Showing 129001 words to 132000 words out of 154870 words

Chapter 44 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1163

wani lokaci ya yi kuradin hakan, yakan zauna a kasa saman kacef ya wara kafafuwansa ya cire mata manyan suturunta ya zaunar da ita a tsakiyar kafafuwansa su yi ta buga gem a wayarsa
Sukan yi baci a haka,
Wani lokacin zai saka kudi ya ce idan ta kayar da shi, haka zasu yi ta kokowa suna karawa yana kilkila dariya yana karawa

Tun tana kawar da lebenta daga bakinsa har ta koyi rikewa da kanta,
Ita kanta ta koyi tsotsar lebensa tamkar ta samu halewa

Sai dai wani lamari fake bata mamaki.....
Abdul bai taba zarce haka da ita ba,
Bata taba yi ba, bata taba maganar haka ake yi da wani ba hasalima a makarantar islamiya ta fahimci miji na zuwarma mace ,
Zaune take da Abdul, tana gannin irin yanda yake da mugun son mu.amalar taba jikin mace
Abubuwa da dama ke shigo mata kwakwaluwa
Me ke faruwa ne?
Shin haka yake da Na.imarma?
Me yasa da dama lokuta sai ya rikice ya damki jikinta sai kawai ya jirkice ko ya mike ya fita?
Me yasa wani sa.in yake saurin sada kansa idan ya kali halitar jikinta?
Shin auren bakin nan ya tsaya ko kala kala ne?

Ta fara yiwa kanta tambayoyin abinda ke faruwa tsakaninta da Abdul

Basu taba furtawa juna kalmar so ba,
Aman shakuwar dake tsakanin su ta kara girmama ta yi nisan da su kansu basu ankara ba

Basu taba kawo maganar BS ba, basu taba maganar wani bayansa ba ,
Bata taba yi masa maganar matarsa ba,
Bai taba kwana a dakinta ba hasalima bai taba hawa shinfidarta ba

Bangaren Abdul kuwa yana cikin wata irin rayuwa ta matsi,
Bukatarta yake , so yake jininsa da nata ya gwaurayu su zamo abu daya so yake ya buda ido ya ganta a matsayin wace ya mayar tasa shi nata
Ya rasa yaya zai yi da abinda yake ji a kanta
Hafsat dai ya gama salamarwa cewa, ya yi zaman kareta , hanata zama da Bs, tsayuwa a duk lokacin da zasu iya yin hira dan ya hana su! Ne kawai bisa dalili kwaya daya tak
Wannan dalilin shi ne ya saka ya kasa mayar da Hafsat mace irin na kowa, shi ya saka masa mugun jin abinda yake ji a tatare da ita
Yana wuni idannuwansa bude idan ya tina cewa waninsa ya wulakanta masa ita!

Yaya zai yi? Yaya zai yi ne?

Yau ta kama daren Laraba

Wajen karfe biyu ya mije da kyar yana layi ya tafi dakin Na.ima

Tarar da maganin ciwon mara ajiye kusa da bed dinta ya yi ,
Audugar mata kuwa ajiye dan nesa da bed din nata ita kuwa ta samu baci

Tsuru ya tsura mata ido, haka kuma audugar, gaba daya jikinsa rawa yake, hankalinsa ne ya ji yana kara tashi fiye da yanda yake tunani

A hankali ya kai zaune yana kallon yanda jikinsa ke rawa sosai da sosai
Zuciyarsa ce ya ji tana wani irin gudu

A hankali yake saka lebensa na kasa cikin bakinsa ya shigo tsotsa

So yake ya saka kanshi hakuri a haka sai dai abin ya kasa samuwa

Da sauri ya mike tsaye yana jin gabansa na faduwa
Juyawa ya yi yana wani irin takun sauri ya nufi dakinta

Idannuwansa har rufewa suke son yi tsabar balakin da ya kuno shi

Yana zuwa ya.......

>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 9??



A hankali ya ce" Hafsat

Hafsat dake lunshe idannuwanta da ta ji sun yi mata mugun nauyi ta amsa can kasan makoshi tana sauraronsa

Abdul ya ce" na gode

Shiru ta yi, bata san godiyar ko ta meye ba, ita dai da son samu ta yi ya yi shiru ta yi baci

Abdul ya kuma cewa" Hafsat?

Da kagauta ta dago idannuwanta, da irin duban ba zaka barni na huta ba?

Abdul ya sakar mata murmushi ya ce" Allah ya yi maki albarka

Idannuwanta ta lumshe a hankali sannan can kasan makoshinta ta amsa da amen ta rufe idannuwanta ta shiga fafutukar neman baci ido rufe

Sai da ya ji lumfashinta ya sauya da na dazu sannan ya mike a hankali ya gyara mata kwonciya

Zuwa ya yi ya kuma dauro alwallah ya dawo ya hau salayarsa,

Sai da ya yi raka.a biyu kawai sannan ya zauna ya shiga jan carbinsa

Ya jima yana jan carbin, kafin yake kai dubansa wajen wayarsa dake ta haske tun dazu

Daukota ya yi ya duba,
Message ne daga number mahaifinsa

Message din ya shiga ya ga kamar haka" Allah ya kara budi Abdallah, mun gode

Bakinsa ya tabe ya ajiye wayar ya koma ya ci gaba da jan carbinsa

Sai da ya kai har kusan karfe biyar sannan ya ajiye ya mike ya dauko maganin dake cikin kayansa

Zama ya yi saman salayar, kansa ya tsayar waje daya yana tunani
Zako ta yarda ta sha?
Zata yarda ta sha wannan maganin kuwa?
Idan Na.ima ta yi masa biyaya ya tabata dan tana yi masa mugun son da ba zata iya musa masa komai girman bukatarsa ba
Aman Hafsat fa? Ya sani sarai ba zata yarda kawai ya balo mata magani ya ce ta sha ta yarda ta sha ba tare da ta san ko na meye ba,
Abincin mai aikinsu bata taba ci ba a kulun sai dai ta cacaka ta mike sam ya rasa me ya sa bale har ya sameta ta nan
Idannuwansa ya rintse,
Shi kam bai san yanda zai yi da lamarin nan ba,

Mayar da maganin ya yi ya koma saman bed din ya kwonta ya rungumeta a jikinsa

Bacinta take hankali kwonce, lumfashinta da dumi dumi sosai yake sauka hakan na nuni da zazabi ke son zubo mata

A takaice dai wannan dare Abdul ya raya shi idonsa biyu, ya raya shi yana begen fulawar dake gabansa kwonce, ya raya shi yana mai neman mafitar yanda zai yi da ita ta sha maganin da yake baiwa yar uwarta, yana son haihuwa fa, yana son samun yaya, da zai samu maza ......sai dai ya san ayya sai ta tabata a kansa, irin yanda ya yi wasa da yayan mutane yana tsoron hakan ta kasance a kansa!


Sai bayan ya gama sallah ya tasheta,

A hankali ta iya mikewa ta sauko daga saman bed din nasa

Kanta na kallon kasa ta samu ta yayumi abin rufar tasa ta nemi hanyar ficewa dan zuwa dakinta

Da sauri ya rike hannunta yana kallonta ya ce" ki zauna a nan Kauriyata plz

Hafsat ta kale shi da kyau sannan ta ce" nan bangarenka ne Abdul, wanda ba ni daya nake da kai ba, matarka na iya shiga du lokacin da muradin hakan ya taso mata, inma tambayeka na taba kwana a nan ne? Ni dakina zan je

Murmushi ya yi yana kallon bakin tsiwar nata, ita dai bata sasautawa kennan dai, du irin halin nan da take ciki na wahalar da ta sha a jiya da dare bai hanata buda dan bakinta ta dan juya shi ba

Murmushi kawai ya yi sannan ya bita da kallo har ta fice a dakin

Wani murmushin ya yi a ransa yana godewa Allah da ni.ima da ya yi masa, du irin abubuwan da ya ringa aikatawa sai Allah ua bashi matayen auren dake rufe ruf abinsa, shi dai haihuwa ne kawai ba zai yi na, ya hakura da haihuwa.


Hafsat na komawa dakinta wayarta ta dauka ta yi kiran number auntynta
Kuka ta fashe mata da shi kafin ta ce" aunty ciwo nake ji

Shiru aunty ta yi, ta dan jima sannan ta ce" Hafsat, kina ina ne? Mijin ki ya zo ne??


Hafsat ta turo bakinta ta ce" eh ya zo, yama jima da dawowa ai, aunty ni ki zo dan Allah ba zan iya tafia ba, ki zo ki kaini wajen Malan!

Aunty ta sauke ajiyar zuciya tana mamakin yaya aka yi Hafsat ke barambarama haka? Koda yake ba sai ta yi kawayen da zasu koya mata yanda zata yi ba sannan zata gane me yaren ke nufi

Cikin hikima aunty ta kwatantawa Hafsat cewa hakan ba wani abu bane zai fice, sannan ta koya mata yanda zata kula da kanta
Sai da ta kwadaita mata ladan hakan sosai sannan sukai salama

Yanda Aunty ta koyar da ita haka ta yi, ta tatare zannin gadon ta kai mashine din wanki,
Sallah ta gabatar

a hankali ta samu ta yi shinfida sannan ta haye gadonta ta nade

Can wajen karfe biyu na rana ya shigo dakin, kwonce take tana ta bacinta hankali kwonce

Abincin da ya shigo da shi ya ajiye sannan ya karasa kusa da ita

A hankali yake shafar gefen fuskarta har ta buda idannuwanta

Murmushi ya sakar mata yana kallonta

Mikewa Hafsat ta yi daga kwoncen tana kallon agogo

Idannuwanta ta zaro tana kallon agogo

Bata yi magana ba ta sauka daga saman gadon ta je ta yi brushing

Tana fitowa ta karasa inda yake zaune

Hannunsa ya mika ya janyoya jikinsa yana kallonta, yanda take sasada kanta abin na matukar birgeshi, ita kam komqi ta yi na jan ra.ayinsa sosai

Abincin da ya shigo mata da shi ne ya miko mata ,

Zaunar da ita ya yi ya shiga kokarin ciyar da ita

Sai da ta kusan rabi ta ji cikinta ya dan daure

Dafe cikin ta yi kadan, sai kuma ta ji ya saki
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta kai dubanta wajensa
Gani ta yi madaukakiyar damuwa a tare da fuskarsa, gannin ta saki cikin nata har sai da ya sauke ajiyar zuciya

Bata nuna komai ba sai ci da ta yi cikin nutsuwa har ta gama

Tana gamawa ya fice da abincin,

Sai da ya ajiye abincin a kicin ya jinginar da bayansa, ajiyar zuciya ya ringa saukewa domin irin rike cikin da ta yi gabansa ba karamin faduwa ya yi ba, me hakan ke nufi?
Tsoro ya ji kar a je maganin da ya zuba mata a abincin dan dabara ya saka mata rikewar cikin

Watsar da abin ya yi ya nemi walwalarsa, karshema fita ya yi ya tafi gidan malan cike da nishadi


A kwanaki bakwai da Abdul ya yiwa Hafsat sun matukar shakuwa
Shakuwa fiye da ta da, domin kwana daya rak ya saka mata ta huta kafin ya shiga horar da halitarta irin tasa

A hankali ta ringa koyon al.amuransa, bata da sanya a abinda ya shafe shi, tana kafa kafa da komai nasa, sai dai abinda ke damunta mararta na yawan yi mata ciwo bayan ba al.adarta ke kusantota ba, sam al.adarta na nesa dan bata ana jibi kawota gidanta ta gama

Bayan wata mu.alar aure da suka yi, Abdul ya kawo mata jus

Hafsat na sha ba.a dauki lokaci mai tsayi ba cikinta ya kule

Wata irin zabura ta yi jin mararta na kara rikice mata,
Da sauri ta nemi sauka a gadon gannin abin na kara hawar mata
Abdul da fitowarsa kennan daga bayi ya tarar da ita tsugune wajen bed din tana mitsitsiya

Da sauri ya ajiye kum din hannunsa ya nufeta gabansa na wani irin mugun faduwa..........yana zuwa ya........





Ku gane, situation din rayuwa na saka mutun da yawa zama wasu iri, zaka ga mutun na rayuwa irin ta bayahude, wanin na canzawa, wani kuwa haka yake tafia har ya tsufa ya koma ga mahalicinsa
Abdul na gudun haihuwa ne dan baya so ya sami mace ya wayi gari ya riski wani ya wulakanta masa ita,
Bai san cewa Allah mai gafartawa bayinsa ne, sannan idan ayyar ce zata kqsance a kansa bai isa ya hana ba, ba.aiwa Allah wayo
Dan haka zan so ku fahimci labarina....ku gane me ya kunsa.....godiya nake>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?>?p?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 0??



Da sauri Abdul ya nufeta, irin yanda take damkar cikinta sai da gabansa ya yanke ya fadi

Da sauri ya cicibata ya dagata ya dorata saman bed din dakin
Du ya bi ya rude, danna inda take rikewar kawai yake hankalinsa tashe

Hafsat dake neman ficewa a hayacinta ta yi saurin damke hannunsa, muryarta na wani irin rawa ta ce" Abdul zan mutu

Da sauri ya mike tsaye ba tare da ya yi wata wata ba ya wawureta daga saman bed din

Sai da ya nufi hanyar bayi da ita sai kuma ya juyo da wani irin sauri sauri gudu gudu ya nufi kofar fita da ita, daidai lokacin tuni Hafsat ta sume, ta fita a hayacinta

Gaba daya Abdul ya rikice, yana zuwa motar da ya bude ya sakata a nan ya lura da ta sume,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une...shi ne abinda ya fada da dan karfi yana kallon fuskarta da ta yi fayau da ita,
Bai wani lura da bai dauko mata hijab ba, haka kuma bai lura da rigar jikin nata doguwar riga ce mai siririn hannu rigar da ta bi ta fitar mata da surar jikinta sosai

Wata irin rufewa ya yi ya zagaya ya shiga mazaunin direva ya tayar da motar

Tuki yake na garari, yana yi yana take dokokin tukin,
A haka har ya karasa clinik
Yana zuwa ya fita a sitin ya kuma daukanta ya nufi cikin dakin likitocin

Tarbansa nourse din ta yi da sauri aka gurguro gadon mararsa lafia aka dorata

Da sauri wata daga cikin nurse din ta danna number docter dan fada masa an kawo urgence
Wani irin zama abdul ya yi kan kujerar dake wajen,
Idannuwansa ya rintse da sauri sakamakon wani irin dokawa da zuciyarsa ke yi,
Walahi rabonsa da ya ji irin haka tun lokacin da ya ga gawar kanwarsa, ya ga ta mahaifiyarsa, sai wanda ya ji a lokacin da ya gane amininsa ne bakin kumurcin da ya hana shi zaman lafiya

Yana nan zaune mutumen da yake docter ya zo ya shige dakin

Nurse din ce ta zo wajensa ta ce" asalamu alaikum

Da sauri ya dago ya sauke dubansa a kanta

Dan gyara tsayuwarta ta yi ta ce" docter ne ya ce a tambayo, shin wani abu ta ci? Sannan tana da ciki? Ta saba irin haka?

Tamkar wanda ke karantar bakinta dan tsai kawai ya yi yana dubanta,
Sai da ta ce" Malan are u ok?

Da sauri ya kawar da dubansa daga kanta, fuskarsa a yannayin hadewa ya ce" ban sani ba

Kara dubansa ta yi daga sama har kasa, yannayin shigarsa ya sakata yin gum da bakinta ta juya da sauri

Tana shiga ta tarar ta farfado aman sai birkidadoniya take ana tareta

Likitan ya gama sauraron abinda aka ce,
Da yake mai hakuri ne sai ya matsa kusa da Hafsat din ya shiga yi mata tambaya a hankali

Kanta kawai take juyawa idan eh ne ko aa ne

Kina da aure?

Hafsat ta gyada masa kanta
Yaushe rabon ki da al.ada?

Hafsar ta nuna masa hannunta wato yatsarta biyu
Tambayarta ya kuma yi kwana?
Ta girgiza kai,
Sati?
Ta gyada masa kai

Shin kin ci wani abin da baki saba ci ba??

Hafsat ta juya masa kai

Ya ce" dama kina irin haka??

Hafsar ta kuma juya masa kai alamar aa

Wajen da ta fi rikewa ya kurawa ido,
A hankali ya ce" kin sha wani magani ne???

Hafsat ta girgiza kanta tana ta mikewa tamkar zata kara sumewa

Dubansa ya kai wajen nurse din ya umarta da a yi mata hoton cikin da na.urar haskawar

Yana gefe yana kallo yanda suka ja rigar,
Sai da aka shafa mata wani ruwa ruwa mai mai sannan aka dora abin haskawar,
A hankali suka ringa bin shafafiyar mararta suna haskawa, lokaci daya kuma suna daykan hoton wajen da ya dace, doctern kuwa yana tsaye yana ganni da kyau

Sai da suka gama sannan ya amsa ,

Sai a lokacin ya tsira ruwan allura ya tsira mata

A hankali a hankali ta fara sauke ajiyar zuciya, a haka har ta saku ta ji ya lafa mata sosai da sosai

Sai a lokacin ta bi dakin da kallo, nurse daya ce can gefe kusa da docter, sai ita dake kwonce saman gado an rufa mata wani abin rufa wajen kirjinta

A hankali ta sauke kafarta daya, dayar ra miko ta sauko cikin nutsuwa baki dayanta ta sauka daga saman bed din
Mararta take ji ta yi mata wani mugun daurewa da nauyi,
Bata yi kasa da gwuiwa ba ta tunkari wajen doctern, shima lokacin ya ga ta sauko

Nurse din ce ta kamata ta zauna a wajen da ya nuna mata

Sai da ta yamutsa fuska domin yana kara murda mata kadan kadan sannan ta fuskanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login