Showing 123001 words to 126000 words out of 154870 words

Chapter 42 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1158

a cikin hannun Aunty ,

Da sauri ta juya domin raf Hafsat ta rike hannun taki saki sai da mama ta janye da karfi ta yi ciki tana jiyo irin yanda Hafsat ke kuka , ita kanta sai da ta labe ta yi hawaye kafin ta saku ta shiga sha.aninta tanaiwa yarta fatan alkhairi


Su Aunty kansu sun yi adu.a da fatan alkhairi a irin gidan da Hafsat ta samu, sun yi fatan Allah ya sa mai hakuri da datako ne mijin , hakan zai sa su jima zaman nasu ya yi karko

Tamkar zata suma a lokacin da zasu tafi su barta
Sai dai aure ne, daga shi sai mutuwa su ke rabaka da iyayenka, da danginka , su canza maka muhali, yannayin rayuwa,
Haka suka rabu da yar uwarsu bayan dogon jawabi da rarashi,
Sun yi mamakin gannin ba wanda ya leko su ko ya aiko masu da sakon su ci kansu, sun kuwa lura da gidan akoy mutun domin fitila a kunne take kuma da dan hayaniya

Suna tafiya ta nemi waje ta zauna kasa saman kafet dinta ta saka hannayenta bibiyu ta yi tagumi tana bin dakin da kallo
Jin abin da gannin abin take a wai, wai ita ce matar Abdul? Mutumen da ta hadu da shi dan kawai ta zama bodyguard dinsa sai gata yau ta zo gidansa a matsayin katarsa?
Rabonsa da ya yi mata wata maganar arziki tun da suka fita zuwa gidan dinki,
Gaba dayansa ya canza mata tamkar ba shi ba, ba wata magana bale kulawa, wai yau ake kawota gidan miji ba danginsa ba wani nasa shi kansa baya nan bare har ta ji kanta tamkar amarya ko ta rufe fuskarta anai mata oyoyo ana zolayarta ana jan rufarta,
Gata dai zaune a dakin da mahaifinta ya wani irin kashe kudi ya zuba mata kaya, kayan alatu, kayayaki masu kyau da gayu, an tafi an barta daga ita sai halinta!

Rufar da ta aka lulubo mata ta yaye baki daya,
Mikewa ta yi tana jin kanta har yanzu da zafi irin kitson nan da aka yaryara mata kananu har haka, kitson tamkar da alura aka yi su, sun yi cas sun cika sun yi tsayo sun kuma zanu

Hannayenta ta bi da kallo,
Ita kanta kunshin jan lalen hannunta na birgeta sosai

Cire rufar ta yi baki daya ta nufi wajen kular abincin da aka kawota da shi
Budawa ta yi hankali kwonce ta zauna ta ci abincinta,
Kanta ta baiwa hakuri cewar zamanta da abdul ba wani zama bane dan ba zai iya da halayanta ba itama ba zata iya da wulakancinsa ba, dan haka kar ta wani saka damuwa a ranta ta tsamure ta lalace a wofi, zata koma kusa da iyayenta soon


Sosai Hafsat ta saki jikinta ta saki ranta a tankamemen bangarenta , bata rasa ci, sha , sutura, kayan kwalam da makulashe, bata rasa abin kallo ba, ga Ac da take sha kowani lokaci,
Sangartarta take zubawa da barna kala kala,
Takan hada fruits ta markade ta juye peak da kananfari da dabino ta zauna ta yi ta sha abinta
Karshema da yawa ta yi ta saka a frij ya zama ruwanta, koda yaushe zata didika ta je ta mike abinta

Karshen neman magana Hafsat na farkawa daga baci ta yi ra.ayin buda facebook, tana budawa ta dora hotonta a dp dinta ba tare da dar ba, sannan ta saka sunnanta tsaf Hafsat maman malan, ta koma Whatsupp ta buda
Sai da ta budar ne ta shiga neman numbobin yan uwanta du ta saka ai kuwa ta shiga takura su sun ki lekota sun kawota har sun kare da ita kennan?

Su kam suna bata amsa suna rarashinta su a tunaninsu ta kwontar da hankalinta har mijinta ya bata damar hawa whatsup da facebook


Saukowarsa kennan daga masalaci
Ya nemi waje ya zauna, balarabiyar dake masa girki ta kawo masa tea da dan abinci kadan wanda salak nema kawai aka gyara da kayan lambu da mayonaise ta juya

Cikin nutsuwa ya sha tea din, yana gamawa ya mike ya dauki wayarsa ya shige can kuryar dakinsa ya dauki wayarsa katuwa kirar iphone 11 pro ya zauna bakin kujera baba ya danna kiran number Na.ima

Na.ima dake kwonce saman bed doguwar kujerar falonta ta daga kiran

Tana dagawa ta sauke ajiyar zuciya sannan ta shiga shasheka tamkar wace zata fashe da kuka

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya ce" menene?

Sai da ta sauke ajiyar zuciya jin muryar muradin ranta sannan ta ce" ka dawo gida

Abdul da idannuwansa ke lumshe ya ce" kin daina fushin?

Na.ima ta yi shiru, sai kuma ta saki wani dan marayan kuka irin na shagwababun yara, tana yi tana jan majina sosai hawaye na bin kumatunta

A hankali ya ce" zan kashe fa

Da sauri ta ce" ka yi hakuri, Abdul dan me mani kishiya? Me na gaza Abdul? Abdul haka zaka ci gaba da aure aure ko fada min ba zakana yi ba bale har na yi tunanin zan samu rarashi?

Idannuwansa ya bude sosai , a hankali ya kuma fadin" Na.ima, tun yaushe kike so na? Wani irin so kike min?


Na.ima ta gyara kwonciyarta ta ce " ina son ka da dukan karfin jikina, ina jin kaunarka har bargona

Abdul ya lumshe ido yana mai jin tausayinta har cikin ransa, a hankali ya kuma cewa" dan me zaki yi fushi dan na sako mace cikin gidana dan na kara raya sunnar ma.aiki da ita? Na.ima, a tunanina ko kura na kawo maki zaki kulata ki ciyar da ita

Zaune na.ima ta mike, a hankali ta ce" Abdul, ko zaki ka kawo min, zan bashi nama, aman idan macen da zata rabarmin ni.imatacen kuma tsadadan jikinka ne, ina kishinta, Abdul.kishiya ka min ba yar uwa ba, ban iya boye abu ba bale na yi munafurcin zan so ta, ban taba ganninta ba, bana so na hadu da ita, Abdul bana son ta!

Abdul dake sauraronta da mamaki ya kali wayar, murmushi kawai ya sakar mata a wayar ya datse kiran


Mikewa ya yi ya bale agogo hannunsa ya ajiye, kansa ya daga ya kali agogon dakin, karfe biyar ne na yama, ya yi daidai da karfe goma sha daya a Niger,

Doguwar fara kar din jalabiyar jikinsa ya cire ya kwonta saman bed,

A hankali ya lumshe idannuwansa,
Murmushi ya saki, a fili ya ce" kina ina? Kina me? Ke da wa? Shin kin saki ranki a bakon waje? Har yanzu kin tsane ni? Na san ba zaki taba so na ba, Hafsat kin raina ni sanadiyar sannin na kayar da zina abin yi a da, da wahala ki ga girmana bayan na sha yin izgili kala kala a gabanki, kin dauke ni mai wulakanta mata dan kin ga rayuwar taka tsantsan da na yi da matata kin dauki hakan a matsayin ni mai kudi ne, mai halayar wasu masu kudin

Murmushi ya yi yana dauko wayarsa ya kunna ya shiga whatsupp dan kiran kampaninsa, a fili ya ce" ba dole ba ki raina ni, ke da kike zuwa ki kakabe min kurar dakin mata kafin na raya sunna? Ke da kike gannin ke ke bani tsaro?

Yana shiga ya yi kiran su, aka hasko masa kayan da ya yi oder,

Yana kashewa haka kawai ya shiga bin sunnayen wayar yana ware wa.inda zai goge daga wayar

Sunnan Kauriyata ya kurawa ido,
Hotonta ne daga ita sai hulaa a kanta ba ko dan karamin hijab bale baba a saman dp

Da sauri ya shiga cikin sunnan yana kallon yaushe rabonta da hawa ko tsohon whatsup ne bai taba sannin tana da shi ba??

Ga mamakinsa a lokacin ma tana online

Lokaci daya ya ji gabansa ya yanke ya fadi, a hankali ya fara share zufa yana kallon wayar,

Ya rubuta message ya fi a kirga yana gogewa,
Ina bata isa na mata message ba, bata isa ba!


Shi ne abinda ya fada

Mikewa ya yi ya dauki wayar tafi da gidanka ya yi kira fada

Ana dagawa ya yi maganar yana bukatar su hadu da wuri yana son juyawa gida


A wannan ranar sai da ya fasa wayarsa sannan ya daina kokarin yi mata magana ta whatsup din

Mamaki kawai yake, whatup?

A washe gari yana fitowa daga meeting din da suka yi, ya zauna a wata yar cafetaria

Ya fara shan cafe din kennan ya dauki sabuwar wayar da ya saka layinsa kirar samsung ya yi gagawar shiga facebook

Tunani ya fada, sunnayenta sun fi million a duniyar nan, idanfa ta shiga da wani sunna daban?

Wata zuciyar ta ce da shi" kai yanzu gani kake rashin jin maganarta har zai sakata ta shiga Facebook? Ba zata aikata haka ba mana Abdul

Wata kuma ta ce da shi" kai rubuta maman malan!


Ai kuwa har hannunsa rawa yake ya shiga dora maman malan

Maman da suka hayo ba kadan bane, a hankali ya shiga bi yana jin zuciyarsa na dokawa

Sai da idannuwansa sukai masa arba da Hafsat maman malan, ya duba da kyau yar ina ce da komai ya tabatar masa Kauriya ce ya ajiye wayar hannunsa

Bakinsa ya hade waje daya ya cije lebensa, lale kauriya ta gama raina masa wayo a gidan duniya, yanzu shi shi shi? Shi zata wulakanta? Talar kanta take ko me? Ko wani rikeken dan iskan take so ya ankara da tsarin kayatuwar halitarta na fulawer da Allah ya kagota irin Mamuda take so? Ni ko? Ya fada a fili wanda hakan ya saka daidaikun laravawan dake wajen dan kallonsa

Mikewa ya yi ya saka bakin gilashinsa ya fice a wajen

Yana zuwa gida ya dauki passport dinsa dake ajiye gaban sif din dakinsa na baci ya shiga dubawa, yana gamawa ya danna kira dan tambayar shin zai samu jirgi ne????????

A ranar bai samu tafia ba ba jirgi, sai an saka shi a tafiar gaba

Bayan kwana uku ta kama lahadi da safe


Hafsat na zaune da aunty Mariam da ta zo kawo mata sauran turarukanta wace bata so zama ba aman Hafsat fir ta boye waren takalminta sai zaunawa ta yi du a takure tana kallon Hafsat da mamaki gannin ta sha wando da riga abinta tana shagalinta ga tamfatsetsiyar tvn gidan na hasko indiyawa suna rawa

Jus din da ta mayar ruwanta shi ta kawowa aunty ta bata

Aunty na sha ta kaleta , jus din ya hadu kauri kitib da shi haka kuma ua sha kananfari, a ranta ta ayanna wa ya koyawa maman malan wannan hadi? Ta san anfaninsa ne?

Gidan ta bi da kallo, ba dati ko daya gidan tsaf tsaf tsaf da shi, ga kanshin turare dake tashi

Da kyar auntu ta samu ta gudu bayan ta kara yi mata nasiha

Ita dai murmushi kawai take har ta tafi ta barta

Dawowa ta yi ta sake wani wanka ta saka doguwar riga marar nauyi fara kal wace sosai ta hade da jikinta dan rigar bata da wani girma bakinta gwuiwarta ta kwonta saman kafet tana kallon fim har baci ya yi gaba da ita


Da kansa ya tuko kansa har cikin gidan nasa

Daga cikin motar ya gyara zama yana hangen bangarorin biyu
Masu yi kasu aiki na ta shawagi, mata ne mazan kwaya hudu ne wa.inda ke tsaron kofa kawai, aman daidai da masu baiwa fulawowi ruwa mata ne, kowace kuma a ma.aikatarta ya daukota, gidan du yan gayu ne ma.aikatan, girki kansa mata uku ke yi, idan wannan ta yi break fast, wancen ta yi na rana, wancen ta yi na dare , sai dai du yin nan da ake basu taba shiga bangarenta ba, hasalima bakinsu bautar bangaren Na.ima domin ko shara basu taba shiga sukai mata ba, yo mai gidan baya nan bai bada umarnin hakan ba, matarsa kuwa bata saka su ba.


Sai da ya jima sannan ya bude ya fito a motar, daga katon kwadon dake kofar Na.ima ya gane bata nan, a hankali ya shiga takawa yana gannin sai a lokacin suka gane shi ne a motar dan sai zubar da abubuwan aikin suke suna risinawa sunai masa sannu da zuwa

Amsa su kawai yake da hannu har ya fice ciki ya karasa dakinsa

Wanka ya yi na kirki da ruwan dumi, sannan ya canza kaya zuwa kananun kaya

Saukowa ya yi ya nufi bangarenta yana ayana irin abinda zai mata na hukuncin buda Facebood da whatsupp ba da izininsa ba ya tura kofar ya shiga ta coridor din dake sada ka da dakinsa domin kowani dagi da hanyar da zata kai shi dakin matan ba sai ya fito ta fili an ga ya shiga dakin matansa ba


Hafsat dake dukunkune saman cafet tana baci bata san da an buda kofarta ba bale har ta yi wani abu,

A hankali ya ringa takawa ya shiga, kamshin turaran wutar dakin ne ke ratsa kofofin hancinsa

Tsayuwa ya yi ya kama tsatsonsa ya buda baki ya ce" *Kauriya* da karfi karfinsa

Wata irin zabura ta yi daga kwoncen da take ta mike tsaye cirrr tana kallon inda ta ji amon murya gaba dayanta a zabure hakan ya saka hannun rigarta ya fado kasa bayin Allahn da ba.a saka masu bra ba suka dan bayana sosai daga sama sannan gaba daya gashin kanta ribom din ya fadi kasa haka kuma rigarta a sama daga kasan har pant din ya dan leko daga baya domin mikewar dama rigar ba mai tsayi bace ta dage mata sosai sai kawai ta yi sama ta haye mazaunanta masu tudu da su

Galala ya yi da bakin da hancin yana kallonta, ba ko kifyawa bale kawai da kai

Hafsat kuwa da ta tsorata kallonsa kawai itama take gana tunanin shi din ne ko kuwa aljani ne? Kun san abin baci da zabura tsoratar cikin baci

A hankali ya ringa takawa yana nufar inda take tsaye....

Sai da ya karaso dan kusa da ita kadan, kamshin humurarta ya yi masa salama sanyaya mai nutsuwa,

Hannayensa ya miko ya....

5?? 6??


Hannayensa ya miko a hankali ya janye gashin da ya zubo ya kare masa ganninta da kyau

A hankali ya mayar da gashin saman kanta , fuskarta ta bayana sosai da sosai

Idannuwansa ya sauke a hankali wajen jan lebenta , jajajir da shi yana kallonsa ko ya ce yana harararsa

Idannuwansa ya lumshe kuma lokaci daya ya saka duka kaf hannayen nasa ya janyota

Da yake a firgicen dirowar da ya yi mata ya sameta sai kawai ta tafi gaba dayanta luuuu cikin kirjinsa

Da sauri ya rintse idannuwansa sakamakon jin wani shok da ya yi tun daga kafarsa har cikin idannuwansa

Kara tintse idannuwan nasa ya yi yana jin wani irin kanshi sansanya da take fitarwa

A hankali ya dora hancinsa a dokin wuyanta,
Idannuwansa ya lumshe dan abin ratsa shi kawai yake, jinsa yake har saman kansa

Caji ne ya fara hawa lokaci daya,
Caji mai karfin gaske kuwa

A hankali ya fara jin jikinsa ya fara dan daukan rawa,
Wata tafia tafia ce ya fara ci a cikin sumar kansa tamkar wata kusa ce a kan nasa ta kunce

Idannuwansa ya buda sanadiyar jin tana jan jikinta daga gare shi

A hankali Hafsat ta zare jikinta daga nasa, rungumetan da ya yi ya saka gaban rigar ya kara saukowa sosai, aman kuma bayan sai ya rufe wato pant dinta ya rufe

Idannuwansa ya kai saman gabar rigar nata,
Sun yi luhu luhu da su daga sama, daga yannayin rigar da ta saka yana iya hangen jajayen kawunansu, sun yi wani bulbul da su sun bada kalar pomme

Wani irin yawu ne ya hadiye, wanda ya saka dabinon makogwaronsa yin sama da kasa tare da yin wani makot da su

Baya son kifta ido, baya son wani motsi a irin wannan lokacin

Da sauri ta juya bayanta daga tsayen da take a gabansa

Kafafuwanta ta daga da sauri da niyar barin wajen sai dai meh, jin muryarsa ta yi ya ce" Kauriyata

Muryar a wani irin kurya ta fito, a shake sosai ya yi amanta hakan ya saka Hafsat juyowa ta dube shi

Bakinta ta dan yatsine sai kuma ta juya, ita fama take ta je ta suturta jikinta domin wata irin kunyarsa take ji, Abdul ne ke kallonta a irin wannan shigar? Harma ta fada cikin jikinsa a haka? Kai gaskiya an yi sakara itama!


Yana ji yana gani take kokarin shigewa dakinta hakan ya saka shi daga kafarsa ya matsa kusa da ita sosai ya ce" malama meye haka inai maki magana zaki bani baya?

Gannin ya kusa cin mata ya sakata daga kafarta ta fada dakinta da sauri ta saka kys

Ido Abdul ya zaro daga inda yake tsaye,
Muryarsa ya daga ya ce" ke, meye haka ne? Ya zaki min irin haka ne? Ba zaki tarbeni ba? Ba zaki bani ruwa ki yi farin cikin ganina ba?


Daga inda take tsaye ta tabe baki itama ta ce" Abdul aikenka na yi ne??


Idannuwansa gaba daya tamkar zasu fado ya fifido, meh? Shine abinda ya fada a zuciyarsa a fili kuwa ya ce" kin isa ki aike ni ne? Meye kike yiwa sauri ki rufe? Wannan berayen abubuwan naki da basu nuna ba? Ke Hafsat kin san karamar bab ce ke! Ki fito ki fada min wanda ya baki izinin buda facebood da whatsup a gidan nan!

Bakinta ta kara tabewa ta haye saman bed dinta ta ki yin magana

Hannunsa ya saka ya shiga dukan kofar, tun yana jijigawa har ya tsaya yana huci ya ce" Hafsat magana nake maki fa, ki kiyayi ranar da zan rike ki da niyar hukuntaki fa, ni ba sakaran namiji bane da matata zata shiga yanar gizo fan tsabar wulakanci harda doro hoto? Kowani banza ya kale ki kennan, ciki harda sakaran tsohon saurayinki ko?

Daga daki Hafsat ta mike ta karaso kusan kofar ta tsaya ta ce" Abdul, ka daina zaginsa, dan ba abinda ya yi maka, kuma Facebook ni ba wanda na tambaya ni na saka kaina

Wani irin ihu Abdul ya yi daga kofar da yake ya kaiwa kofar wani mahaukacin duka ya ce" ma zage shin, shege Allah tsine masa mai kallon matan mutane! Ke zaki jaza masa har ubansa na rufe shi ba shi ba sannan ke kuwa na kakarya ki, Hafsat kika kuma saka wani kato a ranki ban yafe ba, Allah ya mana shara.a da ke, kuma ba karya wuyanki kowama ya huta

Shiru Hafsat ta yi a hankali ta zauna kusa da kofar, murmushi ta yi a hankali a ranta ta ayanna ashe irin ko????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
far nan nada rana? Gashi dai ya kasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login