Showing 117001 words to 120000 words out of 154870 words

Chapter 40 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1161

rabon wani garaje dan Allah ya kashe ni kafin ya fito daga tsatson ki ....Hafsat idan na rabu da ke ni kuwa na rayu a yaya?*



Bayan kwana biyu aka kawo lefen Hafsat
Lefen da ya kara kashe bakin mutanen gidan malan kowa sai dai ya labe daga daki yana leke ba um ba umum,
Anguwa du an dauka, maganar uwar malan kawai ake, da yawa na fadin alkhairin da yawa na kushewa

Kwana biyar kennan da maman malan ke zaune da auren Abddallah a kanta,
Bata kuma jin duriyar BS ba, haka kuma shi kansa abdul din daga daren da ta yi kiran nan nasa da ta kashe bata kuma nemansa ba

A yau ta tashi ta gama shiri da sanyin safiya cikin nikaf da abin hannun da mama ta bata, shima an ce dole sai ta je da kanta gidan mai dinki ne, hakan ya saka mama ta ce maza ta je ta dawo su yi dilkar safe domin ko dilkar basu yi ba

Har ta yiwa mama salama mama ta dawo da ita

A hankali ta ce" kin nemi izininsa ne?

Da sauri ta kalli mama cike da mamakinta, izini? Wai izinin wa?

Mama ta daure fuska ta mika mata wayarta da aka karbe du idan za.ai mata dilka ake amshewar

Amsar wayar ta yi ta kuma kallon mama gani ta yi ta tsareta da kallo dan haka ta danna wayar ta shiga kiran numbersa

Sabon wulakancin da take gani ya dauka yanzu ne ya yi mata dan sai a kira na biyu ya daga sannan ya ki yin magana

A hankali ta yi salama domin mama na kallonta ido cikin ido

Amsawa ya yi yana mamakin salamar daidai ya tsaya wajen danja

A hankali ta ce" an aike ni wajen mai dinki zan je na dawo

Ajiyar zuciya ya sauke kamar wanda ya yi tsere, a hankali ya ce" ki jira

Bai karasa ba ya kashe kiran , ta bi wayar da kallo
Sarai mama ta fahimci abinda ya ce dan haka sai ta dauko kujera ta zauna a kofar dakin mama

Ta kusan minti ashirin a zaunen nan, tana yi tana duba agogon wayarta tana kuma kallon hanyar fita

Kanshin turaran da ta jiyo ne ya sakata yin shiru ta ki motsi

A hankali yake takowa har ya iso inda take zaune
Bai yi mata magana ba sai tura kofar da ya yi ya yi salama

Da mamaki ta dago tana kallon wai da gaske dakin maman zai shiga? Yau ta ga ikon Allah, mazan yayunta basu taba shiga dakin mama ba sai yau shi bakon jiya zai shige har dakin mamanta

Mikewa ta yi ta yi gaba dan har an fara leke, bata son a bata mata rai da safiyar nan

Sai da ya gama gaishe su ya fito ya fita wajen

Ganninta waje tsaye ya sosa ransa, aman bai nuna a nan ba ya bude ya shiga itama ta bude ta shigan

A hankali ya tayar da motar ya dauki hanya

Batai masa magana ba sai murza yan yatsunta da take,
A hankali a hankali har suka karasa wajen da bata fada masa ba sai dai gani ta yi ya kaita ta tabata mama ya tambaya

Fita ta yi ta shiga akai mata aune aunen da za.ai mata baki daya ta fito ta dawo motar

Dagawa ya yi suka fara tafia,
Suna tafiar ya canza hanya a hankali ya ce" bana so kina fita Hafsat,

A hankali ta dan kale shi sai kuma ta kawar da kan nata

Hafsat talk to me;

Dubanta ta kai wajensa, sai kuma ta shiga shashekar kuka,
Kuka take a hankali a hankali wanda ya saka shi ja ya tsaya a cikin kwanar da suka shigo sabuwar anguwar yan gayu ba wasu mutane a waje da yake safia ce sai jefi jefi du suna gida suna baci

Mitar ya tsayar kasan wata shuka,
A hankali ya karkata yana kallonta,
Rufar fuskar nata ya dage ya cire mata baki daya yana kallonta

Gashin idannuwanta sun yi gazar gazar da su, sun shiga idannuwansa har sun zarta

A hankali ya fora yatsarsa saman girarta ya dan shafa kafin ya lumshe idannuwansa,
Muryarsa ya sanyayar ya ce" menene?

Hafsat ta dago da dubanta a hankali ta dube shi,
Muryarta ta sanyayar ita din ma ta ce" Abdul, ina BS ya shiga?

Abdul ya tsura mata ido, gabansa ne ya ji ya fadi lokaci guda,
Bai yi shishigi ba kuwa? Bai sako kansa wajen da zai zauce ba kuwa? BS? Tare fa ka gansu Abdul, shin wannan damuwa da shi ka san da tana son sa, idan fa bayan so din Hafsan ka ta yarda da BS ne?
Gabansa ne ya kara faduwa, hankalinsa ya ji ya tashi a hankali ya saka hannayensa bibiyu ya kamo fuskarta,

Matso da fuskar tata ya yi ya samu da kyar ya hada ido da ita,
A hankali ya ce".......



=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?=?B?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 3??



A hankali ya ce" kin kasance mai fadin gaskiya Hafsana,
Ki fada min, a cikin mazan da suka ringa kawo maki hari shin shi ya samu galaba a kanki ko menene wannan damuwar da shi?

Sai da ta wanna idannuwanta a cikin nasa sannan ta saka hannnayenta biyu ta janye hannunsa

Sakar mata fuskar ya yi yana kallonta, a hankali ta ce" haba Abdallah, me zan yi kwadayi da zaman yau da kulun? Na zauna da kai Abdallah! Bana son irin rayuwar nan, rayuwar da ba kula ba yanci? Ni wa na fi da zan yi tunani ai ni ce zaka waiwayeni? Ni ta nawa ce? Abdul shin ka taba so a rayuwarka?
So wani abu ne mai nauyi mai wahala, Abdul ni na taba so, so yakan saka mutun tsalake maganar manyansa, Abdul Bashir ya nunan so, ya bi ni sau da kafa...ya waka min, ya yi hakuri har na samu kaina sannan ya zo har gidanmu ya nemi soyayata da aurena
Shin me ya tsayar da shi? Ina cike da zulumin abinda ya tsayar da shi mai girma ne, Abdul du irin zagina da ake a kulun sai ya furtan kalmar so

Idannuwansa ya lumshe ya kuma budewa yana kallonta

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta kale shi ta ce" ban san kansu mazan ba bale har na ware shi dan hakan! Ka kaini nesa Abdul, ka yi yawo da ni sama a zuciyarka ka ajiye ni malan kar ka saka na kasa sauka=?D?
Ta karashe tana mai turo masa bakinta sannan ta gyara zama a cikin motar

Murmushi ya yi kawai ya girgiza kansa ya tayar da motar ya harba hanya

Ashe wajen da zasu je din babu ma nisa da inda ya tsaya dan kawai ta kwasan masa kukan rigima ne ya rikice ya ja ya tsaya kar ta halaka shi, da zata san irin abinda yake ji da bata yi haka ba

Kofar gidan ta karewa kallo, tamfatsetsiyen get ne da sojoji biyu a kofa

Buda kofar kawai suka yi ba tare da sun tsaya binciken wanda ya zo ba hakan ya tabatar mata da sun san ko waye a cikin motar

Sai da ya isa ciki sosai ya yi parking

Fita ya yi ya tsaya yana kallon kofar falon

A hankali ta fito bayan ta saki nikaf din fuskarta
Takawa suka yi tana biye da shi har suka shiga falon

Gabanta ne ta ji ya fadi sakamakon hango kanwar mamansa, kuma mahaifiyar matarsa hakimce saman kujerar falon tana amsa waya

Tana ganinsa ta kashe kiran tanai masa oyoyo

Murmushi ya yi ya karasa har inda take zaune ya dan duka ya bata peck a goshinta itin gaisuwar larabawa sannan ya zauna sosai kusa da ita ya rike hannayenta suna gaisawa

Itama cike da kulawa take amsa gaisuwarsa kafin ta tambayi wajen su na.ima

Sai da suka gama gaisawar ya dan waigo sai ya ga Hafsat na tsaye a bakin capet din bata shiga ba ta zauna

Mikewa ya yi ya karasa inda take tsaye ya kamo hannayenta ya janyota a hankali har wajen zama ya zaunar da ita

Dubansa ya kai wajen kanwar mamansa ya ce" ummi, matata na kawo ta gaishe ki

Daga ummin har Hafsat a tare suka dafo kai suka sauke dubansu a kansa

Cikin dakewa ya ce" Hafsat, ga mamana, kanwar mahaifiyata wace ta rage min kadai a duniya

A tare kuma suka kalli junna Hafsat din da maman Na.ima

Bata taba jin zufa ta karyo mata tashi daya sai yau, kan uba, shi ne abinda ta ayanna a kasan zuciyarta, a duniya bata taba haduwa da mutun dan rainin hankali irin Abdul ba,

A hankali ta sada kallonta daga duban mahaifiyar Na.ima,
Ita kam maman na.ima bata ma san me zata yi tunani ba,
Dan haka ta kali Abdul dake zaune yana kallonsu, bin kowace yake da kallo dan ya gane hallin da suka shiga

A nitse ta ce" ban fahimci abinda kake nufi ba, kana nufin aure ka yi?

Keyarsa ya dan sosa irin ya dan ji nauyin nan ya ce" eh moms, yau kwana shida da daura auren, auren ne ya zo kai tsaye hakan ya sa ban shaida maku ba, ita kanta bata tare ba ana shirye shiryen tarewar nata ne

Kanta ta gyada tana kallonsa kafin ta mike ta ce" Abdul mu je ciki ina son gannin ka

Mikewa ya yi ya bi bayanta ,
Suna shiga ta juyo da dubanta ranta a bace ta ce" aman Abdallah ni zaka wulakanta a cikin garin niger ka nunawa duniya ni ba kowa bace haka kuma ka nuna kai ka isa da kanka kai mai kudi ko? Aure ne zaka kara baka sanar da ni ba sai dai ka zo min da yarinya kai tsaye ka wani ce ga matarka? Ka manta y'a ta kake aure idanma baka dauke ni a uwa ba ai zaka sasauta ko dan yar da na baka take zaune a gidanka ko?

Habarsa ya rike da mamaki ya ce" moms aman me ya yi zafi haka?

Tambayana kake abinda ya yi zafi? Du abinda na fada wanene baka fahimta ba na baka haske!

Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" auren ne damuwar ko kishiyar da aka yiwa yar ki?

Idannuwanta cike da bacin rai ta ce" eh dan me zaka yiwa yarinya kishiya ko haihuwar fari bata yi ba?

Kansa kawai ya girgiza kafin ya dan matsa kusa da ita dan ya ga ta soma daga muryarta shi kuwa baya so wata baraka ta fito daga wajenta, ko ba komai fa kanwar mamansa ce

A hankali ya ce" aman ai na fada auren kai tsaye ne ko Moms? Kuma kin dai san ina aure aure ai bai dace hakan ya bata maki rai ba, moms kawai sai dai idan zaki nuna kin fi son Na.ima a kai na ne, ni da na zo dan ki lalaba min ita kar ta daga hankalinta? Kin dai san tana so na bana son abinda zai hanata sukuni

Tsareshi kawai ta yi da ido, a gaskiya dan yar uwarta ne na jini, sai dai rashin mutuncinsa na wahalar da ita, ta rasa a ina ya dauki dabi.ar wulakanta mace haka? Wulakanta mace mana dan mace na sonka sai ka mayar da ita banza? Ai kuwa larabawa akoysu da ririra mace, rayuwar balaraben mutun da matarsa duda shi ba balarabe bane aman ai a can aka raine shi

Shiru ta yi masa hakan ya saka shi sasauta murya ya ce" ki yi hakuri momy, a matsayinki na uwa q wajena ban kyauta ba, aman ki yarda da ni ban aureta dan na wulakanta yar uwata ba, su duka zan hada na zauna da su daga su bani da ra.ayin kara wasu sai dai idan sun gaza da ni ne

Kawar da duban da take masa ta yi, a hankali ta ce" idan ka je ka kawota nan mahaifinta ya rarashe ta, Abdallah ka yi adalci tsakanin su

Kansa ya ringa gyadawa har ta gama sannan ya riko hannunta yana kallonta
Murmushi ya sakar mata a hankali ya ce" ki dauke mu mu duka tamkar yayanki momy, na roke ki...yin hakan zai bani kwarin gwuiwar risinawa koda bana so=?O?


Murmushin ta sakar masa ita din ma sannan suka fito daga dakin

A lokacin da suka fito tana zaune inda suka barta kanta a sade kasa tana dan kada kafarta

Muryar momy ce ta sakata dago da kanta, momy ta ce" yarinya kina zaune ko ruwa ba.a kawo maki ba?

Abdul ya karasa kusa da Hafsat ya zauna saman kujerar , da kafarsa ya dan mintsinota hakan ya saka ta dan matsa kadan tana kallon kasa bata ce komai ba

Daidai nan aka kawo jus, sai dai bata kai ga dauka ba Abdul ya mike ya ce" momy tafia zamu yi

Mikewar ta yi itama ta rako su har wajen mota, bata ce su ci kansu kuma ba sukai salama suka fito a gidan

Sai da ta ga sun fito ta dage nikaf dinta cikin yanayin tashin fitsara ta ce" Abdul wannan wani irin wulakanci ne? Ya zaka dauko ni ka......
Wani wawan birki ne ya taka wanda ya saka taratsun maganar da ta dauka tana zazaro mai ido ta hadiye lokaci guda ta dan yi gaba Allah ya taimaketa da belt a jikinta ya mayar da ita kujerar

Yana tsayawa, bai bari ta dawo a doguwar rikicewar da ta yi ba ya kara daukan hanyar kara rikitata,
Lokaci daya Abdul ya janyo Hafsat jikinsa bayan ya kunce belt din jikinta ya janyota sosai jikinsa ,
Cikin kankanin lokaci ya hade bakinsa da nata....a hankali ya lashi lebenta na kasa,
Idannuwansa dake lumshe ya dan daga gani ya yi ta zazaro ido haka kuma kofofin hancinta kansu sun bubude da mugun mamaki da tsoro

Idannuwan nasa ya lumshe ya fitar da harshensa kadan ya kara lashe lebunanta baki daya, a hanakli ya saka harshen nasa a bakinta yana dan zagayawa hakan ya sa ta kara daga bakin cike da mamakin girman fitsararsa da kallon abinda yake mata wani iri

Abdul ya yi haka ne dan ya kashe bakinta wajen yi masa ihu, ba zai iya daga mata murya ba zai so ta gane haka itama ta daina daga masa murya

A hankali ya karasa damkar harshenta ya shiga kissing passionately, wani irin hucin numfashi ya fara fitarwa lokaci daya hannunsa da ya ririke hannayenta ya sake au ya shiga hayowa da daya har wajen kanta ya talabe bayan keyarta yana kara tsotsor bakinta tamkar ya samu alewar kara

Dayan hannun nasa dake rawa rawa ne ya saka a hankali ya shiga lalubar hanyar da zata bashi damar saka hannun cikin rigarta...lokaci daya kuma yake kokari kara dorata saman cinyarsayana shafa bayanta a hankali yana sama da hannun yana neman zif din rigar tata

Lumfashin da yake saukewa ne ke shiga ilahirin jikinta yana sauka a fuskarta mai wani irin dumi da kanshin maclean na ananas mai sanyi

Ajiyar zuciya yake saukewa a kai a kai, lokaci daya yannayin yanda ya samesu da Muhammad ya fado masa a cikin idannuwansa,
Da sauri ya cika leben nata, q haka kuma ya ririketa a jikinsa da wani irin karfi
Kansa ya cusa cikin dokin wuyanta , muryarsa na rawa ya ce " *HaHafsssssssat, me ya maki a ranar nan?*


Wannan karon damkar da ya yi mata ya fi gigitata fiye da taba mata jikin da ya gama yanzu yanzu, lokaci daya ya birkice mata kamaninsa suka canza mata,
Gaba daya ya hade ya zame mata tamkar kumurci sannan ya yi mata tambaya ya tsareta da wani mugun kallo

Gabanta ne ya shiga dokawa,
Lokaci daya????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
ta shiga tambayar kanta wa? Wa yake tambaya? Me ya yi mata a wace rana????


Hafsat baki fahimci wanda yake nufi ba ko?>??>??>??
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 4??





Cikin bacin rai ya dago da dubansa yana kallonta ya ce" ki bani amsa ke nake sauraro Hafsat, me ya maki? Me da me ya maki?

Wai wa kake nufi Abdul?
Hafsat ta fada tana dan matsawa daga irin maysewa juna wajen da suka yi

A hankali ya maida bayansa jikin kujerar ya jinginar
Ya jima a haka dan a kadan ya dauki minti

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login