Showing 72001 words to 75000 words out of 154870 words

Chapter 25 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1120

wahala dan kuwa wani rami da ya afka sai da mashin din ya yi cili da shi, Allah ya taimake shi kwakwaljewa ne kawai ya yi, haka ya mike ya tayar da mashin din ya kuma daukan hanya

A lokacin da GPS din ke nuna masa cewar ya zo wajen, a lokacin ya kashe babur din ya nemi waje ya ajiye shi da adu.ar Allah ya sa ya tardo shi, dan kuwa jejin nan ba za.a rasa barayi ba

A hankali yake tafe yana sandar wajen bakinsa dauke da adu.a, hannunsa kuwa dauke da yar karamar fitila ta haskawa mai duhun haske,

Wajen shiru, shiru ne gaba daya wajen a haka yake kara shiga cikin jejin yana mai baza kunne yana sauraron du wani motsi


Motsin da ya ji a bayansa ne ya saka shi dukewa cikin ciyayin dake wajen ya tsurawa wajen da ya ji motsin bayan ya dane hasken fitilar

A hankali mitsin ke kara matsowa kusansa, har ya kasance an matso sosai kusan shi

Ido ne ya zaro a lokacin da ya ga mai motsin,
Kai, me?

Mikewa ya yi da sauri ya fito ya karaso wajenta, wada itama motsin da ta ji ya sakata aniyar labewa

Hannunta ya damko ya juyo da ita da karfi , hakan ya sakata zazaro ido tare da jan a.uziya ta kurawa wanda ya damki hannunta ido da taimakon hasken watan da ya raba tsakiya ya haske wajen tar,
mutun mai sanye da wani gajetan wando da riga marar hannun kirki da hular kuku, sai dai kuma fuskar Abdul ne,

Gabanta ne ya fadi a lokacin da ya ce" ke, baki da hankali ne? Me ya kuma fitar da ke a wannan tsohon daren? Bayana kika biyo dama? Ke bakya gudun wannan jejin? Wai wa ya saka ki a sha.anin rayuwata ne da kike daukan irin wannan garajen?

Ajiyar zuciya ta sauke, dan kuwa ta yarda ba aljani nane ya yi kama da shi, shi din dai ne, kennan da ya fito nan ya yo? Au , kennan ya dilmiyar da ita ne? Haba gaske a lokacin da ta so bara masa dakin ya yi gagawar dawo da ita? Ikon Allah zuwa ya yi kennan ya kashe mutumen ko me? Wani haushinsa ne ta ji lokaci guda, shi kennan baya jin bari? Ba zai daina wannan banzan kudurin ba?

Hannunta ta yarfe wanda ya rike mata ta ce" ni ba kai na biyo ba malan, tafiata daban, kuma kar ka kuma rike min hannu, a kan aikina nake

Wani takaicinta ne shima ya ji ya rufe shi, wai aikinta, to ubanwa ya dauketa aiki irin wannan?
Haba sai yanzu ya gane kiran da BS ke masa, wato dan ya fada masa ne ta kara fita ko? Lale yanzu ya yarda da irin taurin kanta, yanzu ya yarda lamarinta sai ita, idan ba kasada ba , mace, ita daya kwal da ranta, ta tashi ta wani dadame da wani shegen wando ta daure gaban goshinta da wani dan siririn gyale ta dunkule gashinta ta shigl jejo yamkar zaTa yi farauta?

Tsaki ya ja a fili ya ce" to sai ki kama hanya ki koma inda kika fito

Hafsat ta dube shi da kyau ta ce" mu juya dai

Ke ni sa.an ki ne wai? Ya ina baki umarni kina kokarin takewa who are u? Umarni na baki ki juya ki koma gida

Hafsat ma ta yi tsaye gabansa, ya kasance suna facing din juna ta ce" idan muka yi fita ta ni da kai, na zama a karkashin, ina matsayin malakar ikonka, a yanzu ka bar uwar malan a daki tana baci!

Takaici ne ya saka shi dafe goshinsa ya nufi Hafsat da niyar nuna mata ya fita iya tsayaya, sai dai wata murya ce ta ce da shi" *kul Abdallah* dukan mace kuma ka koma?

Wani irin tsayawa ya yi, lokaci guda gabansa ya fadi,
Da wani irin sauri ya juyo dan gannin wanda ya yi maganar,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,

Tsaye mutumen yake, ya ja rawanin da ya yiwa kansa ya sauka hakan ya bada damar gannin fuskarsa dake dauke da gemu da saje mai tsayi tamkar tun da ya fara fitar da gemu bai taba askewa ko ya gyara fuska ba
Du irin karancin hasken wajen ba zai taba bace masa ba, du irin yanda ya fito a gabansa ba zai bace masa ba,

Gaba daya jikinsa ne ya kwashi rawa, da sauri ya saka hannunsa jikin wandonsa ya janyo bindigarsa da niyar karasawa wajen mutumen dake tsaye kikam ya ki motsawa ko ya gudu kamar yanda ya yi wamcen karron

Da wani irin gudu ta sha gabansa, ta yi tsaye a gabansa sannan ta nuna masa bindigar dake hannunta gaban goshinsa, cikin karaji ta ce" *walahil azim kafin ka yi harbi zan harbeka Abdul Jabar!*

Sai da ya fan dakata yana kallonta sannan ya yi wani murmushin gefen kunci ya ce" *a kan wannan kudurina kashe ki ba wani abu bane, idan har kin yarda kar ki kauce ki ban hanya!*

Gadan gadan Abdul ya nufo Hafsat dake tsaye tsakaninsa da wannan mutumen dake tsaye shima ya harde hannayensa



Yana zuwa ya danna alburushin bindigarsa ya........





*Ya Allah, shin wa Abdul ya gani haka? Kar kuyi gagawar yanke hukunci fa? Kar ku manta Abdul na tsakiyar makiya kala daban daban,*

*Ya Allah Shin Abdul harbe Hafsat din ya yi?*

Ina muka dosa ne?

*KUTKALE.....KUTKALE...KUTKALE*
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 1??


*GA MAKATSIN SHIRU*




Tabas Abdul ya yi harbi, sai dai a lokacin da zai saki kunamar harbin nasa aka wani irin doke hannunsa hakan ya saka harbin ya bi iska ta gefe,

Bai gama gane abinda ya faru da bindigar hannunsa ba aka yi masa wani bugu a keyarsa wanda ya saka shi faduwa ya sume a wajen


Wani irin ihu ne Hafsat ta saka ta nufe shi ta duke tana girgiza shi hankali tashe,

Muryarta na rawa ta dago ta kali mutumen da ya doke shi, wani mutun ne baki dogo, sannan wadan nan ya dauko bindigar ya mikawa mutumen suka zagaye su

Gabanta ne ta ji ya fadi dan kuwa ta gama sarewa cewar tasu ta kare,

Bindigarta ta wawura ta mike daga girgiza abdul din ta saita bindigar wajen ogan nasu tana kule da na bayanta kar itama ya sumar da ita , cikin karaji ta ce" kai, waye kai?

Datijon nan shima da yannayin tambayar ya ce" ke wacece ke a rayuwar Abdallah da har ya kasa karasowa kai tsaye ya aiwatar da kudirinsa bayan wannan shi ne baban burinsa na duniya??


Hafsat ta saka hannunta ta cire dan kwalin nan ta yar ta ce" waye kai a cikin masu neman ransa? Me ya maku? Me kuke so da shi? Ku barshi haka mana, ku barshi!


Yawun bakinsa ya hadiye sannan ya ce" ba.a koya maki baki amsa idan an maki tambaya a gidanku ba?

Hafsat kam ranta ya gama baci, dan haka ta daga bindigar ta yi harbi a sama ta ce" walahi walahi idan baka ban amsa yanzu ba, to kuwa zan sauke na gaba a kanka, sai dai ku kashe mu ku duka,


Jim ya yi, kafin ya ce" aman ai kin ga jeji ne nan ko? Harbin nan da kika yi kina iya gayato mana ko wani irin mugu ko?


Hafsat kam tunkararsa ta yi ta dangwala bindigarta a gaban goshinsa dan kuwa da kadan ya fita tsayi, bata damu da ta Abdul dake hannunsa ba, cikin kakausar murya ta ce" Qui est tu bordel!
?(who are u?)


Sai da ya saka idannuwansa cikin nata exactly yanda Abdul yake yi idan zai kirta rashin mutunci ya ce" i.m *ABDUL BASID BINE MUHAMMAD*


Ba duka akaiwa Hafsat ba, ba mugun zagi ba, qman sai gata dabas a kasa tana kallon wannan mutumen,

Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une,
Shi ne, mahaifin Abdul ne

Bata gama dimaucewa ba ta ga an karaso da wata mota ana kokarin daukan abdul a saka ciki,

Da gudu ta rike shi tana tambayar inda za.a kai shi?

Amsa ya bata cewa....gidansa za.a mayar da shi, muma zamu tashi daga nan dan kuwa harbin nan ya shaidawa na nesa da na kusa cewar da mutane a wajen, cikin harda sojoji


Tana rike da Badul an saka shi a motar aman ba.a rufe ba cikin sanyin murya ta ce" me ya sa kake son kashe dan cikin ka???

Ido ya zaro da kyau, kamar yanda abdul ke yi idan abu ya bashi mamaki, tabas mamakin yake ciki, wani irin alaka ke tsakaninsa da yarinyar nan mai karfi wace har ya fada mata sirrin ban bayan ya san Abdul da mugun zurfin ciki?

Gannin har ta san haka ya saka shi shima bata amsa daidai da tambayarta cewa" *Ba ni ke son kashe shi ba*

To aman waye? Wa ya kashe kanwarsa? Wa ya kashe mahaifiyarsa? Wa ke bin rayuwarsa? Dan me ake bin rayuwarsa?

Sai da ya waiga, gannin cikin sauri sai harhada komansu suke cikin wasu motocin biyu, ya saka hannunsa a gaban aljihunsa ya ciro wata yar takarda mai dauke da lambar waya ya kama hannunta ya damka mata a hannunta , cikin gagawa ya ce" ki yi ta gwada kiran number nan, du lokacin da na dauka zan baki amsoshin tambayoyin ki, yanzun ba lokaci dan kuwa tuni mai tsare hanyar nan ya shaida cewa miyagu sun fara nufo nan,

Har ya juya zai koma motar ya dawo da sauri ya tsaya kusan Hafsat da ta haye motar tana kallon sa ya ce" *NI ALMAJIRI NE, NA GANE CEWA DUNIYA GIDAN DADI NE GA KAFURI, TUN DAGA LOKACIN DA NA WAYI GARI A CIKIN MUGUWAR KADARA WACE ALLAH YA ANKARAR DA NI KAFIN NA KOMA GA UBANGIJINA NA DAWO NA DUKUFA NAKE AIKIN ALLAH, DU TAKUN YARONA INA SANE, ALLAH YA JIKAN MATATA DA Y'A TA*

Motar ya rufe da sauri ya daki marfin hakan ya saka mai jan motar ya tayar da sauri ya warceta ya durfafa cikin jejin inda aka bar mashin din da hafsat ta sato na yan aikin gidan Abdul din, da kuma na wajensa da ya karba a wajen yaronsa

Sosai ya fafala gudu da su suna ta fafadawa ramuka aman bai rage ba sai da ya fitar da su bakin titi baban ya taka wani irin birki tamkar an dunguri keyarsa,

Kallonta ta sauke daga fuskar Abdul dake wani irin numfashi ta kai kan mai tukansun,
Haba gaske tuki da cin karfi haka ashe wadan nan ne ya ja su ya fitar da su daga jeji, gaba daya tukin a bakin kujerar ya zauna kafin kafarsa ta taba su ambrillage da freins din motar sai yan hannayensa da suke ajiye saman guidon din motar,

Bai ce da ita komai ba ya sauka ya yi gaba sai wani fadin rai yake abinsa

Gaba ta koma ta shiga ta tayar ta harba bakin titi ta shiga tuki cikin kwarewa har ta karasa gidan Abdul

Wannan karron ita kanta ta san ta tabo BS , dan haka da ladabi da biyaya sosai take tsaye gefensa a lokacin da suka shimfide Abdul suka shiga bashi taimakon gagawa har ya dawo hayacinsa ta hanyar sauke ajiyar zuciya ya bude idannuwansa

A fuskokin dake zagaye da shi ya sauke dubansa, daya bayan daya ya bi su da kallo kafin ya kafe idannuwansa a fuskar Hafsat wace da farko ita din ma shi ta kafe da ido tana kallo

Wani irin kallon da bai taba yi mata irinsa ba ya yi mata, kallo mai shige da na tsana, kamar yana jin wani mugun haushinta, hakan ya saka ta sada kanta tana sauke ajiyar zuciya gabanta na faduwa

Cikin kakausar murya ya ce" ku koma bakin aikin ku

Da sauri ta dago kanta tana kallonsa, har suka fice baki daya aka barta tsaye da Muhammad suna kallon sa

Da wata irin tsawa mai firgitarwa ya ce" ke ba zaki koma bakin aikin naki ba ko me kike jira tsaye a kaina?

Da sauri ta juya tana jin gaba daya gaban jikinta na risgarta , wata irin zufa da tsoro ne suka mamayeta,

Tsanata? Garin shiga abinda ba.a sakani ba na jawa kaina tsana daga wajen mutumen da ya bude min sirrinsa??

Idannuwanta ta daga sama ta furta *INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE*


ABDUL kam tana fita ya maida dubansa wajen Muhammad ya ce"
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




3?? 2??




Sai da ya gama yi masa wani kallo sannan ya ce" kai, banma taba sannin irin girman rainin hankalin da ka yi min ba sai yau da na tabatar da abinda na dauki shekaru ina fada maka baka yarda ba!

Muhammad ya nemi waje ya zauna yana dubansa, da irin duban da yake masa a kulun idan ya yi maganar cewa mahaifinsa na raye, ya tabata yau din ma maganar ne dan haka ya yi masa wani zuru yana kallonsa irin kai nake sauraron nan

Abdul ya gyada kansa yana kallonsa,

Girgiza kai ya yi ya Mike ya gyara rigarsa da ta yakune sanadiyar daukansa da aka yi har sau biyu,

Tsaki ya ja a fili mai mugun karfi ya juya ya fita shima a dakin ya bar Muhamad zaune yana mai binsa da kallo

Sai da ya tabatar da ya fita ya dauko wayarsa ya kara shiga dakin ya danna wata number ya shiga waya cikin rage murya sosai yanda idan ba kai ne yake yiwa maganar ba zaka yi ba, hakan ya saka ban fahimci abinda yake fada ba


Abdul, yanda ya ga dare haka ya ga rana, zuciyarsa ciwo take masa, yana mai jin wani irin tsananin haushin Hafsat da ta tare masa gaba ta tsayar da shi wa aikata abinda ya fi buri a rayuwa, bai taba tunanin wata halita zata shiga gabansa , ta tare masa aiwatar da harbe Abdul basid, muten da ya yi sanadiyar mutuwar mahaifiyarsa, da kanwarsa, sannan yake neman rayuwarsa, sai gashi, yarinyar karama da zai yi kanwa ta biyar da ita, yarinyar da bai hada komai da ita ba ta zo ta shiga gaban mutumen da yake nema ruwa a jalo aman ya ji gabansa ya yanke ya fadi, hannunsa ya kwashi rawa?

Saman bed din daya daga cikin sauran dakunnansa ya kwonta ya mike kafafuwansa ya lumshe idannuwansa,

Tamkar an dake shi ya zabura ya zauna, dan kuwa hasko masa ita ne aka yi a lokacin da ta yi tsaye da bindigarta ta yi rantsuwar sai dai ya kasheta kafin ya kashe mutumen nan,
Hannunsa ya saka ya mari gefen fuskarsa ya ce" ABDUL me ya hana ka harbeta kafin ta yi shiru a maganarta? Abdul me ke damunka har haka? Abdul kana ji kana gani ya kubuce maka bayan ka gansa a raye? Ba zaman jeji ba ko zaman cikin rami ko rijiya zaka koma sai na kara samo inda kake , kuma ba wai wannan yarinyar ba, ko wa ya shiga tsakanin bindigata da kwakwaluwarka sai na harbe shi kafin na harbe ka!

Idannuwansa ya kuma lunshewa yana sakar zuci, shi dai a tambaya daya ya tsaya wace ya rasa amsarta gamsashiyar da zata saka shi kawar da kai ya manta komai hakan ya saka shi kwana zaune, yanda ya ga dare haka ya ga rana


Washe gari wajen karfe tara na safe, hayaniyar da ya ringa jiyowa kasa kasa ce ta saka shi mikewa daga saman salayar da ya keana kaiwa Allah subahanahu wata.ala kukansa

Labulen dakin ya dan ja ya leka kansa,

Ikon Allah, shi ne kalmar da ta fara fitowa da bakinsa zubewa lebensa

Ido ya kurawa yan mata biyun da yake hange daga dakinsa,

Wannan matarsa ce Bahija, wace ta gudu ita da Mariam, kwarai wannan bahija ce, dayar da ta bayar da kanta gefe ce bai fahimta ba,
Aa, yaya aka yi bakin fuska suka samu damar shigowa har tsakar gidansa? Yaya aka yi haka?

Tsayuwa ya yi ya harde hannayensa yana kallo da kyau

BS ne ya yi tsaye a gabansu ya ce" dan kina tsohuwar matarsa bai bamu damar dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login