Showing 147001 words to 150000 words out of 154870 words

Chapter 50 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1140

ya tabata da wata ce da tuni ya samu amsar zata so shi ko aa, aman ita ta bar shi a duhu ya kasa gane gabas din maganarta tamkar tandun kwali.

Basu su tashi a wajen ba sai da kiraye kirauen sallah ya fargar da su,
Nan ya taimaka mata suka mike suka nufi dakinsa

A keana biyun nan sun kasance cikin aminci, shakuwa, kulawa, madaukakiyar soyaya

Hafsat cancara kwaliyarta take kafin ta koma bangarensa idan ya fita,
Eh lale bai ji da bakinta ta furta masa kalmar so ba, aman yannayinta , ayyukanta a gare shi, irin yanda a yanzu take bashi hafin kai a bed, harma ta neme shi dan kanta wanda shi kansa yana mamakin dama harijar mace ce ita? Irin yanda idan yanai mata hira take bashi hankalinta baki daya harma ta dara na darawar, na jimami fuskarta ta nuna, komai na zaman lafia sai dai ya godewa Allah
A haka har lokacin fitarta a aiki ya yi sukai wata irin rabuwa tamkar zata bar gari, tamkar ba zasu kuma haduwa ba dan kawai zasu raba kwana na kwana biyu kacal, hakan ya sakata hawaye da ta koma bangarenta sannan ta tashi da azumi domin a gaskiya ita ta san wannan lamari na bukatar mijinta dake damunta ya fice misali, sarai take cikin damuwar rashin mijinta, sai dai ta kwana da sanin ba na ita kadai bane dan haka sai ta gayato hakuri ta yafawa kanta ta tura masa sakon tana azumi danma kar su yi tsamaninta wajen kari da kuma cin abincin dare

Sarai tausayinta da tausayin kansa ya kama shi, a hankali ya mike bayan ya salami Na.ima daga cin abincin safe ya nufi bangarenta kafin ya fita aiki

Dakatawa ya yi daga bakin kofa tun da ya shigo yana kallonta,
Tana yannayin mutun mai sanyi, tana yannayin damuwa

A hankali ya karasa inda take kwonce
Hannunsa ya dora saman mararta ba da nufin wani abu ba sai dai taurin da ya ji wajen ya yi ne ya saka shi sauke idannuwansa a kan fuskarta da sauri

Itama jin ya tabata da kuma jin zafin dana mararta da ya yi ya sakata saurin zabura tana kallonsa

Da yannayin damuwa yake kallonta, a hankali ya saka hannayensa ya janyota jikinsa, cikin nutsuwa ya ce" bab, me ke damun ki??

Murmushi ta kakalo tana kallonsa a hankali ta ce" ba komai, ina azumi ne

Idannuwansa ya lumshe yana kallonta ya ce" me ya sa mararki take da tauri haka?

Kallonsa take, ita kam bara san mararta na da tauri ba dan bata taba ganewa ba, takan ji dau marar tata ta yi mata nauyi sosai, sai dai sam bata taba jin taurinta ba

Kallonta ta kawar daga fuskarsa a hankali ta ce" ban san tana da tauri ba

Mikewa ya yi ya ce" kwonta na ga?

Irin kwoncin da ya tarar da ita ta yi ta kuma yi tana kallonsa
Tamkar wani likita ya kara yaye rigarta ya shiga dana cikin nata a hankali yana kallon yannayinta

Rike hannun nasa ta yi tana yatsina fuskarta dan walahi ita zafi take ji sosai

Daina danawar ya yi ya shiga shafawa a hankali yana kallonta ya ce" yaushe rabonki da al.ada?

Hafsat ta amsa shi a cikin sanyin murya cewa" wannan watan ma na yi

To me ke damun ki?

Hafsat ta daga kafadarta

Abdul kam ji ya yi hankalinsa ya kasa kwonciya, gashi tana jini da sai ya ce cikin ne bai fita ba, mai ke damunta?

Agogo ya kalla ya ga takwas har ta yi dan haka sai kawai ya mikar da ita ya bata hijab dinta ya ce" saka mu.je asibiti

Kallonsa take bayan ta saka din ta ce" aman ni ai lafiata kalau, bana jin wani ciwo fa

Abdul ya gyada kansa ba tare da ya bata wata amsar ba ya kama hannunta ya jata a hankali suka fice

Suna fita motarsa suka zarce
Kys ya yiwa motar kafin su kama hanya

Ita dai kawai kallon hanya take, bata san na me zai kaita asibiti haka ba ita lafiarta kalau
Gabanta ne ya fadi na tunanin ko dai shima yana tsantsamin bata da lafiya ne sakamakon wannan yanayi
Harhade fuskarta ta yi tana jin kamar ta dadage ta zunduma ihu ko zai mayar da ita gida tun kafin ya kaita a fadi wani abinda zata ji kunya

A haka suka karasa cikin clinik din

Wannan karon kin ya riko mata hannun ta yi ta dai bi bayansa har suka shige wajen gannin likitan matan

Sun taki sa.a mace biyu ce kawai zaune dan haka suka zauna suma yana mai binta da kallo sai ta ga ya sakar mata murmushi aman kuma bai yi mata magana ba

A haka har zuwansu ya zo suka mike suka shiga tare

Tun da ya shiga ya ga wani jikeken namiji mai kalar fatarsa zaune yana aikin duba matan mutane gabansa ya fadi, ransa ya yi masa bakikirin ,
Bai aune ba sai gani ya yi har ta zauna a farar kujerar duba mararsa lafia ta bada hankalinta wajen likitan

Sai da ya gama rububuce rubucensa ya dago ya zuba masu kallo,
Fuska Abdallah ya yatsina yana kallonsa, a zuciyarsa kuwa fadi yake mumuna ne kai, sam baka da kyau

Daga kafa ya yi da sauri ya karasa shima ya samu waje ya zauna sai muzurai yake

Likitan da ya gama kallonsa ya ga bai bashi hannu a matsayin wanda ya tarar suka yi musabaha ba kuma dai a yannayinsa bai ga yannayin mai duhun kai ba sai shima ya ki bashi

Sai da ya buda katon litafinsa sannan ya dube su ya yi masu tambayar waye ba lafiar? Yaya sunnansa? Shekarun haihuwarsa?

Tana shirin yin magana ta ji Abdul ya ce" Hafsat , Madame Abdul Jabar, shekarunta ashirin da uku

Kallonsa ta yi, inda shima likitan ya kaleta yana tunanin to ko kurma ce ita din??

Rubutawa ya yi sannan ya basu hankalinsa kacokam ya ce" menene damuwarta? Wace irin rashin lafia ke damunta?

Abdul ya hadiye abin haushin da ya tsaya masa a makogwaro sannan cikin isa shima ya ce" mararta ke da tauri, tana daukan zafi, bayan as nrmal marar mutun bata haka

Kansa ya gyada ya kara yi masu tambayoyin da ya dace kafin ya mike ya nuna mata bed din da zata kwonta kusa da wani allon haskawa wato wata yar karamar tv

Irin kwonciyar da ta yi kanta sai da cikinsa ya juya, wannan a haka din idan ba shi zai haye ruwan cikinta ba gaskiya wani garjeje ba zai kale masa yannayi mace ba ehe!

Bai gama fahimta ba sai da ya ga ya kai hannu zai yaye hijab din jikinta ya kai wajen mararta, waje mai daraja da daukaka a idannuwansa, waje mai tarin sirrinsa

Hannunsa ya kai da sauri ya tare nasa hannun,
Dago da idannuwansa dake cikin gilas ya yi sukai ido hudu,

Abdul ya lumshe idannuwansa ya kuma budewa yana kallonsa bai ce da shi komai ba

Doctern ya saki murmushi kafin ya janye hannunsa a hankali ya juya ya fice a office din

Hade fuska ya yi tamkar bai san meye daria ko fara.a ba inda Hafsat mamaki tamkar ya kasheta

Kanta ta girgiza tana kokarin mikewa da niyar sai su tafi ai tunda likitan ya bara masu office din baki daya!

Bata kai ga tashi ba sai ga likitan ya dawo tare da wata likitar mata

Zuwa ta yi cikin fara.a suka gaisa ta gabatar da kanta ita din ma doctern mata ce

Waje Abdallah ya matsa ya bata ya tsaya gefe kusa da kan Hafsat dake binsa da kallon ga irinta

Shi dai ko a ransa saima maida hankalinsa a wani ruwa ruwan da likitar ta matso ta shafa a marar Hafsat din

Dora abin ta yi ta shiga yawo da shi a hankali tana kallon allon wannan karamar tv din

A hankali ta ce" haka ne doctern, gayanan dan jaririn foetus

Da sauri Hafsat ta rintse idannuwanta tare da jin gabanta ya fadi, Foetus? Aman ai tana al.ada, kennan cikinta bai fice ba? Cikinta yana nan? Gabanta ne ya fadi cike da tsoron me mijin nata zai yi shi da baya wannan ra.ayi a yanzu?

Sai dai yannayin da ya shiga a lokacin da likitar ta tsayar masa wajen da dan karamin halitar da ba.a gama ba aman ana iya gannin abin tamkar wani kadangare sai ya ji gaba daya jikinsa ya dauka

Tsurawa abin ido ya yi, ba.a gama halitarsa ba, bai san kalar da zai bada ba, aman ya ji gaba daya jikinsa ya dauka da kaunar abin,
Ji yayi dama kar ta daina haska masa, ji ya yi dama a janyo wata biyar din da suka rage ya taka duniya ya ganshi,
Kaunar abin, wani irin yamyam ya ringa ji inda ya duka yana shafa wajen
Cikin nata ya dan tada , sai dai ba zaka yi tunanin dan mutun bane a ciki sai dai ma ka yi tunanin nrmal haka cikinta yake

Wata kwala ce ya ji ta tarar masa a cikin idannuwan nasa, a hankali ya karasa kusa da fuskarta ya duka sosai ya kama lebenta
Idannuwansa ya lumshe ya tsotsi na kasan cikin wani irin sanyi sannaj ya saki yana kallonta
A hankali ya ce" ina son ki Hafsat, plz ki so ni? Ki so ni tun kafin yarinyar mu ko yaron mu ya taka kasa? Hafsat zaki bani baby

Idannuwanta dake kallonsa ta ji sun mata nauyi cike da hawaye
A hankali ta ce" Abdallah *I LOVE U*

gaba dayansa ya ji kafafuwansa zasu gagara daukansa, hakan ya saka shi zama saman kujerar dake ajiye kusa

Idannuwansa ya lumshe, sai ga wasu hawaye masu dumi
Yau babar rana ce a gare shi, yau ya tashi cike da ni.ima , Alhamdulilah shi ne abinda ya iya fada

Sai kuma tunanin mahaifinsa ya diro masa a zuciyarsa
Dama haka ya ji a lokacin da ya san matarsa na dauke da cikin dansa na farko? Kai, wannan madaukakiyar soyaya ita uba ke ji idan ka ji zaka samu yaro?

Ajiyar zuciya ya sauke suka mike ya kama hannunta dan du yanda ta ki sai da ya riko gam a hannunsa suka fito

Murmushi kawai yake saki, sai ya kaleta, ita kuwa kunya ta cikata dan likitocin nan sun sha dariyar irin yanda ya zaburo ya ringa bata muah du inda bakinsa ya kai cike da murna da farin ciki gabansu ba wani kunya , harma suka yi sabo da doctern inda ya kara fahimtar inda ya nufa harma ya ji ya birge shi

A hankali ya karasa anguwar da malan ke zama ,
Farin ciki ne ya mamaye zuciyarta a lokacin da ta hangi mahaifinta zaune cikin shigarsa ta kamala

Tana kallon yanda Abdul ya duka yana gaishe shi aman Malan ya mikar da shi yana ta doka masa murmushi

Tana kallonsu har suka karaso wajen motar aka bude nan Malan ya yi tozali da yarsa da yake ji tamkar nama daya kwal a cikin miya

Murmushi ta yi hannunta cikin na malan, shima yana kallonta yana mai jin farin ciki a ransa, ko ba.a fada masa ba shi ba yaro bane, koda basu sani ba shi ya fahimta, yarsa ce fa, shi ya raini abinsa, ya gane me ke tare da mamansa, lale ya godewa Allah, murna ce cike da ransa wace ya salame su bakinsa kamar ya kai kunne

Gidan mama ya ajiye Hafsat inda ya ki shiga ya ce da ita zai je wani waje ya dawo

Bai zame ko.ina ba sai kasan wata bishiya mai cike da innuwa sanyayen waje ne mai cike da ni.ima

Zama ya yi waje guda ya dauki wayarsa ya danna kira

Kiran na shiga aka daga


Shiru ne ya dan ratsa kafin a hankali ya ce" ka dawo cikin Gari Abu Abdellah


Da sauri mahaifinsa ya cire wayar ya kali sunnan, ya kuma mayarwa a kunnensa
Bakinsa na rawa rawa a hanklai ya ce""""
[9/26, 5:28 PM] BAK'A CE: >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 9??


A hankali ya ce" Abdu?

Abdul ya yi murmushi mai sauti ya ce" Abih

Ajiyar zuciya ya sauke, da sauri ya ce" dama zan kuma jin sunnan da murmushi a lebenka?

Abdul ya kuma yin murmushi bai dai ce komai ba

Abdul Basitt ya ce" ko yanzu Allah ya amshi raina na cika burina Abdallah, na gode, na gode, baka san irin farin cikin da ka saka ni a yau a yanzu ba, baka san irin yanda na ji a zuciyata ba

Abdul ya ringa sauke ajiyar zuciya shima jinsa yake sakayau, ashe ka riki mutun kanai masa fushi da gabama ba wai wani jin dadi bane sai tarin nauyin fake azuwa saman zuciyarka da faduwar gaba idan ka ji sunnansa? Mahaifinsa ya tafka kuskure a rayuwa, ya aikata laifi mumuna na hanyar saduwa da yar da ya haifa, sai dai hakan ya faru bisa sharin magabata, sharin abokan zama , banzayen abokai masu kai mutun ga halaka,
An kasheta dan a dora masa laifi
Ya yi nesa da su dan tarin kunyarsu, yana jin kunyar haduwa da mahalincinsa a irin wannan rayuwa hakan ya saka shi kauracewa kowa ya kadaice kansa da neman gafarar ubangijinsa da neman zabinsa
Dansa cilo ya rayu cikin kunci da tunanin bayan bata rayuwar yar cikinsa shi ya kasheta haka kuma ya kashe mahaifiyarsa sannan yake bibiyar rayuwarsa dan dukiyarsa

Du irin abubuwan nan suka taru suka saka gaba mai tsanani da rashin fahimta tsakanin dan da uban
Aman da yake buwayi gagara misali ya kaiwa kukansa
Ya duka ya zubar da komai nasa
Ya kasance babu wani abu tsakaninsa da Allahnsa wanda bai fito ya fada ba,
Ya yi kukan jin kunyar ubangijinsa da irin abubuwan da ya aikata
Ya nemawa yarsa da matarsa gafara
Ya kuma roki da ya tausasa zuciyar dansa cilo ya kasance koda shi daya zai wanki gawarsa ya yisa yana mai bi a hankali yana yi masa shinfidar kabari mai ma.ana,
Sai gashi sarkin sarakuna
Mai mulkin da ba algus
Wanda zaka roka ya baka in ka kuma roka ya kara maka ya yi ta baka ba tare da ya gotanta maka ba
Wanda zaka yiwa laifi mai tsanani idan ka tuba ya karbi tubanka harma ya daukaka ka? Mai annabi aban fati ya nuna masa ranar da dansa na cikinsa ya nemi da ya dawo kusa da shi bama a ya mutu ba
Bashi da bakin magana,
Bashi da abin mamaki
Burinsa ya kafaice ya kai sujada
Idan goshinsa a kas yakan ji kansa sakayau ne, yana jinsa a cikin nishadi kasancewa a fadar Allah, zai je ya tsaftace wajen salarsa, ya kara saka turare ya kai goshinsa kasa ya yiwa Allah kirari, ya yabi manzanninsa da sahabansa
Zai rubar da hawayen farin ciki kafin ya tatara ya kaura kusa da shi

Cikin muryar farin ciki ya ce" Abdallah, Alhamdulilah

Abdul kansa dake jin dadi har ransa ya ce" Abih, zan so ka zauna cikin gidana, kusa da mu duka , Abih zan so matana su yi zumunci da soyayar junansu, zan so su zauna da ni da zuciya daya
Abih, basa fada, basa gaba, sai dai basa shiga harkar junna kuma daya bata damu da halin da yar uwarta ke ciki ba

Shiru Abih ya yi , tun da ya ce ya koma cikin gidansa da zama da ta fado masa a rai,
Da gaske ya huce harma zai yarda ya zauna tare da matansa bayan ya afkawa yarsa ta cikinsa????

Abdul ne ya katse masa tunaninsa ta hanyar fadin" yanzu ita Kauriyata dake cikin wannan yannayin idan aka yi katarin tana da wani bukatar ni kuwa bana nan sai dai ta yi hakuri? An ce ba.a son mai ciki ta nemi abu ta rasa, idanma haihuwa ta kamata bana nan yaya za.a yi kennan? Ko hali na rashin lafia?

Wani murmushin ya saki a fili ya ce" inyeh, zan zama papy? Ita maman malan din?

Shiru abdul ya yi, sai kuma ya ji wani yannayi mai shige da kunya ya kama shi,
A hankali ya kashe kiran yana sosa bayan keyarsa yana murmushi,

Message ya shigo masa mai tsayi , budawa ya yi ya karanta kamar haka" kai zaka zama jajirtacen namiji a cikin gidanka Abdu, kai zaka hada kan matanka, sannan ka yi ta adu.a
Zan dawo cikin gari kusa da kai aman ba zan zauna da tsufana da komai a cikin gidanka ba , aa ba zan sakawa yara ido ba, zan dai kama wani gidan da ya fi kusa da kai, sannan ka sani ba zan lamunce su dorawa dana daya cilo hawan jini ba, koma waye zan dauki tsatsauran mataki a kansa ehe!

Murmushi Abdul ya saki, sai kuma ya rubuta
"HARDA KAURIYATA ABIH?

murmushin shima ya yi ya ce" *Eh harda maman malan, kai koda kai da kanka ne*

Jinsa yake cikin nishadi, karshe dai hirar haka ta kare ya dauki hudubar Abansa cewa ya yi masu jan ido idan suka ki shirya kansu, zaman kishi ai ba hauka bane, kuma aure sunnan ma.aiki ce

Hafsat dake gidansu yau ta yi matukar mamakin irin yanda mamanta ta ringa nan nan da ita,
Bata gama mamakin ba aka shigo da kayan kwadayi wai malan ya ce a kawowa mamansa
Ai kuwa ta hau tande tande tana murna dan kuwa azumi tun a wajen likita ya fice domin sai da ta cika cikinta da ruwa kafin a yi mata aikin da farko ta so kiyawa Abdallah ya ce shi ai dama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login