Showing 9001 words to 12000 words out of 154870 words

Chapter 4 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1147

nan, sai kuma wajen dake huro zafi ,

Fita suka yi, ba wanda ya yiwa dan uwansa magana, inda tana ji, tana gani, tana son ta mike aman ta kasa,

Daga jikin kofar aka bude yar kofa aka turo mata wani faranti mai dauke da magani d goran ruwa da audugar mata , da pant, da kuma wani sabulu dan karami mai kyau,

Ta jima tana hangen abin da juwa juwa, a hankali ta ringa jan jiki har ta karasa wajen da suke ta dauko farantin,
Zama ta yi ta karanta sunnan maganin, bata san shi ba, aman ta ga bayanin na sauke ciwon mara ne,
Bata tsaya wata wata ba ta sha maganin nan sannan ta kwonta nan tana kara cikwuikuye sket dinta tana tare jikinta dan kar ya bata mata jiki,

Ta samu kamar minti talatin, tana barci barawon da ya dauketa, kafin ta farka a firgice,

Dakin ta shiga bi da kallo, sannan ta mike tsaye tana duban wajen, harda su auduga da pant din da aka miko mata,

Kanta ta kara dagawa tana dubam dakin, ba camera, bata ga camera ba, dan haka ta nemi waje ta zauna tana duban waje guda cike da fargabar ina ne nan? Ta san dai ba prison bane,
Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Allah in dai dan a keta min hadi aka satoni aka kawoni wajen nan Allah ka kasheni kafin su zo su fi karfina, Allah kar ka bari su cinma burinsu =?O?
Haka ta zauna, idonta biyu, bata san karfe nawa bane, bata gane lokacin sallah, bata gane dare ne ko rana, sai dai idan ta gaji da zama ta canza waje ko ta mike tsaye ta kama kofar nan ta yi ta jinjigawa aman bata ko dar bale har ta bude,

Magannin nan da alama yana saka baci, domin wani bacin ya kara fuzgarta sai goshin asuba ta farka dalilin bude kofar tata da ta ji ana yi,

Da sauri ta dauki farantin nan ta labe daga gefe, ana budewa ta daga zata kwadawa wanda ta shigo, sai dai ta ji an yi raf da hannunta,

Dubanta matar yar dagwas take da mamaki, wannan kazamar kuma? Ya aka yi aka kawota wannan aikin da sai yayan masu gata, masu gatanma masu hanya, masu hanyar ma sai sun hau table sun zana jarabawa har kala biyar,?

Hannunta da ta tare ta sake mata a hankali, sannan gurds din dake tare da ita ya karbe farantin,
Abincin da aka miko mata ta ga bata ci ba,
Dan haka ta dauko abincin tana dubanta ta kawo mata kusa da ita, inda take tsayen ta mika mata ,
Murmushi ta yi mata ta ce" ciki da yinwa, ko fada ne, bashida wani armashi Hafsat

Ido ta zaro cike da mamakin ya aka yi ta san sunnanta?

Matar ta dafa kafadarta ta ce" kar ki yi mamaki, ba sunnanki kawai na sani ba, harta Malan, da Ummi magaifiyarki na sani,
Ki kwontar da hankalinki, ki ci abinci cikin gagawa mu je ki yi wanka domin yau za.a fara,

Hafsat ta yi dandaja tana dubanta, yau za.a fara? Za.a fara me?

Jiki a sanyaye ta dubeta ta ce" aman dan Allah ina ne nan? Me aka kawo ni yi nan?Allah dai ya sa ba karuwanci kuka kawoni yi nan ba, domin bani da ra.ayin hakan!

Murmushi matar ta yi tana dubanta, eh gaskiya ne, bata da tsoron abu, kuma tana da ra.ayinta, dan haka a fili ta ce da ita" ko daya, ba abinda muke yi kennan ba,
Kin shigo nan gidan ne wajen horon Manyan sojoji ba sojojin dake cikin gari ba, aa , irin wa.inda sai fitina ta ki mutuwa ake kaisu, wa.inda cikin gari kuke kiransu da kurame, wa.inda idan sun je waje dan kashe tarzoma basa bambanci suke hadawa su kashe tarzomar ba ji ba gani,
Sai kuma *BODYGUARD* bodyguards mata da maza, manyan bodyguards masu baiwa shugaban kasa tsaro, da manyan yan siyasan da suke iya biyansu, da manyan bakin da suke shigowa kasa suke iya biyansu, da banban jujun kotu, da sarakan ketare dake iya faukan nauyinsu, ana tura takardunsu ne kasa kasa domin aikinsu bai tsaya iya nan ba, suna da damar fita waje su yi aiki idan ta kama, ana iya daukansu aiki mai takaitacen lokaci kamar sati biyu, ko uku, ko wata, ko wata biyu, ko biyar,
Haka kuma ana iya daukansu aiki na dindindin ana biyansu kudi masu matukar yawa,

Bata tsamaci tambayar da ta cilo mata ba cewa" kennan dai rayuwarsu zata kare a bautawa wasu ba maganar aure?

Sai da ta yi shiru tana dubanta kafin tace" akoy damar yin aure,

Da yannayin izgili Hafsat ta ce" wace iri ce damar? Sannan na ji kin kama sunana kai tsaye, bayan na kasance mai boye sunana, na ji kin kureni ta hanyar kama sunan mahaifina da kiranyen da ake yiwa mahaifiyata, dama dan gari haka yana zama fitacen dan ta.adan da ya cancanci zama gidan yarin *KUTKALE?*

Matsowa ta yi kusa da ita ta ce" daman sai dan jeji ke zama dan ta.ada?

Hafsat ta girgiza kai ta yi murmushin yake ta ce" aman a sanina , kafin a rufe ni, niger kasa ce ta incin kai, kasa ce da mutun keda damar zaban abinda zai yi na aiki a rayuwa, koda kuwa an dora min laifin ta.adanci me yasa ba za.a bani damata na kasancewata yar kasa mai cike da shaidar hakan na zabi aikina? Ko a zaman wata takwas da sati biyu da na yi a gidan yari an canza hakan?

Kallonta ta kara yi tana kara mamakin yarinyar, kuma ba komai ya sa ta biye mata tana bata amsa ba, sai dan ta kara tabatarwa da girman iliminta ta hanyar tambayoyinta, da yannayin da take yin tambayar, dan haka ta ce" eh, haka, Niger kasa ce ta inci,
Anman ke da kika fito a matsayin mai babar laifi a kasa, kika cancanci mugun hukunci ta hanyar rataya ko harbe ki, aman kasa mai adalci ta barki ci gaba da numfashi, harma aka baki opportunity na zama babar Bodyguard da kuma kunada masu tsaronku idan har kuka gama cinye jarabawar nan, me kike nema na kari??

Hafsat ta tsayar da cin abincin da take ta dubeta da kyau, shigarta wando da riga ne, sai dan siriin belt, tsarin yannayinta zai tabatar maka da a cikin hutu take,
Hafsat ta ce" da farko, ba wani ya bani damar ci gaba da numfashi ba face Allah,
Na biyu, kowa da bikin zuciyarsa, kowa da irin salon takun rayuwarsa,
Abinda yake opportunity a wajenki, sai ki ga ni tashin hankali ne, burina bai fi na koma gaban iyayena a karo na biyu, na samu wannan opportunity na kasancewata da su, na yi masu biyaya,
Shiru ta yi na dan lokaci sannan ta mike ta taka ta ajiye farantin fari kal da shi ta kuma dubanta inda ta yi mata nuni da ta dauki sabulun da kayan da aka ajiye mata,

Sai da ta dauka ta zo zata shiga gabanta ta ja ta tsaya daidai ita tana dubanta ta ce" wannan shi ne opportunity mai ma.ana, mai dadi, mai daraja , wanda nake kwadayi a ruhina, ba zamana mai gadin lafiar wani kato ko wata katuwa ba wanda hakan na nufin daga bakin lokacin da zan fara karbar koyarwarku *NA SAIDA RAINA*

Tana gama fada fada ta juya ta yi gaba, nan guards din suka rabu biyu suka saka su a tsakiya,

Tafe suke tana kallon yanda karti ke tafka gudu da duhu duhun asubar nan, sannan kowane kansa a aske tall tall suna ta gudu,
Da wasu na biye da su a mota das a zaune,

Haka suka yi yar tafia suka shiga wani batiment (gini)
Nan ta ga mutane, yan mata tsala tsala suna shigi da fici da tawul a jikinsu, ana iya yi,

Da mamaki suke kallon wace aka shigo da ita, duda basu jima sosai da zuwa wajen ba, aman basu taba gannin mace mai dati irin wannan ba,
Gaba dayanta tamkar an tonota, sannan sket din jikinta du ya yi datin balaki ga karni da take yi, kai ba kyan gani dai,

Haka ta mata jagowa har zuwa wani bangare, nan aka umarceta da ta zauna,
Suka kama kitson kanta suka shiga tsefe mata,
Sai da suka gama tsefe mata shi tas sannan aka bata damar ta shiga ta yi wanka,

Mikewa ta yi tana dari dari ta shiga wajen da aka nuna mata,
Tsayuwa ta yi tana kallon shower, ga soson wanka, ga sabon brosh da makiline, ga abin wanke kai,
Gaba daya ta sansu, domin gudansu ba baya ba, mahaifinsu na kula da komai nasu ,

Har gagawa take , bata cire kayan jikinta ba ta kunna ruwan ya shiga bin jikinta tun daga kanta , aman dati baya fita domin kuwa datin jar ya zama mai maiko ne a jikinta,

Haka ta cire kayan ta sake su nan cikin ruwan ta dauko sabulun ta shiga dirzar jikinta,
Soson ta dauko ta aniya dirzar jikinta da shi , fuskarta ne, wuyanta ne, kunnayenta ne, jikinta ne, hamatarta ne, kafafuwanta ne, ita kanta da ta ga bakin ruwan dake sauka daga fatar jikinta sai da tsikar jikinta ta tashi,

Haka ta yi ta yi ruwa na darwaye mata sannan ta debo abin wanke kan nan ta matso da yawa ta laftawa gashinta da ita bata yi tunanin idan an zo kwonce shi zai tsaya a kanta bama,
Tana laftana tana saka faratunanta tana dirzar kan, ruwa na zuba yana kara darwaye mata, ta yi haka ya kai sau hudu har sai da ta ji wani irin sakayau sannan ta dauki demelin ta kara a kan ta darwaye,
Sai da ta kara wanke soson nan fes ta kara saba masa sabulu ta kara bin jikinta da dirza sannan ta duka ta dauki kayanta ta shiga wankewa tana jin har zuciyarta na tashi,
Du yanda ta so su yi fes ki suka yi, sai dai sun wanku ba laifi,
Abin aski ta dauka ta gyara jikinta gaban madubin bayin, hakama hamatarta tas sannan ta dauki tawul din dake rataye tana mai jin dadin kamshin sabulan da ta yi anfani fa su, ta daura a jikinta bayan ta rataye kayanta da ta wanke ta fito,

Tana fitowa aka shiga dan wanke bayan dakin,

Wajensu ta zo, suma ita din suke jira, dan haka tana zuwa ta zauna , duda jikinta du a tsatsamce saboda bata saba fitowa daga ita sai tawul ba,

Kayanta aka mika mata da bras,

Kallonta ta yi ta ce " bana anfani da bras,

Matar ta ce" zaki fara anfani da ita daga yanzu, domin gudu za.a fara daga yanzu, idan kina gudu ba bras nononki zai zube ne, mu kuwa du wani abinda zai kawo mana cikas bama so,

Ita dai da ido take binta, nan aka busar da gashinta aka daura mata ribom baki dan siriri sannan aka daure gashin da kyau yanda ba zai hanata komai ba,

Wasu mayuka biyu suka bata, dayan suka ce da ita na fatar jikinta ne, dan gyaran fatar jikinta, dayan kuwa ta ringa shafa shi a tafin hannayenta, gwuiwar hannayenta da na kafafuwanta, da kuma tafin kafafuwanta dalin tausi da suka yi, kafafuwan harda dan ysatsagewa suka yi wato faso,

Karba ta yi tana dubawa

Kallonta ta yo ta ce" ba wannan zaki yi ba, tashi ki saka kayanki maza ki bi inda kika ga yan matan nan na bi,

Mikewa ta yi ta saka kayan harda audugarta yar karama wace kamarma baka saka ba dan baka jinta a jikinka, ta saka kayan ta nufi inda ta ga yan matan na bi suna fita bayan ta daura takalmi kafa ciki na gudu kamfanin Gucci

Sai da gabanta ya fadi da ta ga wanda ke tsaye ya hade girar sama da ta kasa,
Wannan datijon ne, da wani a gefensa shima bakin ne kamarsa shima ya hade fuska tamkar an zage shi,

Kanta take sadawa wai kar ya ganeta inda ta je ta ja layi wajen da suka tsatsaya su wajen goma yan mata cikinsu ba ta yardawa, kowace yar dagwas da ita , gashi basuda wani jiki mai girma, sai dai wata ta fi wata tsayi sosai

Fuska tamke yaron ya shigo gabansu ya fara magana kamar haka inda kolon kansa ba gashi ko dis , murya hade ya ce".....





*Domin samun Kutkale naira dari biyu ne, yan niger kuwa 500franc ta Orang Money*
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA, ZAKU YI MIN ENVOI NA DALA DARI BISA NUMERO KAMAR HAKA 92777744 AMAN FA TA ORANGE MONEY.....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6??


*Free page*


*SALAM, ZAKU GA WASU ABUBUWA CIKIN WANNAN RUBUTU NAWA, KAMAWA TA YI, WANI ABIN YA ZAMA DOLE NA SAKA SHI, DAN HAKA KU BIYO NI=?O?


Cikin dakakiyar murya ya ce" kafin ku shigo gidan nan kun yi gudu na kilometa 4 a minti talatin, to yau zaku yi 6 a minti ashirin, ba tserere bane, domin so muke ku zo gaba dayanku a tare, kar wani ya rigayi wani zuwa, kar kuma a bar wani a baya, akoy mai tambaya ne?

Shiru du suka yi domin kuwa kida sunada tambayar ba zasu iya yinta a wannan mutumen marar annurin ba, taf idannuwansa kansu wasu jajajir ne kamar an watsa masa barkono, kai ko da hakoran bakinsa ya cikeja ya tada ka tsaye domin dogaye ne, dan haka du suka yi shiru suna tunanin abin,

Kara maimaita tambayar ba mai magana ya yi?

Tsagal ta ce" wani irin mu zo a tare? A tare zamu yi aiki ne? Ko akoy aikin da za.a iya tura mu tare da sharadin sai mun dawo a tare daya ta kula da ran daya?

Datijon nan ne ya saki murmushi yana dubanta kafin ya gyada kansa,
Sai a lokacin ya matso inda saurayin ya dan matsa masa gefe,

Datijon ya dube su ya ce" ya zaku tsaya gaban mutun ya zayano maku maganganu kuna sauraronsa kuma kuna kallonsa, cikin hankalinku, ba maye kuka yi ba, ba duka kuka sha ba, bayan kun san abinda kuka zo yi , horon aikin zama Bodyguard wanda a kaf cikinku za.a dauki mutun uku zuwa hudu, sauran sai dai a yi wani wajen da su, bayan kun zana jarabawa an tabatar maku da abubuwa na wannan aiki, aiki ne na individual (mutun daya), shi ne za.a ce da ku wajen gudu ku karaso tare tamkar tayar mota da aka daidaita wajen hakan sai kawai ku hafiye?
Murmushi ya yi irin na mugunta kafin ya dubi saurayin nan ya daga murya a hade ya ce" Bg soldier (Bodyguard soldat ), ka fitar da wace ta yi tambayar ma.ana gefe, sauran ka horar min da su ta hanyar yin tsalen kwado dari kafin su yi gudu,

Haka ta ja gefe tana kallon yanda yake tsaye kansu da zabgegiyar bulala suna tsalan kwado suna karawa du wance ta yi da sanya ba wata wata yake dada mata bulala ciki harda wata mai dan kakauran jiki baiwar Allah yar baba da rai ce, ta samu shiga wajen da mahaifinta wani ne, dan haka baki dayansu suka jigata sosai , sannan aka laya su aka sake su gudun kilometer hudu, wanda ta jigata ta ji kamar zuciyarya zata tsaya, domin rabonta da wani gudu mai dan tsayima tun wanda ya kawota gidan yari, hakan ya sa sai da suka rigayeta isawa kafin ta karaso, aman bata yarda ta zauna ko ta fadi ba, jurewa ta yi a du kuwa da irin yanda take jinta zata kife kas ta ki bari sai da ta karasa,
Ai kuwa da gudu take neman ruwa, nan ya dakatar da ita ya hana mata ruwan kafin ya firfito mata da micik micik din idannuwansa ya zazaro mata ya ce" du lokacin da kika yi gudu kar ki yarda ki sha ruwa daga kin tsaya, hakan na tsayar da zuciya, ki bari sai kin jima sannan ki sha ruwa!

Kai kawai take gyadawa inda baki daya jikinta ya jike da ruwan zufa

Basu gama mayar da numfashinsu ba aka nuna masu wajen da zasu shiga dan jim, (dakin motsa jiki),
A cikin dakin ba abinda babu, sai dai su aka yi masu iyaka da duk wani abinda zai saka jikinsu ya yi tauri ko hannayensu su mumurde, abinda ake so a nan shi ne, du mai wata yar guntuwar tebarsa, mai wani lumkilumki a bayansa, da wani mai mundil mundil din hannu du su sabe su zube, slim, su zubar da du wani teba, ko wace ya kasance bayanta ya fice girman musali akoy itama mashine din dake rage masu tudu ko fadi, dan haka cikin gagawa aka shiga horar da su, wanda wasunsu har hawaye suke na wahala, basu saba ba, ba.a saba masu da haka ba,

Haka suka jure sukai ta motsa jiki, ba su su baro wajen nan ba sai kusan takwas, ya rage minti talatin takwas ta yi aka fito da su,

Tsaye ya yi yana kallon yanda suke haki ya ce " daga yau, kulun, karfe shida ta maku a wajen da muka fita gudu yau, zan salameku bayan mun gama karfe bakwai da rabi, kunada minti goma na cin abinci, minti ashirin ku tabatar da kun shirya kowace da kayanta a dakinta ku fito daukan darasi,

Amsawa suka yi a tare sannan kowace ta nufi dakinta cikin gagawa

Tana zuwa ta tarar da abinci sannan da wasu fararan kaya wando da riga suma, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login