Showing 33001 words to 36000 words out of 154870 words

Chapter 12 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1114

harbin daga shi gashinan waje waje radau ya fito a sama

Sai da ya yi wani recherche sannan ya dora wata hanya, wace ke nuna wani mutun tsaye yana ta waige waige bayansa goye da wata jaka sannan kunnensa yana waya da alama wayar a hanzarce yake yinta,

A tare suke kallon mutumen, kafin ya dago da dubansa ya dora saman kanta, irin yanda ta matse masa waje ita kanta bata kula ba, ta raja.a tunaninta da hankalinta kan mutumen nan,

Yannayin kallonsa ya shaida mata yana nufin wannan shi ne, dan haka da sauri ta je dora hannunta saman computern dan gannin hawa na nawa ne, da yannayin da zai kara tabatar mata da wajen,

Da sauri ya tare hannunta, domin gaba daya computern na anfani da emprinte din yatsutsansa ne, dora hannun wani na iya tayar da karan laluwar da ya saka gaba daya a cikin gidan,

Fitar mata da abinda ya tabata take son gani ya yi, yana mai dan kara yarda da yannayin aikinta , domin da wanda bai san aikinsa bane yana iya fita da gudu ya shaidawa mutane ai yana nan, a fantsama a yi ta hauka ba.a samu mutumen ba,

Maimakun ya ga ta fice da gudu sai ya ga ta kara dan abin hannunta ta ce" BS, suspect din mu na hawa na biyu wajen matatakala yana kokarin saukowa, sanye da bakin jeans da riga baka mai dogon hannu, fari ne kar bayansa dauke da jaka baka mai dauke da bindigar,
Yana waya, ku kula yana waya, kar ya jefar da wayar .....

Shiru ta yi ta tsurawa screen din ido , inda shi kuwa ya tsura mata ido yana kallonta,

A sakalce ya ce" ke, yo ke bakya zuwa ne? Kin wani sakani gaba kina kale min na.ura?

Bata daina kallon computern ba ta bashi amsa a takaice cewar" eh!

Murmushi ya yi ya juya ya zauna saman kujera ya daga hannayensa ya dora bayan sumar kansa ya dan daga kujerar daga gaba ya watsa kafafuwansa yana kai kawo yana duban yarinyar,
Bakinsa ya tabe , ya so ta bara masa dakin, shima ya fice ta inda zai gyara shi ko zai damki wannan wannan mai harbin, aman ta wani zauna , shi kuwa ba zai yarda saboda haka wannan yar yarinyar ta gane menene aikinsa har ta falasa shi ba!


A hargitse mutumen yake doka waya wa wanda ya bashi wannan mission din,
Ana daga wayar aka ce da shi" ka tabatar ka yarda layin nan ko ka hadiye shi, sannan ka san yanda zaka kubuce masu, idan kuwa aka kama ka, ka san ko rayuwar wa ka saka a hatsari!



To fa........., shin za.a kama wannan mutumen kuwa?
Yaya tafiar wannan aiki tsakanin Hafsat da Abdul?
Ni.ima fa?
Bs Fa?


Na ji dadin comment din ku sosai wollah,
Ban bayar da amsa ba domin ban zauna ba,
Ina biye da ku kamar yanda kuke biye da ni makaranta *KUTKALE*
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 5??

*DUNIYA MAKARANTA,*

ASALAMU ALAIKUM




A lokacin da su BS suka cinma wannan mutun, sun tarar da shi yana zubar da wata irin kumfa , wato ya hadiyi poison,

Ba yanda basu yi ba dan gannin bai auna barzahu ba, sai dai ina poison din mai karfi ne,
Wayarshi dake yashe dan nesa da shi suka dauka da sauri,
Bayanta BS ya buda dan cire layin, sai dai wayam ba layi a ciki, ba alamunsa,
Cike da jin haushi ya doka wayar da kasa yana fadin shiiit!
Kafin ya kai dubansa wajen yaren dake tare da shi ya basu umarnin maza maza su duduba layin inda ya jefar da shi,

Hafsat dake tsaye tana kallo ta yi saurin maido baya kadan,
Inda ya yi kamar ya labe fuskarsa ta yi zooming,
Nan ta ga yanda ya yi da layin, wato a bakinsa ya saka shi ya taune shi sannan ya ya hadiye,

Bata san lokacin da ta dora hannayenta biyu saman kanta ba, ta janye atach mai ruwan blue din dake kanta dan bada kama, ta yar ta dan ja da baya irin desespoir din nan,
A hankali jiki a sanyaye ta ce" BS, kar ku ba kanku wahala, ya taune layin kafin ya hadiye shi

Sai a lokacin ta tuna da yana zaune a dakin, sai a lokacin ta kai dubanta inda yake zaune,

Kuri ita yake kallo, tun da ya hadiye layin shi ya gani, kuma ya gane nufinsa, aman kuma ya barsu su yi aikinsu,
Yannayin da ta nuna na tashin hankalin echec din abinda ta saka a gaba ya matukar bashi mamaki,
Menene damuwarta haka a kasan zuciyarta? Ko kashe shi aka yi ita fa bata da asara domin kudin aikinta cas sai an cashe mata su,
Abu biyu ke iya saka ta a wannan yannayi, tana da damuwar kanta,
Ko kuwa ta matukar dauki aikinta da mahinmanci,

Ido cikin ido suke kallon junna,
Kafin ya ga ta mike ta tunkaro inda yake zaune,

Sai da ta zo kusa da shi, irin kusan da babu wani space a tsakaninsu ta saka idannuwanta cikin nasa ta ce" ka bamu damar yin aikinmu yanda ya dace,
Ya za.a dauke mu aiki, ba.a bamu wani cikeken bayani a kan aikin ba, ba.a fada mana girman risk din da muke ciki ba, bamu san komai ba, kuma a ce zamu iya yin wani abin kirki? Ya dace kafin mu hau filin aiki mu san ko kai waye, meye sana.arka, meye tarihinka, me ke yawo da kai haka da za.a farauci rayuwarka daga zuwanmu, kafin mu zo an farauce ka har haka? Kana da wanda kake hasashen shi ke neman rayuwarka?

Duka magangannun nan da take masa , cikin yannayi na daure fuska, da kuma iya gaskiyar abinda take son sani kennan take yi, sannan idannuwanta tsai cikin nasa, ba tare da ta ji wani dar ko wani nauyin saka idannuwanta cikin nasa ba, haka ta kare zanenta sannan ta yi shiru tana mai dubansa , hakan na nufin amsarsa take jira.

Kijerar ya ajiye daga lilon da yake mata, sannan ya mike tsaye, wanda mikewa ta saka kirjinsu kusan goguwa da juna har sai da ta dan ja baya,

Tsayuwar da ya yi ya sakata dan daga kanta fan kar ya ga wasa a tatare da ita ko gazawa a idannuwanta ta ci gaba da kallon nasa wanda hakan shima ya so din,

Idannuwansa ya bude mata baki daya yana dubanta ya ce" wacece ke? Su waye mahaifanki?

Kanta ta dafe da yannayin irin wannan tambayar ta isheta , kafin ta kuma dubansa ta ce" ba shi ne abinda ya kawo ni gifanka ba! Dan me kai ba zaka iya bamu information din da muke so ba?

Idannuwansa ya kankance ya matso kusa da ita domin ta kara ja baya irin suna jin har bugun zuciyar juna ya ce" ban ga dalilin da zai saka na dauki karti biyar na tinga biyansu kudin aiki masu tsokar da ba a gine nake ba sai na girgije dan an wawushe ni, sannan kuma na masu rabin aikin!
Me aikin ki ya kumsa? Bincike, shige shige, dan samun amsoshin da suke cikin hadari, mutu ko rai!
Sai ki zauna, ki auna, ki yi aikin ki yanda ya dace, ba wai ni kamar wani sauna na zauna ba kwashe komai na fada maki, na ciyar da ke , kuma na biya ki kudin aiki ba!

Yana gama fada ya juya ya fice a dakin, inda ya nudi dakin Muhammad da sojoji suka kasa suka tsare sai muzurai suke,
Yana zuwa suka bar shi ya shiga....

Mutuwar tsaye ne ta yi, na dalilin irin amsoshin da ya bata, *KARTI BIYAR* , kennan mu duka karti ne?
Wannan mutumen akoy dan wulakanci na bugawa a jarida! Wannan mutumen yana neman fitina da ni! Yana son tashin hankali da ni! Zan kuwa gwada maka na san aikina....
Dubanta ta kai kan computersa, wace ko a dazu da ta dano dan yin zooming din vidion wanda ya zo harbe shi da ta taba ba tare da ta tsaya ya yi mata ba sai da gaba daya gidan ya dauki wata laluwar da ta kara hargitsa masu tsaron, wanda da sauri ta dana buton din dake kashe kukan,
Ta san a cikin wannan computern ba za.a rasa wani abin ba,
Sai dai ba damar tabawa dan yanzu zata jawa kanta taruwa a kai, shi kuma ya tirke ta da tuhumar me ta koma yi.masa cikin computer

Nauyi kanta ya mata, nauyi da zafi, a hankali ta juya ta fice ta shuga fafutukar yanda zata yi


Wannan aikin na bani tsoro Abdul,
Ka duba ka ga yanda wannan abin ya jaza mana balakin da ya taba rayuwar Ummih?

Ka bar wannan binciken mu koma gida Abdul, wanda ke bibiyar rayuwarka, ko kiyar bera ya sha ba zai taka kafarsa saudiya da nufin hakan ba, dan ya san gaba da gabanta,
Aman a kasar nan, tamkar gidan dake bude ne, hayam, baka da wani kariya Abdul, dan Allah ka bari ya dace ka fuskanci rayuwa ka rungumi matarka ku hayayafa ka samu farin cikin rayuwa,

Abdul dake dubansa ya yatsina fuskarsa ya ce" farin ciki? Farin ciki?
Rabona da farin ciki, tun daga lokacin da na kama shi yana dukan mahaifiyata a gaban kanwata,
Rabona da farin ciki tun daga lokacin da na gane ba kowa ne ke dirawa dakin kanwata ba sai shi,
Rabona da farin ciki tun daga lokacin da na nemi mahaifiyarsa ido rufe aman na rasa har ta mutu, ni, na tashi da kudurin bayan ya mutu ma, zan tabatarwa iko cewa shi da wannan marar imanin ne suka tagayara rayuwata,
Duka a kan me?
Dan yana da wannan dukiyar,
Duka dan me?
Dan rayuwar gayu da ta saki, ta sakankance ta bara masa tarbiyar kanwata , wankanta, saka mata sutura, pampos , bata abinci saman cinyarsa, ana dariya ana dauka a waya ana yadawa a duniyar gizo gizo, mutane na yabawa suna tura lyk dan kawai a fada, a dauka, duniya ta yayata,
Duka dan me, dan a yi tunkaho, a nunawa duniya, a kuma daki kirji da akoy kusanci tsakanin dan da uban....
Ba.a ankara da komai ba, aka ci gaba da rike wannan relation din har ta kai idan zai yi tafia da ita yake yi,
Ta fara girma wajen shekara biyar aman baya jin kunyar saka kaya ko tubewa a gabanta ba, domin shi fa yar jaririyar yarsa ce mai tatata marar wayo,
A hankali ta horu da gannin al.aurarsa ba wani abin bane,
Bayan ta tasa har ta kai shekara bakwai , takwasma yakan dorata saman cinyarsa yanai mata cakulkuli domin nishadinsu, idan uwar na kisa ta yi ta kakaba dariya,
Dalilin nisantani daga kusa da su dan na kasance mai nuna ba za kyau irin haka, a islamiya ana fadin hakan,
Tafia ta yi tafia na gane cewar rayuwar da ta zama baka a tare da shi a tsakaninsa da yarsa, wanda mahaifiyarta bata sani ba, sai dankon soyayar dake tsakani, sannan ya cire du wani kuntatawa da yake mata da, ya sakar mata mara ta yi fitsari son ranta, cewar cutar yarta ne ake, kuma hakan ba shi daya keda irin mu.amala kazamar mu.amala a gidansa ba, harda aminansa su suka kwadaita masa wannan lamari, wato gida bai koshi ba ba za.a kaiwa daji ba!

Muhammad da ya rintse ido dan yannayin abubuwan nan na girgiza masa zuciyarsa ya ce" shut up plz man!

Abdul Jabar ya karasa kusa da shi sosai ya ce" Na yi wannan karatun mai cike da hatsari bayan nunawa duniya kasuwanci nake ne dan na bi didigin su,
Ni na san makashina,
Abinda ban sani ba shi ne...waye makashin, waye mataimakin, kuma waye ya kashe Ummih?
Abinda ban sani ba shi ne...waye ya hada ni da jarabar mata? Idan na ga mace, yanda ka ga bindin kare na kadawa ko bunsuru na tabe lebe haka nake,

Baka da tabas Abdul, daga jin maganarsu ka hau haka ka zauna, dan Allah ka daina,

Abdul ya daki karfen bed din da aka yi runfa da shi irin an saki labulayen nan ya daga muryarsa wanda da ace irin ginninmu ne da tabsa du sai an ji abinda yake fadi ya ce" ka ci gaba da boye min kennan?
Baka yarda ba da daya daga cikinsu ne ya kada jirgin da Abdul Basid ke ciki wanda sai da aka bashi damar yiwa mahaifiyata vidion ban kwana?
Baka yarda ba da , qn harbe shi ne sanadiyar arzuzumin wandonsa da baya iya daurewa sai da ya afkawa matar amininsa?
Baka yarda ba da *Ubana* mijin Ummih ya rayu bisa fuska biyu a gaban matarsa salihi a waje dan duniya ba?
Ba zaka yarda cewa idan nace da kai Abdul Basid may be bai mutu ba, yana raye ina iya yin gaskiya?

Yaushe zaka yarda cewa aminan Abdul Basid ke bibiyar rayuwata bisa dumbin arziki da kuma daukan fansar amininsu wanda suke gannin sun kashe maciji ne basu sare kansa kuma suka dandatse kansa ba?

Kai Muhammad Auwal Bin Muhammad yaushe zaka yarda da aikin da nake ba cira na yi daga sama ba, na cancanci zama zakara kuma kwararan mai.......

Dan suuu din da ya ji dalilin kawo hannunsa kusan wuyan rigar dake jikinda ne ya saka shi datse maganarsa tare da bugun zuciya,
A lokaci daya ya kai hannunsa na dama wajen ya lalubo dankaramin speaken da ta makala masa a lokacin da suke tsaye jiki da jikin juna sunaiwa juna kallon doya da man ja, wanda ya lumshe a idannuwanta bai ankara ba, sai yanzu da agogon hannunsa ta shaida masa da haka,

Da hannunsa na hagu ya nunawa Muhammad abin, sannan ya juya da wani mahaukacin gudu ya koma dakin da ya barta,
Sai dai ina bata nan,
Ba ita ba alamarta

Da wani irin sauri har yana hardewa ya kuma fitowa ya daga hannunsa yana yafito du wani ikon dake cikin gidan fuskarsa tamkar na bakin kumurci ya kare masu kallo

Bai ganta ba, babu ita a wajen ba alamunta,

Cikin yannayin damuwa ya kara bin su da kallo baki daya, inda dubansa ya tsaya kan BS,

Takawa ya yi ya karasa gabansa, du girman jiki, da yannayin karfi na BS ashe cika ido ne, a yanzu da Abdul ke sanye da wannan body din sai gaba daya ya dame BS ya shanye,
A tsayima ya fi shi nesa ba kusa ba, dan haka yana tsayawa gabansa ya saka idannuwansa da sukai ja cikin nasa yana dubansa, kafin ya sauke ajiyar zuciya kamar zai yi rada sai kuma ya bude muryarsa ya ce" ina take?


BS da ya fara kokonton yannayin Abdul, cewa du inda ya fito wannan ba kawai elhaj mai kudi zaune da bakin duwaiwai ciki cike da sangarta bane, ya dube shi shima da yannayin kulawa sannan ya ce" wa ce?

Shi kam haushin tambayar ya ji, hakan ya saka shi takawa ya yi gaba kadan, ya kuma dawowa ya ce" yarinyar dake biye da ni!

Sai a lokacin BS ya lura da Hafsat bata wajen, gabansa ne ya fadi tare da tsoron kar a je an dauketa ne?
Da yannayin tashin hankali ya kai dubansa wajen Abdul, sai dai bai tsaya jin amsarsa ba ya juya da sauri ya fita da niyar nemota da kansa, inda su BS suka bi bayansa da abu biyu, bashi tsaro, da kuma neman Hafsat........




*Shin ta ji du abbin nan?Wai waye Abdul? Ina Hafsat ta shiga? Idan Abdul ya ganta, me zai faru da ita? Duba da ta saurari sirinsa, duda kadan daga cikin sirrin ne, wato tsunguye tsunguye.....*
Toh fa


=? ?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 6??



A lokacin da suka fito gaba dayansu da yannayin na zakunna, kowane na jefa kafarsa inda ta je, suka tsaya gaba dayansu a tare sakamakon ganninta tsaye ta zuba masu ido su duka,

Sai da gabansa ya yanke ya bada wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login