Showing 54001 words to 57000 words out of 154870 words

Chapter 19 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1123

sai macen wata yar dagwas da ita yar kwalisa, duda uban ramar dake jikinta dan kuwa bata da jiki ko kadan gaba daya ta gama horuwa ko.inanta ya sabe ya zube aman kyakyawa ce dan lebenta harda dan jan bakinta kalar ja, haka ya kai dubansa wajen jibrin ya ga sai da aka talabe shi du kuwa yanda yake son ya tsaya da kansa ya kasa dan a ciki aka same shi, sai ko Hafsat dake tsaye kikam, ba wata fara.a, ba alamun komai a tare da ita ba zaka gane hallin da take ciki ba, ita dai a tsaye take,
Bin suturar jikinta ya yi da kallo har takalmi sau cikin da ta saka kafin ya maida dubansa wajen BS,
Kai tsaye ya ce" suna iya juyawa da Namijin, aman a bar matan biyu da wanda aka kawo yanzu............................... ya karashe yana mai kara hade girar sama da ta kasa , ya ci wata irin fuska da ta saka bakin gilashin kansa kara fitar da mazakuntar fuskar yana duban BS tsai a gabansa!
[6/24, 4:04 PM] BAK'A CE: >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 3??


Sai da BS ya dago da dubansa da sauri ya dora saman fuskar Abdul, sai dai kuma da wani saurin ya kara kawar da dubansa ya juya dan cika umarnin da aka bashi,

Yana zuwa, fuskarsa tamkar an wanka masa mari ya basu umarnin su juya da Jibrin, a bar Hafsat,
Da mamaki bakuwar da aka kawo wace zata hau wajen Hafsat ta dan matso ta ce" aman, ai GN ya bada umarnin a koma da ita na hau wajenta ko?

Cikin daurewar fuska ya dubeta da kyau ya ce" yaushe aka koya maki yin gardama da mai baki umarni a wajen aiki?

Da sauri ta girgiza kanta wato ba.a koya mata ba, dan haka ya ce" idan mun dawo zaki yi tsalen kwado hamsin punishment din kokarin yi min gardama,

Hafsat sai da ta zaro ido gannin yanda ya ringa bada umarni, daga wannan yar tambayar wannan hukuncin ya hau kanta? Lale ta yarda yana son ta, to haka mana, ita wani irin iskanci ne bata yi masa, har lda kashedi ta sha yi masa ido cikin ido, sai kawai ya yi murmushi ko ya zuciya ya bar mata waje, kai ita yanzu da yake hakama sai ta ji ya birgeta,

Maimakun a mayar da ita daki ita dake jinya, sai tsintar muryarsa ta yi yana fada masu inda za.a je da irin ysaron da za.a baiwa Abdul da Muhammad baki daya,
Sai da ya gama ya kara dubansu ya ce" ku sani, ku rike, ka saka a kwakwaluwarku, rayuwarsu ta fi taku mahinmanci, aman kuma takuma ana so ta ci gaba da wanzuwa, ku saka duk wani kokari naku, sannin aikin ku, wajen gannin kun kare lafiar uban gidan ku! Ba maganar rashin lafia , rashin shiri, a shirye muke baki daya!

Gaba dayansu suka amsa,
Wata doguwar mota mai gilas bakikirin ce aka karaso da ita,

BS na kokarin gyara yanda za.a yi zaman sai tsintar muryar Abdul ya yi yana fadin Hafsat ta zagaya ta shiga ta dayan barin, shi ya shiga tsakiya Bakuwar mai sunna Hasana ta shiga dayan barin wato dai suka saka shi tsakiya, sai Muhammad ya shiga ya zauna a kujerar dake facing din su, su Abdul suka shiga gaba sai sabon Bodyguard din ya hau wani katon mashin sannan sojojin Muhammad suka shiga wasu motocin suka daga,

Tafe suke da gudun gaske, aman daga cikin motar sai ka yi zaton ba.a wani gudu ana dai dan motsawa kadan, dan kuwa ba.a jin komai dake wakana a waje sai a ciki

Zamansa ya gyara yana kada kafarsa da ya dora saman daya, idannuwansa a kan Muhammad wanda ke kallonsa shima da yannayin tambaya, sai dai ya kasa yin tambayar duba da irin yanda Hasana ta tsare su da kallo tsuru ta hana shi motsi, shi sai ma ya fara tsarguwa ko ji take shi ne makashin?

Hasfat kam zaman da ta yi a takure take, domin wannan zaman da Abdul ya yi du irin fadin wajen da tsayin kujerar sai ya wani gaje wajen, haka take samu ta dan matsa aman daga ta matsa sai ta ji ya matso ya kara matse mata waje, wannan dan matsawar da suke nema ya saka Muhammad tsura masa ido yana dubansa,

Abdul ya tabe bakinsa bai ce komai ba, har suka karaso anguwar da ta cika makil maza ne ko.ina manyan mutane ana ta haya haya ana shirin daura auren Elhaj Moctar wato daya daga cikin aminan Mahaifin Abdul, wanda ya je ya dauko yar tasa daga kasar chaina da karfin balaki ya yi mata miji zai aurar da ita bayan ita a chainar zaman kanta ne take , tana tsaka da rayuwar ya kawota ba abinda ya dame shi da tsarkinta ya shiga hada hadar daura mata aure

Abdul na zaune a cikin motar ya ji an fara sanarwar a matso zama daura aure,
Baban dan ministern man fetur ne zai aureta, dan haka wajen sai kara daukan harama yake ana ta cuwa cuwa, mahaifin amarya sai baza babar riga yake hakama mahaifin ango an hadu za.a hada

Sai da ya hango motar da angon ke ciki, a lokacin har sun zazauna saman lafiyayir tabarmar da aka shinfida dominsu alwalin kowane ya matso za.a fara gabatar da daurin auren Abdul ya samu ya bude motar ya fita inda Muhammad ya bi bayansa gabansa na faduwa, su Hafsat kuwa suka mara masa baya suna ta dube dube inda Su BS ma suka kafa suka tsare idannuwansu a kan du wani mai giftawa, haka na kan mashin sai zagaye yake yana kara dubawa, sannan na sojojin Muhammad du sun kafa sun tsare suna sakar masu hanya har suka karasa wajen motar da ya tabata angon le ciki,

Kwonkwasawa ya yi, aka bude masa ya shiga ya zauna,

Ido ya tsura masa kafin su yiwa juna murmushi,

Abdul ya mika masa hannu yana kallonsa ya ce" ango ango, yau aurwnta aman sai cika fuska kake?

Wanda aka kira da angon ya yi murmushin yake bai ce komai ba,

Abdul ya ce" kar ka yarda a daura maka aure da yarinyar da bata yi tsarki ba Almustapha

Almustapha ya dube shi da sauri ya ce" me kake nufi?

Abdul ya ce" koda an daura ba kyau, kai ka san abinda nake nufi, na tunatar da kai ne, kuma ni ba mace bane sa zan zauna baka komai a tsare, kai dai ka yiwa kanka karatun ta natsu, ka tina Allah zaka sabawa wajen yiwa mahaifinka biyaya ko zaka bi Allah ka sabawa mahaifinka?

Tamkar wanda Abdul ya yi masa allurar dawowa daga duniyar summa ya wani zabura inda ya cire hular dake kansa wani shegen aski irin na yan gala ya bayanna a kansa,

Kana gannin lebensa ka ga rikeken dan giya, hakama muryarsa ta shaida shi, aman dan iya shege ya cire babar rigar da aka saka shi sakawa ya dubi Abdul ya ce" ai aikin Allah na gaba da komai Elhaj, kai dai yi jirana a nan na je can na dawo
Ya karasa fadi yana mai nuna masa kafin ya bude motar ya fice da sauri sauri yana washe baki

Abdul kam bude motar ya yi shima ya fito, tsaye ya yo ya bi shi da kallo shi da Muhammad kafin ya yi dariya yana girgiza kai,
Dubansa ya maida wajen Muhammad dake dan waige waige du a firgice yannayinsa yake ya ce" ka san ana iya shege ko alhaji, ka ga ya yi tilif fa, qman da yake neman kubucewa aurwn yake ya tafi da gudunsa wai zai je ya yi aikin Allah

Muhammad kansa sai da ya saki dariyar da bai shirya ba sannan ya ce" Abdul , kai mugu ne

Abdul ya yi murmushi sannan ya gimtse fuskarsa yana mai jin gabansa ya wani irin faduwa,
Da sauri ya shiga waige waige, da hannu ya yi alamun a tafi da Muhammad

Muhammad na gannin haka shima hankalinsa ya fara tashi dan ya san kawai ba zai ce a kai shi mota ba , dan haka ya damko hannunsa ya ce" mu je tare,

Abdul ya girgiza masa kai, sannan ya dubi Hafsat da ta fi kusa da shi ya daka mata wata tsawar da sai da gabanta ya fadi ta hanyar fadin" me kike jira da ba zaki kai shi motar ba??

Da sauri ta saka hannunta da ya fi aikatuwa ta ja Muhammad dake tirje mata kan a taho da Abdul da kyar ta samu ta ja shi suka dauki hanya dan kai shi cikin mota, sai dai karon da suka ci da wani mutun sanye da manyan kaya, ya yi rawani ya dan dakatar da su, inda Hafsat ta dan dubeshi ba sosai ba, sai dai bibdigar da ta ganni a hannunsa ya sakata kwala ihun kowa ya kwonta
Gaba daya wajen ya kwashi kururuwa, masu afkawa gidajen mutane na afkawa, masu shigewa mota na shigewa, masu ihu su antaya a guje suna antayawa, masu kwonciyar suna kwonciyar, su BS ma sun shigo a guje suna nemman kare lafiar Abdul,

Maimakun mutumen ya fice da gudu, sai tsayawa ya yi ya damki hannun Hafsat wanda take faman daukar bindigarta da shi, gashi mai ciwon ne bata jinsa sosai a jikinta sai ciwon da yake mata, gashi ya damke shi da wani irin karfin da ta ji ta kasa katabus dan haka ta saki Muhammad da ya kai kwonce ya dora hannayensa saman kansa,

Damko hannunta da mutumen ya yi ya sakata kallon cikin idannuwansa,
Bata ga komai ba sai wata muguwar tsana da ishirwar balaki, baki ne kirin, cikin idonsa ya kwonta da jini jini alamun baya cikin yannayi na dadi,
Ido cikin ido suka kalli junna kafin a hankali ya motsa bakinsa dake cikin rawani ya ce" Abd........

Bai kai ga karasa fadin sunnan ba, ko tace kunnayenta basu idasa jin me ya yi niyar fadi ba ya cikata ya shige cikin mutanen dake gudun neman tsira hakan ya sa bat lokaci guda ta juyo da niyar ganninsa aman ta neme shi ta rasa, hakan ya sakata durfafar cikin mutane rana ra juyo du wanda ta gani da shigen irin rigarsa tana son ganninsa,

Daga wajen su Abdul kuwa BS na zuwa da sauri ya rike hannunsa ya shiga jan sa
Bai yi gardama ba har sai da suka karasa wajen motar sannan ya saki hannunsa ya bude masa
Shiga ya yi ya zauna, du a tunaninsa su Muhammad na ciki, sai dai yana juyowa ya ga basa nan

Da sauri ya kama zai bude, sai dai BS ya rufe daga waje da KY ya yi gaba,

Aljihun rigarsa ya shiga laluba, aman wayam babu abin budewar, nan ya tuna dinkin sabon dinki ne da Muhammad ya yi masu,
Hannayensa ya dora saman kansa ya shiga bin yanda su BS suka tatare mutane tuni Ministerma an fita da shi da yaronsa inda yaron har an daura aure ya dankara saki kan ai bata da tsarki=?A?

Du mutanen dake wajen, ko nace yawanci sai da su BS suka zagaye anguwar aka rufe aka shiga bincike, sai dai ina basu ga alamun wani mai alamun shi ne Hafsat ta nuna da ihun a kwonta ba, domin abin kunnensu du ya saka kowa juyowa ya ga mutumen a lokacin da ta fada shi yasa kowa daga wajensa ya shiga ihun a kwonta a kwonta,

Sai da suka kusan awa , Hasana na tsaye kusa da motar da Abdul.ke ciki kikam ta tare gaba ta tare baya,

Daga inda yake zaune ya rasa katabus, jikinsa du ya yi sanyi, sai zuciyarsa dake tafarfasa,

Faduwarnan da gabansa ya yi ya samu irinta ne du idan wani abin ya kusanto rayuwarsa, tabas akoy abinda aka so a yi, ko aka yi a wajen nan, gashi ya rufe shi bale ya fita ya bashi taimako ko zasu gane wani abin

Sai da suka gama sannan suka kama Muhammad aka kai shi cikin motar, wanda yana shiga ya shiga Abdul da fada,
Fada yake tun karfinsa cewar" ka bar wannan abin Abdul Jabar, ka bar shi haka, wasa da ran ya isa haka, kai kulun idan ka fita sai an samu matsala?

Yana cikin fadan su Hafsat suka shigo cikin motar, aka kunna motar inda yanzu har BS a saman mashin suke raka motar cikin tukin garari su yi gaba su yi baya

Muhammad fada yake tun karfinsa har ya saka tissu ya share hawaye ne ko zufa ce? Aman a yannayin da yake dole ya baka tausayi, sam sam baya so a taba lafiar aminin nasa, abin na bashi tsoro, shi so yake ya bi shi su juya gida ya koma bakin aikinsa aman firr ya mayar da wannan mission tasa karfi da yaji har kiranta yake mission din da aka turo shi yi.

Shi dai direba na tukinsa cikin kwarewa har suka iso gidan Abdul Jabar,

A daidai lokacin da aka tsayar da mota, du wani bodyguards da sojan cikin motar ya fice, ya kasance Hafsat da Hasana sun bude gefe da gefen motar sunna jira Muhammad ya gama ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????fadan da tamkar aku ya kasa gajiya kuma Abdul din ya ki ya tanka sa gashi da yaren larabci zallah yake yi wanda bai san ba ruwa ruwa haka hafsat ke jin sa ya saka Abdul dago da kansa,
A lokacin da ya bude idannuwansa sai da gaban Hafsat ya fadi, domin daga cikin idon har wani abu tamkar jini jini gefe da gefe ya kwonta,
Saurin kawar da kanta ta yi tana laluben ina ta ga haka?

Muryar Abdul ce ta daki kunnenta cikin yaren larabci ya ce" *ba nace maka yana raye ba? Abdul bas....*

Kafin ya yi karasa ya saka hannayensa gaba daya ya rike kansa, wani irin yamutsa masa kan nasa ya shiga yi nan da nan sai ga habo ya bale ta hancinsa tamkar wanda jijiyar wajen yanketa ne aka yi ba dan jakudawa ne ta yi ba,

Idannuwansa ne suke tafia a hankali, Muhammad da ya rukunkeme shi ne ya basu damar gane Abdul ya rufe idannuwansa, lumfashin sa ya rabu da gangar jikinsa

Lahaula wala kuwata illa billah,

Wani irin tuma BS ya yi ya janye Hasana dake faman kama shi ya kamo shi ya samu da kyar ya ciro shi daga motar,
Sabon Bodyguard dinsa ne ya zo ya kama shi suka ciciba shi sukai ciki da shi inda du aka rufa masu baya banda Hasana da Hafsat,

Hasana kam ta tsaya rurufe kofar motar ne tana tunanin me ke faruwa da wannan gys din da suke baiwa tsaro ne? Larabcin nasa ya yi gagawa da yawa gaskiya bata fahimci komai ba , aman kamar ransa ne ya baci ko me? Waima *ya mutu ne ko da ransa?*

Sai da ta gama gyara komai na cikin motar ta baiwa direban kys sannan ta ga Hafsat na tsaye cikin ranar nan ta kurawa hanyar da aka bi da Abdul ido,

Mamaki ne ya so kasheta, kai, me yarinyar nan ke nufi ne? Dama ta ga an barta ya hana a tafi da ita, to wai wacece ita? Waye shi da har ya isa ya zabar masu wanda za.a je da shi ko aa? Yanzu haka maimakun ta ga an fita da shi zuwa asibiti sai dai suka shiga da shi ciki doctern familly za.a kira masa ko me? Me ke faruwa ne haka?

Cikin izgili ta nufi Hafsat ta yi tsaye kikam gabanta ta shiga binta da kallo kafin ta tafa hannunta tana gyada kanta ta ce""""







>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?>?#?=?9?=?9?=?9?=?9?=?9?=?9?=?9?=?9?=?9? comment plz plz plz plz comment masu zafi zafi=? ?
[6/26, 4:45 PM] BAK'A CE: >د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 4??



Hasana ta ce" hala, menene tsakanin ki da wannan Elhaj?

Hafsat kuwa tamkar mai koyon gane yaren Hasanat ta tsurawa lebenta ido tana kallon yanda yake motsawa tana fitar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login