Showing 105001 words to 108000 words out of 154870 words

Chapter 36 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1135

na neman canzawa sakamakon kokarin tuno irin abinda ya faru tsakaninsa da Muhammad da kuma irin hukuncin da ya yi masa, da sauri ya dauki carbinsa ya shiga jan salatin annabi *MUHAMAD SALALAHU ALAIHI WA SALAM*, yi yake ba kakautawa, a hankali ya ringa jin nutsuwa na ratsa masa zuciyarsa har ya nemi damuwarsa ya rasa
Bai tashi a wajen ba sai da ya rokawa malan gamawa da duniya lafia, domin shi ya bashi sirrin salatin annabi, da ba dan ya riki sirrin nan ba da bai san idan ransa ya baci ina zai tsoma ransa ya ji dadi ba

Sai da ya kwonta saman bed dinsa, yana rintse ido ya ji passsssss
Karar marin da ya sakar mata,
Da sauri ya buda idannuwan nasa,
Hannunsa ya daga yana kallo, hannunsa na dama wanda da shi ya mareta,
A hankali ya mayar da hannun ya ajiye a fili ya ce" aman me ke damun zuciyarki Hafsana? Me ya sa kika zuran ido baki ce da ni komai ba? Na mare ki, na yi maki ihu a kai duka kina kallona baki bani amsa daidai da ni ba? Da gaske sunna mugun takura ki a gidan nan? In dai dalilinsu kike cikin yannayi na rashin walwala zan saka a yi maza a yi aurenki ko na maido ki nan a matsayin bodyguard dina har a maki aure ki yi tafiarki gidanki,

Wayarsa ya dauko yana kallo, sunnan BS dake cikin wayar ya kurawa ido,
Ya so ya rubuta masa message sai kuma ya fasa,
Juyawa ya yi ya gyara kwonciyarsa da niyar idan ya kai gobe lafia zai nemi BS, zasu yi da wajewa idan ya auri Hafsat ya wulakanta masa ita walahi sai ya yi shara.a da shi! Dan rainin hankalin banza dan rainin hankalin wofi, dalilin wulakantata da Muhamad ya yi ba zai yarda kowani kato ya wulakantata a gidan aure ba, idan da hali zai saka camera dan gannin irin zaman da suke dan kar ya je ana cutarta a yanda ta zama lusarar nan yanzu ta rufe ta kasa fadi!!!!!!!!! (Sannu baba)


Sai da mama ta gama salolinta ta shiga dakin Hafsat, nan ta tarar da ita ta yi wani kwonci a takure tana baci sai sauke ajiyar zuciya take

A hankali ta shafi gefen fuskarya da ya tasa kadan, ya kumbura irin an daketan nan, kura mata ido ta yi cike da tausayawa , ko wa ya dake ta? Me ya hada su?

Ledar Boutik din da ta je ta buda ta ga Lipton din da ta siyo,
Murmushi ta yi ta mayar mata da kayanta ta mike ta fita a dakin tana mai yi mata fatan alkhairi a kasan zuciyarta


Bayan Hafsat ta yi sallar asuba wanka ta kuma yi ta canza kayan jikinta na baci, ta saka hijab dinta na sallah ta dauki ledar lipton din malan da canjin jika biyun da ya bata na taxi ta fito

Daya daya cikin yaran gidansu ke wulgawa jifa jifa domin safiya ce karfe bakwai da wani abu gashi ba makaranta,
Da ido suke binta, ba wanda ya gaisheta cikinsu dan kuwa iyayensu sun fada masu daga yawon banza ta dawo kar wanda ya girmamata, gashi dama ta girma fiye da yanda malan ke barin yayansa mata su kai bai masu aure ba, hakan ya sa du suke mata wani gani gani sannan suka yarda da maganar iyayensu

A hankali ta karasa kofar dakin mahaifinta, hannunta ta saka ta tura kofar da salama a bakinta
Tana shiga ta ringa jin maganar hajia, uwar gida kennan ran gida , matar malan ta farko tana magana kamar haka" aman malan yaya zaka ringa nuna rashin adalci a tsakanin yayanka kiri kiri? Nan Zakari tafia ce ya yi neman kudi dan ka hana shi da ya dawo ba irin abinda bai gani ba da ni kansa mahaifiyarsa,
Aman malan ita yar gwal din shekararta nawa bata gida ba aure akai mata ba ba karatu aka kaita ba ba dawan makaranta aka kaita ba? Rana tsaka a dawo da ita cikin yayanmu kananu a shigo da ita cikin gida gaban kowa a ringa yi mata oyoyo ana murnar dawowarta ana rungumarta ana nuna mata farin cikin ganninta , malan baka tsawata ba, baka tara yayanmu baki daya ka yi fada ka hukuntata ba, baka nuna wani bacin ranka ba, hasalima kilaceta ka yi ka yi mata dinkuna, bata yi mana aikin fari bare na baki a cikin gida tana nade a daki tana cin abinda ta yi muradi, tana shan abinda ta ga dama, karshe malan da girmanta shekara kusan ashirin da biyu har damar ta zauna tanai maka zance a cikin gidanka da wani kato wanda ba tsaresu ake bare a san me suke yi ko suke cewa ba, malan a jiya a kawo mana wani gabjejen katon da bashi da fara.a ya zo ya tsaya a gabanmu kikam yana harararmu wai a gidansu ta zauna, a fadi haka a gaban yayanmu warwararu da kananu, malan kwakwaluwar yara me ake so su dauka? Me zai hana su suma gobe su tafka tsiyar da ta tafka su kuma dawo mana gida kai tsaye? Koda yake su sun san ba yayan so bane ba zasu yi hakan ba, aman gaskiya malan korafinmu kawai a san abin yi, idan da hali a fitar da ita a kaita can wajen dangi har a yi mata aure, ko a maida ta gidan su yaron da ya zo jiyan muga idan shi iyayansa zasu aminta anai masu irin haka a cikin gida ba aure ba komai!

Malan dake zaune, tun da ya bata damar magana shiru ya yi yana sauraronta har ta gama,
A hankali ya shiga bin sauran matan da kallo, kowace na zaune kusa da ita da alama shawara aka yi na abinda za.a fada masa , sai aka baiwa wace ta fi kowace tsaurin ido da rashin tsoron zuciya ta fada masa,
Dubansa ya kai kan matarsa, mahaifiyar Hafsat, kanta a sade yake, ko daya ba.a gannin fuskarta bare a gane yannayin da take ciki, sai yatsutsanta da take ta murzawa tana karawa tamkar wa.inda take son canza masu kalar fatarsu dake jikin hannun nata,

Dubansa ya kara kaiwa kan matarsa, wace ita ce ya dace ta zama mai datako, mai tsawatarwa mai tausasa muryarta mai nasiha gare su da shi kansa, aman kananun sun turota ita ce yau ta buda baki, ta daga muryarta sama da tashi, ta gaigaya masa magangannu irin haka a kan *Uwa*, shi da yake rayuwa a takure , yana boye nuna soyayar mamansa a gaban yan uwanta dan a zauna lafia ashe bai tsita ba? Shi da yake nuna kowani da da ya haifa daya ne a wajensa ashe ba tsira ya yi ba? Me ya ragi yayansa da shi? Bukatunsu, tarbiya, ilimi, ko walwalarsa? Ba wada ya hana masu, kowane ya basu wadatace kuwa,
Me suke so da shi ne? So suke ya rufe Mamansa da duka kan laifin da bata aikata ba? Ko a kan zarginsu suke so su dawama harma suke ikirarin ya fitar da ita daga gidansa ? Mamansa? Mamansa ce suke so ya wulakanta haka?

Ajiyar zuciya ya sauke mai karfi wace ta saka mama dago da kanta a hankali ta saci kallonsa idannuwansa sun kada sun yi jajir, tausayinsa ne ta ji ya kama ta, haka kuma sai ta ji haushin Hafsat din, tun tana karama ake irin haka a kanta, a da yana da karfi da yarinta a yanzu da ya fara manyanta ma ba zai huta ba? A bar mata mijinta ya huta haka, in dai a kan Hafsat ne in sha Allah idan bata samu miji bama ita zata kaita inda ta kaita, in sha Allah zata samu ya yarje mata ta kaita nesa da gidan ko kowa zai kwontar da hankalinsa a kan kishin zamanta a gidan da suke, kallonta ta kawar, idannuwanta je suka sauka kan kwalin lipton din nasa da ta ajiye ta juya,
Gabanta ne ta ji ya fadi, kar dai a je ta ji? Dama akoyta sabkon zuwa wajensa su yi karatu kafin su yi ta hirar duniya, yakan yi mata labarai su sha dariya, yakan yi mata bayanin dukiyarsa , kai harma da shawara,

Kanta ta sada, sai kuma jin muryar malan ta yi ya ce"
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 8??




Cikin kakausar murya aba ya ce" ku tashi ku tafi

Kowace sai da ta kale shi, baki mama uwar gida ta kebe kafin ta fara mikewa da sauri ta yi gaba kasa kasa kuwa sai guna guni take

Bayanta suka rufa baya , sai mama kawai a zaune kanta a sade
Aba ya kawo dubansa wajenta, cikin kakausar murya ya ce" ba nace ku tafi baki dayanku ku bani waje ba?

Da sauri ta mike tsaye tana maida kukan dake cin zuciyarta,
Juyawa ta yi har ta kusa fita a dakin ya ce" daga yau a fara shirya Uwata, in sha Allah zan karbi kudin aurenta karshen makon nan!

Mama kam kanta kawai ta gyada ta fice a dakin, wannan shine a dakeka a hanaka kuka, shi dama malan idan ransa ya baci kowama hadawa yake ya hukunta ba ruwansa abinsa,
Yanzu dai sun jaza masu fada da fushin malan, a kan mamansa ransa na kololuwar baci fa!

Sai da suka fita baki dayansu Malan ya dauki katuwar wayarsa irin rakani bayi din nan mai hasken tsiya ya latsa numbobin ya samo sunnan da yake nema ya danna kira

Abdul dake zaune yana shan lipton dan safiar yanzu ta waye a wajensa ya daga kiran cikin nutsuwa ya yi salama

Sai da suka gaisa a mutunce sannan malan ya sauke ajiyar zuciya cikin yannayin nutsuwa ya ce " ka yi hakuri na yi maka kiran samako ko?

Abdul ya ajiye dan abin shan lipton din dake hannunsa ya gyara zama tamkar malan din na gabanshi ya ce" aa, ai na jima da farkawa malan

Malan ya ce" masha Allah, dama ina so ne na fada maka, ka fadawa wannan yaro mai neman auren Uwata, idan har da gaske yake ya turo da magabatansa, sannan ina so ka taimaka min wajen bincike kamar yanda ake yi

Shiru Abdul ya yi, har sai da malan ya dubi wayar yana fadin ko dai bai ji ba network din nan da bashi da tabs

Abduk ya sauke ajiyar zuciya ya ce" in sha Allah malan zan shigo idan na sauka a aiki

Salama suka yi Abdul da malan, nan Abdul ya mike ya nufi dakinsa dan kimtsawa ya tafi wajen aiki

A lokacin da ya fito suka hadu da Na.ima, ta sha doguwar riga ja mai duwatsu, rigar ta bi dan jikinta mai tsari, kokarin karasawa dakinsa take suka hadu a nan falo

Hannunsa ya saka ya kamota jikinsa, goshinta ya sakarea kiss ya shafi gefen fuskarta kafin a hankali ya ce" zan tafi wajen aiki

Idannuwanta ta lumshe kafin ta ce" zan yi missing dinka

Murmushi ya yi mata sai kuma ya juya daga shi sai ky din motarsa ya dauki hanya

Ya yi aikin awa uku, a kampaninsa na atampa daga nan ya dauki hanyar?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? doguwar tafia,
Hankali kwonce yake ratsa jejin har ya karaso dan nesa kadan da wajen sannan ya sauka ya daga hannayensa sama sakamakon mai tsaron da ya kurma ihun ya daga hannayensa sama sannan aka shiga tambayarsa waye shi, wa ya zo nema, wa ya gwada masa wajen?

Shi dai a tsaye yake har suka karaso inda yake suka shiga da shi wajen horon bodyguards din suna masu taka tsantsan da mamakin waye shi kuma daga ina ya zo masu wajen sirrin nan?

Sai da aka yi jiran GN ya zo sannan suka sake shi bayan ya bada umarni

A hankali suke takawa GN da shi, cikin yannayin mamaki GN ya ce" yaya aka yi ka kawo kanka wajen nan?

Abdul ya kale shi ya ce" a ranar da aka maida mu tare da mahaifiyata, tun a ranar na saka maku abinda zai nunan inda kuke dan tsaro,
A ranar na san inda kuke ba.a dai yi falilin da zan zo bane sai yanzu

GN ya jinjina kai yana kallonsa, wato dai shi bai yarda da kowa ba?

Abdul ya ce" waye BS? A ina iyayensa? Ta yaya ya zo base? Menene halayensa?

GN gabansa ne ya ji ya fadi yana kallon Abdul,
Tsoro ne ya ji ya kama shi kar a je BS ya janyowa kansa wani balakin?

Abdul ya juya ya fuskanci GN da kyau , ya yi masa wani kallon dake nufin shi yake sauraro

GN ya sauke ajiyar zuciya ya ce" BS, bazabarme ne, domin ni ne mahaifinsa, mun same shi ne da mahaifiyarsa a lokacin muna soyaya, Allah bai yi zan aureta ba aka aura min wata

Abdul ya kafe shi da ido cike da mamakin wai ashe BS dansa ne? Aman yaya aka yi bai amsa sunnansa ba? Duda ya ji ya ce ba da aure ya same shi ba,
Kansa ya girgiza ya furzar da wata iska daga bakinsa, shi kam bai san me ke damun mutane ba, ya sani akoy kadara aman wai har wata kunya yake ji a yanzu ko me?

Tsaki ya ja a fili ya ce" yaya aka yi ya ci jarabawar zuwa wajen nan, harma ya zama Bodyguard soldier? Shin takardubsa suka bashi dama ko babansa?

GN ya kali Abdul ido cikin ido, sam bai ga tsoro ko alamun zai risina masa ko dan ya girme shi, dan haka gwara ya fito a mutun ya bashi du wasu informations kan questions dinsa, fatansa dai ba wani laifi ya yi ba

Bakinsa ya buda ya zayanewa Abdul du wata tambaya tasa a nan a inda suke tsaye dan GN ya so su karasa su zauna abdul ya ce sauri yake

Sai da ya gama Abdul ya gyada kansa ya ce" masha Allah

GN ya ce" aman, sire wani laifi ya aikata ne?

Abdul ya kale shi, sai da ya gama nazartarsa sannan ya daga kafadunsa duka biyu ya ce" bai aikata ba tukunnan, ka bashi sako yarinyar da yake neman aurenta idan har da agske yake mahaifinta ya ce ya fito a cikin satin nan a yi komai a gama, idan kuma ba da gaske yake ba, abinda nake so da shi shine ya janye a hankali, ba tare da ta zubar da hawaye dalilin hakan ba, dan na tabata zata samu wani idan shi baya yi

Yana gama fada ya mikawa GN hannu suka gaisa sannan ya sakar masa fuska suka yi salama tare da mutunta junna suka rabu

Abdul bai koma gidansa ba masalaci ya je, yana zuwa ya tarar da Malan zaune da jama.a ana ta karatu dan haka ya gaishe su kawai ya juya ya koma gidansa

Da dare bayan salar isha.i suka shigo da malan, sai da suka zauna Abdul ya fadawa malan cewa ya je, ya binciko, in sha Allah ya fadawa mahaifin yaron idan har sun tashi auren da gaske to su fito

Malan kam godiya ya ringa yiwa Abdul, wace har sai da ya gaji da amsawa

Sun jima zaune suna hira jefi jefi, sai malan ya ji Abdul ya ce" wani abu ya faru da ita ne?

Malan ya kale shi, sam bai gane wa yake nufi ba, aman gannin ya yi jim ya saka shi cewa" wa fa?


Abdul ya dago yana kallon malan, shi fa gaskiya ba zai cewa Hafsat wai mama ba, shi kuma ba zai kama sunnanta kiri kiri gaban malan har a je ya daina gannin mutuncinsa ba, dan haka sai ya ce" ita wace za.a yiwa auren

Malan ya kada kansa yana murmushi ya ce" Abdallah, bana son yaro ya ringa yi min dogon zance a gida, ai kawai idan yi yake ya fito a yi a gama, idan kuwa ba shi ne rabon ba sai ya bada waje ko zata sami wani ya aureta itama ta je ta raya sunnar ma.aiki

Abdul ya gyada kai sannan ya kawar da dubansa, wani haushi ne ya ji yana ji, wai ko ta samu mai aurenta, Hafsat din rasa mai sonta zata yi ne? Yarinyar mai daraja mai hankali mai ilimi mai kyau? Me ta rasa a jikinta na mace har da malan ke son saka gagawa a lamarinta?

Yau bai cika dare ba ya yiwa malan salama,

Yana saukowa ya hadu fa ita tana shanya saman igiya, ita daya ce kwal a tsakar gidan da yake lokacin kamar da sanyi sanyi kowa yana daki ya labe, itama wankin kayanta irin dogon wando ne ya sakata yi da dare sannan ta kwashe da wuri dan basa barin kananun kayansu na shawagi a tsakar gidan, wannan mahaifiyarta ce ta yi mata wannan horon

Tsayawa ya yi ya harde hannayensa duka biyu yana kallon yanda take dukawa ta matse kayan sannan ta mike ta shanya saman igiya, har dira take dan ta gyara shanyar da kyau

Idannuwansa ya lumshe a hankali ya furta" ANGEL

Hafsat dake shanyarta bata ma san yana wajen ba, sai da ya ga hakan ba gyara shi zata yi ba da sauri ya matso inda take ya tsaya a gabanta tana shanya kayan tana juyowa suka kusan hada kirji

Da sauri ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login