Showing 42001 words to 45000 words out of 154870 words

Chapter 15 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1116

labarin ta fada da bakinta, meye sirrin rayuwar ki? Me ke damun ki? Me ya kai ki gidan yari da tsauri haka? Wace ratuwa kika yi a gidan yari? Yaya aka yi daga zama budurwar dan ta.ada kika dire a gagarumar bodyguard da kasa da mutan wajen kasa ke rububi? Kin zama karamar hamshakiya daga yar caskale,
Hafsat, wacece ke?

Idannuwanta ta bude daga lumshe sun da ta yi, ta zuba masa su, sun kara wani girma, sun cika da ruwan hawaye, haka kuma bakin na ciki ya kara girma,

Sai da ta hadiyi yawu ya kai sau uku kafin ta dube shi da kyau ta kuma lumshe idannuwan nata ta bude a hankali ta ce" *ina ka je? Ka saka mu a balaki, ka bamu damar kawo maka talafi Abdul, ka taimake ni mu yi mu bar maka gidanka Abdul*
Ta karashe maganar sosai tana mai sauke ajiyar zuciya,

Gabansa ne ke ta faduwa, shi kam ya rasa wannan jarabar da me ta yi kama, du in zai kadaice ya yi koda maganar minti daya da yarinyar sai gabansa ya fadi, baya son faduwar gaba dan kuwa saka shi take jikinsa ya yi sanyi, komaima nasa ya yi sanyi,

Haka ta juya ta fice a dakin ta jingina da kofar ta sada kanta kasa, a rayuwa daga bakin lokacin da ta tsinci kanta a gidan ladaftar da shege wato *Kutkale* ta gane mecece rayuwa da mahinmancin iyayenta, daga wannan ranar idan kana son ka ga ka ruguzata ..to ka yi maganar iyayenta, ka takalo maganar su, a nan har kuka sai ta yi maka, tana son Malan da mama, tana son su sosai, tana son komawa gare su ta yi masu biyaya, tana cikin duhu, shin malan ya daura aurenta? Idan ya daura da auren wani kennan a kanta? Ita din matar aure ce ko me? Idan har matar aure ce, shi ne take irin wannan rayuwar? Ita dake neman sauki wajen Allah kuma take irin wannan sakacin? Yaya take tunanin gannin haske bayan idan har da aure a kanta tana wasa da sunnar ma.aiki?

Idannuwanta ta lumshe, hawayen da take rikewa ya yi nasarar zubo mata a kumatunta, ta bude idannuwanta a kasan zuciyarta ta ayyana Malan idan na dawo, walahi koda mahaukaci, ko wani irin mutun ne ka aura min zan zauna da shi, na yi masa biyaya, malan in sha Allah zan rike mutuncina komai rintsi, malan ka yafe min=?O?
Abdul kuwa yana tsaye yana kallonta har ta fice a dakin,
Shima wani iri ya ji , sosai ya ji ba dadi,
Shi bai yi fitar nan dan ita ba, ya yi fitar nan dan zuwa gannin yar Elhaj da ya kama ya boye a can yankin ghana cikin wata rigar fulaninsu wace ya saka yan tsaro tsareta wanda ita hakan ya yi mata dadi dan kuwa cike take da bakin cikin ubanta ya shiga dakin uwarta ya kuma shiga nata! Gashi kiri kiri ba wata magana dake hadata da uwar tata, uan uwanta maza du an yi nesa da su basa kasar, kai ko suna nan du daga wanda ya mayar da giya ruwan shan sa, sai wanda ya mayar da mata lumfashinsa, ba wanda zata tarba ta yiwa maganar ya fahimta bale har ya ji ciwo,
Tana faman kashe kanta , tana tunanin hakan a tafiarta da ta yi wanda abanta ya sakar mata kudade dan yin yanda take so ta dawo su dora daga inda suka tsaya (wa iyazubillah) , har ta shiga neman abinda zai dauke numfashinta ya shigo rayuwarta ya sace ta, bai san alfarma ya yi mata ba, bai san taimakonta ya yi ba, bai san ya cire mata masifar da ta fi damunta ba, dan kuwa har ta fara bushe bushe, wajen da ya boye ta nan akai mata magani dan ta dawo clean,
Baki dayansu jira suke, jiran ranar kin dilaci suke,

Ya gudu ya je gareta a yau ne dan yana son yi mata wasu tambayoyi a kan aminin abanta wanda ya yi imanin ta sani dan kuwa akoy sakin baki a wajen uban idan yana cikin farin ciki,

Nan ta nemi bashi wuya, dama baya shiga rigar sai ya yi shiri irin nasu, hakan ya saka shi neman yi mata tijara da kyar dai ta sanar masa labarin , ta boye ne dan ya shafi mahaifiyarta ita kuwa har ga Allah tana jin son mamanta a ranta, harma tana fatan idan ta ga bayan wannan lamari da ranta ta je wajen mamanta ta rungume ta.

Daga rigar ma wajen yan sholishon cikin garin ya koma, saman babur din nan na aro, ya saje da su, ya burmu inda suke burmuwa, dan tabatarwa kansa labarin dan aminin Elhaj, shi ne diler din wato mai siyar masu da kwayar wanda suka haifa da matar Elhaj a lokacin da ya yi doguwar tafia wace ta faukan masa shekara biyu harda yan watani......wannan masifa na tafe da su duka bisa tafkeken laifin da suka aikata, harma sula gayaci wani!

Juyawa ya yi a hankali ya shige wankan,
Wankan da ya daukan masa lokaci, kafin ya fito yana tsane jikinsa

Sai gashi fess ya fito da shi cikin dan kankannin lokaci

Doguwar riga ya saka , ya bude frijj dinsa, nan ya ga an cancanza madarar holondia dake ciki, daukowa ya yi yana dubawa,
Bai sha ba ya mayar cikin frij din ya taka ya fita

Yana fitowa ya ganta tsaye, ba wata walwala a fuskarta irin dai a shirye take shirin aikinta,

Dakin matarsa ya nufa, wanda ya saka mata bugawar zuciya na tsoron kar a je ya kuma abinda ya yi jiya?
Sai dai bata iya cewa komai ba ta bi bayansa suka shiga, suna shiga bata tsaya jiran wani abin ba ta je du ta yi binciken da zata yi kafin ta juya ta fita ta ja ta tsaya kusa da abokannan aikinta,

Yana kallonta ya zo wajen kujera ya zauna, ya dora kafa daya kan daya

Saukowa ta yi daga saman bed, gabanta na dukan tara tara tana adu.ar Allah dai ya sa ba abin nan na jiya ya dawo da shi ba, dan yau da ba dan ta wuni gasa jikinta ba, toh da tabas ba zata iya takawa rasss da kafafuwanta ba,

Zaman da ya yi, yana duban du motsinta har ta karaso kusa da shi ta tsuguna ta gaisar da shi,

Bai amsa gaisuwarta ba ta mike ta zauna a kujerar dake facing dinsa tana sinne kai irin kunyar nan,

Hannunsa ya nuno wajenta ya ce" menene wannan kike yi? Irin wannan sada kan haka?

Daina sada kan ta yi aman bata dago ta dube shi ba, dan haka ya ci gaba da fadin" kin san a tarihin matan da na aura ke ce ta farkon da ta kai warhaka bata mutu ko ta gudu ta bar ni ba? Ke ce wace bayan kin ga girmana har na so sakar maki shi sai dai kika kasa dauka sai hakura na yi dan kina ta ihun da ya saka na ji na daina muradi? Kin san da lale masu baki tsaro sun bada kyakyawar gudunmuwa wajen gannin rass har yanzu kina takawa yanda kike so?

Shiru ya yi gannin ta nutsu harma tana dagowa ta dube shi sannan ta sada kanta, ya ci gaba da fadin" bani da time din da zan auri mace kuma na bata tarbiya! Ki gane bana wulakanta dan adam mai daraja, kar ki yarda ki saba da haka domin kuwa idan har na gane haka ko da cikina a jikin ki na wata tara ina iya salamarki, can ki je ki karata da abinki ki bani lafia ni ba zan so ina ji ina ganni mace ta mayar da ni wawa ba!

Ajiyar zuciya take saukewa na dan kukan da ta fara, dan a fada ta dauki magangannunsa, duda bai yi su a lalama ba, bata wani saurari abinda ya dace ta tsinta ba, sai tsayar da hakan na faruwa ne dan ba soyayarta a ransa, dan haka sai ta ji ta muzanta,

Sai da ya gama ya maida dubansa wajenta, sarai ya lura da yannayinta aman ya basar ya mike ya ja rigar jikinsa ya cire kafin ya koma saman kujerar ya yi wani zaman rashin kunya yana dubanta ya ce" yau fa, sai na shiga, zo ki ja ra.ayina=? ?

Ya karashe yana mai lumshe idannuwansa ,
Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta dube shi, jibgin uwannan kai, haka yake a haske sosai? Haka yake? Waima ya shiga ina? Ta yaya? Yau ta shiga yku ta ga abinda ya fi karfinta, gashi ya yi wani ringeshe wato jira yake ta zo ta yi masa abubuwan nan wanda ta dauka na jar fata ne, sai dai ya yi mata nuni da sunna ce kafin ya nemi darara mata ? Kai ita dai tsakaninta da matan da yake daukowa har suka saba masa da irin wannan rayuwar sai Allah ya isa (=?3? to fa, ke, shi da ya dauko sun fa? Fans kar ku yi mamakin irin yanda zai mikewa mace amarya santaleliya irin Ni.ima cewar ta ja ra.ayinsa, idan baku manta ba Abdul fa namiji ne da ya yi mu.amalar jan ra.ayi da mata kala daban daban, wa.inda suka isa da wa.inda basu isan bama duk suka zube suka ririta shi ya wanke su da dala....hakan ya saka shi gannin wanima ya yi rawa balatana dan makadi, kennan wanima ya ja ra.ayinsa ina ga ta sunna?)

Sai da ta cire rigar tata ta sama ta baci, sannan ta duka gabansa irin yanda ya nuna mata a jiya ta yi tsuru tana kallon sa,

Bude idannuwansa ya yi a hankali ya kai kanta, shi take kallo abinta, kallo irin na san gane abu...
Dagowa ya yi da yannayinsa mai nuni da jarabar ta gama motsawa yana dubanta, a hankali ya ce" yaya sunnan ki na gaskiya banda Baby? (Sunnan da yake ji kennan shi tun da ya santa, ko wajen daurin aurensu shi fa sai ya rantse bai ji sunnanta da kyau ba bai rike ba, =?D?=???????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????D?=?D?, zaka fada ne Abdul)

Idannuwanta ta bude da kyau tana dubansa,
Sunana kuma? Wai dama bai san sunana ba?


Jiki sanyaye ta ce" NNNi.uma,

Hannayensa ya saka ya dagota ya dorata saman cinyarsa, a hankali ya matso da ita zuwa jikinsa , cikin yannayin rada ya ce" Ni.ima, Allah ya sa Ni.ima na tare da ke, ki daina langewa ki bani kulawa kin ji?

Kanta ta shiga gyadawa a hankali, tana jin wani irin yannayi na shigarta na sababin abubuwan da ya shiga yi mata ta hanyar anfani da hannunsa da kuma sajen fuskarsa.......


A yau kam abin ya ja daga, dan kuwa ba shi ya fito a dakin Ni.ima ba sai kusan karfe daya, sai da ya gama mayar da ita cikakiyar mace, wanda shi da kansa ya tausayawa yannayin da ta shiga , ta sha wahala ta kirki wace sai da ya talafa mata lumfashinta ya dawo jikinta, tabas ya san dole sai ta ji jiki, shi din bai taba yi ba, ya bita a hankali aman ya girmeta sosai, shi ya sa ya kasance mai tunanin zama da mace biyu, dan a ganninsa irin wannan fitinar da wuya mace daya ta iya dauka,

Bayan ya gama bai tsaya wani gashe gashe ba, da ta farka, kayanta kawai ya iya zura mata ya kwontar da ita ya ba dakin baya, yo shi ina ya san ana wani gashi? Inama ya san ana wani ririta? Shi fa a sanninsa shikennan kafin safe ta ware, dan haka ya fice yana mai jinsa sakayau kam, (wayo Ni.imana, ashe ke wuni da gashinma ba na dalili bane? Yau kam zaki yi gashi)

Yana fitowa ya tarar da ita dai tsaye,

Gaba ya yi tana biye da shi a baya har suka shiga dakinsa,
Suna zuwa ta kakabe shinfidarsa, ta bude frij ta ciro hollondiar nan biyu da ruwan gora ta ajiye ta juya ta fice a dakin inda ya rakata da kallo kafin ya zarce bayi dan yin wanka........



Kwonci tashi, yau har kwannan su Hafsat goma a gidan Abdul, sun ga fitintunnu da abubuwan mamaki da tarin takaici a tare da wannan bawan Allah,
Abdul, bai taba yin wani yinkuri dan nuna masu yana son kare lafiarsa da ransa ba, bai taba basu damar su fuskanci inda zasu kare ba,
Ya sha dan iya shege su fita ya zile masu du tsaron su, du kulawar su ya dawo gida kawai dan ya saka Hafsat ta yi ta balaki kamar ta kai masa mazga yana zaune yana dubanta yana murmushi, kuma du fitar da zasu yi, Hafsat na kula da takunsa basu taba fitar da ba wani abin mahinmanci na lamarin aikinsa ya fitar da shi ba, cikin dabara take hada abinda ta samu itama har ya zile masu!

Kamar yau ma da karfe biyar na yama ,
Abdul ne ya fito daga dakinsa cikin shiga ta kayan gudu, wato yau dole su yi sports dai?

Yana fitowa bai yiwa kowa magana ba ya dauki hanya ya falla da gudu,
Sai da Hafsat ta dora hannu a ka gannin wani balakin kuma, sannan ta cire rigarta ta sama ta fala da gudu ta bi bayansa hakama su BS gaba dayansu sunna biye da shi da wani irin gudu ,

Sunna shan kwana, kamar daga sama wata bakar mota ta shanyo kwanar a guje ta ........... . ........



*Toh fa, lamarin na Abdul ba sauki>?&?
@&,*

Ku yi hakuri da yannayin rubutuna, ina iya yina dan baku pages mai yawan gaske a hakan, ku min uzuri plz=?O? >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 9??




Tun da suka hangi motar, da irin gudun da ta shanyo kwanar da shi ya saka su BS ihun fadin su Abdul su duke!

Hafsat dake kusa da Abdul da wani irin sauri ta saka hannunta na hagu ta janyo damki damtsen hannunsa, da dayan hannun nata kuwa ta dafe kansa ta aniyar dukar da shi kasa,

Wuta ce su BS suka budewa motar domin suma daga ciki hakan suka yi kokarin yi masu, cikin rashin sa.a aka samu Hafsat a damtsen hannu sannan aka samu abokin aikin nasu a kafada,
Gannin zasu cin masu ya saki hafsat dake kasa ya janye bindigarta ya mike,
Irin yanda yake harbi, harbi ne na neman hana su motsi domin kuwa wajen tayoyinsu yake ta nema
Hakan da suka gane ya saka su wani irin jan motar suka aniyar guduwa wanda Abdul ya ki basu wannan damar ya dankara da wani irin gudu yana harbin su, nan ya samu direban nasu wanda motar ta yi masa nida sosai

Yana kokarin ci gaba da harbin bulet ya kare,

Wani irin ihu ya yi ya soke bindigar a jikinsa ya aniya kara gudunsa ko zai cin masu,
Sai dai kafin ya isa sun samu sun canza direba sun ja motar da gudun balaki

Sai a lokacin BS ya karaso da gudun shima yana dubansa kafin ya mika masa hannu kan ya bashi bindigar,

Bindigar ya ciro ya mika masa sannan ya juya yana wani irin jefa kafarsa ya nufo inda suke yashe kowane na jin abinda bai taba ji ba

Hafsat kam ita a ranta ta yi tunanin shikennan mutuwarta ce ta zo, irin yanda gaba daya a lokaci daya ta ji wata irin azaba sannan hannun ya zame mata tamkar dutse ya gagari motsin kirki ya mutun mata ya saka ta sarewa, nan da nan wani irin tsoro da take yawan ji idan ta yi fadan da take da gaskiya a gaban iyayenta ya kamata,

Daidai wannan lokacin Mama dake zaune tare da babar yarta, ta yi tsai ta kurawa waje daya ido

Gannin yannayin da mama ta shiga ya saka asiya zaunawa maimakun ta je ta karo ruwa a saman ruwan kankarar da zata sha ta zubawa maman ido,
Jiki a sanyaye ta kai hannunta ta dafa maman ta ce" Mamanmu, lafia??

Manyan idannun nan masu kama da na Hafsat ta dago ta tsurawa Asiya, sak irin duban Hafsat ne,
A hankali ta nazarci asiyar kafin ta buda baki ta ce" tabas malan ya yi gaskiya, tana raye,

Wani tausayin mahaifiyar nata ne ya darsun mata, a hankali ta kai dubanta kan dan jaririnta da ta haifa yana dan wutsil wutsil din wasansa gwanin sha.awa, ta kuma kai dubanta kan mamanta, kai lale ta jinjinnawa iyayen da suke rayuwa ras ras ras bayan batan yayansu, kai baka ga gawar dan ba, kai baka san ina ya shige ba, tabas da mutuwa ce ya yi da ka dangana ka sakawa kan ka hakurin rashinsa ka fuskanci rayuwa,
Aman a haka, du irin rashin ji irin na maman malan ba ranar banza da ba zai jajanta rashinta ba da fadin shi ya san tana raye,
Gashi yau maman dake bashi bakin ai kawai a bita da adu.a, idan tana raye ina ta shige? Ita din ce ke fadin tana raye kuma?

Yaron mama ta kara rikewa da kyau tana duban Asiya ta ce" a jikina nake jin farin cikinta ko akasinsa, idan tana cikin hali na tsoro...a jikina nake ji sosai sosai,
Tabas Maman malan na raye kuma du inda take

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login