Showing 60001 words to 63000 words out of 154870 words

Chapter 21 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1128

bai wani yi jayaya da hakan ba har ya kai shi bakin kasuwa,

Bs kam da kokari kara ciciba Abdul ya yi ya je ya siyo abin bukatarsa ya dawo cikin motar da shi, sai sakin nishi yake, haka kuma kafadunsa jinsu yake wani iri, sun kage tun ba.a je ko.ina ba

Tuka shi ya yi ya sada shi da asibitin gwamnati , suna zuwa kudin da BS ya bashi ya bashi mamaki, domin kuwa a aljihun Abdul na wandon dake jikinsa dan gajere ya laluba cikin sa.a ya samu kudinmu jika goma goma ya ciri daya ya mikawa dan taxi ya fice ba tare da ya kula da canjinsa da dan taxin ke kokarin bashi shi dai yana tunanin me Abdul zai yi da kudi ya saka su a kanfai? Kanfai mana har cikin karamin wando?

Sunna shiga BS ya zarce Urgence,
Yana zuwa ya ajiye Abdul nan dandar kasa ya je da sauri wsjen likitocin cikin yannayin hadewar fuska ya tambayi docter
Kun san halayar manyan, sai sukai kuri sunna kallonsa, wasu har suna kokarin zilewa dan kiran masu tsaron kofa a fitar da shi dan sam yannayinsa ya basu tsoro, tun bama kansa dake aske tall yake kyali tamkar wanda ya shirbine shi da man gyada na goma

Ciro baje dinsa ya yi ya mikawa wanda da alama shi ne responsable dinsu yana kokarin karantawa ya shiga kara masa haske da nuna Abdul da fada masu cewar yana daf da mutuwa!


Da sauri ya mike ya shiga fada masu abubuwan da zasu kawo , shi kuwa ya saka aka kawo gadon asibiti mutun hudu suka ciciba Abdul suka dora saman gadon aka tura shi aka shiga dakin aiki da shi inda BS ya kasa ya tsare a cikin dakin, su kuwa suka kasa fitar da shi dan kuwa shima a kan aikinsa yake

Gannin mutumen dan gajere fari na kokarin fara duba Abdul BS ya matso ya ce" bawan Allah bafa kai zaka duba shi ba, docter nace a kira min

Hannayensa ya dan watsa kafin ya ce" ai ni din ne, ban yi magana bane dan ana iya zuwa nemana dan cutarwa,

BS ya dubi gaban rigarsa, sai yanzuma ya ga rubutun sunnan mutumen sannan ya ja baya yana jin haushin tsoro irin na mutumen, to sai me? Idan an zo nemanka ba sai ka kwaci kanka ba?

Du abinda suka san zasu yi sun masa,

Ya kawo hankali, ya dawo daga duniyar suman, aman wata irin juwa yake tamkar zai koma duniyar summan domin komai kankantar jinni ya fita daga jikin mutun sai ya juyaka bale fa Abdul ya zubar da jinni sosai, dan kuwa jikinsa ba riga haka BD ya bi duniyar nan da shi gaban kirjinsa du abin jinnin ne, shi kansa BS din jikinsa ya taba bale kuma Abdul din

Sun shiga rudu, dan har haskawa aka yi aka duba ba.a ga wani lamarin da zai mayar da jijiyar wajenta,

Docten ne ya dubi BS ya ce" daman yana irin wannan abin ne? Me kuke masa ya tsaya? Wani abin ake saka masa bayan wa.inda muka yi? Ana iya bamu traitement din sai mu yi masa mu ga ko za.a samu galaba

BS ya shiga matsowa gabansa na faduwa da irin abinda zai fadawa Abdul din, yana tsoron hakan ya jaza masa matsala, eh matsala mana , Abdul dai an fada masa uban gidansa ne, wannan kuma magana ce ake ta rayuwar Abdul dake cikin hadari=??

Yana zuwa ya zauna sosai kusa da Abdul, hannunsa ya kama ya rike inda Abdul ke binsa da kallo

BS ya sada kansa, sannan ya kuma daga kansa yana jin wani iri, wani tausayin Abdul ne ya ji na lokaci daya bayan aikinsa da yake yi, hakan ya saka ya juye harshe zuwa yaren Hausa , tsagwaronta hausa ta yan garin Damagaran,
Hausa ya yi masa ya bashi maganar du abubuwan da Hafsat ta ce,
Yanzu tambayarsa shi ne, yana gannin wannan magana mai mahinmanci ce ? Sannan ta ina za.a saka masa? Yayanene za.a yi? Shi da ya so ya je a samo rubutu da ake yi, somin ana rubutun hakan, aman kuma ga abinda Hafsat din ta ce

BS ya kirayi Hafsat da sunnan da ta zo da shi na aiki ne, dan bai san cewa Abdul ya san sunnanta harma yake kiran sunnan gatsal ba,
Shi dai da ido yake bin Abdul a lokacin da ya nuna masa ruwan zamzam dake cikin gora gangariyarsa da kuma dabino dake cikin gidansa direct daga saudiya

Baya iya magana, ba zai iya rubutawa ba, dan haka da hannunsa ya yi nuni aka karbo kwanon aikin dake hannun Nurse din dake tsaye da likitan sunna kallon abinda zasu yi, ba damar su dakatar da su, ko au hana su, du kuwa irin yanda aka san likitoci da hana magannin hausa, sai dai takarda BS ta saka ba zasu shiga hurumin nan ba, ba zasu hana ba, dan sunna iya hanawar idan wani abu ya faru sunnansu ya shiga ciki dole dole.

Da hannunsa, ya iya da kyar motsawa ya yiwa Abdul kwatancen cewa ya zuba ruwan sannan ya saka dabino a ciki,

Haka ya yi , sai da ya dan jima kadan Abdul ya yi nuni da a zuba masa a hancin

Jim BS ya yi yana duban Abdul, kowa ya sani, irin yanda ruwa a hanci ke gigida mutun, gashi wannan harda wani abu a ciki kuma da dan yawansa
Gannin Abdul na kara galabaita ya saka BS zuwa ya talafi kansa, bai taba jin wani irin tsoron Allah da son ambatonsa irin na wannan lokacin ba, sai kace bai taba gannin mutuwa ko gawa ba, yannayin da Abdul ke kokowa da numfashinsa ya tsoratar da shi, gadhi dai Abdul ya riki sallah, dan baya wasa da sallah, yana nafila, wace sun sha gani da idannuwansu dan idan suka ji motsi dole su leka, du irin danyen kansa ya kiyaye wadinnan, ga bautar Allah daga boye, baya sadaka ya shaidawa duniya zai yi, bai taba bayar da kyauta ya yarda wani ya san shi ne, yana iya yinsa dan gannin ya kare abubuwa da yawa, yana irin wannan jijiga tamkar mai fitan rai, to ina da shi idan ya fadi rashin lafia? Allah fa zai ce ya kiraya shi marar kunya, Allah zai nema shi mai mantap alkhairi, sai daga baya zai nemi Allah ko me? (Ka tashi bawa, ka tuba, domin kuwa baka san zaka kai goben ba? )

Hannunsa na bari, zufa ta wanke masa fuska haka ya samu ya dildilawa Abdul ruwan zamzam din bayan ya yi bismillah

A hannunsa Abdul ya dage idannuwansa, bakin ya bace sai farin ya sake zuwa duniyar summa ko mutuwace? Wace ta tsoratar da shi har ya ajiye kan Abdul ya diro ya dora hannyensa saman kai ya shiga kai kawo cikin tashin hankali.............





..........comment comment commemt
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 6??

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya da jira bane=?O?



Likita ne ke ta kokarin danna kirjinsa,
Kin dawowar da ya yi ne ya saka fa sauri aka kawo abin dannar kirji

Aka mikawa likita aka matso likid din nan aka goga a sama sannan aka shiga kokarin kara tayar da shi ta hanyar murza abubuwan nan biyu aka dora saman kirjinsa,

Sai da ya dago baki dayansa sannan ya koma yarab tamkar matace

Wani ihu BS ya saka a fili ya furta" shikenan, ya mutu, mun karasa masu aikin su, mun kashe shi!

Kallon da docter ya yi masa ne ya saka daya daga cikin nurse kokarin fitar da shi yanzu kam, sai dai tirjewar da ya yi ya sakata sakinsa ya kara dawowa yana kallo za.a dora masa a karo na biyu

Sai da aka kara jonawa aka dora masa,

Wannan karron kam alhamdulilah, yana yin saman da kirjinsa sai ko injin ya shiga bada wani kukan dake nuni da ya dawo duniyar masu rai,
Da sauri Doctern ya shiga gyagyara du abinda zai gyara nurse na daimaka masa tana bashi du abinda ya ambaci sunnansa,

A haka suka gama komai sannan du suka tsaya sunna kallonsa,

Nurse di Docter ya umarta da su je, bayan ya cire safar hannun ya rage daga doctet sai BS tsaye kuri sunna duban Abdull

Ya jima, ya jima sosai, domin a kadan ya dauki minti talatin a wannan yannayin ,
Sai can ya shiga kokarin bude idsanuwansa, sannan bakinsa ya shiga motsawa yana mai adu.ar tashi a barci

Kamar kuma wani hadin baki sai wani bakin jinni bulbul ya bulbulo daga hancin wanda ya sanya Docter zabura ya nufe shi ya saka abu yana dauke jinnin, inda Abdul ya ringa jin wani sanyi sanyi wani sakayau, a hankali abinda ya rike gansa da wani irin nauyi da duhu ya ringa barinsa har ya sake shi baki daya,
A hankali ya bude idannuwansa da suka kara girma sukai jajajir ya sauke a kan BS da docter, sai da ya gama yi masu kallo, sannan ya juya ya shiga bin dakin da yake kwonce da kallo

Shi dai bai ce komai ba, har aka jima sosai domin Docter ya fice da jinnin dan aunawa gannin abinda ya hadasa masa haka, ya rage daga shi sai BS sun yi shiru su duka ba wanda ya ce wani abu, ba wai dan muryar Abdul bata dawo ba, aa kawai bin BS da kallo yake yana tunna wasu abubuwan da ya gani da wanda yake tine, saima suturar dake jikinsa wato daga shi sai gajeran wando

Docter ya jima da fita kafin ya dawo, sai da ya dawo yake tambayar ya shi ko sha wani abu?

BS ya ce" ai bai fara magana ba har yanzu bare na ji abinda yake son ci

Docter ya juya wajen Abdul dake dubansu ya ce " to ka kwatanta masa mana, idan baya magana na san abin wahalar da ya sha ne kafin muryarsa ta saki,

Matsowa suka yi su duka biyun sunna duban Abdul, nan fa suka shiga kokarin yi masa yaren kurumci sunna kwatanta masa abin ci ko na sha wane yake so, kuma wani kalla?

Sai da ya kare kalle su baki dayansu sannan ya yi murmushi yana kokarin mikewa zaune

Kama shi suka yi suka zaunar da shi, nan ya dube su kuma, sannan ya ce" bana jin yinwa

A tare suka dubi junnansu, kai dama yana magana ka ce bai fara magana ba? Docter ya tambayi BS

BS kam mamaki ya hana shi magana bale ya baiwa docter amsa, sai kawai ya shiga murmushin shima yana duban Abdul na kokarin cire allurar dake bashi karin ruwa da kansa,

Docter ne ya ce " aa kar ka cire, wannan na karin ruwaa ne ko zaka ji dadin jikinka

Abdul ya dubi docter da kyau ya ce " likita, ina jin jikina da wani irin karfi walahi, ban jigata ba, hancina ne ya dan zubar da jinni, ba.a dake ni ba,

Docter kam zuwa wannan lokacin baima san abinda zai cewa bayin Allahn biyu ba,

Abdul ne ya dago yana kallon yanda Docter ke kwonce masa yan abubuwan allurar da ya saka ya sasaka masa a jiki ya yi kamar ya daure shi ya ce" likita, bana son ana daure ni, du sai na ji na rikice , in dai ba mutuwa na yi ba, kar a daure ni

Docter kansa kawai ya gyada ya karasa kunce Abdul yana son fada masa sai gobe za.a salame su, domin yama ta yi an fara kiraye kirayen la.asar sai gannin Abdul ya mike ya yi yana kallon dakin bai ga ko irin rigar mararsa lafia ba bale ya dauka ya saia

Dubansa ya kai kan BS dake tsaye ya ce" ina rigar asibiti ne??

Docter ya dube shi da kyau kafin ya yi murmushi ya ce" ai oga bamu da shi a nan mu, wannan dakinma mun tanadeshi dan irinku, ba kowa ake sakawa a ciki ba,

Da mamaki ya dube shi, ya ce" ku su wa? Wace asibiti ce?

BS ya dan zaro ido , kafin ya tari numfashin Doctern ya ce" am, am sire mu je kawai, ga rigata da wandona bara na je cire sai na je na tsayar da taxi,

Abdul kara zaro ido ya yi, taxi? Taxi fa yace? Me ya hada shi da taxi? Shi ko a saudiya bai shiga taxi ba, yana kallo BS ke kokarin cire kayansa, bai hana shi ba, dan walahi ba zai yarda ya ratsa gari ba kaya ba, idan fa ya hadu da wanda ya sani? (Abdul, a taxin? A dazu da ka ratso ko dan kana duniyar summa ne?

Bawan Allah BS haka ya cire kayansa, Allah ya taimake shi, shi wandon na ciki ya kai har gwuwarsa sannan sakake ne, dan haka da mamaki ya bi Abdul da kallo har ya saka kayansa inda sukai masa wani kabe kabe rigar ta wani irin tamke shi dan sun masa kadan, wandon kansa ya tsalake masa sosai tamkar dan izala aman kuma da damamiyar riga,

Ido ido sukai da doctern sannan ya fice ya nemi taxi ya tsayar

Nan fa Abdul ya shiga taxin gidan baya ya hakimce inda BS ya shiga gaba ya fadawa mai taxi cewar sun yi shata har inda za.a kai su

Shi dai Abdul yana kallon gari, da irin yanda motar ke sama da kasa da shi, da irin yanda suke kutsawa sunna wani rin gudu, a haka suka zo suka wuce danjar da ta bayar da jar wuta a guje inda Abdul sai da ya dora hannunsa samman kansa ya leka da kyau ya dubi mai taxi din ya ga ba yaro bane datijo ne sosai aman yake wannan tukin
Sai,da suka zo danja wace polisai ke tsaye ya ja ya tsaya kafin ya lailayo wata ashar ya dura ya ce" mutanen banza ido yay masu kuri, ka fice ka janyowa kanka balaki, to ba dai aljihuna ba!

Abdul kam komawa ya yi ya zauna yana mamakin ashe bai ga komai ba? Shi bai taba shiga taxi ba, yana hawan tsofafin mashin ya shiga wurare masu hatsarin gaske, aman yau gashi a taxi zata kashe shi!

Tafiar da idan a motocinsa nene bai fi su yi minti ashirin ba, sai gasu a minti kusan arba.in

Ko tsayuwar da direban motar zai yi sai da ya wani irin ja ya yi wani kuuuu motar ta fitar fa hayaki sannan ya tsaya ya fitar da kansa ya ce" ikon Allah, jama.a ku ga ginnin gida tamkar ba za.a mutu ba? Yanzu mai gidan nan haka zai mutu yana ji yana ganni a nutsa shi a kabari? Han gaskiyar mabaraci da yace a baku a nan mu a can mu samu

BS tamkar ya mangare mutumen haka yake ji, gashi tsaf sai da Abdul ya gama sauraronsa ya bude ya fita daga motar yana duban yanda BS ke hararn mutumen???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?, aman cikin ikon Allah sai mutumen ya ce" kai yanzu bawan Allah shaye shaye ka yi ka tunkaro gidan nan mai zagaye da arnawan sojoji ko rigar kirki baka da ita , ka dauko wannan shi kuwa da wata riga a dame a jiki tamkar bazawarin kwarto da wani wando ko sauka kasa bai yi ba yana lumshe ido uwa ya hadiyi jinjirar tinkiya?

Tsayuwa ya yi ya dafe tsatsonsa sai da mutumen ya gama ya shiga kokarin tayar da mota yana mika hannu BS ya bashi kudinsa motar sai tayar da hayaki take abinta Abdul ya dubi BS da du ya daburce ya kankance ido ya ce" ni, ni din ne dai bazawarin kwarto? Bama saurayi ba ko *Bashi*?
Ni dai ne mai tsangalalen wando ko? Na gode!

Yana gama fda ya kara gaba abinsa yana tafia da sauri da sauri dan da tazara sosai dan kuwa ta kofar bayan ya saka a ajiye su , to shi wannan direban da ta gaban kofar ya je yaya kennan?

Wai bama wannan ba, a ina sire ya san sunnansa Bashir? Ita mana! Ya huci ita zata fada masa du sunnayenmu na gaskiya?
Wata zuciyar ta bashi amsa inda nan da nan ya ji haushi ya turnike shi, nan kuwa datijon nan ya ce" kai yaro ya haka? Cinye min kudin zaka yi ne ko me? Ka bani kudina ko na fito mu yi wace zamu yi da kai a wajen nan dan bari gannina tsoho, na fi ka iya shegantaka

BS ya ciro jika goma ya dankawa tsohon yana dubansa ya shiga neman canji, nan ya duko ya ce" bab, ai duka na baka, ka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login