Showing 36001 words to 39000 words out of 154870 words

Chapter 13 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1125

irin sautin da kunnayensa suka jiyo masa,
Tsaye take kawai, hannayenta gaba daya a sake, wandon dake jikinta irin mai lafewa a jiki ne aman kuma sakake wajen mazaunanta kawai ya rike , sai riga mai botura da wata a ciki wada dalilin bale boturan da ta yi ya saka ake ganninta, kanta dauke da asalin gashinta ba wancen atach din ba,
Fuskarta babu ko digon kwali bale a yi hangen hoda ko wani abin,
Aman wani fayau da shiga ido da take sai a hankali, dole ta girgizawa namiji lafiyaye zuciya sai dai idan zuciyar taka na hangen wata sai ka kyasa a ranka ka huce wajen,

Hannayensa ya daga ya cusa cikin gashin kansa da ya bar suma ta taru sannan baya gyarawa,

Sai da ya dan waiwaya ya ga tsayuwar me kuma suke a bayansa? Sannan ya daga kafarsa ya tunkareta,
Hannunta na dama ya damka ya jata tamkar rakumi da kala haka ta bi shi ba tare da ta warci hannun nata ba, ba kuma ta yi masa gardama ba,

Da kallo suka bi su, inda BS ya daga kafarsa ya bi bayan su da saurin gaske, sai dai yana karasawa Abdul na banko kofar da wani irin karan sautin dake nuna halin bacin ran da yake ciki,

Wani irin hankadata ya yi cikin dakin dake mamaye da duhu, wanda yake daya daga cikin dakunan gidan, shi kansa bai san ainahin inda zai je ya kuna fitila ba, sannan tun da ya hankadata yama rasa inda ya hankadata,

Garu ya yi nufin kaiwa naushi, wanda sai da ya naushi iska sau uku kafin ya samu hannunsa ya naushi garun da wani irin karfin da da normal ne sai ya ji jiki ainun, aman da yake ransa bace ne sai ihun bacin rai da ya saki murya kausashe ya ce" me kika ji? Me ki ka ji nace?

Inda yake kallo daban, inda muryarta ta fito daban, domin ita a bayansa take, a hankali, cikin mutuwar jiki ta ce" ina bayanka,

Juyowa ya yi ya yi shiru, inda ya dauke numfashinsa, yana so dole ya lalubota ta habyar numfashin da take saukewa,

Fahimtar hakan da ta yi ya sakata tsayar da numfashinta sannan ta canza waje da sauri ta saisaita ajiyar zuciyar da take yi, ta dan labe wajen labulen wajen ta ce" a wajen formation din zama gagarimin sojan dake aiki wa kasashen duniya baki daya, wanda yana da damar yin operation inda ya ga dama, yana da takardun shaidar shi dan kasar da du ya yada zango ne, shi dai wannan mutun ko shugaban kasa na mangarinsa domin ba.a bayar da formation dinsa a kananun kasashe sai irin su chaina, dubai, ko su Saudiya. Japan...da dai sauransu....
Wanda a cikin mutun hamsin bai fi biyar su fita ba, kai ana iya goge kowa a hanawa duka hamsin din!
Sai kuma bodyguard , ana koya masa irin wannan abin a sama sama ba a zufafe ba saboda halin rayuwa......

Labulen da ya damka ne ya sakata saurin matsawa ta canza waje ,

Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta ce" a ciki.... *WANENE KAI ABDUL JABAR ABDUL BASID?*

Gabansa ne ya wani irin bugawa sakamakon irin yanda ta ja sunnansa lokaci daya take neman sannin waye shi, a iya yau, a iya hafuwar yau, awowin da ba zasu fi goma sha biyu ba , wanda da yawa da suke tare shekara da shekaru.basu san hakan ba?

Jikinsa ne ya yi la.asar, sanyi ya yi sosai da sosai, dan haka sai ya daina neman lalubo infa take ya saki abin sauraron da ta laka masa nan ya juya ya lalubi kowa ya bude ya fice a dakin,

Bai yiwa kowa magana ba, sai dakinsa da ya je ya shige ya rufe ,

Bakin bed dinsa ya zauna ya dora kafarsa daya kan daya ya daga kansa sama,

Wasu zafafan hawaye ne suka shiga bin gefen kumatunsa a lokacin da ya tuna mahaifiyarsa da irin rayuwar da ta yi cikin duhu, haka kuma irin mutuwar da kanwarsa ta yi, da irin rayuwar da mahaifinsa ya yi ,
Shi kansa irin tasa rayuwar ta yanzu, wace yake tantiri fitinane a idon mutane da yawa,
Kai innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, shi kam bai ga ranar kudi ba,
Kudi sun saka familynsa a halaka,
Shi da kudin nan na haramun ne, ba zai zauna a cikinsu ko na second daya ba,
Sai dai kudin irin gadon nan ne na iyaye da kakani,
Irin kudin nan na da, manyan kudade da kadarori masu albarka, shi shi daya,

A hankali ya kai idannuwansa kan wandon dake jikinsa,
Jikinsa ya ga ya canza yannayi kamar yanda ya ji a jikinsa.... *mace* yake bukata, mace yake so a yanzun! Wannan lamari ya saka shi dora hannauensa gaba daya saman kansa, wannan wace irin masifa ce aka hada shi da shi? Shi kennan za yana jin bukatar mace kamar yanda yake da bukatar cin abinci a kowani lokaci?
Ni.ima ce ta fado masa a rai,
Ya yi mata zuwan biji biji, wanda bata taba sannin.harkar nan ba aman sai da ya mata zuwa biyu, wai a hakanma ya mike yana shan iska ya koma ne yarinyar nan ta fado masa daki,

Juyawa ya yi ya kurawa waje guda ido, kafin kuma ya saki murmushi, a fili ya ce" makashi, baka da mutunci, wato so ka yi ina ciki ka kashe ni, na jibgunma yarinyar mutane sannan kowama ya ga tsiraicina ko? Harda wannan piciciyar yarinyar domin sai an zare ni daga jikin Ni.ima....
Murmushi ya yi ya juyar da kansa yana mai hangen maganin da ya saya da niyar fara sha, domin ba zai koma harkar da yake a da ba, baya son komawa, ya gwamace ya yi ta kawo matan a matsayin na aurensa yana bin dakin kowace kowani dare har ruwan jikinsa ya kare idan ya mutu ai shikenan kowama ya huta!

Haka ya yi ta abu, bayan ya sha maganinma shi dai ya ji ya dan rage nauyi, aman ba wai wani sakayau ya ji shi ba,
Dan haka alwallah ya dauro ya zo ya hau darduma ya shiga gabatar da sallah.

Ta jima tsaye wajen da ya fice, idannuwanta lumshe, gaba daya ta raja.a tunaninta kansa , yannayinsa, irin abubuwan da yake yi tamkar mai aljannu, kai harma da irin yanda ya shigo da ita da niyar kowace wace, aman kuma da ta tabata ta tabo gaskiya cikin lamarinsa sai kawai ya fice a dakin,
He's a brave man? Or Bodyguard?

A wannan tunnanin ta silale jikin karfen ta jinginar da kanta,
Zurfafa ta yi a tunanin da kulawa da kuncewa,
A fili, kuma muryarta na rawa tamkar zata fashe da kuka ta ce" *shi, nasa iyayen basama duniyar*,

Hawaye ne suka shiga bin kumatunta, hawayen tausayin kanta, da kuma kulaliyar maganar da ta tsinta tasa, innalilahi-wa-ina-ilaihi-raj.une.
Lamarinka, lamarinka ya fi nawa hargitsi..........zan san ko kai waye!


Washe gari karfe tara na safiya ya fito daga dakinsa da ya sakawa kys ya gama ibadarsa ya huta ,
Tun da ya bude ya fito, su su uku dake tsaye suka dan juyo dan gannin wanda ya bude dakin,

Su duka sun sha mamakin a yanda ya bayana yau kuma,
Hashin kansa da ya taran nan ya zauna ya bashi lokaci wajen yi masa gyara irin na samarin america , wato askin nan na yan basket ball mai salo da kyan kallo a ido, sai dai sak irin na yan duniya ne!
Ya rage bajewar sajen fuskarsa ya siririnta shi a fuskar tasa, haka kuma gemunsa ya rage shi sosai ya bar dan kadan da ya yiwa fuskar das da ita ta bada kala,
Lebensa na kasa ya fi na sama girma, yau wajen broshing ya sha garzar da ya saka ya dawo fresh yanda yake da, wato kalar pink mai dan duhu duhu da shi na kasan na saman kuwa baki,
Kamar wanda ya caje gashin idonsa, yannayin kulawar da ya bashi da kayan kulawar ya saka harta da gashin idon nasa ya yi tsai kamar barkonon tsohuwa kirikiri ba tsoro ba kunya yana kallon mutane, haka kuma dara daran idannuwansa sun kara fitowa suna kallon du wanda ya kale???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? su ido cikin ido,

BS da jibrin suka juyar da kansu daga dubansa inda Hafsat gabanta ya yanke ya bada wani irin sautin da bata shirya ba, hakan ya sa ta lumshe idannuwanta tana adu.ar da ta bata karfin gwuiwar controling din abinda take ji wanda ta baiwa kanta amsar hakan ya faru ne dan jiya ta ji wani yanki na sirrinsa , yau da take tunanin ba zai iya mikewa bisa kafafuwansa ba sai gashi ya fito a ba zata, cikin yannayi na karfi,.....eh ta yarda da abinda Ni.ima ta fada a yanzu da safe da ta je gannin ko can ya kwana dan ta dora masa break fast ta tarar da ita zaune bakin bed ta fito a wanka daure da tawul tana gyara fuskarta cikin yannayi na kamar ba abinda ya dame ta,
Da ta tambayeta sir fa?
Sai ta tsura mata ido, can kuma ta girgiza kai ta ce" bai shigo ba tukunnan,

Har hafsat din zata juya ta ji ta ce" Bodyguard,

Juyowa Hafsat din ta yi tana kallonta, nan Ni.ima ta mike daga zaunen da take, ta nufota da wata irin tafia ta tatata ta tsaya gabanta ta ce" ki kular min da tashinsa, zaman sa, motsin sa, cin abincin sa, komaima, hakin kula da shi a wuyan ki, idan har suka cin masa....ke kika kashe shi, ni kuwa ina numfashi ne da numfashin sa, kin ga kin kashe rai biyu! *Ina son mijina, komai irin halayensa*

tunaninta ne ya katse, sanadiyar jin an dauke hular gashin da ta dora ta yau mai shigan blonde,
Da sauri ta zaro ido sakamakon farar rigar dake cikin Costume din jikinsa da ta hanga domin ya matse mata waje irin sosai din nan,

Da sauri ta saka hannayenta ta tare hular gashin wace a lokacin da tana kanta tamtar irin fararan americain din nan, aman yana cirewa ta dawo kamaninta irin filanin nan masu dukan ido da zuciyar mai kallon su.

Da wani irin yannayi ta dago da dubanta ta kai wajen hular gashin, ya riketa taf ya ki sakar mata abinta,
Dubanta ta maido kansa,
Sai da gabanta ya yanke ya fadi sanadiyar idannuwanta da ta saka cikin nasa,
Wani nauyi ta ji idannuwanta na neman yi mata , sai dai ta ki ta cire dubanta a kansa danma kar ya dauka wani tsoronsa ko wani abin ne,
Tana kallonsa shi ya lumshe nasa idannuwan, sannan ya fuzge hular gashin ya jefawa BS da ya kuma juyowa jin shirun ya yi yawa,

A gimtse ya ce" ni da ba arne ba, yaya za.a ringa bina da gashin arnawan!

Shi dai BS tarewa ya yi ya mikawa dayan abokin aikinsa, shi kuwa ya juya da gudu ya koma ya ajiyeta ya dawo,

Gaba yake, tafiya yake hankalinsa kwonce, takalman kafarsa sau ciki bakake sidik sababi fil sai bada kala suke a cikin yannayin tafiarsa,
Bayansa Hafsat ce itama sanye da bakaken kayan wando da riga, sai bakin gashin kanta dake fili ba dan kwali, sai gilas baki da ta saka dan madaidaici tana lure da dukan wani motsins, wanda gilass din na aiki ne.

Motocin da aka janyo ne ya saka shi dubansu, wasu motoci ne da ba nasa ba,
Aman bai yi tambayar ko na waye ba, dan ya san ba zai fice su suka kawo su ba,
Maduban motar da aka bude masa ya shiga ya duba,
Bayan ya zauna Hafsat na zaune facing dinsa, BS na gaba kusa da direban da su suka kawo abinsu, ya mika hannu ya daki madubin motar wanda hakan ya saka su kallon shi gaba dayan su,

Murmushi ya sakar masu ya dage girarsa guda ya ce" dan na kara yarda idan har wanda bulet din baya ratsawa ne,
Kunfa fara jan attention dina, ba laifi kuna kokari..m

Ba wanda ya bashi amsa, saima hankulansu da suka maida bakin titi ana jan motar,
Irin kallon da yake binta da shi, irin tsareta da idannuwansa da yake ne ke sakata tsarguwa walahi,
Banzan kallo ne da shi, irin kallon nan na kurewa mutun waje,
A hankali ta sosa keyarta ,
Ta kale shi a sace ta ga dai shi ko.ina na jikinta ne yake bi da kallo,
Gashin kanta ta saka hannunta sosa, ta kara sosawa irin ta samu kwarin gwuiwa ko zai gane ya daina yi mata wannan kallon,
Aman tana kuma dubansa ta ga ita din dai yake kallo,

Gilashin idonta ta cire, ta wara kafafuwanta, ta dora hannayenta saman gwuiwoyin kafafuwanta ta tsura masa idon itama tare da cuno bakinta da kuro idannuwanta irin kale ni da kyau din nan=?D?

Murmushi ya saki shima ya yi exactly yanda ta yi , hannunsa ya dago ya ka8 wajen hancinta da nufin shafawa, sai dai ta kauce tana hada fuska,
Sai da ya kara sakar mata murmushi ya ce" idan ba Allah ba, ba wanda ya isa ya zana mutun ya fito das da shi, ke wollah kina da kyau, wa kika biyo? Maman ki ko baban ki?

Da mamaki ta dawo da dubanta wajensa, sai dai bata gama mamakin hakan ba ya ci gaba da magana hankali kwonce, wanda du abinda yake fadi kowa na jin sa, ya ce" kin ga, kyakyawar halita da ke, yar caras, ga kugu...
Ya saki murmushi , ya ci gaba da fadin...ga gashi, ga ido, ga dogon hanci, ga dan baki mai dadin tsotsa=?A?.....
Murmushi ya kuma yi, ya ce" ke karantar jikinki da kasancewarki gardi kawai ya bata, kin ga jikin ki karami ne sosai, haba namiji na son ya ringa damka, ba wai ya ringa tsakura ba, kuma yana son ya ji lema ba wai kamas ba,
Kin ga yawo jiki a bude, na busar da mace, ruwan jikinki yanzu haka ba komai , du ya tafi, haka kuma
Shut up!
Ta fada ranta bace, fuskarta har ta yi ja dan masifa....
Sai fai kafin ta yi shiru da hakan muryarsa ta daukaki tata, ta fi tata nuna masifa ta hanyar fadin" *u shurrrp!*

Karya na maki ne? Uban me ya kawo ki harkar aikin da maza ke yi kuma ki ce sai an kiyaye harshe wajen yi maki maganar da ake yiwa maza?
Na fada maki Ke gardi Bodyguard nonsense! Ni zaki biwa rayuwa? Aikin ki, ki tare min harbi, ba wai ki min bincike ba,
Na maki alkawarin sai na binciki taki rayuwar nima!

Mu je zuwa ni da ke!

Cikin yannayin bacin rai Hafsat ta kara matsowa kusa da shi, bayan ta janye kafarta da ya take da takalminsa sako kafafuwanta suka shige takankannin nasa , ta yi zama irin na neman fitinan nan ta dago idannuwanta da suka cika da hawaye dan jin haushi tana kallinsa yana kallonta ta maida hawayenta gaba daya ta ce"


*SUNNAN KA ABDUL JABAR ABDUL BASID* , AN haifeka a cikin niger garin Niamey,
Ka kasance jikan Buraima mai cefa, dan Hajia Mariama Kabir!
Shekara goma sha daya ka yi tare da iyayenka mahaifinka ya tura ka kasar Saudiya dan larantar kasuwanci, wanda kake basaja da shi cewar kai dan kasuwa ne,
Kanwarka ta rasu a shekaru goma sha shida,
Mahaifinka a shekara hamsin da bakwai,
Mahaifiyarka a shekara hamsin da uku,
Kai a yanzu shekarunka talatin da uku da sati hudu da kwana biyar da awa tara da minti arba.in da sakwani........









=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ?=? ? anuna ko=? ?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




1?? 7??


Shiru ta dan yi tana kallon yanda ya tsurawa bakinta ido,
Ta ci gaba da fadin" babu kalar abincin da baka ci, du irin arzikinka kana iya cin du abinda ka samu,
Baka da dar da kwonciya a duk inda ya kama , irin gado, katifa, tabarma, dandar kasa,
Baka da damuwar irin suturar da zaka saka a duk halin sakawar ya kama,

Idannuwanta ta lumshe, jin irin yanda sukai mata nauyi, ta bude ta dube shi ta hada babar yatsarta da ta tsakiya ta ri tap tap biyi da su ta ce" kadan,
Kadan ya rage min na baka labarin rayuwarka Sire!

Abdul Jabar ya lumshe idannuwansa ya dan ja baya ya jinginar da bayansa jikin kujerar da yake kai still idannuwansa a lumshe,
Yana matukar girmama kwazon yarinyar,
Tana auna abubuwa, tana da zurfafa bincike kan abinda ke gabanta,

A haka suka karaso tafkeken ma.aikatar da suka fito dominta,

Fita ya yi a lokacin da ya hangi mutumen na tsaye, wato shi yake jira,

Su BS fitowa suka yi suna ta aikin duba wajen, inda ya yi gaba Hafsat ta bi bayansa,

Maimakun su shiga cikin ma.aikatar sai suka ja suka tsaya gaban mutumen,

Kalon kallo sukaiwa juna shi da Abdul,
Kafin mutumen ya bude hannayensa yana dariya irinta ka ga abin farin ciki kafin ya ce" yarona, zo gare ni,

Abdul sai da ya dane zuciyarsa ya nufe shi ya shige jikinsa duda katon tumbinsa bai bari sun yi gaisuwar yanda ya dace ba, nan sukai gaisuwar larabawa kafi su saki juna,

Mutumen ya ce" ai tunda kace da ni gaka nan tafe na kasa zama sai da na fito tarbanka yarona,
Mu je office din mana

Abdul ya gyada kai yana murmushin yake kafin ya ce" aa, ba sai mun shiga ba ai elhaj, nan ma ya isa,

Dubansa ya yi, eh tabas du yawanci

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login