Showing 135001 words to 138000 words out of 154870 words

Chapter 46 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1139

ya tsurawa fuskarta ido yana kallonta shima,
Sai kuma ya ce" ba ki yi karya ba da kika ce zan so ki dan albarkatun jikin ki, kin san me....nutsatsu ne, wuta suke badawa, suna lasa mon zuma a baki...dan Allah ni da lafiyaye ne dan me zan munafurci kaina? Hafsat, kina da ni.ima, kina bada kala....bakya shaye shayen komai ko cushe cushe...aman kuma tun da na bi hanyar kulum shinfide take da ni.ima=??, ina son jikin ki sosai kauriyata

Yana fada ne yatsarsa mai bima baba na bin dogon hannunta a hankali yana shafawa,

Sai kuma ya ce" a haka kika bi layi, dan kawai kina fushi da ni ko??

Hafsat ta dan buda idannuwanta ta dago da duban nata kadan, a hankali ta ce" ba fushi nake da kai ba, tsoron zama nake da kai....ba zaka iya rayuwa irin na mutane bane Abdul? Muna zaune a gidanka mata biyu, ba abinda ya dame ka da muna zumunci ko bama yi, hasalima mu kanmu bamu san yau kwanan wancen ko na wannan bane da wace ka yi ra.ayi kake gayata! Kana zaune da mu muna tafiar da rayuwa tamkar rainon yahudu ko dan ka tsara ba zaka haihu ba bale ka gyara gidanka ko dan tarbiyar yayanka??


A hankali ya kai bakinsa kan nata,
Rufe bakin nata ya yi ta hanyar shiga kissing dinta a hankali a hankali

Sai da ya yi iya yi sannan ya dan saki bakin nata, muryarsa can kasa ya ce" ba zan kuma ba nace, ina son haihuwar yanzu, a min hakuri na daina, zan ta yi maku ciki kuna haife min du shekara...walahi ko hutu ba zan baku ba, Hafsat ina son yaya sosai fa, tsananin jin son yayan da ban haifa ba tukunnan ya saka ni tsoron kar a cutar min da su

Tunaninka sai ta yaya Allah zai kama ka idan har baka tuba ba?
Mu ba matayenka bane? Ohk kana tunanin ka kilace mu ka rufe mu a gida baka barinmu fita , baka barin maza zuwa inda muke ka tsiratar da mu kennan ko? Idan Allahn ya jarabeka da mu fa??

Idannuwansa ya kura mata ido, ji yake tamkar ya make bakinta kai lahaula wala kuwata illah billah
Falyakul khairan auliyasmut! Ya fada muryarsa na kausasa....

Mikewa ya yi a hankali ya kamata ya tayar da ita tsaye,
Hijab din auntynta ya saka mata ya kama hannunta

Du irin yanda ta so ya saketa a gaban aunty kiyawa ya yi sai auntyn ce ke kakauda fuskarta irin tana jin kunya , haka sukai mata salama suka fice ita dai sai fa suka fita sannan ta sauke ajiyar zuciya a ranta tana girmama eh lale tauri da tauri ne

Suna fita Abduk ya tsayar da adaidaita sahu,
Dan adaidaitan na tsayawa ya karewa motar adaidaitan kallo, kallon Hafsat ya yi yana murmushi ya ce" ita wannan ai kungurguma ce

Hafsat dake wani shasha masa kamshi bata san lokacin da ta saki murmushi ba, sai kuma ta hade fuskar tana kallon dan adaidaitan dake jiran su shiga ya kaisu inda zai kai su

Abdul ya dube shi ya ce""""
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 2??




Abdul ya dube shi ya ce" malan zaka dan saki wannan abin dan ya rufe mana iskar gari??

Mai adaidaitan ya juyo ya kali Abdul da kyau, bai ce da shi komai ba ya saki labulen adaidaitan sannan suka shiga suka zauna

Ko a cikin adaidaitan yana ja ne hannun Abdul na rike da na Hafsat, suna tafe ne a hankali domin ya hana mai adaidaitan yin gudu da su

A hankali yake murza yan yatsun nata, yana yi yana sauke ajiyar zuciya,
Bai taba tunanin idan wai mace tace zata barshi na dukan rayuwa zai ji ciwon kai bama bale wai har ya firgice, sai gashi wuni daya tak da ta dan nuna tana fushi harma ta yi gaba abinta du ya fice a hayacinsa

Hafsat kuwa dake jin irin yanda yake murza mata yan yatsunta bata iya hana shi ba, hasalima shiru ta yi tana sauraronsa, sai kuma a hankali ta ringa jin hankalinta na tashi, ba komai ke tada mata hankalin ba sai irin yanda Abdul ya biyota ya rungumeta a jikinsa, ta ji mugun dadin dadadan kalamansa, sai dai kaf cikin bayaninsa babu inda ke nuni da ya kamu da soyayarta, ita tama fi fahimtar yana girmama wajen hutunsa ne

Daidai adaidaita sahun ya tsaya kofar tamkamemen gidansu Abdul ya fito daga ciki sannan ya fitar da Hafsat a hankali

Masu tsaron kofar da suka zaburo da korar mai adaidaita daga kofar gidan ogansu ne suka yi azamar zuwa dan salamar mai adaidaitan a lokacin da suka fahimci ai ogan nasu ne a adaidaita

Shi dai murtuke fuska ya yi ya kama jan hannun Hafsat suka shige cikin gidan

Tafia mai tsayin gaske suka yi dan sosai akoy tsayi tsakanin kofar shigowa da kuma bangaren Hafsat din, sannan a tsakannin tafiar sun hadu da ma.aikaran gidan jefi jefi, su kuwa gannin Abdul din ne da kansa suke tsayawa su mika gaisuwarsu cike da girmamawa, sannan su bi su da kallo har sai sun fice a gabansu

Suna shiga bangaren Hafsat Abdul ya saki hannunta ya karasa tsakiyar fallon ya zauna ya dafe kansa da hannayensa bibiyu

Tsayuwa Hafsat ta yi daga dan nesa da shi tana kallonsa, a ranta kuwa tambayar kanta take meye kuma??

A hankali ya dago da dubansa ya sauke saman fuskarta
, idannuwansa ya lumshe sakamakon jin yanda zuciyarsa ta buga,
Hijab na yiwa Hafsat kyau fiye da tunanin mai karatu.

Hannunsa na dama ya dago ya mika mata, yana nufin ta zo gareshi

Sai da ra kalli hannun da kyau, sannan ta shiga takawa a hankali har ta karasa kusa da shi din

A hankali ya zaunar da ita sosai daf da shi, sannan ya juya yana kallonta

Bakinta ta tabe tana dan yamutsa fuskarta jin har yanzu ba wai daina ciwon cikin nata ya yi ba, yana yi yana lafawa ne

A hankali Abdul ya ce" na shiga tashin hankali Hafsat, da kika ce kin tsane ni,
Shiru ya yi na dan lokaci sannan ya kamo hannayenta yana murzawa a hankali yana massaging yana kallonta
Hannun ta kalla, sannan ta kali fuskarsa da manyan idannuwansa suka kara girma suka yi mata wani irin nauyi a cikin nata idannuwan,

A hankali ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa ya sanyayar da muryarsa ya ce" *tell me, da gaske kin tsane ni?*

Zuciyarta ce ta ji ta buga mata lokaci daya, a haka kuma ta ji jikinta ya fara daukan dumi harma cikin tafukan hannayenta ta fara jin sunna fitar da zufa mai zafi

Cire idannuwanta ta yi daga cikin nasa, a hankali take son ya sake mata hannu dan gaba daya ji ta ringa yi wani irin abu na shiga jikinta daga jikinsa

Abdul ya ki ya saki hannun, saima kara kusanta kansa da ita da ya yi,
Muryarsa ta nuna mugun raunin da yake ciki ya ce" dan Allah, idan na kasance mai laifi ki yi min nasiha ba ko guje ni ba Hafsat, baki san me na ji ba, baki san irin halin da na tainci kaina a ciki ba.....
Hannun nata ya kai daidai kahon zuciyarsa ya kara tausasa muryarsa
A hankali ya ce" kin ji , har yanzu dokawa take...

Gabanta ne ya kara faduwa, wasu irin kwallah suka cika mata ido lokaci daya

Hannun nasa ta kaiwa kallo da hannunta, tabas zuciyarsa ta canza salon bugu, tana bugawa da mugun sauri ba kamar da ba
A hankali ta lumshe idannuwanta hawayen nan suka samu damar zubowa,
Tana kallon fuskarsa irin yanda du ya matse mata waje sai kawai ta ringa jin ta kasa kwakwaran lumfashi idan ba da nasa na taimaka mata ba

A hankali ta buda bakinta tamkar ba zata yi magana ba, sai kuma ta ce" bugun zuciyar yayi min kama da idan kana da bukatar mace Abdallah
Idannuwanta ta lumshe tana kokarin dane mugun kukan dake tukota wanda bata san ko na meye ba ta yi ta kuma ce" wacece ni? Wa na fi ko halitata aka daukaka fiye da ta sauran? Abdul, dan Allah ka taimaka ka fada min dala dalan abinda ya faru aurena ya juya a wannan ranar

Kallonta kawai yake, hankalinsa gaba daya ya dugunzuma ya tashi, kennan tana nufin bugawar zuciyarsa na nufin dan yana da bukatar mace ne ko? Sai kace wani bunsuru?
Sannan bata bar maganar BS ba kennan?

Kusancinsu da ya matse sosai ya dan sasauta ta hanyar dan ja baya kadan

Hannunta ya sasautama rikon da ya yi mata, a hankali ya ce" Malan ya tura ni binciko masa waye shi kamar yanda adini ya tanada
Na binciko, sai dai na boye masa hasalin waye shi din, ke din kanki ba zan iya fada maki ba dan ban kasance mai tona asirin bawa ba, sannan kowa na da tabo a rayuwarsa sai dai na wani ya girmi na wani

Dan shiru ya yi, sannan ya ce" maganar auren ki, eh ya daina ne dan an bashi zabi, kuma ya zaba
Wani shirun ya yi kafin ya fuskanceta da kyau ya ce" sai malan ya daura da ni

Kallonsa kawai take,
Bata iya cewa komai ba,
Abdul ya karsa sakin hannayen nata ya kara sasauta muryarsa ya ce" na ga mata da yawa, na gan su a matsayin da suka diro duniya..... *sai dai na shigi biyu kacal*
Eh ina da jarabar mace, sai dai ina da kyankyami! Idan min ga na raba shinfida da mace Hafsat ki tabata dan na fita hakinta na igiyar aurena dake kanta ne ko dan ina rayi... *wato ina son abinda ke cikin bujenta!*

Yana gama fada ya mike ya juya ya shige can cikin dakinta ya barta nan zaune, cike da dana sannin tsokano zancen nan haka gashi ya yi tafiarsa bayan ya fada mata magana mai tsayea a rai da saka tunanin dole!
Ita yake zuwarma dan fita hakinta na aure? Kennan ita ke gannin ita har mace ce ko? Yana zuwa ne dan ya fita hakinta na aure

Gaba daya ji ta yi tamkar an lakada mata duka, sosai take ji zuciyarta na kuna na wani irin zafi! Dan me zai wulakanta ta ta hanyar kwatanta mata karara yana zuwar mata ne dan ya fita hakinta? Shi mai wata matar ko?
Ciwon abin ya sakata dage kafafuwanta a hankali ta dora saman doguwar kujerar sannan ta jinginar da kanta ta limshe idannuwanta tana jin yanda ranta ke kara daukaka abin
Adu.a ta shiga yi tana kara lumshe idannuwan nata tana neman sauki wajen Allah.

Ba shi ya fito ba sai bayan salar magarib, daga nesa ya tsaya yana kallonta,
Sam baya gajiya da kallonta dan birge shi take a koda yaushe, sannan jikinta sai kara daukan haske da ma.ana yake

A hankali ya taka ya buda dakin ya fice, buda dakin ya shaida mata da an fita

Kofar ta tsurawa ido dan ko ya wuni a daki ba zata rasa kanshinsa ba

A hankali ta mike ta nufi dakinta tana jin kanta tamkar wata marainiya, sam bata da sukuni bata da wani kwonciyar hankali sosai magangannunsa ke tsaye a ranta, sannan sharetan da yayima haka, fushi yake da ita ne? Ko menene?

Wanka ta fara yi na kirki domin ta wuni ba wankan tun safe rabonta da ruwa,

Tana fitowa ta shiga tsane gashin kanta , sannan ta saka turaran wuta ta rufa ya kama jikinta sosai

Pad ta saka domin kadan kadan take zubar da jinni, wanda ke murda mata cikinta , ba karamin daurewa ne take yi ba

Tana gamawa ta ciro doguwar rigarta na atamfa cikin kayanta ta saka , atamfar ja ce mai adon manyan shuka farare da baki baki

Dan kwali ta daura saman kayan sannan ta balo ubiprophene ta hadiya dan ciwon marar

A hankali ta taka ta fita ta shiga kicin dinta, madara ta kada da siga ta sha dan har jiri take ji na yinwar da ta hana kanta ci

Tana nan zaune har ta ji kiran wayarta na ta zo cin abinci, dama shi take jira ko zata samu ta kwonta

A hankali ta mike ta saka hijab dinta har kasa ta shiga ta kara feshe jikinta da turare sannan ta fito ta nufi bangarensa

A hankali ta tura ta shiga, dariyar Na.ima ta fara jiyowa kasa kasa sannan ta ji muryarta tana magana cike da nishadi

Ita dai bata yi kasa da gwuiwa ba ta yi salama sannan ta nufe su cikin nutsuwa

Tana tafe ne tana jin zuciyarta zata tsinke,
Kallon da ya saba taryota da shi bai wani kulata ba, ko daya bai kaleta ba kamar yanda ya saba tsura mata lumsasun shanyayun idannuwansa masu tafe da wani irin baiwa wa.inda ke sakata jin yanai mata susa a jiki tsabar yanda suke da tasiri a tare da ita ,
Tana kallonsa ko kiftawa babu har ta karasa wajen table din ta zauna

Gaishe shi ta yi a hankali, ya amsa mata kamar wata bakuwarsa sannan ya ci gaba da kokarin zuba abincinsa

Dago da dubanta ta yi ta kale shi, sai dai baima kaleta ba bale har ya gane yarenta

A haka Na.ima da Abdul ke cin abincinsu cikin nutsuwa, inda Hafsat ke dan jujuya spoon din tana jin zuciyarta na tashi

Basu jima suna yi ba suka gama, nan ya mike ya yi masu duba daya ya ce" ina son magana da ku

Su duka da kallo suka bi shi har ya nufi fallonsa, hakan ya sa Na.ima mikewa ta bi bayansa

Hafsatma mikewar ta yi jiki sanyaye ta bi su, suna zuwa suka zazauna saman kujera sannan kowace ta bada hankalinta kan mijinta mai aji!

Abdul dake daura agogon hannunsa kampanin Gucci na farin azurfa ya yi gyaran murya kafin ya fara magana

Magana ce yake cikin daurewa da cikakiken iko wanda gaba dayansu lokaci daya suka ji darr dar dinsa

Hafsat kallon lebensa da fuskarsa take tamkar bakonta, bata taba ganninsa a yannayi na serius irin yau ba, hakan ya saka ta hangi girman darajarsa harma take tunanin irin su Abdul ne sanninsuma riba ne

A hankali ta saci kallon Na.ima, gani ta yi ta bada hankalinta gaba daya da nutsuwarta tana sauraronsa, sai a lokacin ta ga eh tabas idanma Na.ima ta yi kishin mijinta ba laifi bane dan ya isa ya kai a yin,

Ajiyar zuciya ta sauke tana jin tsare tsaren da ya canzawa gidansa,
Ya raba masu kwana, sannan ya tsara tsarin zumunci, ya yi kwakwaran kashedi a gaba, haka kuma ya yi jan ido a fada, ya masu nuni da zaman aure suka zo ba wata wada zata fi yar uwarta a wajensa , idan kwanan mace ne ya soke mai zuwa gyra masa bangarensa da kula da cinsa da shan sa idan ba ita ba har ta fita aikinta, kys din bangarensa ya mikawa Na.ima kafin ya yi nuni da zata fara aiki a ranar,
Daga karshe ya rufe maganar cikin sansanyar murya sannan ya mike ya fara bara masu wajen ya fita

Wani tsadaden murmushi Na.ima ta saki sannan ta mike a hankali cikin shigar nan tata mai razana zuciya ta shige uwar dakan Abdul....danma ba abubuwan jujuyawa da sai ta jujuyasu son ranta, ita yau bata san me ke damun Abdul ba, ga0ba dayansa ya bata lokacinsa , wai Abdul ne harda bata labarin abin dariyarsu a saudiya? Ita dai tana son mijinta kuma batun kishiya kishiya ce idan har kishin take so su yi!


A hankali Hafsat dake ji zuciyarta na tsintsinkewa na irin halin ko in kulan da Abdul ya nuna mata ta mike ta fita ta nufi bangarenta tana ji tamkar zata kife dan wahala

Da kallo ya bi ta daga inda yake tsaye har ta shige bangarenta,
Ajiyar zuciya ya sauke yana mai jin radadin irin yanda sam bata damu da damuwarsa ba, yana cikin yannayi na rokon kulawarta da kasanceewa tare da ita ta yi masa tambaya kan tsohon saurayinta, karshema ta yi masa nuni da idan dai mace ne kowace ya bi, bugun zuciyarsa da ya canza wanda har yanzu idan ya tina maganarta cewa ta tsane shi sai ya ji zuciyarsa ta buga , ta dora hakan kan jarabarsa ce ta motso......
Tabas yana girmama lamarinta a rayuwarsa, ta kasance mai dukan tunaninsa , tana dukan lamuransa , tana hana masa sukuni, tana saka shi jin muradinta a saman kirjinsa, tana motsa masa jinin jikinsa dama zuciyarsa har ya ji muguwar zufa ta wanke masa jikinsa.....sai dai hakan ba zai hana ya hukuntata ba, !


Juyawa ya yi ya shiga motarsa ya tayar ya fice a gidan,
Tuki yake na iskanci a saman titin har ya iso kofar gidansa.... ina, ba zai iya rintsawa ba idan bai jijiga shi ya ci ubansa ba! Yau sai ya gane me ya fi shi ne? Yau sai ya bambance girman iskancinsa bilahi!
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login