Showing 18001 words to 21000 words out of 154870 words

Chapter 7 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1149

abinda zai sadata da tagar dakin yannayi, karshema ta rufe tagar da bakin zannin da zai hana maka damar gannin na ciki ko abinda ke faruwa,

Ita dai kallonta take, tana karantarta, har ta gama komai ta gama caje dakin da komai sannan ko abincin da zata ci ita ta dafa ta kawo mata kafin take yi mata salama ta fita,

Ko da ta fita ba wani inda ta je sai nan kusa da dakin da ta tsaya,

Kwonci tashi, haka suke rayuwa, du zaman da za.a yi a kotu tare da ita ake yi, inda take shige da arniya domin kuwa sam ba.a bari ta yi shigar da wani zai ganeta ba,
Sosai take takatsantsan kan lamarin aikinta,
A haka ta shiga jikin mutumen da ake karar ya yiwa yar yarinyar fyade, ahi kuwa mai kudi ne dan haka yake son batar da shari.ar,
A hankali ta ringa gane abubuwa, ta ringa taro abubuwa,

Wani dare Sahun kafa ya dauke,
Shiru kake ji sai dan kukan tsuntsayen tsakar gidan,

Gilmawar da ta gani daga can lungun dakin baby ya sakata sakawa wajen ido,
Shiru ne ya dauka na lokaci mai dan tsayi, dan haka cikin nutsuwa ta duduba inda take tsayen ta kara duba eh lale dakin Madame a rufe,
Dan haka ta jakuda daga kofar a hankali ta bi hanyar da ta ga motsi,

A hanlai take tafe cikin sanda tana dudubawa, har ta karaso kusan dakin Boy,

Ja ta yi ta tsaya jin alamar motsi ,

A hankali ta kara abin jin maganar mutun ko daga bayan kyaure ko daga nesa ne a jikin kofar dakin ta kasa kunnenta,

Magangannu ne kamar haka........
Ba ita ta haife mu ba, ba uwarmu daya ba ubanmu daya ba da kai, dan me zata hana mu rayuwa tare? Dan me zata hana mu rayuwar soyaya? Ni ina son ka, da soyayarka na tashi, kaf duniya du wanda yace zai rabani da kai, koda kuwa kai ne, na rantse da wanda lumfashina ke hannunsa sai inda karfina ya kare!


Ya zaki ringa magana irin haka a kan macen da ta dauke mu daga gidan marayu, ta bamu tarbiya, ta kawo mu jikinta, ta ririta mu, ta daga martabarmu, ta nuna mana soyaya daya da ba hadi? Ya zaki yi kokarin bijirewa maganar macen da take tamkar mahaifiyarki?

Ta dauko mu ne dan bata haihuwa! Da tana haihuwa kana tunanin kafarta zata je inda muke ne? Da tana haihuwa tsakaninmu da ita sai dai ta bamu sadaka a titi!

Aman nawa basa haihuwar basu nemi talafawa marayun ba? Saurara, ni fa ba butulu bane, tunda muka nuna mata muna son juna ta kiya ni fa na daina wani son ki, daman ke kika koya mani taba sashin jikinki, kika koya mani abubuwa, ki barni na yi mata biyaya dan ni uwata ce!

Cikin dan daga murya ta ce" ni bata haife ni ba! Kuma bana sonta dan tana son raba ni da nake so! Shi yasa ka daina taba ni? Shi yasa ka fara yan mata? Kar ka tsoma kanka abinda zaka yi dana sani, dan kuwa nan ba da jimawa ba zaka zama nawa!

Tana gama fadar haka ta nufo fita da mugun sauri.............



Kallonta yake yanda take rawa da jigidar dake daure a kugunta,
Cikin kwarewa da iya juya kugu take taka rawarta tana bada cas cas cas, haka kuma na kafarta suma suke bada kida,

Sau uku kennan sai ta zo kusa da fuskarsa ya shaki kamshin jikinta ya miko hannu zai cire bras dinta sai ta ja baya ta kuma dauki rawar jan ra.ayinsa zuwa aikata alfasha

Wannan dawowar da ta yi, cikin kwarewa a barikanci ta saka hannunta ta kunce dan yololon abin da ya kasance wanda ya hade bakin dan pant din dake jikinta ta yar sannan ta karasa ta haye jikinsa tana rawar iskanci,

Cikin sanyin murya bayan ya riko hannunta ya ce" shuiiiit, ki?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? bar mani hayaniya kar ki saka ta kwonta!
Kamar ba shi ya yi mata maganar ba ya yi mata wani mahaukacin riko, da wani irin karfin da a yannayin maganarsa ba zaka taba sakowa ranka shi din nan Allah ya hore masa wannan karfin ba, duba da yannayin hutu dake sakashi magana a yangance da kuma sanyi, wai kuma yannayin rikon bai nuna alamar ya saka wani karfin a zo a gani bane

Bras din dake jikinta ya bale sai dai me ciko ne ya fado,
Ashe tudun nan na sama da ya saka saman cika ya batse gaba daya ciko ne ta yi daga kasan ta turo saman,

A hankali ya sasauta mata rikon, harma ya saketa baki daya,
Cikin salon karuwanci ta nemi komawa jikinsa tana wani laudi ita ga zata jashi koda ya ga sirrin cikonta,

Riketa ya yi ya zaunar da ita suna kallon juna ya ce" ke musulma ce??

Tana kane ido daya tana turo yan berayan kirjinta ta girgiza masa kai , amsar eh ita musulma ce,

Habarsa ya talabe da hannayensa ya ce" yanzu karuwancinma ba zaki yi da gaskiya ba? Ai musulmi an sanshi da gaskiya ko? Ya zaki cika taunman pant a nono ki ja ra.ayin maza? Haba cutar ai ta yi yawa, kina tunanin idan kasanki nake so zan zauna kina min rawa ne?
Ni bana zina....aman ina son mata,
Mata ababaden so ne,
Kin san me idan na ga mace wace ta amsa sunnanta nan da nan wannan take mikewa, idan kuwa muna mata ne lafewa take kara yi ta yi kwonciyarta,
Mata duka suna da kyau, sai dai wace ta iya gyara ta fi kowace kyau,
Kin ga bariki ta shaida ki, ji yanda nononki ya dawo dan Allah in dai ba dan da kika haifa ba ya sha dan kar ya mutu ubanwa zai sha wannan yangom din?

Shiru ya yi yana duban irin yanda ta saki baki tana dubansa,
Murmushi ya yi cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin.....


(Ku fa gane, ya fito a wani irin mutun marar sirin baki, sam sam bakinsa bashi da birki, magana zai saketa ne son ransa>?&?
@&>?&?
@&>?&?
@&)
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




9??


*Free page* daga page 10 an gama free



Cikin sanyinsa ya ci gaba da fadin" dan Allah ku yiwa kanku adalci, yanzu ke kin je kin yo shafe shafenki, kin cika hoda ta kara janye fuskarki, kin zagaye lebe ya zama dan dagwas, da a duhu zaki zo mini shikenan kin ribace ni?
Duba ki ki ganni, fatar jikinki ta fara janyewa irin alamun shekaru sun tarun nan aman dai har yanzu wannan bata isheki ba?
Ya fada yana mai nuna .....dinsa,
Manyan idannuwansa ya daga sama kafin ya maido kanta ya ce" da yarintata yanzu ni hariki ta yiwa wulakanci na kale tsohuwa tas har ina shirin mika mata abuna ta yi wasa!
Gaskiya baki yiwa bariki adalci ba,
Ki saka kayanki kin ji? Ba zan iya rike wannan takalman ba,
Ya fada yana mai nuna kirjinta,

Gaba dayanta ji ta yi ta muzanta, so take a hakanma ta kara jan ramayinsa, sai dai ina, ba wani hayanniya ya yi mata ba, aman tana tsoron ta ga hayanniyar tasa,
Dan haka ta mike jikinta na dan rawa ta saka bras dinta, ta nufi wajen kayanta tana faman du ta maida , ta tsinci muryarsa ya ce" menene kika zuba cikin kofin maltina na?

Gaba daya jikinta ya dauki rawa, inda ta juyo a firgice, gabanta ya yanke ya fadi, gaba daya ta rasa bakalin kwarewa a barikin da ta yi, gaba daya ya wani hautsina mata lisafi ita dake dakon wannan ranar bisa biyanta da aka yi kan ta cin masa, sai gashi kamar da wasa gawo na son juyewa da mujiya, yana son karfi da yaji sai ya ladaftar da haukanta a nitse,

Inda inda ta fara, kafi ta sakar masa murmushi ta nufi wajen kofin ta dauka ta ce" oga, abin karin karfi ne na zuba maka dan mu ji dadin rayuwa, tunda ka fasa shikennan,

Murmushi ya yi yana shafa gemun gayun da ya ajiye yana dubanta a takaice ya ce" to shanye,

Me? Ta fada tare da zaro ido a lokaci daya kuma ta saki kofin gaba daya maltinar ta zube kasa,

Da ido ya bi farin tiles din dakin nasa da kumfar Maltina ke ta yi kafin ta farfashe sai ruwan maltinar, a hankali ruwan ya dan gangara hakan ya sa ake gannin color din maltinar daga maroon mai duhu ya dawo wani jajaja ,

Kallonsa ya kai kanta, ya girgiza kai, ya ce" dauko abin gogewa a wancen wajen,

Wajen da ya nuna mata ta je da sauri ta dauko abin gogewar,
Karba ya yi a hannunsa kafin ya duka da wani dan kofi ya dibi kadan, sai kuma yace goge,

A tsorace ta goge tana hankalce da na hannun nasa,

A hankali, cikin sanyin murya ya ce" ki goge da kyau, bana son kazamta ni, ki kwontar da hankalinki, ji ba zan iya kisan kai ba, wannan laifin bana so na tafka shi gaskiya,
Ke yanzu dan rashin imani kashe ni ne kika zo yi, da maganin da ake zubawa bera? Ina laifin ki kasheni da abu mai tsada tunfa dai kin ga mai tsada ne ni, kuma fisabililahi dan rashin tausayi mutuwarma a gabanki kike so na yi? Wannan fuskar taki mai shige da ta dan iskan bunsuru kike so ina kallo har raina ya fita? Ina wa laifin ki turo yar yarinya wace komai ya ji, na more idan na gama sai in mutu ina kallon jan lebe da gira mai kyakyawan gashi? Aman kuri da ido ya na yan shaina kike so ina kallonki har na daina motsi? To ta Allah ba taki ba, tashi ga kudinki ki tafi kin ji? Ki canza sa.a tun kafin ki karasa zama karyar yan bariki.

Ita kam zuwa wannan lokaci lamarinsa ya girmami tunaninta, da sauri ta gama gogewa da hannunta , sannan ta dauki takardar da ya ajiye mata na kudin da zata dauka, jikinta na bari sannan sanyi kalau ta fice daga gidan wannan bawan Allah mai cike da abin mamaki, tabas da wuya a cin masa, ya kasance wani irin mutun mai wasu halaya masu wuyar fasara, ingarma ne, tsayaye ne mai sanyin magana, hutu ya saka shi abin tashin hankalima shi a shanshakai yake dubansa, ashe du haukan da take ya ganta?

Wayar da aka kirata da ita dan bata kwongilar kashe shi ce ta shiga kara,
Sai da gabanta ya fadi a lokacin da ta ga kiran,
Sun bata rabin kudin aikin zasu cika mata rabi idan ta gama, da sharadin ta kuka da kanta idan sunnansu ya fito ko ta kasa cika aikinta,

Jikinta na rawa ta wurga wayar cikin kwondon shara ta canza hanya tana yi tana dudubawa kar a cin mata..... wannan kennan

Ya jima tsaye jikin window din dakinsa na baci,
Tsakar gidan kawai ya tsurawa ido yana hangen mai baiwa fulawowin gidan ruwa da kuma daidaita su,
A ransa yake ayyana shi kam wannan hankalinsa kwonce, ba zai kwonta da tunanin kudi ya kuma tashi da tsoron fita ba, bashi da wata damuwar da ta fi ya samu yan na kashewarsa ya kashe ya baiwa matarsa , burinsa na gaba daya tsayin rayuwarsa basu fi adadin sadakar da yake badawa ba,
Gashi saboda *Kudi* yana haduwa da abubuwan rayuwa kala kala,
Menene na gagawar? Dan adam, menene na zakuwar?
Ya aka yi baya iya hadiye zalamarsa?
Mutuwa ai mai zuwa ce, idan ka yi hakuri zan mutu....koda kai baka ci ba sai ka yi iya yinka iyalinka su ci ko? Tunda ka rantse sai ka ci haram,
Idan ka yi hakuri, shekara talatin ai an raraka, me ya yi saura? Idan na jima na kara saba.in a kai...
Wani murmushi ne ya saki kafi ya shafa kolon dake kansa tal tal ba digon gashi a sama ya yi baya baya ya fada saman bed dinsa ya lalubo wayarsa ya shiga duba hotunna a Instagram, ua ga wace ta masa, ya tura mata adireshinsa kawai, koda ba yar kasar bace ta biyo jirgi, dan kuwa ba zai iya rintsa idannuwansa mararsa da wannan nauyin ba, shi kuwa ba zayana didikar mqgani ba har ya je ya bata mararsa! ......(ALLAH YA SHIRYE MU)



Da wani irin gudun da ta jima bata yi ba, gudun ceton rai ta bar wajen,
Tana zuwa kofar dakin Madame Bilkiss ta ja ta tsaya tana maifa ajiyar zuciya,

Kyam ta yi tana duban waje guda, gaba daya du wani huja dake tatare da ita ne take hadawa kafin ta bi Joli da kallo har ta shigewa ganninta

Ajiyar zuciya ta sauke , ta ci gaba da aikinta kafin lokacin da ya dace ta kwonta ya buga, sai dai ina , bata tunanin zata iya rintsawa a wannan lamarin!


Washe gari bayan Madame bilkiss ta shiga office dinta ta gama caje komai ta fito ta nufi bakar motar dake jiranta,

Tana shiga bata yi magana ba sai takarda daya da ta mika masa,

Ya jima yana duba takardar sannan ya dago da wanni yannayi ya ce" menene hujarki ta fadin wannan gagarumin abin? Kin san da idan har ba haka bane, hakan na nufi da ja da kungiyar lauyoyin garinnnan? Da masu kare mutuncin su, da dukan wani mai nuna tausayinsa kansu? Kin san da bamu da karfin ja da su a haka?

Kai tsaye ta ce" huja kake so? Bani da ita GN, bani da hujar da zan daki kirji na nunota a fili, sai dai ina so ka taimaka kamar yanda na roka, wannan number, itace ta karamar wayar da na samu a dakinsa boye cikin karamin wandonsa,
A saka a cire layi daga cikin layin layikan da ba za.a iya jin hirarsu ba, sannan a saurari abinda suke fada,
Zuciyata ta bani amanar hakan, na yarda da hakan, kuma in sha Allah gaskiyar lamari na cikin nan,

Number dake saman takarda rubuce ya bi da kallo, kafin ya bi bayanta da kallo har ta bacewa ganninsa, ta koma bakin aikinta,

Jujuya takardar yake a hannunsa, cikin zuciyarsa ya kasa yarda da irin girman abin da ta kawo,
Sai dai me, ba zai yar ba, zai saka a bi a boye , idan har hakan ne shikenan, duniya ai ba abinda bata gada ba.

Bayan kamar kwana biyu,
A lokacin , a lokacin har an gama shari.ar an yanke hukunci daidai laifi,
Suna zaune a fallo suna shirin cin abincin da Joli ta girka da kanta, sai zumudi uwar take cikin murnar jolinta ta fara shiga kicin da kyau,

Har an zuba abincin za.a fara ci , Hafsat dake tsaye tana kallonsu Joli ta duba ta ce" wai Mam, ba kun gama shara.ar ba, me kuma wannan abin ke yi tare da ke gar yanzu?

Uwar ta kai dubanta wajen Hafsat, ta ga tsaye kawai take, yau ba gilas din, aman duda haka wani sirri ke tatare da yarinyar, wanda tana so ta san menene shi, tana son sannin wacece yarinyar da du abin shagalta baya dadata da kasa, menene duhun da ya mamaye mata ranta bayan gata yar yarinya, yar karamar attajira , domin a wannan aikin kadai da ta yi ta tara kudi na mamaki, idan aka cire percentage din ma.aikata wanda zai zama nata ba kadan bane, ko tunanin wannan baya sakata irin ka ganta tana ta murna,

A hankali hafsat ta matso sosai kusa da Madame bilki dake son kai abincin nan bakinta ta ce" ashe shi mai bincike, idan ya tashi idonsa na kasa gannin amsar da yake nema a gaban idonsa?

Dago da kanta ta yi tana duban Hafsat, ta sani ne, farin sannin cewa, bata maganar da bata da ma.ana ko wace bata shafi aikinta ba, tunda suka hadu, kusan wata hudu kennan, bata taba koda wasa shiga hurumin abinda bai shafeta ba, du irin cin kashin da joli ke mata kuwa bata taba koda nuna ta san da ita a wajen ba, aikinta ta zo yi, tana kamanta yinsa da dukan gaskiyarta, dan haka maganar da ta fada ya saka madame Bilkiss cikin dan gajeran tunani,

Kasa gane komai ta yi, ta kuma dauka da niyar kara kai abincin bakinta,

Da sauri ta ce" idan kika ci abincin nan, zaki tashi normal ki je dakinki, harma zaki yi wankan minti goma, shafa.i da wuturin minti goma sha biyar , shirin bacin minti biyar, ki kwonta ki fara baci, cikin bacin da bai fi na minti ashirin ba zaki ji gaba daya an hade hanjin cikinki,
Zaki farka da sauri domin takurewar ba ta wasa bace, zaki nemi mikewa ki sha ruwa,
A lokacin da kika sha ruwa, dan lokacin karasawarsa cikin cikinki wajen wannan shinkafa da kika hadiya zai dauki second biyar *kacal*, daga bakin wannan lokacin numfashinki zai nemi gagararki, a hankali a hankali zaki fara fitar da wata kumfa mai kalar shudiya, a haka zaki ringa kaiwa kasa har ki zube kina ihun kiran Bodyguard, aman muryarki bata fita dan ya ci karfinta, cikin haka zaki tafi ta hanyar birkidodoniyar da zata goge kumfar da kika zubar da kashin da za.a dauka du na zafin fitar rai ne, a haka zan shigo na tarar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login