Showing 66001 words to 69000 words out of 154870 words

Chapter 23 - Kutkule Book One Complete Hausa Novel

28 Oct 2025

1130

eh mana Elhaj ta musulunta mana,

Abdul ya gyada kansa, kafin ya maida dubansa wajen Hafsat ya ga kawai mutumen take kallo da sexy eys dinta,
Komawa ya yi ya jingina da jikin kujerar ya ce" wane da wane kika yarda a cikin magangannun nan?

Hafsat da ta yi firgigit ta maida dubanta wajen Abdul, ta kasa cewa komai, dan ita dai ba sannin mutumen ta yi ba, duda yannayinsa na nuni da rashin gaskiya da son dole dole sai ya yi cinvaincre din Abdul din, ba zata iya cewa komai a kan hakan ba,

Abdul ya lumshe idannuwansa ya ce" wato idab mutun baya son gannin abu a zahiri ba zai gansa ba?

Mutumen ne ya ce" Elhaj ban gane inda ka nufa ba

Abdul ya bude idannuwansa aman bai basu damar budewa baki daya ba ya ce" karya kake min Murtala, gaba daya magangannun nan da ka fada ba daya dake gaskiya,
Kai hasalima baka ga wannan matar ba, dan kuwa da ka ganta da ba zaka ce ta musulunta ba dan can dama musulmar ce

Saukin mikewa tsaye ya yi yana zarar ido, hakan ya bashi damar tsayawa kerere gaban Abdul

Ya buda baki zai yi magana sai jinsa ya yi an dangwarar da shi zaune saman kujerar da ya miken,
Mamaki ne ya kama shi gannin yar budurwar an ce ta mayar da shi haka da zafi sannan ta yi tsaye a gabansa wanda yannayin kyakyawar fuskarta da ya nuna hadewa sam ba alamar annuri ya saka shi jin gabansa ya fadi,

Abdul dake zaune a hankali ya bi hannun Hafsat da ta saka ta mayar da Murtala zaune da kallo,
Wandon dake jikinta ne ya kuma bi da kallo , ya dameta sai dai na roba ne hakan ya saka take motsawa son ranta aman du wata halita mai rawa ko mai motsi a wajen tana iya mitsawa in dai Hafsat din ta motsa,
Sannan rigar dake jikinta mai siririn hannaye ce, dan kuwa tun harbin da akai mata ta daina saka mai dogon hannu ko fita zasu yi dan hannun ya warke kar ya danyace
Rigar ta yi mata caras a jikinta, kanta da dan karamin dan kwali baki sidik wanda ta yane kan da shi, fuskarta ba ko digon kwali aman lebenta haka yake jan idon wanda ya kale shi dan tamkar ta goga masa jan baki ne

Lebensa ya hade gaba daya sannan ya tabe bakinsa yana kallonta, irin tsayuwar da ta yi a kan Murtala,

Kansa ya girgiza sannan ya mike tsaye,
Hannunsa ya saka ya mayar da ita gefe hakan ya saka ta zama yar tsuwat a gefensa tana huci dan neman fadan dama take

Abdul sai da ya daura agogon hannunsa da kyau sannan ba zato ba zamani ya saka hannunsa na dama ya dago wuyan Murtala ya ja shi ta wajen kujerar hakan ya saka wandon dake rige da kugunsa janyewa dan kuwa arzunzumi ne harka da yan gayu bai wani daure shi da kyau ba,
Kiiii ya ja shi sai da ya dangana shi da bangon dakin sannan ya saka dayan hannun nasa ya daga shi gaba daya ya raba shi da dandar kasa ya rike masa wuya sosai yana dubanda ido cikin ido ya ce" yaushe na zama bolar da har zaka daga muryarka a kan tawa? Bayan karya da cin amanar har raini zai shiga tsakanina da kai? Ka manta a gidan iskancin da na hadu da kai a irin halin da kuka hadu? Ko dan kana tunanin kai lauya ne sannan ka girme ni zaka raina ni?

Murtala dake harhaba kafafuwansa dan neman a sake shi, du idannuwansa sun ruruko yana ta kokarin yin magana a hakan ko zai sake shi sai rike hannayensa yake aman Abdul ya kasa sakinsa sai kara matsar masa wuya yake

Da sauri Hafsat ta matso ta tsaya ta ce" Abdul, ka sake shi, kar ka kashe shi Abdul=?O?
Idan ya kulata to lale dakin ya amsata,
Gannin yana neman yin kisa ya sakata dan kokari matsawa ta saka hannayenta dan kwaljwace wuyan Murtalan a hannun Abdul

Hannayen nata ya yarfe da hannunsa na hagu, bai saki murtalan ba ya hankadata da hannun nasa hakan ya saka ta yi tagal tagal ta hadu da kujerar wajen ta ja ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya kafin ta tsinci muryarsa a kausashe ya ce" *Ke, bilahilazi kika yarda kika kara taba wannan jemagen sai na karya maki wuya!*

Yana gama fadi ya sake shi nan ya fadi yana kakarin tari , shi kuwa ya duka ya lalubi wayoyinsa ya juya da su ya fice ya nufi dakinsa ya rarumi computernsa ya zauna ya jona wayar ya shiga aiki yana mai jin shi bashi da abinda zai iya yiwa wannan mutumen ya huce sai dai idan zai kwakule masa idannu ne ya soye ya huta!

Hafsat kam sai da ta sha jinnin jikinta a lokacin da ta ga ya nufo kamar ita zai damka , sai kuma ta ga ya fice a dakin,

Ajiyar zuciya ta sauke a fili ta zabgawa hanyar harara a ranta kuwa ta ce" dama na bari ya hayeka a mikewar da ya yi dazun, ni na ga jaraba! Malan ana kare ka kana hana mutun aikinsa!

Juyawa ta yi ta fice a dakin ba tare da ta kuma bi ta kan Murtala dake yashe a nan ba ta fice gaba dayanta ta zagaya wajen sojojin dake gadin bayan gidan ta samu daya ta amshi aron mashin dinsa ta haye ta harba titi

Gudu take tamkar ba zata karasa inda ta nufa ba,
A haka man mashin dinta ya kare ta tsaya ta zuba harma ta yi guzurin wani, sannan ta dauki wayar da ta gama bincike ta kare a sunnan wani gagarumin malamin islamiya dake raye a kauyen garin Minna din, wanda ke rayuwa daga shi sai almajiransa, aman kuma mutumen har ya iya hawa social media, ba komai ya ja hanlalinta yau tsayun kwana biyar a kansa ba sai sunnansa,

Sunnansa *Muhammad bine Abdul Basid Abdallah*

Ta zama wata irin mutun ce mai kurmuwa dukan wani abinda zai bata damar samun gaskiyar abinda ke boye a tatare da Abdul, ba ruwanta da me zata tarar? Waye shi mutumen? Burinta ya kasance shi ne!


A lokacin da ta shiga cikin jejin, a bakin wata rijiya ta ga mutun zaune yana rubutun allo,

Babur din ta tsayar tana son saka jak ta ajiye mashin din mutumen ya dago da kansa daga saman allon karfen da yake rubutu samansa

A tare gabansu ya yanke ya fadi, a wannan lokacin a wannan wajen ya mike ya durfafa cikin jejin wanda kafin hafsat ta sauka a mashin din tuni ya bace mata bat ta nema ta laluba kamar ta yi hauka ba shi ba alamarsa

Wajen allon ta je ta tsugunna ta dauki allon da tawadar,
Yatsarta ta saka ta lashi tadawar, ta daga idannuwanta ta kai wajen rijiyar,
Ba komai ake rubutawa a jikin allon ba sai astagafari,
Mutumen ba wani yaro ba aman irin yanda lokaci daya ya bace mata ya tsoratar da ita

*Wannan mutumen shi ne ya damki hannunta a wajen daurin auren dan minister da yar Elhaj,*

Ta shiga rudu, waye shi? Ko shi ne mai wannan sunna? Me ya sa a page din da yake yawan rubutu baya saka komai sai jawabi da gargadi a kan zina? gashi dare na kokarin yi mata a jejin da ta daina gannin ko wulgawar tsuntsu ne bare na mutun.

Zuciyarta na son gaskata mata hasashenta, runguntsumin tashin hankalin Abdul na ture komai,

Idan haka ta kasance ina zai shiga da ransa?

*Wai wa ke neman ranka Ya Abdel?* hafsat ta mike ta kuga haka wanda gaba daya sai da wajen ya amsa da amon muryarta ......


Allon nan ta dauke ta juya wajen mashin din tana kokarin hawa ta tayar ta hang...........




Comment , comment, comment
>د?=ؔ?>د?=?n? @&? *KUTKALE*=?n? @&?>د?=ؔ?>د?


*(PRISON)*

NA
*SAJIDA*

Marubuciyar

DUK KARYAR KADA

YAR MAHAUKACIYA

DAGA TAFIA DAUKAR SOJA

NEMAN NA KAINA

BANI DA ZABI

IDAN KA RAINA INDA KAKE

BAK'A CE

INA KUKE MASOYAN NOVELS DINA, GANI NA DAWO DA SABON SALO, SABUWAR TAFIA,
NA ZO MAKU DA SABON NVL DINA MAI TAKE *KUTKALE* WATO GIDAN PRISON,
WANNAN NVL ZAI ZO MAKU DA LAMURA DA YAWA, KU BIYO NI KU SHA LABARI........

*WANNAN NOVEL NA SIYARWA NE, DU MAI SO ZAI IYA TURA KUDINSA TA wannan acct NAIRA DARI BIYU : Usman Muhammad 3072998062 First bank. Sai ya turo shaidar ya biya ta wannan number +22791466605....sannan a yi adding dinsa cikin grup, MUTANENA NA NIGER KUWA SANADIYAR RASHIN SAMUN ORANGE MONEY DA KUKE YI, KUNA IYA TURO HOTON KATIN SAHELCOM KO NA AIRTEL TA NUMBER KAMAR HAKA 91466605 SAI A SAKA KU A GRUP DIN, .....* taku ce, Sajida=?
?=?
?=?
?=?
?




2?? 8??





Tana kokarin tayar da mashin din ta hango wani irin mutun,
Mutun ne zabaya namiji kuma wada ,
Kai ba dan ba dan ba sai tace ko ta yi gamo ne? Dan kuwa mutumen tsayawa ya yi yana kallonta kamar ya ga bakuwar halita

Adu.a ta yi sosai ta tofa masa yana kallonta tana kallonsa,
Gannin ya ki motsawa ya kuma kin yi mata magana ya sakata saukowa a hankali ta nufe shi inda gabanta ke luguden kida

Tsayawa ta yi dan nesa da shi ta yi salama,

Ga mamakinta sai ta ga ya matso kusa da ita sosai

Sai da ya daga kansa ya kaleta domin ya matso kusa da ita kafin cikin muryarsa dake nuni da manyantakarsa ya ce" ke kuwa, kin ari musulunci ne ko musulmar ce ke?

Kanta ta sada dan kallonsa da kyau itama kafin ta ce" kama gare su ne musulmai ko salamana ne bai cika ba?

Kansa ya gyada kafin ya juya da niyar tafiyarsa ,
Gane hakan da ta yi ya sakata matsawa da sauri ta ce" dan Allah, ka taimake ni, ina son sannin waye Muhammad bine Abdul Basid Abdallah? Ko zaka iya kai ni inda yake?

Sai da ya kare mata kallo sannan ya ce" ki je dare ya yi, ki dawo zan kai ki wajensa, aman yanzu akoy nisa ga kuma dare

Ta so ta yi magiya ko zai saurareta, sai dai gannin bashi da niyar hakan ya saka ta juyawa ta hau mashin din ta tayar ta dauki hanya wanda a lokacin tuni isha ta kawo kai, a kadan zata iya kaiwa awa uku ko zata isa

Gudu kawai take yi, gashi a lokacin da zata bar gidan Abdul sai da ta ajiye du wani abin aikinta da zai bada damar a san inda ta nufa, ta tabata yanzu an farga da bata nan, fatanta kar ta kai BS bango ya dauki mataki a kanta ya kawar da wani gudun bacin ranta ya saba mata!


Ta jima, ba karamar wahala ta sha a hanyar ba kafin ta karasa anguwar, a haka har ta karasa kofar gidan

Tun daga irin kallon da sojojin ke binta da shi ta dan sha Jinnin jikinta, sai dai bata saka komai a ranta ba ta samu ta shigar da mashin din ta karamar kofar sannan ta sauka ta shiga tura shi ta ci uwar tafia kafin ta karasa farfajiyar gidan

Dare ne, aman ko.ina ya dauka da hasken fitila , hakan ya saka du wani mai motsi ana iya ganninsa da dukan abinda ke tare da shi

Tun da ta shigo gabanta ya yanke ya fadi, dan kuwa du wani bodyguard da ya kwana ya tashi a gidan yana tsaye cirko cirko , BS sai doka waya yake haka kuma sai duba agogo yake, gefe kuwa Abdul ne tsaye hannayensa cikin aljihun wandonsa ya zubawa hanyar da ta fito ido


Turus ta yi da babur din gannin yanda BS ya nufo inda take tsaye gadan gadan ta tsura masa ido sannan ta sadakar cewa idan ya zo yana iya dauketa da mari

BS na karasowa hannunta dake rike da mashin din ya damka yana dubanta ya ce " ina kika je? Ke da wa kuka je? Me kika je yi? Bakya tsoron wata fitina ta same ki?

Idannuwanta ta kikifta tana kallonsa,
A hankali ya sasauta damkar da ya yiwa hannunta ya rage ihun muryarsa ya ce" baki damu da damuwata ba? Ya dace ki damu da aikin ki, dan wanda ya dauke mu ya san takun mu

Yawun bakinta ta hadiye a lokaci guda kuma ta dan leka bayansa,
Ido hudu suka yi da Abdul sannan ya juya ya shige ciki ba tare da ya ce da kowa komai ba

Sai a lokacin ta jinginar da mashin din dake kauri ta ce" BS, ka yi hakuri, na gaji da zaman waje dayan ne, shi yasa na fita na sha iska

Hasana dake tsaye ido ta zaro tare da fadin" me? Ke kina da hankali kuwa? Ke Bodyguard har wani lokacinki gare ki bale muradinki? Ki dubi idannuwan mutane ki ce wai kin tafi shan iska? Ba laifi, tunda kin shawo iska sai ki zo ki zagaye balbalin gidan nan sau hamsin!

A tare suka dubeta, daga BS har Hafsat,

Hafsat kam dukawa ta yi ta kara gyara takalmanta sau ciki sannan ta cira da gudu da daren nan ga tarin gajiya , ga yinwa, ga bukatar yin wanka ta shiga gudun punishment domin kuwa Hasana dai ta isa ta sakata ko ta hanata a bangaren aikinta dan gaba take da ita ya zama wajibi ta yi mata biyaya

Hannun Hasana ya damka ya juya da ita da wani irin karfi ya hankadata gefe inda ba za.a iya hangosu ko a ji maganarsu ba ya ce" ke a wa zaki shiga hurumin da ba.a saka ki ba? Ina ruwanki da amsar da ta bani? Ke idan a halayanki zan bi ki kina tunanin zan bar ki ki numfasa ne?

Bayanta da ya buga da bango ta dafe kafin ta ce" BS , saboda na hora yarinyar dake kokarin rainaka a gabana ne kake wulakanta ni haka? Menene tsakaninka da ita? Wacece ita? Me ya sa na ga du kuna wani rawar kai a gabanta? Idan tana zagayawa da wancen da muke yiwa aiki kaima kwoncin kake da ita ko?

Cikin daga murya ya ce" ki rufe min baki da fadin magangannun da ba tsari a nan,
Kin ga yarinyar can da kika raina? Ni ita nake so, kuma ki daina kokarin zaginta dan ko daya , ba irinki bace, yanda take jana a kas ya saka nake kara mutuwa kanta, ta san ina sonta, har yanzu ta kasa so na, dan haka ki girmamata kar ki yarda ki mayar da ita abokiyar gabanki , dan na rantse maki ta ishe ki tuwo da miya

Sosai magangannun nan sukai mata zafi, tana dafe da bayanta ta ce" aman ka san da ni kake soyaya ko? Kuma ka san aikinka ya haramta maka soyaya da dalibar da ba.a yaye ba ko?

Sai da ya shafa gaban goshinsa da sankon kansa sannan ya ce" to ki tona, ke bari ki ji, abinda zai hana ni samunta daya ne, idan ta ce da ni Bashir ka barni haka, bana son ka!


Yana gama fada ya juya ya fice ya tsaya can gefe yana hangen yanda Hafsat ke gudu tana raba hanya,
Kwarai yana da damar hanawa, ya isa ya hana dan shima yana matsayin gaban Hasana, sai dai ba zai shiga ba ko dan ya kori tsargi sannan ya rike girmansa a wajen yarensa, tausayinta yake ji, kaunarta yake yi, ji yake dama zai karbar mata gudun!


Abdul dake tsaye kusan windows din dakin Muhammad ya rike dan labulen ya tsura mata ido yanda take gudu, Muhammad na yi masa magana shi walahi kwata kwatama bai san me yake cewa ba, a haka ya juyo ya ce" *daga ina take?*

Muhammad dake dana waya yana nuna masa sabuwar motar da kanfanin Helix suka kera wace ke da tsananin tsada ya dago yana dubansa
Sai da ya matso inda yake tsaye ya ce" wa kake tambayar inda ta je?

Sai a lokacin Abdul ya farka, tamkar an dan tsikare shi ya dubi Muhammad da kyau, sai kuma ya shiga takawa ya ce " ina zuwa.......

A wannan dare haka kowa ya yi barci zuciyarsa a cinkushe, tun daga Abdul, Ni.ima, Hafsat, BS , Hasana, da du wani ikon dake gidan wanda sanadiyar rashin gannin Hafsat da tabatar masa cewar ta fita a mashin ya saka tayar masu da hankali da rantsuwar su saurari du irin abinda zai sameta walahi da hannunsa zai masu! Hakan ya saka du suka firgice suna masu jin haushin juna da jin haushin wanda ya ara mata mashin din

Ko da safe ba wanda ya shiga sabgar wani, kowa bakin aikinsa yake tun safe har yama,

Ko da yama ta yi , yauma fitowar ya yi , sai dai yau wani bakin yadi sidik ne ya saka ya fito ya nufi wajen shakatarwarsa

A lokacin da ya zauna ya mike kafarsa ya kali BS dake kai kawo ya ce" ka ce da dayar nan ta fita can baya ku kuwa ku zo kai da wancen ina son gannin ku

A nunin da ya yi, yana nufin a cewa Hasana ta fita, su kuwa ya nuna su zo saman kujerar dake kusa da shi yana son gannin su

Abinda ya bukata BS ya aiwatar, inda suka zauna a kujerar dake gabansa su duka suna kallon yanda ya tsura masu ido ya kalli wannan ya kalli wancen

Sai da Abdul ya gama kallon su sannan ya ce" *wai ku yaushe kuke zance ne? Wace irin soyaya ce kuke haka bakwa bata kulawa? To yau ku yi zance!*

Sai da suka kalli junna sannan suka kale shi a tare tamkar hadin baki,
BS ya dan gyara zamansa yana kallon Abdul,

Abdul ya girgiza kai ya ce" kai yanzu, katoto da kai, kake jin tsoron wannan yar yarinyar? Bashir maza ka rako duniya ko me? Ka fito kace da Hafsat cewa kana son ta aman sai ka ringa hauka har kowa ya gane kana sonta ita ka kasa fada mata kiri kiri?

Sai da BS ya mike tsaye, sai kuma ya koma ya zauna tamkar an dangwarar da shi yana zare ido yana kallon yanda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login