Showing 102001 words to 105000 words out of 154870 words

Chapter 35 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1168

taso sa kansa ya miko mata yana kallonta, da yannayin gimshewa ya miko mata makekiyar wayarsa ba tare da ya yi wani dogon magana ba ya ce" No

Wayar ta kala, sannan ta bi hannayen nasa da kallo masu dauke da gashin jiki sosai kalar fatarsa dan ba bakake bane gashin a haka har ta kai fuskarsa dake dauke da dan karanmin saje dan siriri
Sai da ta wana idannuwanta tana kallon yanda yake wani tsarewa yana wani kamewa abinsa
A hankali ta yarfe shi da idannuwan nata da suka dauki bakin kwali suka kara fitowa radau da su sannan ta buda labanta cikin wani yannayi na shegantakar da ta koya wajen Abdul a wani irin hankali ta ce" *Baka da saje da gemu*

Tana gama fada ta karbi jakar kayan ta juta da canjinta tana sakawa cikin pos dinta

Idannuwansa ya firfitar da matsanancin mamaki sannan ya kali madubin wajen da ya zagaye ko.ina,
Na farko a rayuwarsa an fizga shi, wai bashi da saje, saje kuma a me?
Ina ba zai barta ta tafi haka ba bayan ta zama ta farko da ta ki shi fan saje

Juyawa ya yi wajen yaran nasa ya ga du sun kawar da dubansu a kansa wato suna kallon du abinda ya faru?

Juyawa ya yi ya shiga bin bayanta a hankali jar suka fito bakin inda zata dauki taxi

Shi dai bai gane taxi ne zata dauka ba sai da ya ga ta tsayar da daya yace ba can ya nufa ba mamaki ya kara kashe shi,
Bama ta da motar kanta? Aman ta iya dizga namiji kamarsa? Ko dai dan ya biyota ne? Aa, ko dai tana da aure? Ko kuma mata take so?

Shi daya ya yiwa kansa tambayoyin da sun kai biyar aman ba amsa dan haka yake tsaye yana magana ko zata saurare shi har ta amsa kiran wayar da ajau ta yi mata inda ta fadi sunnan Boutik din fa take sannan ta ci gaba da neman taxi domin lokacin saukar aikin yama ya yi taxi na wahala sosai bare anguwar yan gayu taxi na wahala sosai.......
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 6??






Suna nan tsaye kusan minti ashirin har ta fara kitan layin Malan dan ta fada a zo a dauketa sai ga wata mahaukaciyar hamer baka wulik ta tsaya a gabansu sai maskin sabuntaka take tana dana ashar din rashin mutunci ita kadai sai lillon iskanci take tsabar an murxata an yi gudu da ita, bakaken gilas ne a jikinta gaba da baya hakan ya sa koda wasa ba.a gannin na ciki komai kwakwarka dan sabuwa ce , komanta sabo ne

Daga cikin motar ya kare masu kallo lafin ya sauke gilashin yana jinjina rainin hankalin Hafsat, ta sab sarai ko waye a motar aman ta wani kawar da kanta tana kallon wannan jajir fin uwa gwonda,

Dariya ya yi a lokacin da yake sauke gilashin ya rage sautin cikin motar ya kali na tsayen
Muryarsa ya dan daga dan zuwa lokacin ta ga dama ta kallo infa yake ya ce" tsakaninka da Allah da wannan tsatson tamkar zaka karye da kuma wannnan jar fatar taka uwa yumatir ne zaka zo ka tsaya gaban wannan yarinyar kanai mata bunsuranci kaima ga namiji ko? Yanzu kaima dan iska ne?


Daga Hafsat har mutumen kallonsa suke baki da ido bude,....
Hafsat har sai da ta murje idannuwanta tana kallonsa, dama kiran da ya yi mata dan ya tardota infa take ne?

Kanta ta girgixa ta kara dagawa mai taxi hannu aman ya fice ba tare da ya tsaya ba

Abdul ya sasauta murya ya ce" Kauriyata mu je mana

Dai da ta galawa motar harara sannan ta ce" wai kai haka Malan ya yanka min ragon sunna?

Abdul ya kikifta ido yana kallonta sannan ya girgiza kai ya ce" aa

Ta kebe bakinta gefe sannan ta kawar da kai

Mai jan kunnen nan da wani mamakin kuma ya kalli Hafsat, gannun kamar fitsara ce ta yiwa wannan fitsararan aman ya bata amsa a sanyaye

Ki shigo mu tafi kin ji?
Abduk ya fada cikin muryar rarashi da kwontar da murya

Motar ta karewa kallo, sannan ta shagwabe fuskarta ta ce" ni aa, ka je kawai

Fuskar ya kurawa ido dan ta yi hakan ita kanta bata san ta yi ba aman ba karamin kashe shi abin ya yi ba,

Motar ya shiga citewa a ky sannan ya ce" idan baku shigo ba, na rantse zan fito na dauke ki na saka ki a motar nan bayan na fafala maki mari

Hafsat ra kale shi da kyau ta ce" Malan fa? Ya hana ni shiga motar karti!

Sai da ya zazaro ido sannnan ya yi murmushi ya ce" daga wajen malan din nake Maman malan

A hankali ta faga kafarta ta nufi mitar cikin nutsuwa ta bude ta shiga ta zauna
Mai siyar da shadojin nan na tsaye yana kallon ikon Allah yau ya hadu da tantiran da suka fi shi iya shegantaka har Abdul ya tayar da motar ya harbata bakin titi
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" gaske kike dizga maza!


Abdul na fara tafia ya juyo ya kali Hafsat, bata ankara ba ta ji ya saka yatsarsa ya lakaci man leben da ta goga a bakinta,

Kansa ya girgiza ya ja tsaki ya ce" kema yanzu sai kwaliya da saka kaya masu maki kyau dan ki yi samari ko? Samarinma maimakun ki sami jarumi ingarma aa sai wannan lange langen tamkar igiyar leko? Hafsat kin ji kunya, kin ji kunya kin kara jin kunya!


Hafsat ta lumshe idannuwanta tana jin yannayin wani iri, Abdul ne ya dawo niger da zama? Shine da walwalarsa? To aman yaya ya yi da damuwar Muhammad? Yaya ya yi da Muhammad?

Abdul ya kaleta ya ga shi ke haukansa ita batama san yana yi ba ya girgiza kai daidai sun tsaya a danja ya yi shiru

Hafsat ta karkato ta kale shi a hankali ta ce" me ya sa jiya ka min magana kuma ka min banza a waya? Sannan wama ya baka number wayana ne?

Abdul ya juyo yana kallonta ya ce" number wayarki satowa na yi a wayar malan a lokacin da zai ja salar juma.a ya banu komai ajiya ni kuwa na koma gefe na sata!
A jiya kuma a daidai lokacin da muke magana da ke madame ta farka, tana farkawa ta jefo min kallon kauna, lokaci daya na rikice na fita a hayacina, kin san lafia idan ta yi yawa , ga na koshi, a hankali na kamo matata na kwontar na.....
Niyar Abdul fayace mata abinda ya yin sai horn din mutane ya saka shi waiwayawa ya ja tsaki ya tayar da motar ya kara daukan titi a nitse yana tafia a hankali

Cikin nutsuwa Hafsat ta ce" sai mun biya ta chateau 9 na kai dinkin Aunty

Kansa ya gyada mata ya dauki hanyar chateau noeuf din, aman yana tafe yana neman fitina yana takalarta rigima ita kuwa ta yi malakas tamkar ba ita ba

Sai da suka tsaya wajen dinkin ta sauka ta nufi ciki a ranta tana girmama girman masifar Abdul, wai yaushema ya zama haka ne? Wato duka kaf masifar da yake era mata ne yake sauke mata a yanzu, to wai inama tuwansa ne? Ita kam ta ga ta kanta

A lokacin da ta bayar , Nadiar ta umarci daya daga cikin yarenta fa ya dauki awon yannayin jikin Hafsat,

Dan kwalinta ta warware dan ta ce a yi mata baban wuya sosai

Daukan abin awon ya yi da litafin rubutawa ya zo da nuyar dauka sai ji suka yi Nadia na gaishe shi ta mike da kanta tana tambayar dinki aka kawo ne?

Kallonta ya yi yanda man shafe shafe ya bi ya kokona mata fuska, shagon cike da karti sai dinki suke da wasu irin manyan yan mata irin yan dunuyan nan kowace sai fama take da atach cike a kai ya kada kansa sannan ya kaleta ya ce" ke baki iya aunawar bane zaki saka wannan ya dauki awonta ko ita tace sai namiji?

Kallonta ta kai wajen da ya nuna, da sauri ta ce" yi hakuti oga,
Sannan ta karasa ta karbi abin awon ta shuga auna Hafsat da kanta

Sai da ta gama Hafsat ta tambayi kudin, nan ta yanka mata tsada sosai na dinkin nasu ita da auntynta , dan haka ta buda jakarta ta ciro kudin ciki baki daya ta mika mata ta ce zata kawo sauran idan an gama

Yana tsaye yana kallonta har ta gana ta fice ta shiga motar kamar ta zabga masa mari dan haushinsa take ji sosai,

Daya daga cikin yaran ya yafito ya juya shima ya buda motar ya shiga,

Cofre ya ja ya janyo yan jika goma goma har kwaya takwas ya mika masa ya rufe motar ya kana hanya

Yana kama hanya Hafsat ta kale shi ta ce" Abdul, ya isheka haka ka ji ko? Mme ya shafe ka da dinkina ne? Makan da zaja ringa yi min ihu a ka wai yarka ce ni? Haba haba, kuma walahi idan ba.a yi min wuyan da na zaba ba ba zan saka shadar ba, kuma sai ka mayar da ni ma karbi canjina dan ban iya almubazaranci ba!

Satar kallonta yake yanda take daga murya tana dukan cinyarta wai ita nan tsakaninta da Allah masifa take masa?
Bakinsa ya hade sannan a hankali ya ce" kin zama fitsarara kin gama! Hafsat ba dai ni ba ko? Ni dai ne ko? Na ji

Shiry ta yi tana kikifta ido tana kallon hanya har suka shigo anguwarsu,

Suna shigowa ta sasauta muryarta ta ce" Abdul, dan Allah ka ajiye ni a nesa da gida na karada gidanmu a kafa kar a je wani ya ga an ajiye ni a wannan motar a ci gaba da jifana da munana kalmomi fa munanan furuci ka ji?

Kallonta ya kara yi, yanda ta marairaice, wani tausayinta ne ya ji ya tsirga masa, dan haka ya fage gudun aman bai tsaya ajiyetan ba

Tun tana kallon kamar zai ajiyeta har ta ga ya iso lusan gidansu,

Sai da ya tsaya kofar gidansu ya danna horn

Wangame get din gidansu aka yi dan ana tunanin malan ne zai sako motarsa, sai dai gannin wannan wuleliyar mota ta saka mai budewar kansa yayansu tsayawa yana kallo

A hankali ya ja motar ya shige cikin gida da ita,

Motar ya tsayar yana kallon yanda du ake lekowa ra taga ana kallon abinda ke faruwa

Tsoro ne karara ya bayana a fuskarta, harma wata kwallah ta tarun mata a idannuwanta, kallonta ta kai wajensa a hankali ta ce" ka san a zaginsu wanda ke tayar min hankali har nake tsoron wataran su kaini bango? Bama son suna saka mahaifiyata a shirmen su, idan sun yi kirana da karuwa shin du lalacewar uwa zata aiki danta ya je ya yi karuwanci ne? Abdul me ka yi haka? Yaya zaka sako ni har cikin gidanmu da irin wannan motar? Wa zai ki yarda cewa ni karuwa ce?

Sai fa ya rintse idannuwansa sannan ya bude, bai taba tunanin hannunsa zai kai jikinta ba sai yau, dan kuwa hannunsa ya daga ya tsinka mata marin da ya sakata saurin saka hannayenta bibiyu ta rufe fuskar cike da tsoro tana kallonsa

Sai da ya daki kujerar motar hakan ya sa mitar ta dan motsa dan gaba dayansa ya girgiza
Yatsarsa ya nuno mata da kakausar murya ya ce" ba zan lamunce wani ya kiraye ki da wannan sunnan ba tare da na halaka shi ba kafin ya gama furta kalmar karshe!
Kin ci sa.ar ke ce, kema kuma na farko ne! Walahi Hafsat Muhamadu kika kuma kiran kanki da wannan kalmar sai na cire harshen daje cikin bakin ki na cinye, idan kika kuma sai na lalata maki rayuwa ta hanyar hana ki farin ciki, Hafsat Allah ya isa idan kika kuma kiran kanki da wannan kalmar, na tsani wannan kalmar ga makiyina bale wace na fi a duniya!

Motar ya bude ya saka kafarsa waje daya, har jikinsa rawa yake dinkin kaya blu fin shada ce a jikinsa harda hula ta mugun karbarsa
Har ya juya zai fita ya dawo yana kallonta ya ce" dama motar malan ce da aka kawo, idan kin yi niya ki fito ki shiga ciki, iran baki yi niya ba ki zauna ki dawama a nan!


Da kallo ta bi shi har sau da ya fice yayansu na kallonsa sannan ta lumshe idannuwanta hawayrn suka shiga bin kuncinta,

A hankali ta waiga nan gabanta ya kara bugawa dan gannin du sun firfito sunna tsaitsaye ba wanda babu cikin matan gudan da yayansu ciki kuwa harda bakuwar kanwar aunty amarya

Jikina ne ya dauki rawa gannin mamanta na nufo motar.....
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




4?? 7??





Jikinta ne ya dauki rawa gannin mamanta ta nufo motar,
Kanta ta sada da sauri ta shiga murza yatsutsanta, ta saka a ranta ne tata ta kare, sai da ta yi mata nasiha, sannan tun da ta dawo kulun famanta nuna mata ta karyata abinda ake fadi a gidansu da kuma anguwarsu

Shirun da ta ji ne ya sakata dan dago da kanta,
Tsai ta tsayar da dubanta ga al.ajabin da take hange,
Malan ne da amininsa ladan, da kuma mama a gefe tana amsa gaisuwar Abdul da ya duka har kasa kansa a kas yana gaisheta,
Malan ne da kansa ya yi kiranta ta fito su gaisa da mutumen da Hafsat ta yiwa aiki

Ita kanta tamkar wani sirikinta sai kara gyara zumbulelen hijabin jikinta take tana amsa masa cikin nutsuwa inda kunyarsa ta lulubeta dan ba karya abdul akoy cika ido da siffar kamilin mutun

Sai da suka gama gaisawar Mama ta yi ciki kusa da yan uwanta, nan malan ya fara shiga ya ga kowace da shigar kamala ba wace ta yi shigar da zai ji kunyar nunata dan haka ya kara yiwa Abdallah iso ya shige suka shiga saman malan
Gannin har an fito a sallar magariba sun kasa bata waje ko zata fito ya sakata ziro kafarta a hankali ta fita a motar da lipton din malan sai yar pos dinta

Bata kula kowa ba ta shige bangarenta ta nufi dakinta

Tana shiga ta fada bayi ta zauna ta shiga kuka, ita kanta bata san kukan me take ba, mari dai a gidan duniya ba kalar wanda bata sha ba, ta sha dukan balakima bare wani mari can?

Sai da ta ji muryarta na shakewa sannan ta sasauta ta kunna ruwa ta wanke fuskarta ta dauro alwallah ta fito a dakin

Sallah ta tayar cikin nutsuwa ta gabatar sannan ta mike saman bed ta kashe wayarta gaba daya ta shiga neman hutu

Abdul kam sai da matan malan suka hau da kansu daya bayan daya suka gaisa, ya gabatar da shi a matsayin wanda Hafsat ke gidansu
Ido ido suka ringa yi kowace na ciki na ciki har malan ya salame su suka fito a dakin

Sai da Abdul ya kusan raba dare dan kuwa sun jima da malan suna tataunawa kan lamarin duniya, kafin ya mike ya sauko bayan sun yi salama da malan ya roki da ya yi zamansa ba sai ya raka shi ba

A lokacin da ya sauko ya dan jima yana kallon kofar da ya tabata ita ce ta mama, kuma a ciki dakin Hafsat yake,

Sai da ya ga daren na kara yi sannan ya juya ya fice a gidan ya tarda direban da ya kawo masa wata motar har ya fara baci bawan Allah ya tashe shi suka tafi

Ko da suka karasa gida wanka kawai ya yi, ya gabatar da shafa.i da wuturi, ya gama adu.o.insa, har ya zo shafawa ya lumshe idannuwansa, wata adu.ar ya yi kamar haka" ya Allah, ka kare ni da mugayen mutane, Allah ka bani amini mai tsoronka wanda zan shiga aljanah dalilin zumuntar mu, Allah ka raba ni da mugayen mutane

Bugun zuciyarsa ne ya ji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login