Showing 99001 words to 102000 words out of 154870 words

Chapter 34 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1132

masoyinta na da wanda sanadiyarsa ta afka tashin hankalin rayuwa

Ta jima tana juya wayar kafin ta kai ta saka a caji ta ci gaba da sha.aninta

A rana ta shida mai dinki wato hajia Farida ta kawo dinkunnan da mama ta bata ,
Ai kuwa dinkuna ne masu shegen kyau rufafu tsararu sannan na gayu masu tsadar gaske,
Ba karamin farin cikin kayan nan ta yi ba, haka ta hau sama wajen mahaifinta dan yin godiya, tana zuwa ya kara mata abayoyi kala biyar masu shegen kyau na yayi dukansu masu botira da mayafansu bakake masu tsari

Kanta kawai ta sada ta rasa bakin magana, a hankali ta dago da idannuwanta sai ta ga mahaifin nata na kallonta yanai mata murmushi, ba komai yake jin dadinsa ba sai yannayinta na yanzu, wai mamansa ce ke nuna farin ciki dan an saya mata sutura, yarinyar da a da hayowa zata yi, ba ruwanta da neman izini sai dai ta afka idan a gaban wa sai dai ta fadi muradinta na kudi ta karashe da fadin" kuma a bani ko na je saurayina ya bani!
Sai gashi yanzu a gidan duniya Allah ya nuna masa ita tana godiya harma ta rasa bakin godiyar

Hannunsa ya daga mata dan ya tabata tana iya yi masa kuka a gurin , shi kuwa baya so , dan haka ta mike har ta kusa fita ta tsinkayo muryarsa ya ce" su ABDALLAH zasu dawo gari da zama karshen satin nan, kwana biyu ina tsaye kan saukar alkur.ani a gidan da zai zauna , kulun muna zuwa a sauke a yi sadaka dan gudun fitinar zamani

Sai da gabanta ya fadi, a ranta ta ayanna me kuma zai dawo da shi kasar Niger?

Kafadunta ta daga a lokacin da ta tuna asalin dan niger din ne shima fa, haifafan garin ne, haka kuma dangin da suka rage masa yan nan ne wato matarsa da kanwar mamansa

Bata baiwa Malan amsa ba sai karasawa da ta yi da murnarta suka dadaga kayan da mahaifiyarta kafin su shiga yi masu turaran wuta da adu.ar Allah ya sa a mora lafia


Bayan kwana goma

Kwonce take tsakar dakinta wajen karfe biyar na yama, juyi kawai take tana tunanin wai yau zata yi zance, zancen ma da BS, zuwansa biyu sai yau Malan ya bashi damar ya zi su gana

Mikewa ta yi zaune tana kallon madubin dakinta mai tsayi, kanta ta girgiza ta koma ta kwonta gashi har karfe bakwai din ta kusa,

Tana nan kwoncen har karfe shida ta buga, buda kofar da aka yi ne ya sakata mikewa zaune tana kallon yayarta da ta shigo da yaronta da ya fara rarafe yana yawonsa ko.ina

Bayan sun gaisa ne yayar tata ta bita da kallo,
Can ta ce" Maman malan, ni ba bako aka ce zaki yi yau ba?

Hafsat ta dubeta ta ce " eh

Yayarta ta ce" to ya haka baki shirya ba

Hafsat ta kaleta da mamaki ta ce" shiryawar me kuma auntu ? BS ne fa??

Sai da ta rike habarta sannan ta yi dariya ta girgiza kai ta ce" dan BS ne shine ba zaki kimtsa jikinki ba? Oya tashi tashi malama

Mikewa Hafsat ta yi tana kallonta kafin ta shige ciki ta dauko abaya daya daga cikin abayoyin Aba ta saka abinta a nan sannan ta shiga saka turarukan wutar da ta miko mata

Tana kokarin yana mayafin dan kwalin ta tsayar da ita ta zauna ta dan gyara mata fuska da kwalinta sannan ta yana mata dan kwalin a kanta

Tsaf hafsat ta fito tamkar ba ita ba, wani irin kyau ne ya bayanna a tare da ita wanda ita kanta sai da ta shafa gefen fuskarta sannan ta yi murmushi


Ana fitowa sallar magariba aka suka zauna tsakar gida inda malan ya basu minti talatin su gana

A zancen nan Hafsat banda tambayoyi a kan aiki ba abinda ta tsare BS da shi, shi kansa sai ya kasa wani yi mata zancen soyaya sai da ya tashi tafia ne ya ce da ita" Hafsat, ina son na turo a yi komai da wuri a gama, dan kin ga malan baya son dogon zance

Sai da ta ji gabanta ya fadi, ta dan tsura masa ido aman sai ta kasa ce da shi komai,

Murmushi ta sakar masa sannan ta shige ciki da dan gudu gudu hakan ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya juya ya tafi ya shiga galeliyar motarsa yana tunanin sai dai a waya ya mata maganar aikinta da kuma dukiyarta


Can wajen karfe biyun dare, dare ya tsala Hafsat na zaune tsakiyar gadonta daga ita sai dan gajeran wandonta da yar rigarta na barci ta yi zuru da wayarta a hannunta tana dannawa tana game

Message ne ya shigo mata kamar haka " *KAURIYATA, NA KASA BACI*

kurawa harufan ido ta yi tana kallo, bugun zuciyarta ne ya canza lokaci daya hannunta ya fara rawa,
Du duniya ba wanda ke haye mata irinsa, shi ne, walahi shi ne

Wayar ta ajiye tana kallon rubutun tamkar wanda ya yi da hannunsa idan hasken wayar zai dauke sai ta danna ta kara kallo

A hankali ta rubuta " *ME YA HANA KA BACI?*

mikewa ya yi zaune daga kwoncen da yake yana mai hararar wayar, kafin ya rubuto " *ke, gida kika je kika tara samari haka? Bakya dan jan aji daga yi maki magana har ki bani amsa ko kin sanma da wa kike magana ne?*

A lokacin da ta karanta sai da ta saki murmushi, sannan ta rubuto" *na san ko kasuwa na yi a tsakiyar dare irin na barawo? Dole bazawara ta ringa damka da karfi karfinta mana*

Wani uban tsaki ya ja a lokacin da ya karanta message din,

Zama ya gyara ya shiga dandankara magana son ransa, har ya so saki sai kuma ya koma da baya ya zauna ya jinginar da kansa jikin bed din, ajiyar zuciya ya sauke yana kallon waje daya sai kuma ya rubuta message kamar haka" *Na yi missing din ki amaryar BS*

Numfashinta ne ta fara ji yanai mata sama sama, lokaci daya kuma ta koma ta mike kafafuwanta saman bed din , sai da ta yi mika nitsatsiya sannan ta rubuta message kamar haka.........
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 5??

Sai da ta yiwa kanta fada kan irin rikicewar da ta yi dan kawai ya rubuto mata haka sannan ta rubuta" *NI KUWA, BANA JIN KEWAR KA*

murmushi ya saki , sannan ya ki bata amsa ya dai kurawa magangannun su ido yana kallo haka kuma Na.ima dake gefensa tana kallonsa bata dai san me yake yi a waya ba, aman kuma ta ga ya bada hankalinsa sosai hasalima bai san ta farka daga bacin gajiyar da ya tara mata ba

Hafsat dake jiran gannin amsarsa na ya rama da fada fada ta ji shiru sai abin ya dameta,
Tunani ta yi kan yanzu fa ba aiki take masa ba, mutun ya nuna damuwarsa a kanka bai dace ka yi masa abinda zai iya taba ransa

A hankali ta rubuta message kamar haka" *Yaya jikin ka?*

Mikewa ya yi zaune yana murmushi mai sauti, sannan ya bata amsa da" bani da lafia ne?

Hafsat ta yi shiru da wayar a hannunta, ajiyar zuciya ta sauke sannan ta rubuta" *malan meye wai? Zakana wani neman bani wahala ka manta da maman malan kake magana?*

Wannan karron har sai da ya buda hakoransa wajen murmushi, a fili ya ce" come on, relache toi, i really miss yannayinki,

Na.ima dake kallonsa ce ta yi motsi irin wanda zai saka shi gane ta farka

A hankali ya kai dubansa kanta, bata sanye da riga sai gajeran wando baki mai santsi
Yan berayan mamanta ya kalla haka kawai lokaci daya siffar Hafsat ta fado a ransa

Wani irin mikewa ya yi tsaye ya rintse ido lokaci daya, a hankali ya yi baya baya ya jingijar da bayansa jikin garun wajen,

Sai da ya jima a jaka kafij ya buda idannuwansa ya ga dai kuri shi take kallo

Takowa ya yi inda take ya tsaya mata kerere yana kallonta ya ce" ki daina zamarmin ba riga dan Allah, idan nemanki na yi ina gamawa ki saka rigarki....hakan zai sama min kwonciyar hankali

Yana gama fada ya juya ya nufi bayi ,
Da kallo ta raka shi tana mamaki halayarsa,
Mikewa ta yi ta shiga saka rigar a kasan zuciyarta kuwa ayyanawa take cewa.... ban san yaushe zan fahimceka ba, tanzun kuma wane zan yi? Nan ka ce da ni na ringa zama ba kaya, nicema nake saka wandon nan dan ba zan iya zama haka ba, kuma yanzu k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?aine da cewa na ringa saka kaya hankalinka zai fi kwonciya?

Tana gama sakawa wayarsa ta dauko ta ajiye masa gefen gado ta yi tsuru tana kallon wayar, da wa yake magana? Da wa yake nishadi har haka? Wacece ita? Wata dabara, wani irin kyau, ko wani irin iya girki ta iya wanda ya saka shi sakewa da ita har haka?

Gabanta ne ta ji ya fadin mata lokaci daya, ta sani ba tun yau ba ko ba dade ko ba jima Abdul sai ya kara aure dan kuwa a da can ma ta san da ba mijin mace daya bane bare a yanzu da yake jajan wai dama haka take da son jiki?
Tsoro ne ta ji ya rufe mata zuciya lokaci daya, in dai wannan da yake magana da ita budurwarsa ce kuma aurenta zai yi ai kuwa da zaune bata sameta ba, tabas da ta hadu da tsayuwa kennan, dan tana tunanin auren so kennan, ganninsa ma zai iya yi mata wahala

Tana cikin tunanin ta ji ya janyota baya, wato saman bed din, gaba dayanta ta tafi jikinsa a hankali ya saka hannunsa cikin rigarta sannan ya ja hannunta ya kai wani sashe na jikinsa daban wanda ya sakata jin gabanta ya kwonci kwonci ya fadi, aman da yake yanzu ta gama daukarwa kanta niyar gwada juriyar sai ta rintse ido ta shiga bashi hadin kai du da irin tarin tsoron kasancewarsu abu daya,


Hafsat dake jiran amsa shiru shiru haushi ne ya isheta, cike da jin haushi ta ajiye wayar kasa ba saman bed dinta ba dan kuwa an hanata ajiye waya kusa da kai dan babu kyau yana hadasa rashin lafia

Kwonciya ta yi saman hannunta na dama bayan ta gama adu.ar baci ta yi shiru tana kallon waje daya

Wani uban tsaki ta ja ta mike ta zauna saman gadon tana kallon waje daya

A fili ta saki wata yar karamar dariya kafin ta tafa hannayenta, hannun nata ta dago ta zunguri kanta a fili ta ce" Hafsat baki da mutunci, ke da zaki yi baci kina mai yabon ma.aiki aa sai kawai ki je duniyar baci kina hangen rayuwarki ta Bodyguard? Rayuwar ta hatsari? Wace har harbi akai maki a can? Wajen da kika hadu da dan rainin hankalin nan wato Abdul?

Kanta ta girgiza ta ce" to ki yiwa kanki fada, ki yi aurenki ki tafi abinki, ki je ki yiwa BS biyaya, .....

A daren nan ta jima tana kokowa kafin baci ya dauketa , hakan ya sa da asuba sai da mama ta shigo dakinta da kanta ta tasheta tana yi mata fadan cika dare dan kar ta fara makara a sallah kuma!


Ranar Lahadi da yama wajen karfe biyar Hafsat ta gama shirinta tsaf cikin sabin suturunta sannan sabin shiga a wajenta wanda ta mayar shigarta na yanzu wato Abaya

Ta yane kanta, fuskarta ta gyarata daidai misali ba abinda ta saka mai yawa ko mai daukan hankali sosai aman a banza dan kuwa irin yanda hankali ke kaiwa kanta abin ba.a cewa komai

Ta jima duke dakin malan tana shafa fatiyar adu.ar tsarin da yake ta binta da ita, shi kam dan an fito masa da cewa haka zata yi ta zama a gida sannan aka daure shi cewa ai Allah ke tsarewa da shi aka bi, da ba zai taba yarda ta fita ba sai dai idan za.a kaita dakin mijinta


Sai da ya gama sannan ya dauki kudi jika biyu ya bata tare da cewa ta shiga taxi idan ta gaji

Mama dake tsaye murmushi kawai take zubawa, a ranta kuwa fadi take wai a nan malan gani yake yana mugun kokari na boye soyayar yar tasa, yanzu ba fita bane zata yi? Ta tabata ta siyarwa kanta jaje kennan, idan kuwa maman malan ta yarda ta kai magariba to fa tabas zata ga malan a bayanta ya je nemanta

Sai da ta rakata har tsakar gida, kiri.kiri mai dakin tsakiya ta yi dariya a bayane sannan ta ce" wani lamarin sai a gidan mu, yaro ya je bariki ya dawo a ci gaba da ririta shi ana kara tura shi wani barikin

Ikon Allah ko kallonta Hafsat bata yi ba bale ta nuna ta ji me ta ce ko ta tankata, wannan abin shi ke kara basu haushi dan irin ta tanka mutun din nan irin na da a yi ta masifa har yayansu su kai mata duka su ce ta yiwa masu rashin kunya basa samu, du inda ta je din nan ya kware su dan magana ba irin wada basa yaba mata aman sai ta zama tamkar dutse ta ki motsi ta ki nuna ta ji bare har a yi fitinar da zata fitar da malan ! A haka basa tunanin zasu ci galaba a burin sakawa uban ya tsaneta harma ya koreta, wau shi malan karfin imani da daukan kadara ko? Yarinya ta je yawon ta zubar ta dawo masa aman ba wanda ya ji inda ya yi mata fada da daga murya ma bale a yi tunanin duka da kora, aa sau nasiha da nuna soyaya!

Tsaki ta ja masu mai karfi sannan ta ja gefe ta tsaya tana kallonsu tana son jin me za.a cewa Hafsat

Mama ta kali Hafsar fuska a hade ta ce" *ANMIH,* ki tabata magariba ta yi maki a gida in sha Allah, Allah ya tsare ki da dukan sharin abin shari, Allah ya kare ki ya shirye ki

A hankali Hafsat ta amsata da amen Mamana, sannan ta juya ta sa kai ta fice tana dariya cikin ranta, sarai ta gane nufin matar babanta so take ta tankata a dawo kada mata rashin mutuncin, bata san Kutkale da horon zama Bodyguard ya horeta zama kurma sannan makauniya gaban du wani abinda ta yi niya, sai ta yi niya zata tanka koma menene, idan ta ki ba zata tanka komai ba walahi!


A hankali take tafia da pos fara kal a hannunta har ta isa bakin titi
Tana tsayar da taxi ta fada masa Butik din da zai kaita sannan ta shiga gidan gaba ta daura belt ya ja suka kama hanya

Kanta ta sada dan irin yanda fuska da yawa ke binta da kallo irin kugun kallon nan mai sakawa a fadi,
Ta san kallonta suke dan su gane wai ita ce ko ba ita ba?

A haka mai taxin ya tsaya ta cire kudinsa ta bashi ya bata canji a cikin kudin da Malan ya bata

Sai da ta daga kanta ta karanta tankamemen rubutun dake jikin Boutik din kafin ta zagaya a hankali ta je hanyar shigar

Matar dake tsaye da abin caje mutun ce ta cajeta sannan ta shiga
Sai da ta yi tafia mai dan tsayi kafin ta tura madubin wajen ta shige
Zuwa ta yi wajen accenseur ta shiga domin inda zara yi siyayar dole shi zai kaita ki ta yi ta hawan matatakala har sai ta hau hawa tara!

Tana fitowa a nitse ta taka ta je wajen da ake siyar da liptom din, lipton din malan kennan, wanda yake anfani da shi

Gidan Lipton din kansa abin kallo ne, kwaya daya ne ta siyo aka saka mata a jakar Butik din, sannan ta fita ta nufi ainafin aiken da akai mata wato siyen shada gizner ta babar sallar dake karasowa tata da kuma ta yayarta wace yayar tata ce da kanta ta kawo mata kudin kan ta je ta siyo masu ta kai masu wajen mai dinkinta

Tana shiga wajen mai tsaron wajen wani bature ne jajajir da shi da gilas dinsa na karin ganni yana zaune da jaridarsa a hannunsa yana karantawa da ganninsa saurayi ne mai jinni a jika hutu ya kwonta masa

Wajen shadojin ta je tana dubawa cikin nutsuwa ba tare fa ta yi kwaramniya ko ta tsaya a cito mata ba

Tun fa ta shigo yake kallonta, dan da yawa wasun idan suka shigo sai su wani zarto wajensa su shiga tambayarsa inda zasu je su dauko abinda suka zo nema bayan ga komai a ajiye idan ka zo zaka kala ne a katon screnn din kana dudubawa har ka samu wace ta yi maka sai ka nuna a ciro maka ka biya kudin ka juya abinka aman sai an yi ta basu wahala

Mai ruwan maroon mai manyan zane ta tafi da ita, dan haka sai kawai ta danna daidai ita sannan ta juya ta je wajen biyan ta ciro kudin a pos dinta ta mika ta tsaya tana jira mai gidan nasu ya bata canjinya ta juya abinta

Canjin ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login