Showing 138001 words to 141000 words out of 154870 words

Chapter 47 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1126

KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 3??



Sauka ya yi daga cikin motarsa ya je wajen mai gadi

Salama ya yi masa a mutunce harma sukai musabaha kafin ya tambayar shi ko mai gidan na nan? Wato BS

Gannin irin motar da ya fito, irin yannayinsa, da kuma zuwan mutuncin da ya yi masa bai tsaya wani tsaye tsaye ko tambaye tambaye ba ya budewa Abdul gida bayan ya tabatar masa da BS na gida yanama bayan gidansa wajen hutawarsa

Sai da ya karewa yannayin gidan kallo kafin ya tabe bakinsa ya shiga nema hankali kwonce

Da kyar ya gane yannayin gidan dan tamkar gidan barawo sai lunguna lunguna

Hango shi ya yi zaune saman tapi mai fadi, gefensa budurwar nan ce da suka bashi tsaro tare , cikin shiga mafi muni sannan sun mayar da hankali kan begen juna a irin wannan yannayi

Kansa ya gyada kafin ya yi murmushi ya karasa inda suke

Bai yi masu salama ba, haka ya ya karasa infa suke, sosai ya matse masu waje ya yi masu kerere a ka a tsaye

Da wani irin sauri suka zabura du suka mike suna kallonsa,
Kallo daya ta yi masa ta gane shi, du kuwa da irin yanda ya gyaru????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? ba uwar kasumbar nan, ba hadewar fuskar nan, du yannayinsa da sauki sosai,
Murmushi ta yi ta daga hannunta ta sara masa tana kallonsa, bata damu da wanda take tare da shi ba ta kashe murya ta ce" sire ne da kanshi?

Abdul ya zuba mata ido yana karantarta na dan kankannin lokaci,
Murmushi ya yi kafin ya kada kai,
Hannunsa na dama ya daga ya shafi gaban goshinsa, a fili ya ce" kai, bariki, bariki ba sana.a ba, idan kana son ka zama sakarai wanda bai san ciwon kansa ba sannan baya kishin kansa...to fa biyewa bariki,

Kallon BS da ya hade rai ya yi kafin ya kara kallonta ya ce" ke yanzu tsakaninki da Allah da aikin ki, iyayenki da rai, kina musulma, ba laifi da dan kyanki sannan yannayin jikin ki wanni zai iya kwasa a haka dan shi abin ra.ayi ne, ki rasa abinda zaki yi a rayuwa sai bariki? Ke kuwa hau din bai miki adalci ba ki duba ki ga yanda kika make wata garjejiyar muryarki kina gaishe ni bayan da na shigo hannun wannan shegen a cikin rigarki yana laguda wannan shanyayun abubuwan tamkar slifas tsofi kuma nima kike kashe min wadinan tsofafin idannuwan naki so kike mu hadu mu uku ko me?

BS dake kallonsa da mamaki, ga dumbin haushinsa na auren Hafsat da ya yi dan kawai ya ce ya zabi aikinsa a kanta baima tsaya ya ga daga baya idan bai auretan ba kamar can dama son ta yake, kamar mai jira ya aureta a ranar ya kale shi da kyau ya ce" *ABDULLLLL......*
bai bar shi ya kai karshen maganarsa ba ya dauki lafiyayen hannunsa, ido da odo , gaba da gaba, ya dauke BS da wani irin gigitacen marin da sai ya rantse bai bai taba jin mari mai sakawa a ji shiru irinsa irinsa ba

Daga shi har Budurwar tasa ido suka zaro suna kallon Abdul, wanda a yannayi na ko in kula ya daga masa hannunsa sannan ya nuna masa yatsarsa daya ya ce" ai ka yi hakuri na gama da ita sai mu yi dan dan kai na zo nan din ko?

Kallonsa ya mayar wajen budurwar ya ce" yanzu tsakani da Allah gajen hakuri dai ai bashi da kyau ko?

BS da ransa ya gama bacewa ya data hargagi yana daga murya ya ce" ni ka mara? Ni ka mara a cikin gidana? Kai waye? Takamarka kai banbana ne a wajen aiki? Shi ne zaka shigo har cikin gidana ka mare ni? Abdul Jabar idan kana tunanin ko na kai kararka za.a bani hakuri ne a min wasa da hankali dan kana baba a niger ni zan nuna maka nima shege ne, da wajen da baka isa ka ja da ni ba! Wannan marin da ka yi mini sai na yi maka dubunsa! Sai ka gane ka shiga gonar da bata dace da kai ba!

Hannunsa ya kuma dagawa ya wanka masa wani lafiyayen marin, wanda ya harzuka BS ya nufi Abdul da mugun bacin rai ya cakume shi

Daga daga sukai a wajen kamar zai kai shi kasa daga baya baya dan tura shi baya ne yake da dukan karfinsa, sai dai kafin ya karasa aiwata hakan Abdul ya ja tunga, ya tura ya tura ya yi kokarinsa tabe shi ya kayar sai dai ina ya kasa yin hakan

Sai da suka riki hannun juna da kyau kafin Abdul ya saki hannun nasa da zafin nama ya warci kafar BS ya nausa shi da kasa
Bai yi kasa da gwuiwa ba ya bi shi ya bashi kyawawan naushi hagu da dama har sau hudu hannunsa a dunkule a fuska

Sosai gefen bakinsa ya fashe ya fara jini, daidai mai gadi ya samo mutane dan tun hargowar BS ta farko ta fargar da shi ba lafia ba nan suka hadu suka dage Abdul daga kansa mai gadi sai dora hannu yake a kansa yana tunanin tasa ta kare a gidan yana kallon Abdul irin kallon nan na ashe baka da kirki?

Da sauri Abdul ya warce hannunsa daga rikon da wani kakauran saurayi ya yi masa ya kara durfafar BS da aka mikar ana bashi baki

Da gudu suka tare kowa na kokarin gannin ya raba fadan da mamakin zaratan samari masu kudi da kyau suna fada a irin wannan lokacin? Me zai hada su haka?

Hannun ya kuma kwacewa kafin ya yiwa BS mugun kallo , da wata murya mai nuna bacin rai ya ce" kai karami ne a duniyar bariki! Aunawa na yi na ga ba sana.a bace! Bashir na baka dama kaf garin niger kwararo kwararo du wani dan iska, dan kwaya, dan tasa, barawo, ko dan ta.ada ka kawo ku farauci rayuwata! Zaka gane kai wawa ne!

Hannunsa ya kuma kufcewa daga hannun mai gadi dake dunkule hannayensa yana magiyar ya tafi dan Allah

Har ya fara tafia ya juyo da wani yannayi tamkar zai kuma kara rukunkumar BS din wanda shi kansa sai da ya ji gabansa ya fadi yana kokarin mikewa tsaye dan ji yake bayansa tamkar ya bala masa shi

Abdul ya nuno shi da yatsa ya ce" dan ubanka da lalatatu ake neman yin bariki ba da kyakyawar kadara ba! Na ji bakin cikin horo da ka bata na tsayin shekara kana kaleta, na yi bakin cikin sannin da ka yi mata, na maka rantsuwa da Wanda ya busan numfashi ka kara koda mafarkinta ne sai na kwakulo maka ido na soye na baka ka cinye! Shege mai zalama

Kallo ya bi mutanen da kallo ya juya ya fice a gidan baki daya

Mai gadi kam sifsifsif ya fice, da kansa ya kori kansa aiki a gifan BS dan ya san idan har ya yarda BS ya wartsake daga rikitar da ya shiga sai ya wulakanta shi fiye da tunaninsa, dan kuwa a yana binsa sau da kafar nan ma yaya aka kare bale yau ya buda kofa an shigo har gida an ci ubansa?

Abdul da ya koma motarsa sai da ya ciro tissu ya goge gefen hannunsa da ya yi masa mugun yago wanda ya saka jini fitowa
Tsaki ya ja yana kallon yanda ya yaga masa rigar jikinsa ya tabe baki a fili ya ce" mai fada irin na mata

Tada motar ya yi ya nufi cikin gari dan bashi da jiyar komawa gidan nasa a irin wannan lokacin

Hafsar kam ta wuni cikin zulumi da tunani, daga baya ta baiwa kanta hakuri ta nemi bed ta mike dan wani irin baci ke damun idannuwanta

A kwana biyun nan da Na.ima ta yi kwata kwata bata samu fuskar Abdul ba,
Idan ba lokacin cin abinci ne ya yi bama sam bata ganninsa, ko wajen cin abincin sai ta yi dagowa goma sam bata tsintar idannuwansa a kanta kamar yanda ya saba binta da kallon nan mai sakata jin wani irin shauki

Ba wani cin abincin take ba, dan gata gabanta hasalima ita bata sha.awar cinsa har a gama, sam baya ce mata ta ci ko ya dameta da murmushi, baya taba jikinta ko ya rakota ya rungumeta a jikinsa, ita kam ta rasa gane kanta, ba zata boye ba tana missing din hakan
Tana jinsa da matarsa suna magana a hankali, harma ta ji tana dariya

Ba wani abu tsakaninta da kishiyarta, basa fada sam, basa yade yaden magana, aman kuma basa shiga harkar juna,
Idan sun zauna cin abinci zasu gaishe da juna a gaisuwa mai gajarta,
Ba wani dake shiga harkar wani, idan daya na magana da miji ba mai tankawa, ba ruwansu da junansu, basuma shiga sabgar juna ba bale idan wata ba lafia su yiwa juna ya jiki, ko idan abin dadi ya samu a yi maka murna ko na jaje a yi maka jaje.....wani kishi suke na shiru wanda kowace a zuciyarta kadai ta san irin abinda take ji kan yar uwarta

Suna ciki da cin abinci a yau da ta kama aikin Hafsat, Hafsat da ta fi kusa da Abdul, tun da ta shigo yau din ma da wani zumbulelen hijab har kasa a jikinta, ra samu waje ta zauna

Bayan gaisuwar nan ba abinta ya hada ta da su duka mai tsayi ko mai zurfi,
A lokacin ta lura da ciwon dake hannunsa wanda ya yi kama da an yayage shi sosai din nan dan kuwa sosai wajen yana da girma

A ranta ta afka duniyar tunanin me ya same shi? Me ke damunsa? A ina ya ji ciwo haka?

Sai da ya gama cin abincin ya kale su baki daya,
A hankali ya ce" Hafsat?

Dago da kanta ta yi da sauri ta sauke idannuwanta a cikin nasa, wanda ta ga ya yi saurin kawar da duban tsakiyar idon da ya yi mata na yan sakwani
A hankali ya ce" tafiar, yau ne da yama...zan yi kwana biyu ne, Na.ima tafia ta taso min dazu da safe

HAfsat ta tsura masa ido sosai, sam ba gaskiya a kan lebensa hakama furucinsa
Lokaci daya ta ji ta muzanta, du irin sanyin ac din dakin sai ta ji ta fara hada gumi, gaba daya lamarin yana sukar nutsuwarta

A hankali ta yi murmushi tana kallonsa, murmushi irib mai fitar da sauti sannan ta ce" eh, ai ka ce daga mun gama cin abinci zaku tafi jiya da ka yi kirana da dadare, shi ya sa nake son mu yi salama na koma kaina ke dan min ciwo me amor

Daga shi, Har Na.ima kallo suka bita da shi, shi yana kallon mamakin gila masa karyar wai ya yi kiranta jiya da irin yanda ta nuna halin ko.in kular da ta nuna na zai yi tafia a irin wannan lokacin da yake ranar aikinta, kennan ita ko a kwalar rigarta ko? Yana so ta gane kurenta na kiea masa sunnan wani kato ua horata sai dai yana gannin kamar ya yi hakan da wuri dan sam ba soyayarsa a zuciyarta bale har hakan ya hanata sukuni

Ita kuwa tana dubanta da mamakin yaya aka yi tun jiya ya sanar da ita yana da tafia bayan ba aikinta bane, wani faduwar gaba ne ta ji ta ziyarceta da tsoro, tashin hankali wanda ba.a saka masa rana ......kar dai a je wannan ita ce wace ta sacewa mijinta zuciya??

*Na san ni mai laifi ce, dan Allah ku min uzuri...idan fa wa.inda suka saba min novel dina sun san bana wasa da typing ko jan rai, idan haka ta kasance a yanzu ina mai fatan a yi min uzuri......lafia uwar jiki=?
? na gode*


[9/12, 8:06 PM] BAK'A CE: >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




6?? 4??


A hankali ta katasa maganarta tana dubansa kasa kasa irin duban nan na kasan ido, kafin ta mike cikin nutsuwa ta zagaya kusa da shi
Rankwafawa ta yi a hankali inda kamshin turarenta ya shiga hancinsa, kanshi mai saka nutsuwar zuciya
Ita kanta nata idannuwan ta lumshe jin nasa kamshin ya jara cika mata zuciya

A hankali ra mana masa kiss a kuncinsa, ta rage murya sosai da sosai ta ce" Allah ya tsare

Tana gamawa ta mike ta tafi , har ta fice a falon nasa da kallo suke binta su duka kafin a hankali ya mayar da dubansa wajen Na.ima
Gaba daya fuskarta ta canza yannayi, yannayi na bacin rai da tashin hankali da wani kallo irin na ka ci amanata!

Mikewa ya yi da tissu a hannunsa ya fice a wajen ba tare da ya furta kalma daya ba

Yana shiga dakinsa ya je ya shiga canza kayan jikinsa,
Ya zo daidai bala mabalin ya rintse idannuwansa da sauri dan kuwa zafin kiss dinta da karansa ne ya daki kunnayensa lokaci daya kuma ya buda idannuwan nasa ,
Sun kade tamkar ba nasa ba, yana jin lamarinta da dukan karfin jikinsa da tunaninsa, yana jin du wani abinda ya shafeta a gangar jikinsa,
Bai san yaya aka yi ya yi sake har haka ta same shi ba, yana kallon ina? Dan me ya yarda har irin wannan abin ke kokarin cin karfinsa? Ya sani ita ce ra farkon da ta yi masa musu, ta farko da ta yi masa tsayaya, ta farko da ta yi masa fada, ta farko da ta fashe da kuka dan abinda ya shafe shi shi ba wani ba, ta farko da ta tsaya kai da fata take nuna masa hanya, mahaifinta ne na farko da ya dube shi ba tare da ya san shi ba, na farko dake dubansa da tarin dukiyar tasa da takamarsa ba ruwansa ya saka shi a hanya mai bilewa ha wani dar ko tsoron kar ya kubuce masa tunma kafin ya zama sirikinsa,
Tabas ta taka mahinmiyar a rayuwarsa, ta girgiza tunaninsa, aman kuma shi kansa ya yi mugun saken da ta cin masa a lokacin da vai shirya ba,
Wai shi maman malan zata nuna bai isa ba? Ba zata nuna ta damu da shi ba? Kennan ba zai taba samun matsayi a zuciyarta ba du kuwa da irin yanda yake kokarin yi mata biyaya a bukatunta?
Shi ke binta ba ita ke binsa ba, ashe haka ne idan kai ke son mutun dole kai zaka ringa binsa du abinda ya yi niya? Ba laifi ta je din!

Ya karashe yana mai daukan wayarsa da makulin motarsa

Fitowa ya yi ya fice a dakin ba tare da ya rufe ba ya yi gaba abinsa

A motarsa ya shiga ya kama hanyar tuki, bai dauko komai ba sai katinsa ta banki sai takardunsa na zuba mai a stations
A irin lokacin nan ya shiga tukinsa ya dauki hanya mai tsayi dan niyarsa zai yada zango a garin maradi, garin da yake son buda reshe na kampaninsa mai tatar mai

Ya wuni cir yana tuki da kansa dan kwata kwata baya jin dadin yannayin da yake ciki, yakan yi murmushi ya girgiza kansa, dan bai taba tunanin zai kamu irin wannan kamuwar haka ba, sai dai ya tabata ba wani abinda zai bashi wahalar da ta fi wada ya sha na tsayin rayuwarsa , ya ga rayuwar da baya tunanin da mace ta ki shi zai mutu, tunda har yanzu zuciyarsa ke harbawa yanda ya kamata baya tunanin soyayar mace zai tsayar da ita sai dai idan lokacinsa ne ya yi

Yana zuwa hotel ya sauka,
Wanka ya yi ya dauro alwallah ya gabatar da sallar shafa.i da wuturi sannan ya zauna bakin bed din dakin

Hannayensa ya saka saman kansa yana dan yin gaba da baya da hannun nasa

Mikewa ya kuma yi ya dauki jakar goyon fa ya zo da ita ya zuge zip din jiki

Takardu ya shiga fitarwa sannan ya ciro laptop wani dan karami ya bude ya kunna shi

Da wifi din hotel din ya shiga internet,
Sai da ya gama aikin da zai yi sannan ya shiga tarin messages din da ake turo masa wa.inda ba kowa bane sai mahaifinsa

Du messages din magangannu ne na rayuwar yau da kulun, baki daya nasiha ne na zamantakewar rayuwa,

Ajiyar zuciya ya sauke bai kashe laptop din ba ya samu waje ya kwonta ya lumshe idannuwansa

Wani irin yarr ya ji tun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login