Showing 45001 words to 48000 words out of 154870 words

Chapter 16 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1118

a yanzu tana cikin hali na tsoro,
Maza ki saka hijabin ki, ki haya sama wajen malan ki shaida masa cewa adu.ar da za.a fita yanzu inji ni nace a rokarwa mamansa sauki!

Ajiyar zuciya ta sauke ta dauki hijabin nata ta fita dan kaiwa sakon mahaifiyarta, domin kuwa ba.a koya masu musu da iyayensu ba, ko Hafsat ta fita daban ne a cikinsu dan idan Hafsat ce har Malan ta sha hayawa dakinsa tace da shi Babana, kan abinda ka yanke a gidannan ni bai min, ba zan bi ba! Sai dai ko wace wace

Da kyar ta samu ganninsa, domin sai samun baki yake masu zuwa karbar adu.a a yamacin nan,

Sakon na isa kunnayensa kansa ya gyada yana murmushi,
Ba komai ya saka shi murmushin ba sai gannin yau ta yarda da maganar cewa mamansa a raye, shi kam ya jima da yarda da hakan, karin tabacin hakan shi ne irin yanda ya jita a jikinsa amasalaci ranar juma.a, sannan aka sumar masa da malan,
Dan haka ya sakawa Asiya albarka ta mike ta fito tana mai taya iyayenta adu.ar baiyanuwar daya daga cikin yayansu, wace ta tabata soyayarta ta darsu a ran malan tun da ya amshi haihuwarta, ta ci sunnan mahaifiyarsa, kuma ta yi kama sosai da mahaifiyar tasa sai yan abubuwan da ta dauka na mamanta irin ido da yannayin kallo da kafarta da yan yatsuntsanta, aman har miskilanci na mamansa ne, ta zo ta sauke alkur.ani a kananun shekarunta, ta hadace ta dandamki litatafan adini take shigarsu a guje, ta zo harkar boko ta ce kauce ban wuri, kai wani lamarin harda baki dan kowa dai kowa dai maman malan, maman malan, hakama mahaifiyarsu du irin yanda take nunawa maman malan sun tabata da ace wata mai bin sahun iyayen ce, da ba zata iya boyo soyayarta ba, ko dan irin baiwar da Allah ya yi mata na abubuwa da yawa....

Kallonta ta kai kan Abdul majid, yayansu ne baki daya yana shirin haurawa sama wajen malan ta gaishe shi ta yi gaba aman sam ba kamar yanda can da baya suke yar ganewa juna ba, da kallo ya bita yana mamakin tana fushi da shi dan ya fadi gaskiya a kan kanwarta ne? Dan kuwa tun lokacin da ya ce su daina damun kansu kan wata maman malan, dan kuwa shi a irin iya shegen yarinyar nan in dai ba mutuwa ta yi ba, to kawai ta shiga yawon duniyarta ne aman malan ya kasa ganewa sai asarar kudinsa da lokacinsa yake a kan yarinyar dake kokarin hadasa masa ciwon hawan jinni!....................................................................
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 0??

Kafadunsa ya daga ya ci gaba da haurawa sama wajen malan.

Wannan kennan


Abdul na zuwa wajen da suke bai tsaya wata wata ba ya kinkimi hafsat ya dora a kafadarsa ya nufi gidansa da wani irin sauri bamashi da niyar kula maganar da BS ke yi masa ya shige gidansa inda BS ya shiga neman layin asibiti dan a zo a dauki Hafsat da Jibrin din yana mai mamakin inda kuma Abdul zai kai Hafsat

Yana shiga bai zarce ko.ina da ita ba sai dakinsa na baci,
Yana zuwa ya shinfideta saman bed dinsa ,

Juyawa ya yi ya dauko yar akwatin aikinsa ya bude ya zauna ya ciro kayan aikinsa,

Sai da ya zuba alcohol ya yi disinfect wajen kafin ya dauko wani sixo ya dubi yanda Hafsat ke lumshe ido ya dago ya yi mata rumfa kadan ya saka hannunsa na haku ya rike hannun nata da kyau yanda ba zata iya motsawa ba ya saka sixo din nan cikin ramin harbin ya shiga kokarin jan bullet din,
Wata irin zufa da wani dan ihu ne ta saki tana mai rike hannunsa tana kwalkwacewa, aman ina ta kasa cire hannunsa bale har ya cikata ta kwace nata hannun, har sai da ya ciro ya gama wanke wajen ya gyara ya rufe mata sannan ya cikata ya juya yana tatara kayan ya mayar baki daya inda ya dace sannan ya juyo inda take idannuwanta rufe ruf sai sauke ajiyar zuciya take irin ta wahala sosai din nan,

Kujera ya janyo ya maida bayanta kusan gadon ya hau ya dora kansa saman bayan kujerar yana dubanta,

Murmushi ya saki ya ce" yanzu da a kanki ne suka harbe ki da wannan karin gashin da kike kakabawa kulun ina keacewa da sai dai ki mutu ido daya a bude daya a rufe kina gannin yanda malakiri ke nuna maki zaki fada ne idan kika je da wannan karin gashin mai mayar da ke irin yan iskan nan na turai,

Shiru ya yi yana gannin yanda take marmarmar da idannuwanta kafin ya ci gaba da fadin" ni, ban san wata irin marar jin magana bace ke Hafsatu!

Ido ta bude cike da mamakin sunnanta gatsal da ya kama eai harda wata tu ya kara,

Bakinsa ya tabe ya mike daga saman kujerar yana dubanta ya ce" a tashin min a bed, sai wani bankaro min kike kina nuno min abinda ba tayawa zan ba bare na siya malama mike harbin bullet a hannu ba zai saka ki kuka bama bale har ya kashe ki! Kin wani yi min dare dare a bed an samu laushi ko?

Kanta ta girgiza daga kwoncen da take kafin ta shiga kokarin mikewa , sai a lokacin ta ga rigar jikinta, sannan ta tuna irin yanda ta ringa bankarewa dan zafin ciwo ashe wannan dan sharin yana kallonta har ya yi mata wata fasara daban,

A lokacin da ta zauna, gashin kanta gaba daya ya yo gaba ya rufe mata fuskarta ,
Daidai lokacin ya dawo a hankali ya zauna,
Hannunsa ya kai wajen gashin kan nata ya janye a hankali, wanda hakan ya sakata dago da idannuwanta ta sauke saman fuskarsa,

Lumshe idannuwan nata ta yi ta kuma budewa, yatsina fuskarta ta yi hakan ya baiwa gefen kumatunta damar lotsawa gaba dayansu haka kuma saman goshinta ya yi wani dan limki limkin da ya fitar da yarintar fuskarta da kuma tsantsar shagwaba,

Murmushi ya saki ya kai hannunsa wajen fuskar tata da gangan dan yana so ta cike abin na karshe dake bashi dariya, wato harare,
Ai kuwa ta dala masa harare ta kawar da fuskarta cike da tsiwa da nunin ita kar ya taba mata fuska!

Sai da ya talabe kumatunsa yana kallonta sannan ya ce" kina da kyau Hafsatu

Kara kallonsa ta yi da kyau, ya ilahi, wannan mutumen kamar aljanni? Hafsatun ya kara fada, ba ko dar? Sunnan maman malan ne fa? Yo ko ita bata fadin sunnan dan kunyar malan take ta kama sunnan mamansa...haba du rashin jinta tana kunyar wannan, idan ta kai ga kama sunnan maman malan ai ta idasa rikicewa ba damar tarota.

Tana cikin wannan tunanin ta ji ya ce


Sunnana *ABDUL JABAR ABDUL BASID BINE IBRAHIM*
kamar yanda kika ji an haife ni a wannan garin, a karkashin inuwar wannan gida da kike ciki,
Na kasance dan Abdul Basid da Mamana ...ba zan kama sunnan mahaifiyata ba ki gane dai=? ?,
Mahaifina ya taso cikin dukiya, gaba da baya ya gaji arziki na iyaye da kakani, sannan ya taso cikin sangarta dan kuwa du abinda yake so afkawa yake kansa tsaye ba ruwansa, iyayensa basa kwaba basa nuna masa bacin rai sai dai su yi ta rarashi dan ya kasance shi daya suka malaka duniya basu da wani sai shi,
Haka ya yi ta yin mugayen abokanni, wanda a irin haka ya bata rayuwar makarantarsa, ya lalata karatunsa na islamiya ya dawo ya zauna a gida inda iyayen suka rungumi abinsu ba abinda ya dame su da matsa masa kan ya koma ya nemi karatu a ganninsu dan ya yi neman kudi ne ko? To ya huta abinsa kudi an tara masa wanda zai shana harma jikokin jikokinsa su shana ba ruwansa!
Ya yi rayuwa, kafin aurensa ya haihu da wata mata wace ke masu aiki, aman iyayensa suka daure masa a lokacin da ya nuna baya so a sani kar a hana masa auren budurwarsa da yake so kamar rai sai suka kori yarinyar da dan danta ta shiga duniya wace har yau ban san inda suke ba,
Bayan aurensu, da shekara uku ta haife ni, dan baki na fado abina irin fatar babana, dan jariri baki da ni, hakan ya sa banyi wani farin jini wajen mahaifina ba du kuwa da irin yanda nake kama da shi,
Babu wata shakuwa, ko soyayar gaskiya tsakanina da mahaifina, tun ina yaro na gane yana kiyaye lamarina, dan haka na ringa wayo da abubuwa a zuciyata cewar mahaifiyata ita ce duniyata, shi kuwa *dayan* ya dace na saka masa ido!

Shiru ya yi yana kallon yanda ta zaro ido da ya ce dayan,
Murmushi ya yi ya kai hannunsa wajen kumatunta ya ce" wai ke komai kika yi sai kumatun ki sun loba?

Kanta ta girgiza kafin ta ce" Abdul ci gaba,

Fuskarsa ya yatsina ya ci gaba da fadin" ina da shekara shida aka haifi kanwata, mai sunna Humaira,
Humaira na da wani irin kyau, da shiga rai, ga girma ga gashi, yar fara da ita kamar ke, dan bakinta ciwat abinda ba irin lebena ba=? ?

Shiru ya yi yana kallon kasa kafin ya ci gaba da fadin" Humaira da Abanna, suna da shakuwa ta mamaki, shakuwar dake bani tsoro, sai dai ta zama abin ado a wajen Ummihna,
Abahna ya rasa iyayensa a daidai wannan lokacin hakan ya sa kudi ya karu komai ya sakar masa ya zama wani hamshakin da kowa ke son sanni bale har ya yi abota da su,
Daidai nan ya lalubo manyan abokanansa da sukai karatu a turai kafin a kore shi, ya kirawo su ya mayar da su aminnan shawara, sannan ya basu aiki a wajaje da dama domin su su uku ne, ya raba masu mukami ya sakar masu dukiya, hakan ya sa suka shiga damawa suna cin karansu babu babaka,

Hafsat, sun kasance wasu irin mutane masu wasu irin dabi.u mugaye, dabi.unsu babu tsafta ko tsari a ciki,
Suna shaye shaye abinsu wato mayen yan gayu, suna baja kolinsu inda biyun suka auri masu jan kunne mararsa adinni dayan kuwa ya auri yar uwarsa wace itama muguwar yar hannu ce

Hafsat mahaifina ya mayar da su abokanai na kud da kud sannan ya cire masu iyaka da gidansa,
Koda yaushe sukan zo gidannan su baja kolinsu sannan su tatara su watse,
Abinda zai baki mamaki, du irin zaman da zasu yi, du irin jimawar da zasu yi da shi ba zaki ga sun tashi sun yi sallah ba,
Tun yana yi idan suna nan har ta kai ya koma biye masu ba zai yi sallah ba sai sun tafi ki ga yana ta maida salloli yana ta ramuwa,

Sun kara koya masa kara damkon zumunci tsakaninsa da Humaira,
Mamanta bata gannin komai tana sakin baki tana dariya zai dauki yar ya je bayi da ita ya yi wanka a gabanta , ya yi mata ya nadota ya maido ta,

Irin kusancin dake tsakaninsa da yar ko da uwar, ke abin ya huce gona da iri, a cikin gidan ni aminin mamana Humaira ta abanta,

Nakan yi magana idan na ga wasu mugayen wasan nakan jawo ayar da malan ya fada min na nunawa abana ba kyau fa, ya daina wasu abubuwan domin mu musulmai ne, akoy irin shakuwar da adinnin mu ya kawo mana tsakaninmu da iyayenmu tsaftataciya,
Nakan saka Ummih gaba ina son nuna mata wasu abubuwan, aman sai ta dauki hakan a matsayin ina jin kishin kanwata ne, da irin yanda Abanna ke son ta fiye da ni,
Ke karshe a daren da na ga wani mugun ganni Abanna ya fito daga saka Humaira baci, a lokacin mamanku ta jima da yin baci , da na shiga dakin na tarar da ita bakinta sai tanda take, hakan ya saka ni zuwa na kai bakina dan jin kanshin me take ci cikin baci? Dan ba zan boye maki ba ina son kanwata tamkar raina, kuma Allah ya yi ni mutun mai shegen shige shige, shegen karambanina ya jiyo kanshin sperm wanda na san sperm ne sanadiyar irin hirar da abokin abanna ke yi a gabana, harma wani lokaci na ga condom a dakin bakin mu bayan abokin Abanna sun zo tare da matar dayan abokin sun shige dakin sun dan jima sun fito, a nan ne na shinshinna harma na rike mugun warinsa a hancina,

Tsoro ya saka ni kwana a tsaye, har lokacin da Banna ya fito, nan na tarbe shi nake fada masa me ya kai wannan abin bakin joli?

A ranar na sha duka da zagi, kan dalilin da bashi da dalili,

Kwana biyu tsakani aka daga da ni garin saudiya karatun kasuwanci

Na tafi da burika a rai na, na tafi da abubuwa a rai na, na tafi da bakin cikin rayuwar gidan mu,
Ban tashi dawowa ba sai da na shekara takwas,
A lokacin da na dawo baro baro na ga komai, irin yanda Mahaifina ya mayar da kanwata matarsa ta biyu,

Shiru ya yi, idannuwansa na kallon kasa, cike da wata irin kunya, a hankali ya dago da dubansa ya ce" ni ni Abdul na ga bakar rana, na ga ranar da ba zan iya mantawa da ita ba, na kasa gane girman bakin kadarata, gani a tsaye, bakin balaraben da ya sauke alkur.ani, ya zurfafa a karatun islamiya, na fito shar da ni dan saurayi mai zamani, mai boyayiyar rayuwa ta fannin aiki, gani tsaye na kasance dan fasiki mai neman yar sa ,

Ki ji fa sharin zina, ki ga sakamakon zina,
Daga lokacin na daina gannin kima da girman wanda ya haife ni, daga ranar na dawo na zama wani tantiri a gaban ubana, nakan kirashi da kai babanmu da wata irin murya ta zan bashi umarni, nakan yi masa duban kaskanci wanda hakan ke tayar da hankali mahaifiyar da ta yi sake da ragamar tarbiyar yarta ta dawo kukan irin yanda bama shiri da ubana da kanwata, dan kuwa harta ita kafin na gane cewar an bata tarbiya ne da horen sex, sex da mahaifinta, ba.a kula da makarantarta ba bale ta gane ba kyau, bata da kawa bale wataran ta gane ba kyau, bata da wasu shekarun da zasu fahimtar da ita, gashi ba da karfi aka koya mata ba, an koya mata ne ta silar soyaya da ja a jiki da tarairaya , har ta zama wata irin harijar karfi da yaji wace na takaice maki sanadiyar mutuwarta dare biyu ya kaurace mata bisa dalilin da ban san ko na meye ba hakan ya sakata a tashin hankali, ta yi kiransa ta fada masa a waya idan bai yi mata ba zata fadawa Ummih ta saka ya yi mata,
Daga nan bamu tashi da komai ba sai gawarta, wace nake kan binciken cikin shi da aminan nasa wanda ya kashe ta,

Kin san tarayar da ba Allah a ciki, Allah na tarwatsata cikin hikima da ruwan sanyi,

Haka ce ta faru da tarayar su,
Sun juya masa da wasu gigitatun kudi, hakan ya sa ya dauke masu kafa, harma ya shiga dora du wani abinda ya malaka da sunana, wanda a lokacin na kai shekara ashirin da biyar a duniya,
Wani irin fada ne suka yi a cikin wani gidan mu dake bayan gari, wanda suka yi tone tonen asirinsu , nan suka gane suna bin matan junnansu aman shi ba.a taba bin tasa ba? Wato ummihna,

A nan daya ya ce" ka kwonta da matata, aman ni ban taba kwontawa da taka ba? To ka sani, kan na mutu sai na ga daya, ko na kwonta da matarka ta kowani hali, ko na mayar maka da dan naka da sai yanzu kake son sa kare shi ya kwonta da matarka!

Wannan lamari ya batawa mahaifina rai, ya kai dubansa inda nake zaune cikin mota, a tunaninsa bana jin abinda suke fada domin bayan nisa dake tsakanin mu, cikin mota nake a rufe ruf, bai san ya turani aikin kasuwanci ne, ni kuwa na yo nawa karatun dan kawai na tona masa asirin irin rayuwar da yake yi da kanwata wajen mahaifiyata ko zata farka ta raba, sai gashi tun ba.a je ko.ina ba an kashe ta, wanda na likun masa dan gane shi ya kashe min Humaira? Ko kuwa wani ya saka ya kashe ta?
Gannin kamar hankalina baya kansu ya saka Abana wankawa Elhaj mari ya ce" kai sakarai, *RAMATU* kamila ce, yanda na bareta a leda, ni daya na san hanyarta, mace ce dake zaune a karkashina ba wai fin karfina ta yi ba, in sha Allah sai dai ka mutu da bukatar gannin haka, ni kuwa ni zan nuna maka na fi ka iya shegantaka dan irin yanda kuka kwadaita min y'ata, kuka kai ni kuka baro, sai na gwada maka gannin idonka sauran aminnan naka ba iya matanka suka tsaya ba, har yarka suna bi wace kake kishi kamar ranka!

Shiru ya yi na dan lokaci,
Kafin ya dago ya dube ta,
Yannayin idannuwansa suka kara sakata a halin tashin hankalin wannan lamari, kafin ya ce" na yi kuka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login