Showing 78001 words to 81000 words out of 154870 words

Chapter 27 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1159

damko ba, aa damtsen hannun ne

Basarwa ta yi ta shige gaba da niyar fitan itama,
Abinda kunnensa ya jiyo masa na muryar Hasana tana fadin" sire kar ka fito, domin an harbe Matar da ta fita yanzu ne, yanzu haka gatanan su BS sun shigo da ita ana duba ta

Da sauri Hafsat ta juyo da dubanta wajensa, aman sam bata fahimci halin da yake ciki ba dan kuwa fuskarsa bata nuna mata ba, sai ma juyawa da ya yi da wayar dake hannunsa ya nemi waje ya zauna ya shiga dadana wayar

Tagar dakin ta duba da kyau ta ga a rufenta take dan haka ta juya da sauri ta fita itama ta nufi wajen su BS dake ta haya hayar aikinsu suna bata taimakon gagawa kar ta tafi dan samun labarin abinda ya faru, dan kuwa sojojin nan ne suka kawota da gudu suna fadin tana tuki bata idasa fita a anguwar ba aka harbeta, su kam sun hadu da wani irin aiki mai gardama, sun rasa gane abinda ke faruwa,
Mubarack, abokin aikin su BS ne ya dago daga kokarin tsayar da jinnin ya ce" oga, wannan dole a yi gagawar zuwa asibiti, tana zubar da jinni kar ta kai inda zata kasa daukan hakan

BS ya gyada kai ya juya wajen Hasana ya ce" zaki shiga da ita gari ta hanyar baya, ki samu wanda zai duba lafiyarta, ki kula fa

Hasana ta yi gagawar amsa masa, nan suka kamata suka fice da ita da niyar kai ta asibiti dan kuwa sam bai ji ransa ya amsa da barinta a gidan nan ba

Hafsat biye take da bayan BS tana sauraron irin yanda yake kara shirya shirin kare Abdul, du irin tsare tsaren tana sauraronsa da kyau tana kuma shanyewa a cikin kwakwaluwarta,

Suna haka har suka shige tsakiyar dakin inda ya juyo yana gyara bindigar dake hannunsa ya kalleta zai ci gaba da maganar ya yi shiru yana kallon yannayinta

Muryarsa ya sasauta ya ce" me ke damun ki?

Saurin girgiza kai Hafsat ta yi, tana nufin ba komai ba

BS ya yi murmushi yana kallonta ya ce" kina tsoron wani abu ya same shi ne?

Da sauri ta kara kallon sa tana kikifta idannuwanta sak yannayin wace ke firgice na tare da ita, sai dai bata bashi amsa ba

Kansa ya gyada ya kara rage muryarsa ya ce" kar ki manta waye shi, ko daukan mu da ya yi ba dan zamu iya yi masa wani abu ba sai dan ya rufe ko shi waye wa duniya

Kara zuba masa ido ta yi tamkar tana son karantar wani abu a fuskarsa,
Tana son BS ya shiga lamarin binciken nan na cikin gida, ita ta san waye BS, mutun ne mai shegen naci da shiga waje mai hatsari, da ace yana cikin wannan lamarin ta tabata komai na iya faruwa, ta tabata kai da tuni ya kara mata haske a wajen da take gannin duhu,
Sai dai ina, ba zai yiwu ta fito fili ta fada masa ainahin sirrin Abdul din ba, domin kuwa ko ba komai sirri ne

Kansa ya girgiza ya juya ya nufi dakin da bakuwa mai sunna Furaira ta zo, ita kuwa ta koma wajen dakin Abdul

Dakin Abdul din ta tura ta shiga bayan ta bubuga an bata damar shigowar

Zaunen dai inda ta fita ta bar shi, nan ta hango shi,
A hankali ta karasa tana kallonsa ta tsaya dan kusa da shi sannan ta ce" BS ya ce na ringa dafa maka abinci daga yanzu, idan da hali ka daina fitowa har mu ga tafiar Bakuwar nan

Sai da ta gama Abdul ya gyada kansa , a hankali ya ce" ba zan iya ba

Hafsat ta gyada kan itama ta ce" dama na san ba zaka yarda ba

Abdul ya ce" Hafsat, ni mai taurin kai ko? Ni mai gardama ko Hafsat? Kin ga dai ina cikin damuwar an harban min abar kaunana, kar ki karan wata damuwar!

Bakinta ta yatsina ta daga kafadunta tana kallinsa sannan ta juya ta fice a dakin

Murmushi ya saki bayan fitarta yana girgiza kansa,
Wayar dake hannunsa ya danna kira

Ana dagawa cikin mutunci da girmamawa suka gaisa da shehin malamin sannan ya shiga kora masa bayannin wani rudun da ya tashi da shi a yau

Cikin nutsuwa Malan Muhammad mahaifin Hafsat da Abdul ya saka aka samo masa numbersa na whatsupp suke magana har suka yi mugun sabo yake karbar adu.o.i na neman tsari , a hankali har ya aminta ya yi masa voice cewar yana cikin duhu mai tsanani, yana son adu.ar da zai lazumta ko Allah ya warware masa haske a duhu
Shi ne ya ringa taimaka masa da adu.o.i da shawarwari, a wadinnan lokutan har ya bashi kadan daga cikin labarin rayuwarsa ya boye masa wasu, ya dai shaida masa ana harin rayuwarsa ne,
Cikin muryar datako ya ce" Abdul Jabar kana ji? Ba wanda ya isa ya saka , ko ya hana sai Allah, tabas Allahn da ya ankarar da kai cewa ana harin rayuwarka, shi ke tsare ka, ina so ka farga cewa da ya yi niyar baiwa mai bin sahunka sa.a a kanka da tuni mai faruwa da kai ta faru,
Mai runfar na sama yana kallo Abdul,
Kuma wannan magana da ka ce an fada maka cewa makashinka na tare da kai, kar ya baka damar zargin kowa, wannan ma kuskure ne, ka dai ci gaba da adu.ar in sha Allahu Allah zai kawar da mai son kawar da kai da kansa

Kansa yake gyadawa har ya gama sauraron muryar datijon mai magana cikin nutsuwa, wanda ke amsa kiransa bayan bai taba haduwa da shi ba, bai san ko shi waye ba, bai san ko mai niyar cutar da shi bane ko na kirki ne? Wato su dai malamanmu Allah ya saka masu da alkhairi, suna aikin Allah tare da dogaro da shi da zuciya daya da imanin du abinda ya same su daga shi ne,
Ajiye wayar ya yi yana lankwasa yatsutsansa,

Ya yi mata magana kan kar ta saka kanta a wannan lamari, lale zai ji dadi idan ta bi maganarsa, shi ya sa bai mata maganar da wata hayaniya ba , ya bita a laluma ya kwatanta mata wannan sako daga cikin ransa yake

Wani digon tsaki ya ja ya mike ya shiga cire kayansa dan kara shiga ya yi wanka ya je bangaren bakuwarsa mai rawar kai, wace ya dasawa hajia=? ?, a fili ya ce" Hafsat, bakya jin magana! Mai taurin kai kawai! Uwar gardama,=?D?, mai kyauna=? ?


Hafsat na fita a dakin Abdul zuwa ta yi ta dauki abubuwan aikinta ta fito cikin tafiar basarwa irin tana cikin aikinta ne na kare lafiar Abdul ta nufi garden ,

Tana zuwa wajen abin shilawar wajen ta je cikin sando ta makala abin hannunta sannan ta bar wajen ta kuma dauki hanyar dakin Furaira

Tana zuwa sojan dake kofar tsaye ya hanata shiga, ya ce oga ya hana kowa shiga

Bakinta ta yatsina ta juya tana kallon yannayin wajen da fatan abinda ta wurga a lokacin da ta daga hannunta da niyar shafa gashinta ya makalu a labulen dakin,

Bangaren su Abdul ta koma cikin nutsuwa take takunta ta nufi dakin Ni.ima

Tana zuwa ta shige dan a nan ba wanda zai hanata shiga

Tana shiga ta tarar da Ni.ima na zaune gaban madubin dakinta ta dira kanta saman table din madubin hannunta rike da tamfatsetsiyar wayarta

Bata ji shigowar mutun ba hakan ya sa bata motsa ba, wannan ya baiwa Hafsat damar aiwatar da du abinda ya kaita dakin sannan ta juya ta fice ba tare da ta san ta shigo dakinta bama ta lula duniyar tunanin damuwar dake damunta

Haka Hafsat ta kara sadadawa ta shige dakin Muhammad domin sojojin dake gadin kofarsa sunna tsakar gida sai zagaye suke tun da aka yi harbin nan,

Sadadawa ta yi ta shige dakin, abinda ya kaita ta aiwayar ta zo fita kennan ya fito daga bayi daidai kuma Abdul ya shigo dakin

Da mamaki Abdul ya kaleta, inda Muhammad ya ce" aa, yau harda yar rakiyar taka kake tafe har cikin dakin nawa?

Abdul ya tsurawa hafsat ido, ita kuwa ta sada kanta kasa ta raba shi ta fice a dakin hakan ya baiwa Abdul damar shigewa ciki yana mai jin ransa na suya,
Me ta zo yi dakin nan? Me ya kawota? Ba dai abinda ya hanata ne take kokarin daura aniyar yi ba?

Haka ya je suka tatauna da amininsa, dan uwansa kafin ya mike ya zarce dakin Furaira

Gaba daya hirar da ya yi da matar bai fahimci komai ba sai tsabar bariki dake dawainiya da ita,
Karara ya fahimci cewa abin duniya ya rufe mata ido, kuma shi ke janye da ragamar rayuwarta
Dan haka ya biyewa sallon kidanta suka doka gangar iya iyawarta ya bari bangarenta bayan ya nuna mata kudi akoysu, wanfa hakan ya sakata kara share waje ta baza tabarmarta



Kwonci tashi, har an kara sati biyu cikin wannan hali,
A cikin gidan Abdul, an ci gaba da fuskantar hatsaririka kala kala,
Du wani wanda ke gidan ya koyi sannin mahinmancin lumfashinsa, irin hare haren da aka ringa kawowa ya saka kowa ya gane cewa rai ba karamin abu mai daraja bane da Allah ya arawa bawa wanda yake iya karbarsa a kowani lokaci, hakan ya saka musulman ciki suka kara mayar da kansa wa Allah, christocinma suka kara rike adinnin su,

Har yanzu Furaira na gidan, wanda take son fitarsa ido rufe aman cikin ikon allah Allah hakan ya gagara ta rasa dalilin da ya sa du irin iya barikinta da wayonta ta kasa samo kalaman da zasu saka shi barinta tafiarta dan kuwa tana son fita a gidan

Hafsat na nan har ta fada ina nufin ta rame tsabar irin yanda ta sakawa kanta damuwar wani a ranta, dan kuwa ta zama tamkar fatalwa wajen iya leken asiri da daukan rahiranni tana hadawa a cikin kundin bincikenta dan samun amsa gamsashiya wa hasashen da take wanda ke nukurkusarta ita kanta yana bata tsoro, dan kuwa amsar da take hangowa bata tunanin idan ta fito fili za.a wanye lafia

A tsakiyar daren talata, a wannan rana ce Hafsat ta saurari wayar da ta firgitata,
A wannan rana ne ta fito da niyar zuwa dakin Abdul a talatainin dare,
A wannan rana ne aka wayi gari ba Hafsat ba labarinta,

A lokacin da BS ya shiga dakinta gannin har karfe tara da rabi ta fice bata fito ba bayan hakan ba sabonta bane yana shiga ya tarar ba computenta, ba wayarta, ba du wani abin aikinta an kwashe babu ita babu alamunta,
Hakan ya saka kansa sarawa ya fito da gudu yana harhada du wani ma.aikacinsa suka rarabu suka shiga nemanta ilahirin gidan

A haka ya je dakin Abdul da ya gama ganawa da Ni.ima ya shiga a firgice yana mai tambayar a yau ko ya ga Hafsat?

Abdul dake zaune saman salaua ya dago a hankali tare da rintse ido dan irin yanda gabansa ya yanke ta fadi ya kali BS ba tare da ya yi masa tambaya ba, yana jiran karin bayani

BS ya ce" mun nemeta bata nan, wannan batan ba irin wanda ta saba ficewa bane domin ba kayanta a dakinta

Wata irin mikewa Abdul ya yi tsaye, lokaci guda kuma ya dafe kujerar dake kusa da shi domin wani irin jiri ne ya ji ya zo ya rufe idannuwansa,


Da wani irin ihu ya ce" ina take? Ina ta shiga?

A hankali kuma ya shiga rage muryarsa yana magana tamkar wanda ya zauce cewa" sai da na hana ki, sai da na hana ki, kin gano ne? Kin gono ko waye? Kin gano an ganki kafin ki fada ne? Ina kike? Kina ina? Ki zo gare ni?????








...........saura kirisssssss
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 5??




Ki zzo gare ni Hafsat,
Ya karashe yana mai dafe kansa da dukannin hannayensa kafin yake mikewa kuma da wani irin sauri

Fita ya yi ya nufi dakin da computersa ke girke,
Yana shiga ya kunna ya kamo ya shiga bi yana kallo daya bayan daya

Ba abinda ya gani sai duhu ridim , wato wanda ya dauki Hafsat ko waye ya san inda camerorin suke dan kuwa baki daya sai da aka rufe su aka hana gannin abinda zai wakana

Gaba daya Abdul ya fita a hayacinsa, du wani abinda zai tunkara dan gannin ya sameta, ya ganta ya duba , ya bincika aman babu, babu ita babu alamunta

A hankali ya ringa jin wani irin zazabi na son rufe shi, hakan ya saka shi neman magani ya hadiya kafin ya juyo inda ya tara gaba daya mutanen dake cikin gidan, wato du wanda ya kwana ya tashi a gidan nan in dai mutun ne dan adam yana halarce a tankamemen falon Abdul du suna zazaune kamar yanda ya umarta shi kuwa yana tsaye dafe da kansa, ciki kuwa harda matarsa ta sunna da kuma Furaira

Sai da ya gama saisaita kansa sannan ya shiga bin kowa da kallo,

Sai fa ya gama kare masu kallo kafin ya hadr hannayensa cikin wata murya mai nuna tsantsar tashin hankali ya ce" koma wanene a wannan waje, na roke shi da ya saketa ya kama ni,

Na yarda, ya gane menene lagona ya kuma dakan harbi a lokacin da nake barci,
Ina mai rokarsa, idan har da dan sauran imani da kuma sannin zai yi kwonciyar kabari ya sakar min ita ta yi tafiarta nesa da ni, nesa da hargitsin rayuwata,

Ya karashe yana mai kara bin su da kallo,
Gaba daya, yana iya cewa gaba daya sun nuna fuskar basu san abinda yake nufi ba, kai ko wa yake nufi gaba dayama, dan haka ya kara gyara tsayuwa ya ce" daya daga cikin ma.aikatan gidan nan aka dauke, wace ke gadina mai sunna Hafsat, mun wayi gari babu ita ba labarinta, ba kayanta sama ko kasa,
Sasauta muryarsa ya yi irin na wanda ke azabtuwa da lamarin ya dube su duba irin na neman agaji ya ce" shin , da wanda ya ga Hafsat?

Kallon kallo suke yiwa junna, aka dauke wata? Mai bashi tsaro? Aa, kuma? Hankali nan ya fara tashi, da yawa suka shiga mikewa ana mayar da su zaune, inda Ni.ima ta kure shi da kallo, Furaira ta dafe kunci cike da mamakin wannan gida, Muhammad kuwa ya karasa kusa da amininsa ya shiga tausar sa yana bashi hakuri

Abdul ya gyada kansa sannan ya ce" ban so mu shiga fannin neman juna ido rufe ba, ban so mu shiga fannin da zan fita farautar mai farautana ba, walahil azim idan ban kashe shi da hannuna ba sai dai karfin ikon Allah, *tunda ya yi gigin taba min ita* nima sai na taba shi!

Abdul na gama fadar haka ya juya ya shige dogon lungun daka iya kai shi dakinsa yana mai jin wata irin juwa na neman dibansa ta kayar

Da sauri Muhammad cike da tausayin aminin nasa ya dafa kafadarsa hakan ya saka Abdul rage saurin tafiar da yake

Muhammad ya ce" Abdul, menene kuma? Me ke damunka haka da yarinyar kuma? Eh tabas dole hankalinka zai tashi da wannan sabon lamarin, to aman sai na ga abin na taba ka sosai, ko da wani abu tsakaninka da ita ne?

Abdul ya tako da sauri inda Muhammad ke tsaye ya kama hannunsa da karfi kafin Muhammad ya ankara ya dora hannun daidai wajen zuciyarsa,
Sai da ya furzar da huci ya ce" ta bani tsaro fiye da tsaron kanta ne? Dalilin ta dauki harbina ne? Ta iya zama da ni ne? Ko dan na ga tausayina na zahirin gaskiya a fuskarta ne? Tun da abokin aikinta ya fado dakina gudun zuciyata ya ki komawa yanda yake da, kuma yana yi gabana na faduwa ne,
Muhammad, nawa suka kashe? Nawa suke son kara kashewa? Ni na san ba son kashe ni suke yi ba, dan walahi da son kashe ni suke son yi na san da tuni sun cin min, Muhammad so suke su haukata ni? So suke na zama dan gidan su? Ko takarduna suke bukata? basu da wasa Muhammad, basu da wasa......


Ya karashe yana mai dora hannunsa ya share zufar da ta zubo masa

Muhammad dake kallon sa da yannayin tsoron yannayinsa ya ce" Abdul, soyaya kake da ita ko kwonci?

Abdul ya saki hannunsa ya ce" ba zaka fahimta ba,
Ita din ba zata kwonta da dan iska ba, bata taba yarda na rike hannunta a yannayin lafia ba bale har a zarfe wani waje da ita ba,

Shiru ya yi yana kallon kasa , sai kuma ya yi murmushi ya ce" so? Soyaya? Ina na ga halin yin soyaya ni? Ta ina zan soma? Ko daya , ba wannan wasan tsakanina da ita, soyaya suke da mai gidan su, wato BS

Ya karashe yana mai duban gefensa sannan ya saki murmushi ya daki kirjin Muhammad ya ce" zan iya hakurin rashin da aka rigaya akai min, bana jin zan kuma iya rintsa ido idan bamu yi fada yau ba

Nan ya bar Muhammad tsaye ya shige ya saka suturar kirki ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login