Showing 57001 words to 60000 words out of 154870 words

Chapter 20 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1154

da harufa, tamkar da gaske tana fahimtar abinda take fada, ashe ita bata ma san me take cewa ba,

Zagayeta ta yi ta nufi ciki tamkar ta kifa,
Tana zuwa ta tarar an rufe dakin, bodyguard din nan sabo ya tsare kofar ya caka fuska,

Shi kansa uban gidansu ne, dan haka ba zai yiwu Hafsat ta kawo masa wargi ko wani gatsali ba, kusa da kofar ta je ta tsaya ta tsura masa ido tana kallon sa

Shima ita din ya kala, mamaki ne ya kama shi irin yanda ta tsura masa ido, dan haka da girarsa ya yi mata alamun tambayar lafia?

Kanta ta sada ta kasa bashi amsa,
Suna wajen nan wasa wasa har docter ya zo,
Cikin wani irin sauri bodyguard din nan ya caje shi sannan ya bashi hanya ya shige,
Abin ya baiwa docter tsoro, domin wannan jinnin da yake fitarwa ta hancinsa dole ya fitar da shi a hayacinsa, kuma a iya binciken da ya yi da abubuwan da ya dauko da aka fada masa cewa habo ne bai ga wani dalili ba, kuma ya bayar da du abinda ya dace a yi an yi dan ya tsaya aman ina, haka suka talaba shi suka yi ta bubuga goshin , shima dai sai ya yi kamar ya tsaya aman daga sun kwontar da shi sai ya dawo, gashi dai tamkar gawa dan ya fice a hayacinsa tuni

Doctern ne cikin wani yannayi ya ce " sai fa mun je asibiti da shi, idan ba haka ba kuwa za.a iya rasa shi a kowani lokaci

Cikin tashin Hankali Muhammad ya dube shi kafin ya yo gaba ya fito a sukwane ya nufi dakinsa

Cikin hanzari ta mike ta bi bayansa sai dai nan ma an hana ta shiga sanadiyar sojojin dake wajen

Me ya yi? Oho sai fitowa ya sake yi tamkar ya tashi sama , fuskarsa jaga jaga da hawaye nan Hafsat ta tare shi tana tambayarsa jikin Abdul din

Sai da ya dan dubeta, sannan ya girgiza mata kai ya rabata ya shige

Hannayenta duka biyu ta dora saman kanta a fili ta furta" shikennan, sun cin maka Abdul,

Hannunta mai ciwo ne ta ji kamar wani abin ya kara sukarta, dan haka ta dan ajiye shi a ranta tana tunanin harbin ne ke hadasa mata haka, aman a hankali sai ta dan juyo hannun dan dubawa

Sai da gabanta ya fadi irin abinda ta gani, rubutu ne, da larabci a bayan hannun nata,
Da sauri ta juya ta fada dakinta ta kunna wutar dakin ta je gaban madubi ta ja ta tsaya tana kallon hannun,

A hankali ta karanta abinda aka rubutan kafin ta fasarce da kalmar hausa cewa *maganin ruwan zamzam da dabino ta hanyar da jinnin ya yawaita*

Ta karanta ta maimaita ya fi a kirga kafin kamar a mafarki abinda mutumen da ya damki hannunta a wajen taron nan ya dawo mata,
Tabas wannan mutun shi ne ya damki hannunta daidai wajen nan wanda ta gani rike da bindiga har ta yi ihun mutun da bindiga,

Da sauri ta ruko idannuwanta domin kuwa ba zata manta ba da ya fadi haka sai da ya kure mata waje kafin ya furta mata sunnan *ABDUL*

Baya baya ta yi dabas ta zauna a kasa,
Tsoro da rudu ne suka shigeta a lokaci daya,
Ta shiga rudanni tsakanin amsoshi biyu ta fanni biyu,

To waye shi? Me zai saka shi ceton Abdul? Idan fa ba cetonsa bane zai yi aa karasa shi ne zai yi ta wannan hanyar? Aman kuma ruwan zamzam waraka ne, tsaftacen ruwa ne, zai cutar da bawa ne?
Eh to ana iya hada shi da wani abin ya cutar din mana,
To aman da dabino ne aka hada shin fa, dabinoma ai warakar ne,
Yannayin mutumen bai bata kalar mai tausayi ba,
Yannayinsa bai yi mata nuni da zai iya ceto ba, idannuwansa sun tsoratar da ita, irin rikon da ya yi mata ya tsoratar da ita,

Tana nan zaune tana sakawa tana warwarewa har ta ji alamar kukan ambulance

Mikewa ta yi cike da mamakin ambulance kuma? Ina kwakwaluwar BS zai bari a kai shi asibiti a ambulance? Idan fa an yi haka ne dan a tarbi motar a karasa shi?? Baya tsoron daga ambulance din wani mugun abin ya same shi??

Da sauri ta nufi hanyar fita ta fice a dakin ta tunkari dakin Abdul din

Tana zuwa yanzun tsaye ta yi gaban Bodyguard din ta bashi bayannin ita ke kula da ci shan Abdul, ya dace ace tana kusa idan za.a saka masa karin ruwa da du wani abu, idan ya hanata shiga Abdul ya tashi zata kai karansa wajensa dan kuwa ya hanna mata yin aikinta yanda ya kamata

Sai da ya yi mata kallon baki da wayo, sannan ya yiw BS magana da abinda Hafsat ta fada,

Jimm BS ya yi na dan lokaci kafin ya ce" barta ta shigo

Hanya ya kauce mata ta shiga ya bi bayanta da kallo yana mamakin to idan ta fadawa Abdul din sai me? Shi ya san kan aikinsu ne? Kuma yayama aka yi take kama sunnansa kai tsaye tace *ABDUL?*

Tana shiga wajen BS ta zarce tana kallon yanda Abdul ke kwonce shame shame an cire masa rigar jikinsa daga shi sai wandon rigar , likita da Muhammad na kusa da kusa da shi
Haka kawai ta ji zuciyarta ta karye, ya salam, mutun, mutun ba komai bane, mutun ba komai bane, yanzu Abdul ne lokaci kankani ya dawo haka? Mutun shi ya dauki kansa wata tsiya!

Sai da ta yi da gaske ta hana idannuwanta zubar da hawaye, a haka ta karasa gaban BS dake tsaye ta dago da idannuwanta ta lunshesu sosai ta bada kalar tausayi da son ya saurareta ta ce" BS, ya zaka yarda a tafi asibiti da shi?

BS ya tabe baki yana kawar da idannuwansa daga yannayin fuskarta fanma kar zuciyarsa ta karye ya ce" kin san dai a haka ba za.a iya tafia da shi asibiti a motarsa ba ko? Dole sai an jona masa abin taimakon da dole sai an saka shi a ambulance domin a ciki ne za.a iya samu!

Hafsat ta kara matsawa kusa da shi sosai , ta rage karfin muryarta ta ce" mutumen da ya rike hannuna, dubi abinda ya rubuta min a bayan hannu, idanfa an saka masa poison ne sai wannan ne makarinsa?

Wani duba ya yi mata kafin ya ce" ta ina aka kai gareshi? Marabinku da shi shigarsu cikin motar dan minister, jikin ku jikinsa fa, a iska aka saka? Idan a iska ne yaya aka yi mu bamu shaka ba?
A abin sha aka bashi? Sannin kanki ne ko abinci bai yarda da shi ba , shi ke girkawa ya ci da kansa ko *abincin ki* bai yarda da shi ba!

Da sauri ta dube shi, wai ko abincinta, dan me za tana wareta da su?
Kanta ta kawar tana dubansa ta ce" wannan likitan, baban likita ne da ake takama da shi a garin nan, tun da na shigo ni banda kame kame da desespoir din dake nuna bai san kan abinda ya hadasawa Sire wannan rashin lafia ba bana gannin komai,
Yana maimaita ko ya shaki wata iska ne? Ko wani abin?
Yace a kai shi asibiti dan su shiga bincike su ga abinda ya same shi ya hadasa masa haka, binciken da kan iya daukan awowi domin inji ke bada amsoshin ba mutun ba,

Shiru ta yi kafin ta kara dubansa da idannuwanta da suka ciciko da kwallah cikin wani irin sanyi da murya mai rawa rawa ta ce" *idan fa ya mutu kafin lokacin?* jinni ne fa ke zuba daga hancinsa *Bashir*

Tsai ya tsayar da idannuwansa cikin nata jin yau na farko kennan da ta taba kiran sunnansa kai tsaye, ashe ta san sunnan? Ashe ta san sunnansa?
A gaskiya maimakun yannayinta ya saka shi cikin shaukinta sai ya saka shi cikin halin damuwa, shi fa ko me za.a ce ba za.a iya saka shi yarda da wai Hafsa na haka dan samun yanci bane! Dan haka shima cikin dakewa ya ce" idan ya mutu, ai lokacinsa ne ya yi, akoy wanda ya isa ya hana shi tafia ne?

Mamaki, tsoro, duka suka daketa tana duban BS yana dubanta ya furta mata haka?
A hankali ta hadiyi yawun dake bakinta dan kadan wanda da shi da babu kusan daya, ta lumshe idannuwanta hakan ya saka hawayenta zubowa bisan kumatunta,

Wannan karron muryarta ta daga ta ce" na rantse da wanda raina ke hannunsa idan akoy wanda zai fita da wannan mutumen yau sai dai idan harbe ni zaka yi kafin a fice da shi! Ban ga wani dan adam din da zai kara nisan kusancina da Malan ba!

Juyawa ta yi da sauri tana kokarin ciro karamar bindigar dake kugunta BS ya yi saurin damko hannunta ya juyo da ida inda du su Muhammad da docter suka juyo wajen da suke dan kuwa da gaske ta tayar da kukuma gata tsurut a gabansa

BS na kallonta da takaici ya ce" kin san ba ke daya ke anfani da bindiga a wajen nan ba ko? Kuma kin san gaba dayanmu manyanki ne ko? Ke ko kunya bakya ji saboda shi zaki yi haka?

Hannunta ta fizge ta ruruko idannuwanta, wato dai masifar ta motsa ta ce" me ya kai kudi daraja a wajenka? Kai saboda kudi kana iya yin komai ko? A tsaka mai wuya muke daga ni har kai! Ka harbe ni kawai ka huta da ni, idan ka harbe ni me za.a yi? Ba abinda za.a yi kana iya cewa kan aikinka kake na tare maka hanya BS!

Hannunta ta kara fuzgewa daidai lokacin Hasana ta shigo domin dai sabon Bodyguard dinma na casan kokowa da Ni.ima wace sai zuwa lokacin da ta ji kukan Ambulance ake fada mata mijinta ne ba lafia dan haka ta fito da rigimar sai ta je inda yake

Hasana na shigowa ta kai dubanta wajen BS tana jiran umarnin yanda za.a yi da Hafsat, sai dai ga mamakinta sai ta ga ya saki hannun na Hafsat din ya barta sai da ta fara tafia wai kamar BS ya sandeta ya buga mata hannunsa dake mike a bayan keyarta hakan ya hadasa mata zuwa duniyar summa

Bata gama jin tsanar Hafsat ta darsun mata ba sai da ta ga BS ya kinkimeta ya dorata saman kujera mai cin gurin mutun hudu ya mikar da ita ya gyara mata kwonciya sannan ya mike yana kallon Muhammad dake jefo masa kausasun tambayoyi kan abinda ke faruwa,

Muryar docter ce ta katse masa hanzarinsa inda ya furta cewa maza a shirya shi a dora shi kan gadon mararsa lafia a fita da shi a saka shi Ambulance


A lokaci guda BS ya mike ya zuba masu ido su duka ya kalli wannan , ya kalli wancen, ya kalli Hafsat dake kwonce filat da ita,

Ya shiga rudu, gashi a tsaka mai wuya........

Sai da ya fara tafia ya ce"""




*shin, za.a yarda a fita da Abdul bayan tabas gaskiyar Hafsat ne komai na iya faruwa, dan kuwa ko doctern kansa ana iya sayensa irin wannan naci na a fita da Abdul? Waye wannan bawan Allah da ya damki hannun Hafsat? Zai bada taimako ko zai cutar ne? Meye dalilinsa na yin daya cikin biyun? Me ya faru a wajen daurin auren da Abdul ya tarwatsa? Hafsat, me ke damunta? Idan wannan magani da ta fada na cutarwa ne fa? Idan aka ki yi masa kuma a je shi din ne magannin da zai bashi taimakon? Ku biyo ni mu je zuwa daga alkalamin yar mutan Niger........*



Dan Allah ki yi hakuri da rashin yawansa, ina jinyar yar muleka=??=??=??=??

=؃? >د?=ؔ?>د?=?n? @&?
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 5??

*wannan nvl na kudi ne, idan kin biya kin shiga na roki alfarmar dan girman Allah ba dan ni ba kar ki fitar min da shi ki yi hakurin har na gama shi sai ki fitar da abinki ki yi yanda kike so da shi bani da matsala da hakan, dan Allah idan kin san dan fitina, ko dan ki wulakanta min kika shigo ki min magana pc daga ni sai ke na biya ki kudinki wato naira 200 ta hanyar accnt din ki ko kati, dan alfarmar soyayarku da annabi muhammad kar ku fitar min da novel, ku bari na gama shi, in sha Allah ba mai tsayin da zai saka ku gajiya da jira bane=?O?


Sai da ya fara tafia ya nufi wajen gadon da Abdul.ke kwonce kafin ya juyo cikin tsawa ya dubi Hasana ya ce" zaki je ki saka matarnan ta daina mana ihun batancii a wajen nan ko sai na wanka maki marin da zai dauke jin ki ne BD?

Da sauri ta kame masa sannan ta juya ta fice dan fitar da Ni.ima a wajen nan

Bayan fitarta tsayuwa ya yi gabansu yana dubansu daya bayan daya,

Shi bai ga wani allamu na rashin gaskiya a tatare da su ba, aman du da haka sai ya ce" bafa za.a shiga ambulance da shi ba, zan tuka motarsa na kai shi asibitin naku , ku ban kwatance

Muhammad ya dafe kansa cike da takaicin wannan lamari ya ce" wani irin kai zaka kai shi? Kai a wa? Ni na fi kusanci da shi a wannan lokacin, rayuwarsa ita ta fi min komai mahinmanci , dan me zaka ce kai zaka fita da shi? Bayan ka ji bayanin likita cewa dole sai an bashi taimakon oxcygene a tsayin tafiarsa?

Kansa ya girgiza ya matso sosai kusan Muhammad ya dube shi ya ce" kai ka san ko waye shi, nima na san hakan, an bashi horon nitsewa cikin ruwa tsayin minti ashirin tare da rike numfashinsa, ya yi kuma ya ci,
An saka shi a rami an rufe irin na gawa sai dai fa ransa kuma a zaune, sannan ramin mai dan fadi ne aman ba oxygene, haka yana shakar oxygene dinsa har ya kare a hankali ya silale ya tafi duniyar suma

Kai ka san me da me da me ya gani wanda mu fada mana ne ake cewar idan muna son zama irinsa sai mun je mun ga wannan rayuwa,
*Mutuwa* ina jin ba yau ba yake gwadata, idan har ya mutu a yanzu a hannuna, toh fa ba wanda ya isa ya tado shi, aman ba zan yarda a fita da shi a wancen motar mai kuka ba! A matsayin na shugaban masu bashi tsaro ina da dama da ikon yanda za.a yi da shi, kai harta likitan da zai ganshi ina da damar zaba, dan haka na yanke hukunci!

Muhammad ya girgiza kansa cike da tashin hankali ya ce" to sai dai idan da ni zamu je, ba zan yarda a yi wasa da rayuwarsa ba, !


BS ya daga kafadunsa sannan ya juya wajen da Abdul yake, sai da ya saki wani nishi dan walahi a dazuma da bai idasa fita a hayacinsa ba sqi da suka kama sannan suka iya shigowa da shi, to ina da yanzu da ya gama ficewa a hayacinsa lumfashi kawai yake ja aman jikinsa du ya mace sai bin mutane yake da ido kuri .......Abdul an ji jiki.

gannin docter bai ce komai ba ya daka shi janyo gadon mararsa lafian ya kama Abdul ya dora shi da kyar ya gyara kafafuwansa ya kare masu kallo ya ce" kar wanda ya fito sai nan da minti biyar, Muhammad ka same ni cikin motar

Shi kam Muhammad bai san me zai ce ba, hankalinsa du ya dagu, kar dai a je likitan nan da ya kirawo mai cutarwa wa lafiar Abdul ne? To aman ai likitan mahaifin Abdul din ne, wannan shi ya ci gaba da duba lafiar Ummih wato mahaifiyar Abdul har ta rasu, shi bai san wani likita dabana da zai iya kirawowa Abdul, aman gashi yana tsaye sai wani abu ke faruwa,
Dubansa ya kai wajen Hafsat dake summe, hakan ya saka shi bufar frijj neman ruwa ya watsa mata ko zata dawo hayacinta ta fada masa abinda ke faruwa? Gasbi BS ya fice tun tuni, docter kuwa sai duba agogo yake


BS na fita da gadon nan maimakun ya bi hanyar da zata fitar da shi tsai sai kawai ya juya ya canza hanya ya shige ta kicin ya tafi,
Ya jima yana ta fama dan hanyar sai da ya yi da gaske gadon ya ratsa domin kuwa dan lungu ne ke raba shi da hanyar ya shige ya samu ya fitar da gadon ya isa har bakin titi ta wata hanyar daban ba hanyar da kowa ka iya ganninsa ba sannan ya dakata ya samu ya ciciba Abdul ya riko kafadunsa ya sauke shi a saman gadon ya dora hannunsa na dama saman kafadarsa ya talabe tsatsonsa sannan ya shiga dan tafia da shi a haka har ya kawo bakin titin da ya tsayar da taxi ya shige ya umarce shi da fara biyawa islamic kems kafin yaa sada shi da dan karamin asibiti habo dan uwansa ke yi

Shi dai dan taxi tukinsa ya yi normal, yana gannin yanda BS ke ta faman gyara Abdul, aman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login