shiga

Nana mariama dake tsaye bakin Pamp ta dago da sauri jin muryar mahaifinta da kuma kamshin turaransa

Idannuwanta ta kwalalo waje baki daya, lokaci daya kuma ta gyara zaman hijab din jikinta ta ce" Aba???


Malan ya gala mata wani mugun harara, ransa bace ya ce" ina take??

Marima ta yi gagawar juwaya ta tafi dakin, bata jima ba sai ga Hafsat ta fito, a kan rigar nata dan kwali kawai ta dora ba abinda ya shafeta ,

Tana fitowa ta nufi malan da yannayin rigima

Bata san da haka ba, bata taba tunanin haka ba, bata taba zaton hakan zai faru ba, sai ji ta yi na farko a rayuwarta mahaifinta ya wanka mata mari

Daga Abdul, har Nana mariama idannuwa suka zaro a fili a tare kuma suka Furta Aba=?3?
Ba.a taba yi ba, hakan bai taba faruwa ba, malan bai taba daga hannunsa a kan mamansa ba, bai taba taba lafiar jikinta ba, hakan ya saka lokaci daya Hafsat ta duke a wajen a kan kafafuwanta
Kanta ta sada kasa, gaba daya jikinta ne ya dauki rawa

Hankali tashe Abdul ya nufeta, yanda ta dukan shima ya duka, gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, lokaci daya kuma ya kuma dago da dubansa ya kali malan, muryarsa har rawa take ya ce" Aba, nine da laifi fa, walahil azim nine da laifi ba ita ba, Aba ka san me na mata? Aba magani fa.............
Da sauri ta dago , duban da ta yi masa bai hana shi son karasa maganar tasa ba, gannin da gaske fadi zai yi ta saka hannunta da sauri ta rufe bakinsa, lokaci daya kuma hawaye na zuba a idannuwanta tamkar an bude fanfo

Aunty nana mariama dai jikinta ne ke bari tana kallon mahaifinsu,
Bata taba tunanin zai saka hannunsa ya mari mamansa ba

Mamaki ne ke neman kashe malan gannin wai Abdul haushi ya ji dan an daki mamansa bayan yanzu ta gama rashin da.ar ce masa ta tsane shi! Ita kanta maman nasa kuma bata so mijin nata ya fadi laifinsa

Daina cewa abinda ya yi niyar cewa ya yi, sai kawai ya ce" ki tashi ki koma dakin ki, shi ne tabatuwar kwonciyar hankalinki mamana

Yana gamawa ya juya ya fita,
Yana fita Hafsat ta saki hannunta daga bakin Abdul ta mike

Da sauri ya mike ya bi bayanta sunna shiga dakin nana Mariama ta ja yan yayanta ta hana su shiga ta zauna sai zarar ido take

Abdul na bun bayanta ya ja ya tsaya , a hankali ya ce" Hafsat....

Hafsat kamar jira take ta juyo da sauri , cikin bambami ta ce" me kuma kake so? Mahaifina ka je ka tiso? Me yasa ba zan yi daraja a idannuwanka ba Abdul ka dake ni kuma ka hana ni kuka?

A hankali yake binta da kallo, sam baya sonta da irin haka,
A hankali ya ce" ki daina daga min murya Hafsat, ba kyau..nine mijinki, ke kuma matata, ba kyau kina daga min murya komai bacin rai

Hafsat ta yatsina fuskarta ta juya dan cikinta ba wai gaba daya ya daina murda mata ba,
Juyawar da ta yi a hankali ta durkusa tana kara damke mararta

Da sauri ya je wajenta ya duka shi din ma ya dora hannunsa a saman cikin nata,
Shafawa yake yana adu.a a hankali a hankali har ya lafa mata,
Muryarsa ce ta kara rikicewa a lokacin da ya ce" ki yi hakuri, ban yi haka dan bana son ki ba, hasalima ban san idan zan kwatanta maki kalmar nan ta inda zan bi ba
Hafsat, ki yi hakuri, ki rufa min asiri mu koma gidanmu, ba zan kuma ba, ita kanta Na.imar zan hana ta sha
Hafsat kar ki guje ni dan na kasance mai laifi, kiyi min nasiha ki dawo ki cancane ni,
Fada fa kike min ki tirsasa ni abinda na kauce, dan me yanzu zaki guje ni?
Dan Allah, na tuba...kin ji?

Hafsat da idannuwanta ke lumshe, tana sauke ajiyar zuciya tana sauraronsa
Abdul

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login