Showing 15001 words to 18000 words out of 154870 words

Chapter 6 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1165

abokin aiki fiye da taka, iya girki, kai du wani abu na rayuwa ana koya masu cikin kwarewa da hikima,

A haka suka dauki wata uku, wanda zuwa lokacin su bakwai kawai suka rage,
Sai ya zama wata irin rayuwa ta ba mutunci, ba tausayawa dan uwa, uwa uba harin rai, somin kuwa a bakwai din nan ba wace ke so a cireta, gogagu ne, fitatu ne, a haka aka fara sama masu mission dan kara tabatar da hazakarsu, mission din da idan sun fita ana biye da dukan wani motsinsu,

A haka wata mata ba za.a kirata datijuwa ba, ba kuma za.a kirata da yarinya ba, ta dauki Hafsat a matsayin wace zata bata kariya na tsayin wata biyar sakamakon wata shari.a da ta dauka, domin lauya ce mai zaman kanta, kuma gagarumar yar kasuwa ce, hakama gidansu an tara, tana aikin lauyanci ne dan ya kasance passion dinta,
Matar bata da aure, aman kuma yayanta biyu wa.inda ta yi adopted,
Tana zaune da su a gida guda inda su kansu sun girma sun zama baban saurayi da budurwa sosai, sannan suna karatu ne a kasar,

A lokacin da aka gama bata labarin irin aikin fa zata yi, aka bata damar yin tambaya, ta jima tana rubuta dalilin aikin nata sannan ta dago da kanta ta ce" wace irin shari.a ce ta zata gabatar? Da wa da wa shari.ar ta hada?

Sai an fada maki sirin shari.ar ko me? Da kike son sannin sirrin shari.at bisa wani dalili?

Hannayenta ta hade waje guda , dogon wando sakake ne jikinta sai riga mai hannaye daidai gwuiwar hannu, sai hula irin ta mazan nan wace ta yar kofar bayanta ta fitar da gashinta dake daure da dan karamin ribom, ba wani abin kwaliya a fuskarta ko dis, aman wani sirririn sirin kyau ne a tatare da ita, ita kanta idan ta mike din zaka yi mamakin wannan yar abar har zara iya kare lafiar wani?
Aman kuma mu je zuwa dai,

Cikin nutsuwa ta fitar da harshenta ta lashi lebenta na kasa, sannan ta fitar da hakoranta na sama ta dantse leben nata,
Sai da ta yi wal wal da idannuwanta sannan ta ce" wannan bai shafeka ba!

Da mamaki yake dubanta, shi ne bai shafa ba? Shi zata rainawa wayo? Karamar yarinya dan tana ganninsa a bagas? Dan tana tunanin zama Bodyguard din fake kila wa kala shine har zata fara maida masa magana haka gatsal? A me ta dauki kanta? Bayan ga mutanen da suka fitar da ita suna jiranta su daga?

Muryarsa ya daga ya ce" ni zaki maidawa magana a haka tamkar wani sa.anki ko wani class dinki? Ko yau kika fara aiki baki isa ki kamo ni a dukiya ba sai kin yi aikin shekara ashirin na rayuwarki! Shi ne zaki kalleni ki ce da ni ina ruwana? Kin manta ni ke hora ki?

Datijon da ya daukota daga kutkale, wanda shi ne mai gidansu baki daya ne hankalinsa ya kawo wajen hayaniyar da SB yake yi, dan haka ya mike ya nufo wajen ba tare da ya yi ma masu jiran nasa magana ba,
Nan matar ta mike itama da dan sauri ta bi bayansa, dan kuwa ba mai hana shiga a kofar,

Cikin nutsuwa daga zaunen da take ta ce" aman ai na ga nan ba filin horo bane bare in bi du abinfa ka ce ko?

Me ke faruwa? Ya jefo tambayar a dake, sannan fuskarsa ba alamar sasauci

Gaba dayansu suka mike suka sara masa,
Nan ya shiga kora masu bayannin abinda ya faru,

Dubanta ya yi ya ce" baki dauki lesson din ladabi da biyaya bane na maida ke baya ko me?

Kanta ta girgiza tana dubansa ta ce" GN, an yi mana lessin din ladabi da biyaya, kuma an yi mana ta mahinmancin lokaci da maida amsa wajen da aka yi tambaya da kuma kiyaye yin tambayoyin da basu da ma.ana!

Ido suka zari su duka, sun gama sarewar shikenan ba za.a dauketa ba, tana zubawa wanda ya horata irin wannan fitsarar wa zai dauketa? Bayan wannan ai sai ta bata image din wajen, dan kuwa an sansu da bin na gaba da su ido rufe,

Bai so haka ba, sam bai so haka ba, irin abubuwan da ya take ya kutsa ya tarba dan gannin ya cirota daga cikin gidan yari, bai so haka lokaci daya ta tarwatsa komai ba, dan kuwa a lokacin da aka yi shari.arta yana wajen, yana zaune a wajen, shi da shi aka kama dan ta.adar, ya san waye shi, sannan a lokacin da aka bata damar ta yi magana a kotu magangannun da ta jefowa lauyan suka kara saka shi shakun abinda ake tuhumarta da shi du kuwa da irin yanda lauyan ya tafi da imanin du wanda ke wajen,
A haka ya ringa bibiyar zamanta a gidan yarin, a hankali ya ringa samun amsoshin wasi wasin da ya ringa yi kanta, sai dai baban tashin hankali maganar dake dakatar da shi wace kaf anguwar su yarinyar ba wanda ke mata shaidar arziki, wani idan ya buda baki ceqa yake wa wai Khadija? Ai sunnayenta da yawa muguwar yar daba ce....
Su sunai haka fasara daban ta irin mugun rashin jin maganarta, da mugunta wajen fadanta,
Iko kuwa zai yiwa maganar fasara daban duba da irin halin da aka kamata aka ce itace da hakan,
Suturar da aka kamata da ita, ba wani dan kwali, ba hijabma sun taimaka wajen bada gudunmuwar rashin samun tudun dafawa,
Hakan ya saka shi jin tausayin irin hidimar da mahaifinta ke yi, da irin hirarsa dadaya da ya tsinta a masalaci da aminansa kan yarinyar, ya saka masa tausayi da son yin ceto,
Shi ya saka shi ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya hana kansa baci sai da ya samu ya yi convaincre (ya ci galaba) din wanda ya yanke mata hukunci aka yarda da zata iya wannan aiki, aka bata dama dan karancin shekarunta da tarin iliminta ana hasashen zata kawowa kasa ci gaba, aka kawota sai gashi du ta shanye wahalhalun da jarabawar da yawa sai yanzu da za.a fita da ita take faman farke komai a gaban wannan lauyar da tana iya ja da kowa bata da dar, wanda hakan na iya ja, a yau a yanzu a mayar da ita gidan kason da bata taka ba, bata karya ba!
Hakan ya saka shi tafka mata tsawa ta hanyar fadin" *LA FERME SOLDAT* (CHUTUP SOLDIER)

Shiru ta yi da maganarta sannan ta kame ta sara masa,

A hankali matar ta karasa shigowa tana dubanta da kyau, sai da ta gama karantarta ta ce" menene dalilinki na son shiga hurumin shari.ar bayan ke kariya kawai aka ce ki bani?

Shiru ta yi kanta a sade, jikinta kam ya mutu dan karara ya fada mata cewar ta maida hankali, wannan aikin shi ne tikitin fitarta daga *KUTKALE*,

Hankalinsa ya maida wajen lauyan ya ce" MADAME BILKISSU, ki yi hakuri, zamu maida ita baya mu bata horo,

Kanta tsaye ta ce " ina son na ji amsar tambayata,

Kallonta ya yi da yannayin takaici ya ce" ki bada amsa!

A hankali ta dago da dubanta ta saka dara daran idannuwanta cikin na matar ta ce" na yi wannan tambayar ne dan ina son na yi bincike a tsanake kan wanda ya dace na fi saka idona a kansa a harkar aikina,
Shin wa.inda kuke shari.a da su ne? Abokin shari.arki da su ne? Ko kuwa a cikin gidan da kike rayuwa ne? Ki yi hakuri aman an koya mana cewa mu kasance komai ba jikinmu ya zama idannuwa, kwakwaluwarmu ta kasance tana aiki kowani lokaci, aman kuma mu tabatar da muna da abinda zamu fi sakawa ido,
Ba nan na nufa ba, ta yiwu wa.inda kuke shari.a da su, kaurin sunansu ya sa aka kalubalance su cewar menace din da kike samu na za.a kashe ki su ne, mai yiwuwa wani ya fake da haka ne dan ya cinma wani burinsa,
Makashi, baya bada damar a gyara ko ya yi kisa, makashi na yin kisa ne sai dai kowace wace, an kwana da sannin cewa ba zaki ja da baya kan ra.ayinki na shari.ar da ta tunkaroki ba, kokonto ne ya darsun mani na cewa, wanda kike shari.a da shi....anya kuwa mai laifi ne kamar yanda ake hasashen yana iya bi ta kasa ya tsorataki dan ki bar shari.ar da kike? Ko dai kaurin sunnansa ne ya jaza masa jafa.i?????
Ta karashe tana mai duban GN wanda ta yi maganar kaurin sunna ya jazawa mutun balaki da biyu.....

Gaba dayansu ita suke kallo,
Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da Hafsat ta ce.......
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




8??


*Free page*




Gaba dayansu ita suke kallo,
Lokaci guda Madame Bilkissu ta kara shigowa face to face da hafsat ta ce" wani diplom gare ki kafin ki shigo nan?

Zata bada amsa GN ya yi gagawar matsowa ya ce" Confidential ne Madame,

Dubansa ta yi da kyau kafin ta dubi Hafsat ,
Agogon hannunta ta kalla ta ce" ta mini, na fasa cinikin farashin daukan nata, a bani ita a kudin da aka yanke min,

Ba karamin mamaki hakan ya basu ba, sai dai ba mamaki kadai ba, harda tsoron kar aje da biyu ta yi haka? Ya kama GN, shi kuwa SB shiga kimtsata yayi yana fadin Allah ya sa kar ta je ta tafka iya yin nata ta hanyar bada labari har ta tona asirin gidannan!

Haka aka hada mata abubuwan da ya dace, sannan aka bata wani dan abu dan karami aka ce ya kasance koda yaushe cikin kunnenta, banda wanda da shi dan baya son ruwa, ta kiyaye ruwa ya shige shi,

Karba ta yi ta saka a kunnen nata, wanda zai ringa basu damar jinta da kuma yi mata magana ne, sannan zai basu damar gyara mata abin gyarawa har dai lokacin da za.a magance menace din dake tunkaro wace zata kare lafiyarta,

Haka ta je suka shiga mota, nan su duka aka rufe idannunsu suka dauki hanya,
Sai da suka jima sunna tafia sannan aka tsaya,

Cire mata abin idon, hasken ranar da ya tandi idonta da fatar jikinta ya sakata saurin rintse ido sannan ta kare da hannunta,
A hankali take jin ranar a jikin fatar jikinta har ra iya supportg dinta, yaushe rabonta da rana haka? Yaushe rabonta da su hade haduwa irin haka da rana? An jima, a gaskiya an jima, sai tace tun da aka daukota daga *KUTKALE* ,

Lauyar na kallonta ta ce da ita " mu je,

Bin bayanta ta yi suka nufi motar da ta zo da ita,

Har zata saka ky ta bude motar su shiga, Hafsat ta yi gagawar dakatar da ita,
Ky din motar ta karba tana dubanta kafin ta ce" duniya ta ci gaba fiye da tunaninki,
Ana saka yar karamar Bomb wace zata daki wajen gidan mai ta tayar da mota cikin kankannin lokacin da damar da gareka kawai ta ka saka kys din motar ka juya kys din ne,

Ki matsa,
Da mamaki take kallon yarinyar da ta tabata ta haifeta da cikinta, aman wama ya san da ta zo wajen nan imba gidan Oga da ta fito ba wanda ya sakata zuwa nan ta tsaya za.a dauketa?
Ko daga gidanta danta kawai ya farka, da ta shiga dakin Joli tana ta magana aman ina nauyin bacin nata ya yi nisa haka ta fito ta yiwa Kader salama ta tafi,

Kai, anya kuwa? Ta yaya? Ta ina? Muna dai samun bindigogi a kasa, irin wadinnan miyagun kayan aikin ai sai wajen manyan miyagun mutanen,
Sai dai ba zata hanata ba, ba zata yi mata katsalandan a sha.annin aikinta ba, zata bata dama ta warware basirarta .....

Cikin jakar bayanta ta ciro wata yar sanda karama wace ta danna wasu butons jikinta sai ga abin ya dan kara tsayi,

Zuwa ta yi ta kara shi daga kasa wajen gidan man,
Wani dan kara abin ya fara yi tsut.tsut.tsut....

Dakatawa ta yi tsai tana jin irin ihun da GN ya yi na fadin" Yes, Yes, Yes,

Tsayar da murnar gannin abinda ta samo ya yi dan har yaren sun fara taruwa wajensa,

A hankali ya ce" ki jata ku nemi motar haya ku karasa inda zaku, zan turo a cire,

Bata bada amsa ba ta je wajenta ta damki damtsen hannunta na hagu ta shiga tafia da ita,
Da yake itama mai ilimi ce, kuma ta san da ganganci hakan ba zai faru ba sai da kwakwaran huja, dan haka sai ta bata haddin kai suka shiga tafiar gagawa har ta tsayar da motar da ta yarda da ita suka shiga suka dauki hanya,

Sai da suka fara tafia ta samu kira daga wajen danta, tana dagawa ya ce" Mam kuna ina ne? Ni yinwa nake ji,

Amsa ta bashi da gatanan zuwa gida ya dan yi hakuri kadan, ina yar uwarsa ne? Ta farka?

Cikin shagwaba ya ce" ta farka gatanan sai kumburi take wai kin tafi baki tasheta ba,

Murmushi ta yi ta ce" ganinan, sai na zo,

Haka suka kashe wayar, kiran GN ya shigo wayarta ta daga,
Tana dagawa ya ce" Madame, za.a kai maki motarki cikin gari sai ku karasa da ita gidan, an cire bomb din

Cikin mamaki ta ce" da gaske an samun kuwa?

Amsata ya yi da" eh, bayan fitarki a motar aka sakata,

Doguwar ajiyar zuciya ta sauke, ta saci kallon Hafsat ta ga tsai kale kale take ta ce" to aman ya aka yi ka san gida muka nufa?

A nitse ya ce" ki yi hakuri, zamuna jin du maganarki ta waya da du wanda ya yi kiranki, haka itama mai baki tsaron zatana jin komai,

Kanta ta gyada ta kashe wayar,
Sai da ta ajiye wayar Hafsat ta ce" daga yanzu har zuwa lokacin da asirin mai bibiyarki zai tonu kar ki kuma fadawa kowa inda kike, ko abinda kike shirin yi,

Da kallo ta bita, ita kam yanzu ta kara tsorata da lamarin mai bin bayan nan nata, harda Bomb? Me ya yi zafi har haka? Idan kuwa shari.ar nan ce gwarama ya yi da aniya dan ba zan barta ba!

A hankali ta ce" y'ayana ne,

Eh na sani, Muhamad kike kiransa da boy, yaro saurayi dan shekara ashirin da takwas sai wace keda suna Mardiya kina kiranta da Joli mai shekara ashirin da tara, kin dauko su a gidan marayu na Garin dutsi, dukansu farare ne , yarinyar bata da jiki sosai, namijin ya fita jikin girma duda ta girme masu,

Dan tsagaitawa ta yi ta juyo tana duban yanda ta cika da mamakinta ta ce" kina yi masu so na hakika, bakya hada su da kowa,
Da kyau ta kara saka idannuwanta cikin nata ta ce" *harda su nake nufi*

Lauya take, babar lauyar da ko lauyoyi suna tsoron karo da ita, saboda nacinta kan gaskiyarta, tsayuwarta kan kafafuwanta,
Aman a yau sai da gabanta ya fadi yannayin yanda yarinya karama irin wannan take tsaye kan abu, sannan ta iya duban idan mutun ta nanata gaskiyarya,
Ina, ta ji wani shayin yarinyar, da son sannin wacece ita ya darsun mata,
A haka har suka zo inda tace zasu sauka,

Da suka sauka wani lamari ya so ya shagaltar da ita, ba komai bane sai ganninta a waje, gata a filin Allah, da kafafuwanta, da ranta, tana shakar numfashi,
Inama inama, inama zata iya gannin koda wulgin mahaifinta da tawagarsa ne? Inama zai bilo ta gabanta a daidai wannan lokaci?
Sai dai ta sani karfin jini da haihuwa ne zai saka ya gane wada ke gabansa, a yanzu haka idan ka ganta zaka yi tunanin irin fararan fatar nan ne wato nasaru,
Kanta ra saka hular gashi mai ruwan fara kar wace tamkar gashinta dan kuwa baba ce mai tsada kuma an yi mata baban dinki,
Idannuwanta sanye da bakin gilas,
Lebenta sanye da jan baki ja mai haske,
Tana sanye da suit bakake sai farar riga a ciki,
Hannunta rike da jakar aikinta,
Daga ciki jikin wandonta da yar karamar bindigarta a hade da bel din wandon jikinta

Sau hudu kennan GN na kama sunnanta, kafin ya daki table din gabansa da hargagi ya ce" BD O1 ki bani amsa!

Da sauri ta zabura ta amsa shi,

Nan ya ce" ki nutsu, kina cikin tafe ne a hadari, ki tabatar kin sadata da gidanta lafia,

Sai a lokacin ta farfado da kyau kafin ta juya wajen Madame ta je da sauri ta shiga motar ta yi mata ky,

Bismillah ta yi a ranta kafin ta dubi JPS ta fara neman gidan matar da kanta sannan tukinta ne na fari a cikin gari dan haka ta tafi a hankali har suka karaso...


Tana tsaye wasu jibga jibgan y'aya suka fito a sangarce dan tarbanta,

Dakatar da su Hafsat ta yi ta hanyar su gaisa nesa da nesa

Da mamaki gaba daya suke kallonta,
Uwar ta ce" ah no, ba zai yiwu ba, y'ayana ne fa, kice ba zan rungume su a jikina ba?

Maganar da aki mata ne ya sakata dan ja baya tana kare masu kallo irin yanda du suka rufeta da tambayoyin me hakan ke nufi? Wacece wannan? Me ya kawota gidansu,

Reaction dinsu ba wata bace sai nuna tashin hankalinsu na ana bibiyar rayuwar mahaifiyarsu, daga nan suka rankaya baki daya ciki,

Sosai ta cancanzawa yannayin dakin Madame Bilkiss zama, kwata kwata ta canzawa du

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login