Showing 114001 words to 117000 words out of 154870 words

Chapter 39 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1160

ambaci cewa su sun zo ne dan ubanta mutumin mutane ne, sun zo ne dan kawai su amsa gayatar mai zuwa gayar mutane, aman kowa ya sani ko sadaka zai bayar da yar nan tasa sai ya hada da bada hakuri da jari harma da wajen zama, dan a yi hakuri a zauna masa da ita, yarinyar da ta sha marin saurayi? Daidaiku ne suka yi mamaki rashin zuwan ango a kan lokaci, sai dai daurin auren da aka kusan karfe goma na dare ya saka mutane da yawa mikewa tsaye daga zaunen da suke......

Dubansu du suka kai wajen mutumen da aka ce shi ne mijin Hafsat, nan yan kananun magangannu suka fara tashi, sai dai a lokacin da ya yi bayanin kyautar uwa da ta uba sai baki ya mutu, ya kasance du wanda suka yi ido hudu da shi sai dai ka ga ya sakar masa murmushi ko yana kokarin karasawa dan ya samu shiga a hankali aka fara canza salon zagi zuwa yabo, a hankali aka fara dan yaba magana cewa" ai ita uwar malan barta da fadanta, aman yarinya ce mai mutunci da mutunta wanda ya girmeta

Malan dake zaune, zuwa wannan lokacin ajiyar zuciya kawai yake saukewa sannan yana bin mutane da kallo, a yau ya ga rana ta mamaki, rana wace a yau kawai Allah ya nuna masa mai zaune da shi dan rufin asiri da mai zaune da shi dan moriyar wani abin,

Ashe dan adam yake?

Marokiyar nan sai da ta ja ta tsaya ta kara rangada buda,

Wani tsaki ne yayar su Hafsat ta ja, kafin ta ce" wai Ummah, ba za.a tsawatarwa mutanen waje idan na cikin gida sun zame mana dole ai banda na waje

Maganar da marokiyar ta fara fada ne ya sakata katse maganarta, lokaci daya kuma ta zabura ta mike da niyar fita

Hafsat da ta dago kanta da sauri, lokaci daya ta hango wayarta ta bada wani haske,

Mikewa ta yi ta lumshe idannuwanta sai kuma ta bude tana dariya dariya hadi da kuka, irin emotion din nan,
A hankali ta buda bakinta ta ce" ni na san wani abu mai girma ya tike shi, mama, na san zai zo komai dare, mutumen da ya gama min rantsuwar irin soyayar da yake min?

Sai da ta gama maganar ta nufi wayarta,
Dai dai nan marokiyar ta ce" *lale komai nata daban ne, tauraruwa ce yar malan, mai sa.a ce maman malan, uwar masu gida wanke ki bamu ko jikokinmu sa dauko wannan farin jini da farar sa.a, yau ku zo ku duka ku gaisar da masu garin, ta auru, uwar malan ta auru, sai da ta dandanje ta zabo dalele kakarfa, sai da ta gyagije ta dauko zakara mai takun zaki, to yaya zata yarda yan bukulu su gane mata shi bayan tanai masa takun kura wace safiya maraicenta ce? Ba fa dan iska bane dan baiwa ne, maman malan ki je da ni na zauna a gidan gilas domin ko a aljanna in sha Allah muna fatan Allah ya yi mana domin*

Daidai nan du matan da suka rarage du sun halarta suna kallonta, kowace jira take, sauraro take ta fada mata sunnan mijin da take yiwa wannan uban kirarin sai kace wace ta auri dan shugaban kasa ko wani gagarumin dan kasuwa?

Da sauri Nana mariama ta ratsa su, bata iya yiwa kowa magana ba famanta ta karasa wajen marokiyar nan,

Tana zuwa ta ce " ladiyo, me nake ji kina fada kamar an dara auren maman malan?

Bakinta ta buda ta ce" aure kuwa gangariyarsa, sanadiyar na rangada gidar daurin auren nan kin ga damin da ya bani angon da kansa

Hajia mama da gabanta ke tsale yana wani irin dokawa, hankalinta a tashe ji take tamkar ta matse wuyan ladiyo ta matso ta ce" ke dallah rufe min baki, waye mijin wa sunnansa, waye shi a garin nan da zai iya daukan kyauta irin haka ya maki dan kawai kin yi murnar daurin aurensa da yar da ta gama yawo?

Du kallonta mutanen wajen suke, dan sam bata iya ta rufe abinda ke ranta ba a irin wannan lokacin

Sai da ladiyo ta rangada guda ta matso sosai kusa da Hajia mama ta ce"


A daidai lokacin ne Hafsat ta dauki wayar andoid dinta kirar samsung ta duba message ne akai mata

Buda message din ta yi tana murmushi dan ta tabata albishir zai mata ko ya yi mata barka

Message ne kamar haka

*zaki rayu kuwa da ni? Tsoronki nake, ina tsoron haduwata da ke, sai dai na ceci jin kunya da kuma kwana da zulumin malan, mama, su aunty da ke kanki, ki gafarce ni da kalmar da zan fada, aman daga yau igiyoyin aurena sun rataya a wuyanki, Hafsat U.R MINE*

Wayar dake hannunta ta daki, lokaci daya ta kwala ihu ta silale nan kasa

Su mama da basu bi aunty Mariama ba suna zaune suna sauraron abinda ake fada daka dakin ne suka zabura a tsorace suka yi infa Hafsat take yashe a sume

A daidai wannan lokacin Ladiyo ta ce" mijin da aka aurawa uwar malan lale shi ne uban masu gida

Sunnansa *ABDUL JABAR ABDUL BASID* wannan da NURU WALAM ke talar shagunansa a dukan kafofin talabijin dake niger, wa.inda du abinda aka saka idan aka cire za.a saka wani sai an hasko daya daga cikin shagonsa an yi talarsa ,
Wannan yaro karamin mai tashen....

Ke ki rufe mana baki , mu zaki kawowa zancen banza a nan? A ina? A ina zata ganshi? Wacece ita? A irin wannan anguwar? Kin san da wa kike magana?

Amaryar malan, jinnin sarauta, yar shuwa ta fada da wata irin tsawa tana katse ladiyo, daidai nan baban dan hajia mama ya shigo gidan a wani irin haukace, wanda yake adawa da yayan Maman su Hafsat, bale Hafsat din

Yana shigowa ya ce"....
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




5?? 2??




Yana shigowa hankalinsa tashe, karara fuskarsa take hargitse har ya kasa zama ya taya mahaifinsa salamar mutanen da suka rage ya afko gidansu a orin wannan lokacin da yan uwansa da iyayensa da bakin fuska ke tsaitsaye ya ce" ummah, ummah kin san waye wannan Abdallahn? Wannan yaron gayen dake zuwa gidan nan ne, wanda ke da iko da cikin gidan nan fiye da mu yayan da Malan ya haifa,

Hankalinta ne ya kara tashi ta ce" kana nufin dama shi ne mai wannan dukiyar? Wannnan yaron mai shige da yan daba mai magana ba risinawa mai yi mana kalon sa.aninsa shi ko wa?

Harde hannayensa ya yi ya ce" shi fa, shi da kansa


Wani wawan tsaki ta ja tana waskewa ta ce" dama wa zai kwasa idan ba abokin yi ba?

Da sauri nana Mariama ta kaleta, tana yin shiru amaryar malan ta ce" ai dama sai abokin aiki ya san kan aiki, wa zai dauki saura? Ai shi dai da ya saba shi zai kwashi abinsa

Nana mariama ta kaleta da kyau, wani abu ne ta ji ya kasa ficewa a kirjinta, a yau ta ji ba zata iya yin shiru ba dan haka ta ce" eh ai ba laifi bane, idan kika ga har ya kara nacewa mota tabata ya ji dadin tukinta, wata mitar dan ubanta komai gyaran da za.ai mata ba zata tashi ba sai dai ta ja kara ta zubar da bakin hayaki!


Guda matar nan marokiya ta kara saki tana dariya, domin kamar an saka su buda baki a tare abinka da ko.ina haske na haska dakin sai ya kasance du ana kallon su

Wace ke bima mama ce ta ce" ikon Allah, Mariama dama kema baki da kunya? Dan kanwarki ta auri mai kudi har bakin ki ya bude? To a yi dai mu gani ku tsaya ku ga zaman kafin ku fara takun kasaitar

Sai da ta juya dan nufar dakinsu ta ce" zama daram Uwar karuwa a cikin wuta!


Du da kallon mamaki suka rakata, domin kaf a cikin yayan mama ita ce mai lafia , koda an tabota takan labe ta sha kuka ne bata tankawa bata kula kowa haka har Allah ya rabata da rayuwar gidan malan

Sai bayan ta shiga cakartun magana ya bi bayanta, bata damu da juyowa ba ta yi shigewarta falo ta shige cikin dakin mama

Tana shiga ta tarar mama na shafa goshin Hafsat sun shinfideta saman bed sun gyarata sauran na tofa mata adu.a

Yannayinsu ya shaida mata da suma ta yi, da sauri ta karasa tana tambayar me aka yi? Menene?

Mama ta ce" wayar ce ta yi kara , sako ne tana dubawa sai kawai ta ihu ta fadi, mun shafa mata ruwa kamar ta farka aman kuma kin ga idannuwan a rufe mu dai munai mata adu.a

Zama itama ta yi tana gyarawa yarinyarta hijab din jikinta sannan ta dauki wayar ta duba message din

Bakinta ta tabe ta ajiye tana hararn Hafsat din a kasan zuciyarta kuwa fadi take banza ba suma ba sai dai ki mutu muna nan ma ga irin lokacin da zaki dauka baki farfado ba!


Suna nan zaune su Mama sai tofi suke mata suna tofa mata adu.a aunty nana mariama kuwa na zaune gefe tana baiwa yarda madarar da ta kada mata

Gidan ne ya dauki shiru, shirun lokaci daya haka marokiyar kanta ta yi dif tamkar ta fita a gidan

Dan lokaci aka dauka sai ga Malan ya bayana a kofar dakin yana salama

Mama ce ta mike da sauri ta nufi kofar tana goge fuskarta tana gyarawa dan ba zata so ya ga yannayin da take ciki ba

Cikin nutsuwa ya shigo dakin,
A hankali yake bin su da kallo, kafin ya amsa gaisuwar da suka jero masa sunai mata su duka

Sai da ya gama amsawar ya ce" Alhamdulilah, zaku iya tashi mazajenku na waje suna jiran ku

Ba wace ta tsaya tsaye tsaye du suka mike suna daukan abubuwan da suka san nasu ne, sukaiwa mamansu salama

A hankali malan ya karasa bakin bed din da mamansa ke kwonce

Ido ya tsura mata na dan lokaci, a hankali ya ce" mamana, tashi mana, ba kyau fa irin haka

Idannuwanta ne suka dan yi rawa jin muryar babanta, tana son buda idannuwanta tana tsoron ta bude ta ji wannan labari mai kama da almara, ita bata san da me zata kwatanta wai wai tap, ina ba zai yiwu ba, ba zai taba yiwuwa ba! Ita ta rayu da Abdul a matsayin mijinta? Mutumen da suka raina juna? Mutumen da karara ta san waye shi a harkar mata? Mutumen da macen dake gidansa kanta sai dai ta isko shi? Abdul bai iya yiwa mace yar murya ba bale ya rarasheta, bai iya bin mace ba, bai iya yabawa mace ba, ta rasa wani banzan tunani na kar ya bar malan cikin zulumi ya saka shi wasa da maganar aure, shi kennan a wasa da komai rayuwarsa zata kare? Haba dan Allah! Bama zai taba yiwuwa ba

Murmushi malan ya yi gannin bakinta na murgudawa da alamomin tsaf ta farka , kansa ya girgiza yana girmama rigimarta, wato a haka take a sankame du sun zagayeta bayin Allah

Juyawa ya yi ya yafito mama da hannunsa ya yi gaba

Sai fa mama ta dan kara waigawa tana mamakin malan hala bai san a sume take ba yake mata magana? Ko ji yake da gangan ne?

Da sauri ta taka ta cin masa ta karbi kys din hannunsa

Sai da suka haue sama ta ga matan gidan a tsaitsaye da alama kowace ya kiraya

Bude dakin ta yi sannan ta koma karshe ta tsaya, sai da malan ya shiga, suka shige sannan ta bi bayansu

Zama malan ya yi a babar kujerar da yake zama wace ba mai hawa sai shi

Su duka a kasa suka zazauna suka tankwashe kafafuwansu

Sai da malan ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce" tsarki ya tabata ga Allah ubangiji subahanahu wata.ala,
Alhamdulilah,
Kamar yanda kuka ji, an daura auren mamana yau bisa sadaki mafi kankanci jika goma , sai kyautar uwa da ta uba mota kirar Ferari daya daya, sai motar jigilar kaya wato babar mota ta uba, sai kujerar haji in sha Allah ta uwa uba da yan uwanta da iyayenta wato ku

A tare suka kalli juna sannan suka kale shi

Malan ya ci gaba da fadin" za.a kawo lefenta jibi idan Allah ya nuna mana sannan za.a saka bikin kusa kamar yanda kuka sani bana taron wunin biki a gidana, ba.ai min kade kade bale wata diner, almajirai nake tarawa a wuni ana sabkar alkur.ani mai girma da neman zaman lafia a wajen Allah

Shiru ya yi yana kallon yannayin kowace, shirun da ya biyo baya daga garesu ne ya saka shi guara babar rigarsa yana sauraron su

Hajia mama ce ta muzguta ta ce" uhum

Malan ya saki murmushi yana kada kai, sauraron su kawai yake yana jiran jin fatan alkhairi daga bakin dayarsu, aman cikin ikon Allah shiru ba wace ta yi fatan alkhairi

Dubansa ya kai wajen mama ya ce" Ramatu

Da sauri ta dago da dubanta ta kali malan

Malan ya gyara zama ya ce" daga yau, na umarce ki da ki nuna kulawa wa yayan da kika haifa, na soke maganar jin kunya kawar da kai ko kara, na umarce ki da ki buda baki ki yiwa yarki adu.a, ina so ki kula da shirye shiryen tarewar yarki!

A karo na biyu ta kuma kallonsa, kwarai ba wasa da gaske malan yake, da gaske yake ba wasa a maganarsa

Hannayenta ta hade ta shiga murzawa a hankali ,
Cikin nutsuwarta ta ce" Alhamdulilah, Allah ya basu zaman lafia

Malan ya gyada kansa yana murmushi ya mike ya shige ba tare da ya kuma tankawa kowace ba

A hankali ta mike itama dan ficewa a dakin dan gaba dayanta hankalinta a tashe yake , bata taba irin haka ba, ba.a taba haka da ita ba, hasbunallahu wani.imal wakim

Tana fita a dakin ta kama sauri, aman cikin ikon Allah sai da hajia mama ta cin mata, matar sosai dajikantaka ta fara bayana a jikinta aman dan tsabar fitina ta riko hijabin mama ta ce"malan ya yi haka dan ya nunawa duniya daban take da sauran ko? To kudinsa baya damuna! Sannan bana son kujerar makar domin ni ba zan je bautar Allah da kudin haram ba!

Ita dai mama tsayuwa ta yi sai da ta gama ta sakar mata hijab ta shiga daki

Tana shiga ta ga wayam ba Hafsat,
Da sauri ta daga kafarta ta shiga dakinta

Tarar da ita ta yi tsaye, daga ita sai dan dogon wando da rigarsa sai kai kawo take,
Yannayin fitina da neman balaki ya bayana a tare da ita

Kallon tsaf ta yi mata kafin ta tabe baki, lale Hafsat ta raina mata hankali, kuma ta yarda da ake cewa likita ya fi kowa rikicewa idan abin ya shafe shi.

Sai da ta gama kallonta sannan ta ce" ki lulube jikin ki, daga yanzu bana son na kuma ganninki ba da lulubi ba kafin a kawo magungunnan ki

Da kallo ta raka maman nata, iyeah? Shi ne abinda ta fada

Da sauri ta warto wayar nata, karfe goma sha biyun dare ne fa aman da yake ranar ta zo masu wani iri du gidan malan yara kananu kawai suka samu rintsa idannuwansu

Wayar ta danna ta danna masa kira

Ta yi ya kai sau hudu kafin ya daga da wata irin murya

Sai da gaban Hafsat ya fadi domin muryar wani irin kasa kasa, sannan bata fita da kyau

A hankali ya ce" Hafsat

Hafsat ta kara rintse idannuwanta ta kai zaune saman bed din dakinta
Niyarta ta daga murya ta darza rashin mutunci sai gata da sasauta murya ta ce" Abdul, dan me zaka min haka? Me na maka ne wai ni? Dan me zaka saka a aura maka ni bayan ka san da wanda ke so na yake shirin zuwa ya aure ni? Yanzu idan ya zo sakina zaka yi a kara aura min shi ko me?


Abdul ya kara lumshe idannuwansa yana sauraronta , a nitse ya ce" *ni ban aure ki dan na sake ki ba*

Me kake nufi da baka aure ni dan ka sake ni ba? Wani irin aure kake jiran yi da ni haka? Baka so na Abdul, bana son ka!, dan me ka min haka? Ta fada muryarta a sanyaye haka kuma tana rawa rawa

Abdul ya sauke ajiyar zuciya, a hankali ya ce" *na san bakya so na, ban roki ki so ni ba, Hafsat baki ga lokaci ba ne ni? Lokacin neman nutsuwa ne, idan kuwa zaki iya....ina nufin idan har kin san kina bukata, a yau kin saka haka a ran ki .... sai na sauka daga nan na zo in hau naki bed din*

Abdul ya karashe yana mai duban Na.ima dake kwonce kusa da shi

Shiru ya ji wayar, ba magana dan haka ya dubi screen din,
An kashe, murmushi ya yi yana girgiza kansa, dubansa ya kai wajen Na.ima, baci take kashirban, baiwar Allah, a gaskiya yana tausayinta, shi baima taba tunanin ta yanda zai fadi abu sai wannan lokacin

Kwonciyarsa ya gyara yana mika, a hankali ya furta" *na san bakya so na Hafsat, na jima da sani....sai dai ba zan iya sakin ki ba, ke na yiwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login