Showing 48001 words to 51000 words out of 154870 words

Chapter 17 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1122

da idannuna, barci ya gagare ni, naa yi nesa da iyayena domin a lokacin suka koma wani gidan ni kuwa na zauna a nan,
Tsakani shekara biyu Mahaifina ya shirya tafia,
A cikin jirgin da ya shiga aka nuno shi anai masa vidio, inda ya nemi yafiyar mahaifiyata a baibai, sannan a lokacin sai da ya gama komansa a tsare, aka dauke maganar a tv aka nuno faduwar jirgin da yake ciki, wai ya mutu, ta hanyar shahada

Hawayen dake bin kuncinta ya bi da kallo, sannan ya ci gaba da muryarsa dake fita da sanyi ya ce" kennan a sakarkaru aka dauke mu? Ni da uwata!

Da mamaki ta yi masa wani duba,
Zamansa ya gyara ya ce" an taba mutuwa haka? Irin a dauke shi sai da ya gama komai sannan ya mutu!
Abdul Basid bai mutu ba saboda dalilaina kamar haka,
A cikin jirgin da ya fadi, dukan wasu abubuwan da suka shafi Abdul Basid an gan su banda agogon karfen da ya gada wajen babansa wanda wuta bata narkar da shi tono shi ake a cikin kasa, wanda baya yawo ba shi, bale tafia mai nisa, yana ji da agogon nan fiye da komai dan ji yake kamar yana tare da babansa ne!

An cire kudi, cefa milliard dari a cikin acc mai sunnansa dake kasar misrah a daidai wannan tashin hankalin wanda shi bai san ba ni ina da damar sannin hakanta dalilin girman aikina da darajarsa ina da damar sannin manyan sirrikan da suka shafi ahugaban kasama bale Abdul Basid,
Sai abu na uku, bayan gama takabarsa da Ummih ta yi, dif sama ko kasa ba manema, ba alamun su, gata yar dagwas, ga cefa, wanda duniyar nan ta zama ko baki da kyau idan kina da kudi za.a yi rububun ki, aman ko kare bai yi shayin giftar uwata ba,
Wannan aikin jinnin Ibrahima ne bama bari mu so abu wani ya so shi sai dai idan mun mutu>?&?
@&

Abdul Basid na raye, ya mayar da du wata dukiya tasa da sunana ya juyo da abokanan gabarsa kaina,
Ana farautar rayuwata dan a ci wannan arzikin ne, ni na tabata masu son kashe ni basu fi aminan mahaifina ba dan kuwa duka kaf arzikin da suke takama da shi din har yanzu sunna aiki ne a karkashina, wanda na tabata suna tsoron na tsige su rana tsaka, du cin da zasu yi basu tara na ci gaba da wadaka ba, gashi sun dogara da kudin, an hada ni da harkar mata, wanda da na ga abin ya yi yawa na shiga asibiti aka yi ta bincike ba.a samu wata malatin da zata hadasa min haka ba,
Hakan ya sa aminina ya dafe da nema min a cikin saudiya, har ya hadu da wanda ya fadi maganar da ta tino min da maganar da aka yi cewar za.a mayar da ni tamkar kare....
Shaidata ta biyu kennan,

Sai kashe min uwa da aka yi, ummih ta rayu da tsoron ko wasu abokannan harkar mahaifina ke bin mu da shari? Dan ban taba yarda, koda wasa na kara kokarin nuna mata wani lamarin da zai sakata zuciyarta bugawa, ta kasance jarumar mace, ta rungumi gawar yarta, ta rungumi ta mijinta da bata gani ba, sai take cike da tsoron rasa ni,
Ni kuwa ina mai kauce mata shiga dagar abinda nake ciki na irin hare haren da ake kawo min, aman cikin ikon Allah ta shige ta yi kane kane,

Tanbayoyina shi ne.......
Shin cikin aminnan Abdul basid ne?
Aa , Abdul Basid din ne da kansa ya ga na ki sakar masa arzikinsa kuma na ki mutuwa zai fara kasheta dan ya san idan ta mutu ta mutu da ni ne? Ko a sangartar tawa na janyo wanda ya harbe min uwata? Ni na kashe uwata?

Hafsat dake zaune ta dora kanta saman cinyarta ta fashe da kuka, kai, ina, dole ta yi kuka walahi, dama abinda ya gani, kuma ya rayu da shi kennan? Duda haka yakan yi murmushi, shin idan ya yi murmushi har zuciyarsa ne kuwa? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, wayo harta da lamarin matan nan an hada shi da shi ne?

Gyaran muryar da ya yi ne ya sakata tsagaita kukan, a hankali har ta yi shiru ta kuma dago da kanta ta tsura masa ido kamar yanda yake kallonta,

Sai da ya jima a haka sannan ya kawar da dubansa ya ce" *ke ce mutun ta biyu da ta san komai a kaina bayan Muhammad, na baki kadan daga cikin labarin rayuwata, wanda ya dace ki sani wato a dunkule....idan kina so ki fita ki fadawa kowa, idan kina so ki rike min sirrina dan ban yarda na baki labarina ba sai da na yarda da irin gwaje gwajen da na yi maki, ke ko dalilin daukan bullet din da ya dace na dauka da kika yi kin ci ki san ko ni waye dan haka ke nake son sannin labarin ki dala dala daga bakin ki*

Hafsat ta sauke ajiyar zuciya , ta dan motsa kafadarta ta lumshe idannuwanta kafin ta nisa ta shiga bashi labarin ko ita wacece,
Irin rayuwar da ta yi,
Irin hatsabibancin da ta yi,
Jarabar fada, kiriricew, rashin tsoro, neman fitina, rashin gudun bacin ran iyayenta har kawo abinda ya faru da ita da taintar kanta da ta yi a cikin *KUTKALE* , kawo inda take zaune a gabansa,

Ga mamakinta sai ta ga yana dariya, kamar ba shi ne ya gama bata labarin irin mumunar rayuwar da ya yi, da kuma irin yanda ake harinsa,
Hannunsa ya daga da jinjina ya ce" ashe ni da kauriya nake tare?

Idannuwanta ta fitar tana dubansa kafin ta girgiza kanta ta ciciba ta mike ta dauki magannin da ya ajiye mata nan ta juya a hankali ta fice a dakin,

Idannuwansa ya lumshe ya mike ya haye bed din da ta tashi ya kuma lumshe idannuwansa a fili ya furta" malan ka fa iya haihuwa Walahi....ina son mace marar jin magana=? ?


Hafsat kam na fita dakinta ta nufa,
Tana shiga ta nemi waje ta zauna nan kasa ta fashe da kuka, kana tunanin kana cikin tashin hankali da muguwar rayuwa sai ka hadu da wanda ya dame ka ya shanye,
Gashi dai bawan Allah, yana ji yana ganni abubuwan nan suka ringa faruwa da shi, kuma yana ci gaba da walwala da tunanin samun sauki nan gaba da fama kan ya ga haske ya gurfanar da wa.inda suka kashe masa kanwa da mamansa ?

Shiru ta yi ta kurawa waje daya ido, a fili ta ce" kana baban ma.aikacin da baka fada min ko aikin menene ba aman kuma kake takaita zarginka da binciken ka?
Shin ina *MAI AIKIN DA AKA KORA DA CIKIN YAYAN KA?* su baka ma san inda suke ba a duniya, baka neme su ba, baka bincike su ba! Su waye su? A ina suke? Ba lale ne zarginka ya zo gaskiya ba Abdul...


BS ne ke tsaye da waya a hannunsa a cikin asibiti da kyar ya samu GN cikin yannayin gajiyawa ya shiga zayanno masa irin yanda wannan mutumen da suke yuwa aiki wato Abdul ke mayar masu da rayuwa marar dadi, su kam ya isa haka, gashi yana faman rasa mutun biyu du a sakacinsa,

GN ne ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce" BS ka san da wa kuke tare?
Kana tare da GNB na saudiya baki daya wanda shi daya ya fita a shekarar horonsa , kana tare da uban gidanmu ne,...ina mai tabatar maka du abinda yake yi, ya sani, yana sane, ka bi shi kawai, ka sada kanka ka koyi aiki, sannan ka sani kar ka yarda ka nuna masa da ka sani, nima na sani ne da na matsa kan tambayar shi din ko wanene, kuma na fada maka ne dan ka kula, kar ka janyowa kanka dama mu duka abinda ya fi karfin mu,!




*To fa readers ga Abdul, ga Hafsat*
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 1??

Mamaki ne ya cika zuciyar BS, haskiya ne, shifa ya ga abubuwan da suke da girman da isa da iza ba zata saka a koya ba , sai dai idan an ginaka da abin,

Wayar ya kashe ya koma ya dauki jibrin da aka gama yiwa dinki suka nufi gidan Abdul dan ba zai yiwu ya bar shi ya yi jinya a asibiti ba,

A lokacin da suka karaso, ya jima tsakanin dakin da aka baiwa Hafsat da nasu, yana ta kai kawo kafin da kyar ya iya bugawa yana saurare da bugawar zuciyar Allah ya sa ta bashi damar shiga, dan wani irin kwarjini take masa kamar ba yarinya karama ba.

Amsawa hafsar dake zaune kasa bayanta jingine da gadon dakin , laptop gabanta ta yi shiru tana duban screen din cike da rashin kwarin gwuiwa domin kuwa lale Abdul ya bata labarinsa aman ba wai ya bata sunaye bane, komai a dunkule a baibai ya bata, ta tabata ya yi haka ne dan karta ce zata shiga lamarin da ba nata ba, ya yi haka ne dan kar wani ya kutsa kai cikin abinda bai shafe shi ba,
Gashi dai tun da ta shigo sallah kawai ta iya yi ta samu waje ta zauna tana ta binciken abubuwan da ba amsa, sai canke canke take ko zata dace har BS ya shigo dakin nata,

Waje ya samu ya zauna a kasa kamar yanda ta zauna yana kallonta,

A hankali ya ce" yaya jikin ki?

Hafsat ta dube shi da kyau tana mai rufe laptop din,
Hannun ta kalla, sannan kuma ta dubi BS , kafadarta ta daga kadan kafin a hankali ta ce" Alhamdulilah,

BS ya kureta da kallo, a nitse ya dan muzkuta yana dubanta sannan ya ce" wa ya cire maki bullet din?

Itama wannan karron tsura masa idon ta yi, sannan ta ce" Abdul ne,

Abdul? Ya maimaita yana mai nuni da wata manufa, sannan ya kawar da kansa gefe yana dan murmushin yake ya kuma dubanta ya ce" da sunnansa kike kiransa haka?

Dan sasaucin dake saman fuskarta ta yi kokarin kwashewa, inda ta dora yannayin rashin walwala sannan ta kawar da dubanta daga kansa,

BS ya juyo da nasa duban jin ta yi shiru, ya dago hannunsa yana dubanta ya ce" kar ki yaudari kan ki, kar ki sakawa kanki wani tunanin abinda ba zai taba yiwuwa ba, kin san shi kuwa? Kin san ko shi waye? Kina kokarin yin wasa da wuta, kina son saka kanki a halaka ne? Ki sauko daga inda kika hau, aiki ya kawo ki, ki yi shi kawai, ki duba ki ga yanzu da harbin nan a wani wajen da zaki mutu aka yi shi da shikenan kin mace wajen kokarin gannin kin birge shi ko me?

Da sauri ta juyo da dubanta wajensa,
Ta jima tanai masa wani kallo kafin ta sada idannuwanta , ranta ne take jin???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? yana wani irin tafarfasar da ba zata so yin wani furuci a gabansa a wannan yannayin ba,
Me yake tunani da ita, au shi ba zai cire wannan shirmen dake dawainiya da shi a kanta ba? Dan ita bata ga dalilin da zai saka shi duban kwayar idannuwanta ya jefeta da magangannun dake nuni a sakarai ya dauketa ba, an fada masa tana neman kai ko ta zo dan haka ne?

Sasauta yannayin muryarsa daga bacin rai zuwa rarashi ya yi ya ce" ba ina miki haka dan na tsaneki bane, ina so ne ki farga tun kafin ya zame maki matsala

Hafsat ta dube shi da idannuwanta ta ce" kar wani yannayi naka da ka kasa daidaitawa ko tsayarwa ya kai ka aikata baban kuskure a rayuwarka BS! Kar ka mayar da abokiyar hamayarka....
Shiru ta yi na dan seconni kafin ta dago da idannuwanta da yannayin she's vry serious da abinda take fada kafin ta taune lebenta da hakorinta ta ce" *dan walahi sai na bika har gawarka sai na yi kokowa da ita!*

Idannuwansa ya zaro yana dubanta, inda gabansa ke tsannanta faduwa kan irin lamarinta,
A dan hargitse ya ce" saboda shi din ne zaki mayar da ni abokin gabanki ko me kike nufi?

Hafsat ta kankance idannuwanta dan jaraba hannunta na ciwo aman bakinta ya ki mutuwa ta ce" dan me saboda shi? Me kake tunani tsakanina da shi? Ina jin da ni fasika ce, da na jima da bayar da kaina kafin na shiga *kutkale!*

Aman ai dan na yi maganar nan ne kika bata rai haka ko?
Ya fada yana dubanta da kyau yana dan matsawa kusa da ita kafin ya dakata yana dubanta , sasauta murya ya yi ya ce" bana daukan ki a fasika, bana miki kallon wawuya, hasalima idan har ya kai ki wajen da zaki sha wahala zamu sha ta tare ne,

Shiru ya yi gannin ta kura masa ido, daya daga cikin sunnayenta ya zaba dan kiranta domin ta hana shi kama na asalin, a hankali ya ce" Ummi, ina son ki, kin jima da sannin haka aman kike wasa da zuciyata? Bayan kin san da daya daga cikin sauran na so, da da gudu zata amince min harma ta bini inda zan je ko? Ki bari haka, ki daina haka, ya karashe yana mai dubanta kamar yanda take dubansa,
Sai da ta lumshe idannuwanta ta ce" BS, ka yi hakuri ka ji? A yanzu, babar damuwata shine na fita a aikin nan lafia na samu incina na yawo inda nake so a lokacin da nake so, na sadu da iyayena mu sansanta tsakanin mu, walahi na fada maka gaskiya rabona da na ji wai ina iya soyaya tun wace ta kai ni *KUTKALE* me ta anfana min ne soyaya? Ita ta saka na kara zama fitsarariya, dalilin soyaya na tarbi gaban malan gaban yayansa masu jin kunyarsa na yi tsalen albarka na ce" *Malan, ba aure zaka min ba? To sai na yanka mijin!*

Haka ya bini da kallo da adu.a, na sha na tashi tsakiyar dare na ga mamana na tofa min adu.a, cikin ikon Allah sai na je na yi wanka wai na wanke adu.ar dan ta dankwafar da ni ne take min tofi salon a min auren ko yana wulakanta ni na zauna ko? To kar ta kuma min tofi!
Dalilin soyayar nake duban du wani yayana da ya yi garajen tsawata min na lalaya masa maganar da zai ji ya tsane ni har karshen rayuwarsa,
Dalilin soyayar na ringa kirta rashin mutunci da nake jin daidai ne, kaina daidai yake da na kowa idan dai za.a taba min abin so na! Wata alfarma ta yi min soyayar dake saka ni fita tsakiyar dare tare da kato mu je gidan rawa ni ba karuwa ba, ni ba arniya ba, ina kallo ana abubuwan da ba daidai ba aman a gobema na koma dan bacin ransa na nufin tashin hankalina?
Ita soyayar nace dan ubanta me ta tsinana min bayan *bakin jini, hau, tabewa, shiga uku, rayuwar da ko a mafarki ban taba tunanin ganina ciki ba, wato rayuwa irin ta dakarun sojoji?*

Tsagaitawa ta yi da maganar da take yi jin kanta na sarawa ta dube shi ta ce" ban ce bana son ka ba, ban kuma ce ina son ka ba, hasalima na mance kalar soyaya ne...ko nace na rasa sunnan da zan bata, *fara, ko bak'a* aa, *zaki ko madaci ce?* , *rayuwa ko mutuwa ce?*, a yanzu burina shi ne *ABDUL* ya rayu, ya fita a damuwarsa ko zai salame mu mu koma gaban GN ya bani inci cikake na arta a guje sai gaban Malan

Shi kam du kallonta ne yake, wai bata soyaya? Wai ta daina so take son fadi? Shi kam ya kasa yarda, yana tsoron irin yanda kusancinsu yake da girma tsakaninta da uban gidansu ya girmami tunaninsa ya zarce mizanin dan bashi tsaro ne kawai

Kansa ya kawar gefe, har tsakar ransa yana jin haushin irin yanda yake wareta ita kadai yana bata kulawa, du sun lura ba shi kadai ba irin yanda yake sakar mata murmushi ko idan ita ta yi masa tambaya zai tsaya ne ya bata amsa yanda take so , yana bata lokacinsa , har tsayuwa yake ya cire mata hular gashin dokin da take dorawa, yakan dora kujera idan sun biyo bayansa in ya zile masu ya zauna dangagal a matsayin da gare shi a dukiyarsa ya ringa binta da kallo tana faman kuftayar a saketa ta yi masa kashedin kar ya kuma yi masu haka, da an harbe shi fa? Me yasa hannayin damuwar da take nunawa ke birge shi? Ko meye hakan ke nufi? Ita kanta takan nuna bacin ranta da dukan karfinta tamkar an taba rayuwar wani na jikinta wanda take matukar so? Eh lale haka ake koya masu, ana koya masu cewar rayuwar wanda zasu je baiwa kariya ta fi tasu mahinmanci, su baiwa rayuwar girma su kareta da dukan karfin su, aman ita ta zurma da yawa, ta shiga da yawa, haka ake yi?

Har ya mike, ya dawo ya tsugunna yana dubanta kafin ya ce" ki kwana lafia, ki kwontar da hankalin ki, in dai gidan nan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login