Showing 39001 words to 42000 words out of 154870 words

Chapter 14 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1119

da Elhaj ake kiransa, kai harma matansa, sai dai kuma a yau Shi Abdul da ya fadi kalmar sai ya ga kamar da nufin wulakanci ya fada ko da niyar zagi, domin dai *bako* shi ake kira da Elhaj a saudiya, a dan yana kiransa dad, ne ko yace da shi Uba, ko dan tsakaninsa da mahaifinsa, aman a yau ya kire shi *Elhaj*,

Murmushin yake ya saki ya ce" aman ya kana mai guri, ka zo kuma ka tsaya a kofa?

Abdulma ya sakar masa murmushin ya ce" ka san, bawa na iya malakar guri, sai dai ya zamo masa fage....wato fili,
Yaya maganar kayan nan, an saka su du inda ya dace?

Elhaj ya gyada kai tare da bashi gamsashiyar amsa,

Abdul ya mika masa hannu da niyar yi masa salama,

Har sun juya sun fara tafiya ya juyo ya ce" *ni ina mutuniyar, Baby kennan sarkin son dadi, koda yake, dadin ce*

Wata dariyar Elhajin ya saki yana sosai keyarsa har Abdul ya shige motar suka zo suka tashi motar Elhaj na tsaye suka bar wajen,

Hankici ya ciro ya goge zufar dake goshinsa, kafin ya danna kira a wayar dake hannunsa,

Ana dagawa ya ce" bafa zan iya wannan lamari da yaron nan ba, kamarma ya san me ya shiga tsakanina da baby ka ji maganar da ya fada min?

Shiru dai ba amsa kamarma an kashe kiran,

Sauraronsa da yake ya saka shi yin tsitt, sai dai maganar da Hafsat ta fada ya saka shi saurin kallonta,

A nitse ta ce" in dai munafukan ne, ba zasu yarda su ja maganar a waya ba Sire,

Da sauri ya dube ta, abin kunnenta ta nuna masa,
Kan uba, yaushe ta lika masa abin sauraro, wato shi ya yarda ya shige jikinsa ya laka masa abin sauraro ta haka, ita kuwa ta saka masa a lokacin da ya cika shi ymta matso tana yin kamar tana kakabe masa jikinsa,

Murmushi ya sakar mata, jin wani irin birge shi da ta yi, yana son ya ga mutumen da ya san ciwon kansa walahi, hakan na masa dadi sosai a rai,
Wani irin attention dinsa yarinyar nan ke kara ja du haduwarsa da ita daga jiya zuwa yau,
Yana kallonta tana kallonsa har aka kai shi wajen da zai sha caputulo,

Fita ta yi ta saka aka ajiye masa saman table bayan ta yarda da hakan ta kimtsa wajen shan ta fada BS ya fada masa suka fito suka shiga wajen,

Zama ya yi ya dauki jarida ya shiga karantawa, hakan ya bata damar karasawa kusa da BS suna dan dube duben yannayin wajen da mutanen dake dan shawagi a wajen,

A hankali ya ce" kar ki mance karkashinsa kike, kar ki manta uban gidanki ne a yanzu, yana da damar yi maki tsawa, wulakanta ki, ya taka ki, du abinda yake so, ke kuwa dole ki yi hakuri,
Bana son abinda zai jaza maki matsala a wannan mission din, bana son dalilin haka a taba lafiarki ko kudin da za.a biya ki, fatan kin fahimta,

Sai da ta dan waiwaya ta hango shi, ya kare fuskarsa dai da jaridar hannunsa yanda suka bar shi haka yake ta juyo wajen BS ta ce" damuwarka kennan? Ni damuwana na yi na gama na samu liberty din fita kamar kowa,

Idan har kika bata mission din nan kin san da baya za.a maida ke, jiya me ya hada ki da shi ya fito nemanki haka? Kar ki yarda kuma ya yaudare ki, domin kin san aiki ya hada ku, daga shi babu wani, koda ya yaudare ki toh ya kare da ke ne,

Tsai ta yi tana dubansa, shifa du wani waje ya nufa, shi fa tarin kishi ke dawainiya da shi,, dan haka ta girgiza kai ta kuma duban cikin cafetaria din dan gannin ko ya fara shan caputulon?

Sai dai abinda ya bata mamaki, irin zaman nan dai da yannayin rike jaridar da ya yi tun na farko bai gyara ba, bai canza ba,
A hankali ta matso ta kurawa hannayen ido, ba damar gannin kafafuwan domin table din rufafe ne kuma mai girma,

Hannun ta kara kurawa ido kafin gabanta ya fadi,
Da gudu ta nufi cikin ta shiga da sauri ta karasa ta warce jaridar dake hannun wanda ke zaune a wajen da ya dace ace Sire Abdul ne ke wajen,
Gabanta ne ya fadi wannin wani dan kyakyawan saurayin da ba shi ba zuru sai zarar ido yake,
Irin juyowar da ta yi ta dubi BS ne ya saka shi zaro ido domin ya fahimci me hakan ke nufi,

Da sauri ya bude yar karamar computer ya danna abin localization dan samun inda yake dan kuwa jikin rigarsa suka laka masa abin,

Sai dai abin haushin yana karasowa inda ta dora kafa daya tana bin saurayin da kallon takaici ta dago ta dube shi ta ce" mutumen da ya iya guduwa a irin tsare shin nan da muke, idan har ya yi gigin bari mu gane inda yake ta hanyar barin abin localization a jikinsa ai da ya zama lusari,
Rigar ya yiwa wannan saurayin kyautarta da sharadin ya zauna ya kame da jaridar nan na wasu yan lokuta,
Shi kuwa da yake banza ne ya zaunan kuwa!
Ta karashe tana mai dukan table din da karfi yannayinta na nuna tsantsar bacin rai na rainin hankalin da Abdul ya yi masu,

BS kam dubanta ya yi cike da kulawa, gannin ranta ya kai kololuwar baci ya saka shi yin gaba yana mai cewa" ki hanzarto mu je nemansa

Sai da ra mike ta bi wajen da kallo, haka kawai zuciyarta ke fada mata yana wajen, sai dai bata ganshi ba, bata ga alamunsa ba, dan haka ta juya ta bi bayan BS ta bude bayan motar ta shiga suka daga suka nufi gidansa ko can ya koma,

Zuru ta yiwa waje daya cike da jin haushin kanta, yama aka yi ta fito ta bar masa wajen bayan ta gama fahimtar mutumen lale na cikin hadari kuma shi da kansa yana mai kara saka kansa a hadarin? Yama aka yi ta yi saken yin hira a lokacin da ana iya harbe kan wanda suke baiwa tsaro?

Kanta ta girgiza ta jinginar da jikinta jikin motar ta lumshe idannuwanta,
Murmushi ta saki a fili kafin ta dubi BS dake bin du wani motsinta da kallon mamak8n yanda take abubuwanta, ta ce" ka san me? Shi din, bayan sannin abinda yake yi da ya yi, ya kuma kware a aikinsa, tabas jarumi ne!

BS ya kauda dubansa daga kanta ya mayar bakin titi har suka karasa gidansa,

Du inda suka san zasu same shi a cikin gidan sun duba, aman ba shi ba alamarsa,
Sai a lokacin kuma suka fara afkawa cikin tsoro, tsoron da suka shiga ba na komai bane sai na tunanin idan fa dauke shi aka yi aka raina masu hankali da wannan saurayin?
A lokacin da ta yi wannan tunanin sai da hanjin cikinta ya motsa tsabar kaduwa da ta yi,
Ba shiri suka juya wajen, sai dai saurayin na nan bai wani tafi ba, da alama wajen nasu ne, nan yake wuni idan ya zo, yana ta aikinsa da mutanen wajen,

Jiki sanyaye suka koma gidan nasa, du sun yi wujiga wujiga a tsakar gidan, har sun yi kiran GN sun sanar masa inda cikin tashin hankali ya nemi layin ogansa ya fada masa.......

Muhammad kansa tsaye yake cike da tsoron fitowarsa , shi fa ya zama na daki, baya zuwa komina, hakama Ni.ima sun tsatsareta sun canza mata yannayin gadon dakinta, kai windows din gaba daya sun rufe shi ruf irin yanda ba za.a iya hango na ciki ba du jarabar mutun,
Tun da ta ji hayaniyar ana neman mijinta hankalinta ya gama tashi, gashi babu waya kaf gidan du an cicire sai tasa da ta masu tsaronsa kawai, ta rasa ina zata tsoma ranta ta ji sanyi dan kuwa tana son fita sun bi sun tsare sun hanata fitowama bale ta nemi yanda zata yi ta samu labarin inda yake,

Hafsat kam, haka ranar nan ta daketa, yama ta yi ta kasa tsaye ta kasa zaune, ita fadan da GN ke yi tamkar zai ci namansu danye ba shine damuwarta ba, wani irin abu take ji mai shige da matsannanciyar damuwa kan rayuwarsa,
Tun a jiya da ta ji kadan daga cikin labarinsa take jin wani irin tausayi da jinkai a gare shi, tsaye take, ta yi shiga ciki da fitowa ya fi a kirga,
Bata kai ko ruwa bakinta ba bale cikinta ya tsamaci wani abin,
Ta gama fita a hayacinta ga GN fada kamar ya shako su ta computer da ya yi vidio call ya yanyanka su ya huta,

Wasa wasa har aka fara kiran sallar magariba, aka gabatar da sallah aka gama, inda duhun magariba ya fara sanyo kai

Wani babur ne aka budewa gidan ya shigo, wani irin hayaki babur din ke yi da wani shegen kuka irin ya tsufan nan har yana faman bugawa dan kansa,

Gaba dayansu ido suka bi babur din da shi da mamakin ya aka yi aka budewa wannan babur haka gida ya shigo?

Tsayar da babur din ya yi ya sauka,
Kayan dake jikinsa kansu ba da su ya fita ba, du ya yi wani budu budu da shi haka yannayinsa na nuna a matukar gajiye yake,

Basu gama yarda da shi bane sai da ya karaso inda suke tsatsaye da shirin ko ta kwana ya ja ya tsaya ya rike kugu yana mai bin su da kallon nan na son kure mutun kafin ya sakar masu murmushin nan na raini ya ce" hi!

Dankari, gaba dayansu da mamaki suke binsa, kafin du a nufe shi masu bashi tsaro suka fara tunkararsa inda BS ne shugabansu shi ya dube shi da girmamawa da yannyi na son jin gaskiya ya ce" sire, aman ina ka shiga? Me ya same ka haka? Wannan suturar fa? Wannan yannayin fa? Bamu ga fitarka ba sai nemanka muke tun da safe?

Abdul ya gama sauraronsa da kyau, kafin ya kai dubansa wajen Muhammad dake saurin karasowa shima da yannayin murnar gannin shi da aka yi,

A hankali ya ce" kana zance a wajen aiki yaya zaka gane na fita? *baka san aikin ka ba Bodyguard soldier*

Yana kokarin ratse su sai ga Ni.ima da gudunta ta fito, inda macen dake bata tsaro ke biye da ita tana mai son dakatar da ita kar ta karasa wajen nan aman ina

Tana zuwa jikinsa ta shige ta fashe da kuka,

Sororo ya yi yana dubanta, basu gama gannin hakan ba ta cika shi da jin haushi ta juya ta dale mai bata tsaron nan da kallo inda gaba dayansu sai da suka zaro ido, tunbama Hafsat dake cike gefe tana kallon du abubuwan dake faruwa,

Cikin muryar kuka ta ce " ya zaki hana ni fitowa na ganshi? Ke din banza ke din wofi? Aikin ki bani tsaro ba bani umarni ba, dan me zaki hana ni fita kuma yanzu da ya zo ki hana ni fitowa ganninsa? Mai kashe mun ya jima bai kashe ni ba a kansa!

Gaba dayansu kallonta kawai suke, inda Hafsat har wani sarawa kanta ke yi na irin abubuwan dake faruwa a yau din nan,
Haushi bai kara kumeta ba sai marin da aka wankawa abokiyar aikinta sannan aka wulakanta ta dan kawai ta yi hani da kar ta fito wajen da ake iya daukan ranta a banza?

Idannuwanta ta rintse , gannin ya cika hannun Ni.imar kuma ya nufi wajen Muhammad da abinda Ni.ima ta yi ya kashe masa jiki yana dubansa,

Yana zuwa sukai gaisuwar larabawa kamar yanda suka saba,
Muhammad ya rike hannunsa da kyau ya ce"ka je ka yi wanka,

Murmushi ya sakar masa kafin cikin dabara ya sinar masa da abin hannunsa , da ido ya yi masa signal din yana zuwa,

Dubawa ya yi ya ga du sai kallonsa suke , da hannunsa ya yafito Hafsat dake tsaye fuskarta tamkar ta fashe da kuka dan haushi ya ce" uzurina na je, wanda bana son bindina na biye da ni....ku gane man, yanzu na dawo gidan farautana, zo mu je ke mai kula da ji ki duba dakina, na wuni bana ciki kar a je wani ya yi ajiya =? ?
Ya karashe yana mai kane ido daya ya juya ya yi gaba ba tare da ya baiwa BS amsar tarin tambayoyinsa ba, ba kuma tare da ya kula irin abinda Ni.ima ta yi ba,
Haka suka juya suka bi bayansa, sauran suka koma bakin aikinsu,
Haka mai tsaron ni.ima ta kuma bin bayanta tare da namijin cikin yannayin nuna halin ko.in kula da abinda ya faru da ita domin qn hore da hakan na iya faruwa da su,

Idan Hafsat ta tankawa abubuwan da ya yi, to tabas rigar jikintama ta yi magana,
Haka ta fara shiga dakin , ta nufi wajen bed dinsa ta fara bincikawa, ta koma dakinsa na baci ta bincika, ta dawo ta shiga bayi ta hada ruwan wankan bayan ta bincika ta kuma gyara komai, ta fito da niyar barin dakin ta ganshi tsaye daure da tawul, jikinsa sai warin rana yake da alama fitar nan da ya yi ba karamar wahala ya sha ba,

Murmushi ya sakar mata ya ce" yau ba fada ne my Bodyguard *budurwar dan ta.ada?*

Dan tsai ta yi, kafin ta girgiza kai ta kara daga kafa zata fita ya ce" *Nadia abdallah* (wato sunnan da aka basu kennan na Hafsat a can gidan formation)
Ya dan taka ya bude bayin yana mai cire tawul din jikinsa gaba daya sannan ya ce or *Hafsat Muhammad* , ba zaki ban muryarki na ji ba?


Da wani irin sauri ta juyo , juyowar da ta tsorata ta, ta.......




.............comment nah?.......
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 8??



*HELLO READERS, DAN ALLAH KAR KU DAMU DA YAWAN PAGES, DU RANAR DA NA GA DA HALI ZAN KAWO MAKU 2, AMAN A HAKANMA KUN GA AI DA YAWA>?#?*



Irin dirar da ya yi ya kare ainahin wajen da ba.a son gannin da tawul dinsa kafin ya dafe goshinsa ya leko gaba dayansa yana daura tawul din ya dubeta irin yanda ta rintse ido, bata ga ainahin abinda ba.a son a gannin ba, aman ta ga cinyoyinsa, kai harma da kusan cibinsa ta gani, ga kirjinsa dake dauke da wani gashi tsakiya har zuwa cikin tawul dinsa, wanda da gangan yake aske sauran ya bar iya nan su wani bada kala,

Kansa ya dafe da hannunsa ya fito daga bayin ya karaso inda take tsaye ya tsaya sosai daf da ita, ba abinda ya dame shi da irin yanda jikinsa ke bugawa sanadiyar wuni cir a wajen da sai shi kawai ya sani, ba wanka ba iska, gashi garjejen kato me zai hana shi bugawa? Ya dubeta da kyau ya ce" yanzu, fisabililahi, banda soyaya da dan ta.ada da kike wai harda neman gannin ogana? To me kike son ganni in ba fitina ba, Hafsat shekarunki duka duka 21 fa, kin shiga ta da biyu yau da wata hudu da kwana ashirin da biyu da awa ashirin da minti goma sha hudu da second tik tak tik tak tik tak......., yaushe kika san dadin namiji haka? A gidan yarin *KUTKALE* , ko a yawon neman fada lungu lungu? Ko dai da saurayin naki ne dan gidan abansa? Ko mijin da aka baiwa ke sadaka ya dana ne can dama a biye ba.a sani ba?

Da sauri ta dube shi, duba irinnan tsoro, da fargaba,
A hankali ta ce" kaka je neman labarina ne? Dama fitar da ka yi tawa ce?


Wata dariyar da ya jima bai yi bace ta kubuce masa, kafin ya dubeta da kyau ya ce" du na rasa aikin yi, na tashi na fita zuwa neman labarin ki? Kin manta wanda ya dauko ki daga gidan yarin gaba dayansa a tafin hannu na yake? Kin manta yanzu duniya ta zama ta yanar gizo?
Ina zaune sai da na gama hutawa, na shiga yanar gizo na bincika wacece ke, nan aka bani labarin da na kasa hadiyewa, dan haka ina zaunen nan ina shan shayi hankalina kwonce na danna kira aka bani cikaken wacece ke, duka a yan mintunan da basu cika sitin ba, wato awa! Yaya zaki yi tunanin darajar ki, ko haye min da kike zai saka har na yi irin fitar nan da na yi dan sannin ke ko wacece?

Ba ke ce yar gidan malan ba? Wace kika ci sunnan mahaifiyarsa, kin taso cike da abubuwan mamaki, kin kare a soyaya da dan ta.ada da dan gidan dad? Abinda ya fi tsaye min a rai shine dan ta.ada, ta yaya? A ina kika gan shi? Na kasa yarda da hakan, ni ba sakarai bane da za.a bani wannan labarin na hadiye, ki sani wani labarin duniyar medias, da bakunnan mutane basu isa su baka ba, kamar yanda kika ji wasu abubuwan a kaina, baki isa a duniyar bincike ki san wasun ba sai dai idan ni na fda maki, haka naki labarin rayuwar ban isa na san wasu abubuwan ba, du irin fitinata da neme neme na, du karfina da dukiyata sai idan mai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login