Showing 51001 words to 54000 words out of 154870 words

Chapter 18 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1117

ne za.a turo wa.inda zasu canje ku, domin kun ji ciwo ba zai yiwu ku ci gaba da aiki ba, a gobe gobe GN zai turo masu canzarku ke da Jibrin, a mayar da ke camps, hankalina zai fi kwonciya, ki je can ki yi jinyar hannun ki, idan kika warke sai a sama maki wata mission din mai sauki ki yi ki gama a baki damar fita inda kike so, a lokacin da kike so!

Yana gama fada ya juya ya bar mata dakin cike da yannayin damuwa, da tsoron rasata, dan shi sonta yake , koma mecece ita sonta yake

Da kallo ta bi shi,
Ya Allah, hakane fa, za.a iya mayar da ita fa, shikennan yanzu ta sha bulley din banza kennan? Eh mana tunda dai wata mission din za.a kuma fitar da ita, bayan ta shiga wannan? Bayan ta sha wahalar nan maimakun idan an mayar da itanma a ajiyeta a matsayin ta gama fita mission da sunnan camps din sai dai a turata wata?

Idannuwanta ta rintse tare da shiga tashin hankali, ita fa so take daga nan ta je camp a matsayin wace ta ci nasara ta samu incinta!

A hankali ta buda idannuwanta ta shiga kokarin mikewa bayan ta kashe laptop din

Fitowa ta yi ta nufi dakinsa kanta tsaye,
Tana zuwa ta shiga bugawa, jin shiry ya sakata kara kunnenta, sai dai abinda ta dan fara jiyowa ne ya sakata saurin matsawa gefe tana mai jin gabanta na faduwa,
Sai a lokacin ta dafe kanta da hannun da bashi da ciwo ta ayyanawa kanta cewa....kema baki da kai, a wannan lokacin kike tsamanin samunsa a hayacinsa?

Zama ta yi a wajen, inda BS ya yi kai kawo ya fi a kirga yana aikinsa bai ce da ita komai ba, ya ajiyeta a zata yi ta gama ne,

A kadan sun kwashe awa uku a wajem, daga masu baiwa Ni.ima tsaro, da BS da ita kanta,
Suna kallon juna lokaci zuwa lokaci, suna jiran fitowar Ni.ima , kowa na kallon kowa da ido , basu da abin cewa, sunna zaune ne, kowa kuma ya san me ake yi a cikin dakin, basu da katabus sai ido, dan kuwa rabonsa da ya je dakinta tun da ya mayar da ita cikakiyar mace, ya kasance ita ke zuwa kowani lokaci ya bukaci hakan bisa abinda ya dora mata

A lokacin da suka ji karan buda kofar kowa ya kawar da kansa sannan ya kimtsa kansa,

BS kuwa murmushi ya sakarwa Hafsat yana mai yi mata nuni da ba ta gani ba?

A lokacin da Ni.ima ta fito daga dakin ta yi gaba suka bi bayanta Hafsat ta mike ta nufi dakin da niyar shiga,.

Damtsen hannunta BS ya rike ya saka idannuwansa cikin nata ya ce" zaki je ki wanke abinda baki saka bane ko zaki je ya gama koshi? Ki farka, ko aure yake ba zai aure ki ba!

Hannunta ta fuzge daga rikon da ya yi mata, ta zabga masa wani harar tsana zata yi magana kennan idannuwanta suka sauka saman Abdul dake tsaye yana hangen su,

Kwafa ta yi ta nufi dakin da niyar idan ta fito zata kirta masa rashin mutuncin da ba zai taba mantawa da ita ba

Tana shiga ta rufe dakin ta yi tsaye gabansa,
Da alama bai jima da fitowa daga wanka ba dan kuwa jalabiyar jikinsa na like masa a jikin,

Kawar da fuskarta ta yi dan ita ta tsani wannan kallon rashin kunyar da yake yiwa mutane, sam bai iya kallon adini ba!

Ba wani kwane kwane ta ce" *Abdul, ka hana a tafi da ni gobe, dan Allah=?O?
Dan karamin tawul din da yake tsane kansa ya dan yarfe ya matso kusa da ita a hankali ya ce" kin shaku da dan baiwa Abdul ne kema? Wai ya aka yi mata basa son yin nesa da ni ne?

Bata san lokacin da ta dawo da dubanta wajensa ba, kai wannan mutun idan da asirima to walahi da hali,
Kanta kawai ta iya girgiza masa kafin ta yiwa fuskarta kalar kaucona ni Hafsat,

Abdul ya dora mata tawul din mai dan lema lema wanda ya gama gogo ruwan kansa a kafadarta ya yi gaba ,

Janye tawul din ta yi ta ajiye nan tana yatsina fuska ta juya inda ya nufa ,
Gani ta yi ya ciro karamin wando yana kokarin saka abinsa bayan ya san tana dakin
Da sauri ta juya gaba dayanta, inda ya saci kallonta ya yi murmushi tare da girgiza kansa,
Wandon ya saka sannan ya mike da kyau ya nufi wajen bed dinsa ya zauna,
Fuskarsa ya talabe da hannu daya yana kallonta kafin ya yi gyaran murya

Idannuwanta ta bude a hankali, ganninsa zaune ya sakata sauke ajiyar zuciya,
Wajensa ta nufa, ta samu waje ta zauna tana dubansa a sace sannan ta ce " dan Allah, ka yi min alfarmar nan,

Abdul ya saki talabe fuskar tasa da ya yi ya ce" dalili?

Hafsat ta tsayar da dubanta kansa ta ce" savoda ina son na gama aikina daga nan lafia, ina son inci,

Abdul ya tabe bakinsa sannan ya kuma dubanta ya ce" ke yanzu kina mace har wani inci kike tunanin samu? Tafia ta yi tafia fa aure za.a maki, ki je ki yiwa mijin bauta, yi na yi bari na bari, ki masa girki, ki yi shara, ya maki ciki ki haihu ki shayar da su daga shi har yaron ki rin.....

Dan Allah ya isa, wai kai da kowama haka kake magana marar da.a ko nice kake yiwa kallo mn yar bariki? Ka je ka yiwa matarka mana? Sai ka 2ani saki baki kanai min magangannu mararsa da.a? An gaya maka ni yar iska ce?

Kallon da yake mata ne ya sakata tunawa da a gaban wa take,
Hakan ya sakata yin sororo, tsawa fa ta daka masa, ta yi masa tsawa , bayan yana mai gidanta kuma ta zo neman alfarmarsa ne?

Nan da nan idannuwanta suka ciko da kwala,
Juyawa ta yi ta shiga tafia a hankali tamkar kazar da kwai ya fashewa a ciki,
Har ta kusa fita ta ja ta tsaya tare da juyawa ta dube shi , a hankali ta ce" ka manta abinda na zo nema, dan ban ga anfanin karasa aiki a cikin irin wannan rayuwar ba,

Hawayen idannuwanta ne suka zubo daga kwarmin idon, muryarta ta shiga rawa ta bude dakin ta dago da idannuwanta ta dube shi ta ce" *ni ba yar iska bace Abdul*

Sakin kofar ta yi ta fice a dakin da saurin gaske, inda ya mike da sauri ya sauko daga saman bed din da niyar bin bayanta, sai dai me ya tuna, me ya hana shi? Ya dakata ya dafe goshinsa da yake jin ya wani irin sara masa,
Hannunsa ya kai wajen madubin dakin nasa ya daka da mugun karfi kafin ya saki ihu mai cin rai

Idannuwansa ya dago ya kai dubansa wajen madubin, yana mai jin zuciyarsa na wani irin tafarfasa, jajayen idannuwansa ya kai wajen da ta tsaya a hankali ya ce" ba zan kuma yarda na saka rayuwar wani a hatsari ba Hafsat, ki gane.....ni kuma ba mahaukaci bane soyaya aka hana min yi karfi da yaji..............

Wani murmushi mai kama da na yake ya yi mai ciwo sannan ya ce"
*kWANA goma sha uku kacal, kwana goma sha uku kacal kina faman tarwatsa ni? Ba zan baki wannan damar ba, na fi kowa sannin ke ba yar iska bace Hafsat! Aman zan je da ke a yar iskana=??*
[6/24, 4:04 PM] BAK'A CE: >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 2??


Koda Hafsat ta koma dakinta wanka ta shiga ta yi ta fito ta saka wata riga fara dake cikin kayanta ta zauna tana kallon waje guda,
Kwata kwata wani lokacin idan ya yi irin abubuwan nan sai ta ji ta tsani kanta,
Mikewa ta yi ta dubi madubi,
Tabas yannayinta tamkar ba yar musulmai ba, suturar jikinta a kulun ba kamilaliya bace irin ta yayan musulmai,
Gashin kanta rabon sa da dan kwali ya zauna daram a kanta ba lokacin sallah ba tun tana gidan mahaifanta,
Sam aikin zama bodyguard ba aiki ne da zai ja maka mutunci da girmama ba a kasar Musulmai,
Kai dai kulun ka kare a saka wando, da rigar da ba zasu iya hanaka gabza fada ko dankarawa da gudu ba ? Kai dai haka zaka kare a bushe?

Zama ta yi tana mai jin haushin irin yanda yake nuna mata iya shege a fili duda ba shi ne na fari ba, aman nasa na yi mata ciwo, bata san dalili ba, bata san me yasa du idan ya ambaceta da gardi, ko yace da ita a bushe sai abin ya yi ta yi mata yawo a kwonya!

Tsaki ta ja tana zabgawa bed din da zata kwonta harara a fili ta ce" ba dai na shayar da uban ba, aa shima na mayar da shi cikina na haifo shi! Kuma gwarama na bar aikin naka dan banda neman kai ni barzahu ba abinda yake, ga wulakanci! In sha Allah zan tafiata gobe ka je ka zama abinda zaka zama sai me? Idan ban samu incin daga wannan aikin ba sai me? Na yi hakurin duka wannan lokacin dan wannan ba zai kashe ni ba!

Haka ta yi ta magangannun bacin rai, har ta raba dare kafin ta yi kwonciyarta a nan kasa ta nemi rintsawa,

Du irin yanda ta cika dare, kiran sallar farko a kunnenta, dan haka ta ciciba ta mike tana mai jin hannun ya dan yi mata nauyi dan kuwa ko ba komai ciwo ne da ya kwana ya yi tsami bale harbin bindiga

Zuwa ta yi ta yi wanka, ta kiyaye wajen bata jika ba, haka ta gama du wani uzurinta ta dauro alwallah ta fito,
A daidai lokacin da take kokarin tayar da sallah ta ji shigowar mota,
A hankali ta daga labulen dakin tana hange,
Bakar mota ce ta shigo , gannin BS tsaye a wajen motar ya sakata juyawa ta tayar da sallarta, sai da ta gama a nitse sannan ta dauki dogon wandonta baki da riga baka ta saka, rigar mai karamin hannu ce bata dora ta samanta ba dalilin ciwon hannunta,
Bata shafawa fuskarta komai ba, sai harhada kayanta da ta yi cikin yar akeatinta dama kayan ba wasu masu yawa bane sai bindigarta da ta daura a tsatsonta ta ja rigarta ta rufe bindigar,
Wajen madubin dakin ta je ta tsaya, tsurawa madubin ido ta yi, a hankali ta furta" shikennan, haka zaki bar shi tsakiyar wannan tashin hankalin?

Fuskarta ta yatsina ta dubi madubin da kyau ta ce" kwarai, mutuncina, da son haduwa da iyayena ya fi mani aikin nan da kowama, dan haka zan kara gaba!

Murmushi ta yi ta duka ta dauki akwatin ta shiga janta a hankali, kanta bude ba dan kwali sai gashin kanta da ta daure da dan karamin ribom,

A lokacin da ta fito katon falon gidan, BS ne kawai tsaye ,
Ido ya tsura mata, kai yarinyar ta hadu ne, du irin gudun da aka sakata bai saka mazaunanta rage fadi da tudu ba, cikinta kiwa tamkar babu hanji a ciki, fatar jikinta wani urin fresh da ita, domin kuwa mayukan da sabulansu na wanka ba jagaliya bane, sun karbeta sosai, haka kuma gashin kanta baki ne sidik ba yambo ba komai, haka yake halitarsa ce, ga cika ga madaidaicin tsayi, gaban goshinta ya fi cika da suma luflufluf haka yake, girar fuskarta har cajeta take ta daidaita ta yanda take so, hancinta ya ja ya tafi tsuwait har kusan dan karamin madaidaicin bakinta mai dauke da lebunna kalar pink, idannuwanta manya manya ne masu hasken fari bakin cikinsu mai girma ne sannan ko ranta ya baci sai dai su cicika da kwala,

Shi kansa bai san da ya zuba mata ido ba sai da ta zauna saman kujerar zaman mutun daya bayan ta mayar da jakarta gefe ta dan jingina suka shiga zaman jiran fitowar Abdul da ya san da zuwansu tun jiya da sare

A hankali ya karasa inda take zaune ya zauna shima,

Sai da ya hadiyi yawun neman kwarin gwuiwa ya ce" fuahi ake da ni ne?

Bata buda gazar gazar din gashin idannuwanta ba ta girgiza masa kai kawai,

Kyakyawan dogon hannunta fari kal wanda baya dauke da gashi ko dis , damtsen hannun shar da shi du irin formation din da ta samu bai saka ya yi mundil mundil da shi ba, ya dan kara girma aman bai zama wannan kigi kigi din irin na maza ba ya bi da kallo,
Sai da ya karewa wajen kallo sannan ya kai dubansa kan fuskarta, da son samunsa ne, ya watsa mata selfi a ajiye a gaban wayarsa ya ringa kallo idan ya samu lokaci sai dai ya san bama zai samu hakan ba dan haka a hankalin dai ya ce" yaya jikin ki?

A hankali ta buda bakinta ta dane zuciyarta dan kar ta dankara masa magana ta ce" alhamdulilah

Shiru ya yi shima, bai matsa a kusa da itan ba, bai kuma kara yi mata magana ba, yana mamakin irin yanda sam baya gabanta, ba wani ziga kai ba, ba komai ba irin yanda manyan yan matan cikin gari ke binsa yana jan su a kasa yana tafka masu iya shege da yaudarar soyaya sai gashi yana bin yar yarinyar nan tana faman jan sa a kasa, ko yanzu wace aka kawo ta canjeta babar bodyguard ce, kuma ta yi kudi sosai yanzu haka daga america aka daukota aka yo nan da ita, yar kwalisa , yar cakwas da ita, ita kanta soyaya suka yi ya yarda ita daga baya , ko yanzu yace su koma zata yarda da gudu ne, aman ita ga damarta a hannunta tana wasa da ita.

Wasa wasa a nan a zaune sai da suka kai wajen karfe tara da mintuna, suna yi suna kallon agogo, aman ba Abdul ba alamunsa,
Shi dai BS yana zaube bai yi gigin zuwa taso shi ba, hakama ba wanda ya yi gigin hakan domin dai su BS ne mai gidansu, umarnin da ya bada shi za.a bi dole, shi kuwa an fada masa waye Abdul din, dan haka yake kiyayewa

Goma saura kadan alamun bude dakinsa suka bayanna , dan Haka da sauri BS ya mike ya koma wajen kofar ya tsaya hakama Hafsat ta mike tana jiran fitowarsa, inda BS ya shaidawa na wajen cewa zai fito dan haka kowa ya kama kansa

Sai da Abdul ya gama wana kys din kofar sannan ya bude ya fito,
A lokacin da ya fito maimakun ya tsaya ya bi abinda ake juransa dominsa, sai ya shiga dayan lungun da zai sada shi da dakin Muhammad,

BS juyowa ya yi ya dubi Hafsat dake tsaye itama,
Ai kuwa yannayin da ya nuna ita sai ya bata dariya ma, dan haka ta murmusa tana dubansa sannan ta kauda kanta, a ranta kuwa tana ayyana baka san rainin hankalin Abdul har inda ya kai ba kennan, muna iya wuni a wajen nan idan ya yi niya!

Abdul na zuwa ya samu Muhammad ya gama shiryawa, shima cikin shirin manyan kaya kamar yanda Abdul din ya saka irin dinkin yan nigeria , shada har da hula kuma du sun karbe su sun fito da su das gwannin sha.awa,

Muhammad ya dube shi da kyau bayan sun gaisa ya ce" yanzu sai ka je daurin auren nan Abdul? Kai wai ina ruwanka ne ma da shiga wannan lamarin? Shi mahaifin nata ba ya san daga inda ya daukota ba? Kuma dai ya san ba zikiri ake a wajen ba abinda ya kaita take yi ba wata damuwa, to yanzu dan zai mata aure fisabililahi Abdul sai ka wani saka mu shiga ta mutunci tamkar zamu je yin abib kirki ?

Abdul ya zauna saman kujera yana dubansa ya ce" Muhammad, Muhammad ya rab, Muhammad kana so kennan mu zuba ido a daura mata aure bayan da dati a jikinta? Ina laifin ta kilace kanta har datin dake jikinta ya barta? Shi kennan dan son kai sai ya rufe ya baiwa wani? Ka ga idan zaka bi ni aikin Allah tashi mu je, idan kuwa tsoron mutanen dubiya ya fiye maka aikin ubangijinka kuma Fine, ai yana kallon ka

Muhammad kam ya shiga cikin tsaka mai wuya, ya dirmiya shi a cikin lamarin shaku kuma ya hada shi da Allah, shi bai san yaya zai yi ba, walahi yana son barin garin aman irin hadarin da Abdul ke shiga ya hana shi motsawa, yanzu mai gaba daya zai dulmiya su a wani lamarin

Turarensa ya kara fesawa, ya gyara zaman hularsa, wato ya kafeta a kansa sannan ya dubi Abdul ya yi gaba ya fara tafia

Murmushi Abdul ya yi ya mike shima ya bi bayansa suka fito gaba dayansu,

Sai da suka fito farfajiyar gidan ya tsaya yana sauraron BS dake masa bayannin an kawo wa.inda zasu dauki wajen bodyguards dinsa da aka harba

Juyawa Abdul ya yi da bakin gilas din idannuwansa ya shiga bin su da kallo,
Wanda aka kawo namijin sosai ya girm8 jibrin, alamun karfi da jajircewa sun bayana a tare da shi,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login