Showing 36001 words to 39000 words out of 261165 words
Chapter 13 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
hanyar aikatawa. Haka rayuwa take, duk inda kika samu mutum da mugun hali zaki samesa da ƙyaƙyƙyawa kuma”.
“Hakane kam Amina” na faɗa ina sake juya maganganunta a cikin raina.
Tunda na dawo gida maganganun Amina ne kawai keta kai kawo a raina, na idar da sallar la'asar ina cikin naɗe abin sallar Aunty Shahudah ta shigo, sosai nayi mamakin ganinta harma fuskata ta kasa ɓoyewa, dan tunda aka bani ɗakinta bata sake shigowaba, hasalima a wancan lokacin catai ƙyanƙyami kayan ciki take tunda na taɓasu.
Sai da ta gama ƙarema ɗakin kallo sannan ta zauna a bakin gado, fuskarta wasai babu alamin turɓune wa kamar yanda takeyi da, sannan babu kallon banza balle hantara.
“Oh, sai kallona kike tamkar kin samu tv Bilkisu”. Murmushin da ban shiryaba nayi, dan inaga yaune karan farko dana fara jin sunana a bakinta, nace, “Aunty Shahudah ai mamakin shigowarki nan nake, nasan dai.....” sai kuma nai shiru ban ƙarisa ba. Batace komaiba sai gefenta data nunamin da hannu alamar na zauna. Nima ban musaba na zauna ɗin inata ƙara mamakinta dai. Cikin katsemin tunani tace,
“Bilkisu aiki nazo kimin, konawa kike buƙata zan biyaki”. Kallonta nai da mamaki, sai kuma na girgiza kaina, “Aunty Shahudah ni yanzu dan zaki sakani abu har sai kin biyani? Bana buƙatar ki dinga kallon haka tsakanina dake, ki sakani kominene kike da buƙ
ata a matsayinki na wacce take sama dani kuma nake ƙanwarki, nikuma nai miki alƙawarin inhar baifi ƙarfin himmata ba zan yimiki shi”. Tai guntun murmushin da ke ƙarama ƙyaƙyƙyawar fuskarta ƙyau tana jinjina kai, Tace, “Bansan haka kike da kirkiba ai, amma duk da haka zan biyaki, domin aikin ya cancanci hakan”.
“Humm” kawai nace mata.
Ta sake muskuta zamanta da cewar, “Waje ɗaya kuke aiki da Broth ko?”. Nasan Yah Qaseem suke cema haka, dan haka nace mata “Eh”. Tace, “Yauwa, a Station ɗinku, akwai wanda nakeson kimin aikin a kansa, sunansa Jawaad, bai zama lallai ki sanshiba, dan shi mutumne da baya shiga kowane tarkace, yanzu ɗinma sai munyi shawara da dogon nazarin da har zaki iya samun kusancin taimakon nawa a wajenshi, dan nasan bazai kulaki ba kai tsaye”. Ta ɗanso bani dariya a maganganunta, amma sai na danne banyiba, dan nima nasan gaskiya dukta faɗa akan halayyar Boss, to amma yanda take faɗan magana a habaice kuma tanason na mata aikine ya saka abin son bani dariya. Tace, “Abinda yasa na zaɓeki a aikin nan saboda, baki da surutu, sannan kin iya hausa sosai, zaki fimu sanin hanyoyin da zaki fahimtar dashi ya fahimta saboda shi mayen son yaren hausane”. Yanzunkam kasa daurewa nai sai da na murmusa, banda shirme irin nata dasu da suka ɗauki yaren wani wata tsiya, ai sai sakarai ke ƙin yarensa.
“Tom aunty Shahudah, yanzu mikikeso nayi ni?”. Jim tayi alamar tunani akan abinda ke'a ranta, sai kuma zuwa can ta sauke numfashi, “Zan ringa baki saƙo kina kai masa kulum, wannan shine kawai aikinki, idan kuma ya tambayi wani abu game dani, sai kisan yanda zaki tsarashi da manya-manyan hausarnan naku. Amma dai Aamilah zata sake miki bayani yanda zaki fahimta, danni harma narasa yanda zaki sake ƙara fahimtata”.
“Karki damu Aunty, ko a yanzunma na fahimceki, matsalar kawai shine yanda zan samu kusancin dashi, da har zan sako masa babbar magana data shafi rayuwarsa ne, dan kinga wannan babbar maganace data kasance sirrinsa da ya shafesa ba zancen aikiba, amma namiki alƙawarin zan gwada ta wasu hanyoyi, saiki dage da addu'a kuma”.
“Okey, zuwa anjima zamu fita ni da Aamilah, zamu sayo abinda zakije masa dashi ranar Monday”. Na jinjina mata kaina kawai, dan bansan miyasa take bani tausayiba yanzu, na kula tana sonshi sosai, to ai Boss ya cancanci a soshi, sannan ita kanta ina mamakin yanda ya iya sakaci da wannan ƙyaƙyƙyawar halittar, ba namiji irinsaba hatta dani mace aunty Shahudah na birgeni, tana cikin mata ƙyawawa ajin farko da ba cikin baƙaƙeba kosu kansu fararen ta shiga cikinsu saisun yabata, sun dace sosai matsayin ma'aurata ita da Boss, ‘sai dai nikam ta yaya zan tunkaresa da maganar nan?’.
JAWAAD
Tun sanda yasha maganin sai ya dinga samun nutsuwa a hankali harya farajin ɗan ƙarfi bayan tafiyarsu bilkisu, sai kuma yaƙi da zuciya, sosai maganin na masa aiki, amma yasan wataran zai daina tamkar yanda na bayama sukai yayi suka shuɗe, ko abokinsa Doctor Sooraj ɗin da ya bashi shawarar amfani da wannan maganin ya tabbatar masa na wani ɗan lokacine kawai, babbar mafita shine yay aure, inba hakaba ƙwayoyin da yakesha domin kare kansa daga faɗawa halakar da yake gudu to lallai zasu iya masa illa ma wataran, tunda har ALLAH ya bashi lafiya da muhalli, dukiyar aure mi yakema zaman jira? Idan matarsa yakeso ya dawo da ita mana yabar cutar kansa. A lokacin da Dr Sooraj kema Jay wannan maganar ƙin ce masa uffan yay, daga ƙarshema sai yay masa sallama ya baro office ɗin.
Da daddare bayan tafiyar su Ummah gida ya samu kira daga Uncle Nasir, duk da bayajin ƙwarin jikinsa haka ya tashi ya fita bayan ya saka dogon wando a jikinsa, dan harma ya riga yay shirin barci shi. Kansa tsaye falon Uncle Nasir ya nufa, bayan yay sallama aka bashi izinin shiga sannan ya shiga, Uncle Nasir na zaune shida matarsa suna hira da kallon labarai, ya gaishesu da girmamawa. Duk fuskokinsu ɗauke da fara'a suka amsa masa, Uncle Nasir yace ya taso susha Fruit salad ɗin da yake sha, Jawaad ya amsa da, “Alhmdllh Uncle na ƙoshi”.
“Aiko saika shashi” cewar Hajiya Sumayya matar Uncle Nasir, ta cigaba da faɗin,
“kai yanzu Jawaad kenan ka girmi cin abincin kowa a gidan nan?, tunda kai aure shikenan, da ai ba haka kakeyiba, mu yanzu ka yayemu daga iyayenka kenan?, inaga ko shayin wajenan rabon daka shashi tun daren ɗaurin aurenka da Shahudah, to ni dai yanzu kamar yanda na saba a baya kullum zan zubo abinci na aiko dashi sashenka, idan kaso kaita jerenshi kamar ɗakin amarya”.
Murmushi yayi tare da kai hannu ya shafi kansa, yace, “Nayi laifi Ammi, amma ayi haƙuri, kinsan yanayin aikinmune yasa, wani lokacin bana shigowa da wuri, kuma ina fita da wuri, amma daga yanzun indai na dawo da wuri zanyi magana a kawo mani”. “To yanzu naji magana, bara na zuba maka fruit salad ɗin”.
Uncle Nasir dake saurarensu yace, “
Ke nama lura sake ɗaure masa ƙugun zama babu aure kikeyi, yanzu ba zancen adinga kai masa abinci nai zamanyi ba, zancen wadda zata dinga dafa masa kamar kowane magidanci zanyi”. Tace, “Ah Alhaji indai nan ne aini ina bayanka, ga ƙannensa nan su Abdur-rahman za'ai musu haihuwa ta bibbiyu, shiko ya zauna ruwan ido kamar wanda bai ɗanɗana auren yajiba”.
“Barsa, ai na shirya maganinsa wannan karon, idan har bai shiryaba ni a shirye nake na zaɓi ɗaya daga yaran gidanan na aura masa”. Da sauri Jay ya kalli kawun nasa harda waro idanu. “Kalleni da ƙyau fa, ALLAH inhar baka yunƙuro a cikin shekararnan ba, a yaran gidanan zan aura maka, karkuma ka ɗauka maganar wasa nake maka, gobema insha ALLAH zanje na sami Alhaji babah muyi magana (Kakansa mahaifin Mamansa), idan kuma matarka kakeso ka dawo da ita”. Shiru Jawaad yayi baice komaiba har Uncle Nasir ya gama masa faɗa sannan ya bashi haƙuri akan insha ALLAH zaiyi abinda sukeso, amma su ƙara masa lokaci.
Uncle Nasir yace, “Ba damuwa, ALLAH ya kawo mafita, amma ranar lahadi idan ALLAH ya kaimu akwai meeting da za'ai ƙarfe huɗu, sai kai ƙoƙari ka halarta, karka bari ayi kuka da kai kamar ko yaushe dan ALLAH”.
“Insha ALLAHU Uncle zan kiyaye”.
Ya daɗe a sashen suna hira dan sai kusan ƙarfe ɗaya ya koma sashensa, kasancewar yasha barcin rana sai bai iya yin na darenba da wuri, lap-top ya buɗe ya shiga wasu ayyukan, sai wajen biyu da rabi ya rufe ya tashi, alwala yayo yay nafilfili tare da jero doguwar addu'a akan mahaifinsa da mahaifiyarsa, dama sauran al'umma baki ɗaya.
Sakamakon rashin kwanciya da wuri ya sashi makara sallar asuba, ya tashi a gaggauce ya nufi toilet ya ɗauro alwala, bayan ya gabatar da salla yay wanka ya gyara gadonsa sanan yay shirin fita, Gimba ya tafi gida weekend, dan haka shi da kansa yaja motarsa sai ƙaton gidan gonarsa da ya gada wajen mahaifinsa dake can asalin ƙauyen kakansa Alhaji Yusif, inda sukai rayuwa da kakarsa mama maryam, garin kuma da mahaifinsa yay rayuwar ƙuruciya harma data girma. Sosai an samu cigaba da abubuwa masu dama a cikin ƙauyen wanda duk sanadin mahaifinsane, an musu titi, an kuma kai musu wuta, ga dam ɗinsu da har yanzu suke noman rani, dan garin yana ɗaya daga cikin manyan garuruwan da ake amfanuwa da nomansu da kiwo a jihar tasu dama maƙwaftanta baki ɗaya. Alkairin mahaifinsa da shi kansa wanda yakeyi yasa a kullum yake mai daraja a wajensu, idan yaje ji suke tamkar su haɗiyeshi, saika rantse wani sarakine.
Kamar yanda ya saba gidan mai gari ya sauka, dan haka ya keyi a duk lokacin da yaje ƙauyen, hakan na ƙara masa daraja da kwarjini, kamar yanda shima yakejin daɗin abinda suke masa ɗin, dan maigari yana masa abu tamkar uba, kasancewarsa abokine ga mahaifinsa Abdul-aziz tunna ƙuruciya. Ya samu tarba kuwa ta mutuntawa, inda akaita haba-haba dashi da abincin gargajiya masu tsafta kamar yaune aka fara ganinsa matsayin baƙo. Sam Jawaad bashi da girman kan zaɓar cima ko raina cimar ƙauye, hasalima suna masa saɗi fiye dana zamani, idan har yaje ƙauyen nan komi suka bashi cin abinsa yake, saboda yanada yaƙini akan tsaftar iyalan baba maigari, tun yana ƙanƙanin yaro mahaifinsa ke zuwa dashi, hakama mama maryam na kawosa kafin ta rasu, hankalinsa kwance yaci ya ƙoshi, dan dama da yunwarsa yazo, bayan sun gaisa da baba maigari da jama'ar dake fada suka nufi gidan gona shi da Abbati ɗan b
aba maigarin da zasuyi sa'anni da Jawaad, dan abokinsane na amana, dukkan sirrin gidan gonarsa yana hannun Abbati, shike kula da komai, Abbati dukda yayi karatu har matakin degree na biyu yana zaune ne anan ƙauyen tare da iyayensa, iyakarsa yaje birni wajen aiki ya dawo garinsu ya kwanta, matarsa ɗaya da ƴaƴa huɗu, yayi ɗan gininsa na zamani saboda ƙauyen yanzu yanada dukkan cigaban da ake hangensa a birnin, kuma mafi yawansu sunada aƙidar son zaman gida sai dai waɗanda aiki ya tilastama komawa birnin akan dole, dan a dalilin Abdul-aziz mahaifin Jawaad ƙauyen yanada manyan ƴan boko matasa masu jini a jika dake taka rawar gani sosai a sassan ƙasar.
Suna tafe suna hirarsu cikin nishaɗi, inda Abbati keta kiran sauran abokansu dake gida ta waya yana sanar musu Jawaad yazo. Jawaad ya fige wayar yana hararar Abbati, “Malam ya isheka haka, sai gayyatomin ƴan iskannan kake salon kuzo ku addabeni da surutu mara ma'ana”. Abbati ya kwashe da dariya, “Oh ashe kana tsoron surutun namu? Ai indai kaga munbar maka surutu kuwa sai kayi abinda mukeso, ka dubemu daga mai yara uku sai masu huɗu amma kai ka zauna ruwan ido Jay, ai kosu Jabeer da kuke tare a birni sunada iyalansu, wai kodai da kurwanka Shahudah ta tafine bani labari kafin su Isa su zo”.
Kafin Jay yay magana sukaji ance, “Ai gamu mun iso”. Daƙƙuwa Jay ya watsama abokan nasa huɗu da suka iso wajen yanzu-yanzu, waɗanda suma duk sunyi karatu kowa da abin yinsa, kuma suna bada gudunmawa a gidan gonarsa suma. “Duk kunci ƙaniyarku zomayen banza, uwarwa ya gayyatoku nan?”.
Dariya suka sanya baki ɗaya, Labaran ya dunƙule hannu ya bigi damtsen hannun Jawaad yana faɗin, “Bar wani mazurai gaye, munfika ƙarfi fa inma hayaƙin kakeji, dan mu kullum matanmu ƙara mana sukeyi” duka shima Jawaad ya kai masa, Labaran yay saurin duƙewa. “Ɗan iska da ka tsaya naima fuskarka damage sai naga ƙarfin da Asiyan ke baka, mara mutunci”. Dariya suka sanya su dukansu, Aminu yace, “Mudai mun gaji da ganinka haka ALLAH kuwa”. “Gaskiyane Aminu, ya kamata ka duba Jay” cewar isa. “Hakane kam lokaci baya jira fa, kullum girma muke ƙarawa ƙuruciyarmu na guduwa” cewar Salisu dake dafe da kafaɗar Jawaad. Murmushi kawai Jawaad yayi, yasan halin abokan nasa, tunkan yay auren farkoma haka sukaita addabarsa, sai da akai bikinsa da shahudane suka sama masa lafiya, yanzunma ko waya yake dasu faɗansu kenan, shi kansa ba auren bane bayaso, gidan jiya yake tsoron komawa........ Adam ya katse masa tunani da cewar, “Idan kuma a birnin babu wadda tai maka ka duba a garin nan mana, auren nan shine cikar martabar mutum”. Abbati yace, “Maganarku nakan hanya ƴan uwa, ko ɓato maka rai akai daga waje kana shigowa gida kaga iyalanka sai kaji ka huce, musamman idan kayi dace da macen datasan yanda zata tattali dukkanin farin cikinka, koda gajiyarka ka kwaso kanada inda za'a nuna tausayinka a sauke maka ita da kulawa”. Jawaad ya shafa kansa yana sauke numfashi da girgiza kai, “Kudai baku da magana saita aure dai jarababbu, ko hutawa bakwayi, karku damu zanyi, kumin addu'a kudai. a tare suka shiga masa addu'ar kuwa kafin su fara bashi hannu suna gaisuwa.
Jawaad nason abokansa na ƙauyensu, dan suna bashi nishaɗi da faɗa masa gaskiya komai ɗacinta, shiyyasa ko kansa ɗaukar zafi yay a wajen aiki tuni yake ƙoƙarin ware weekend ɗin da zai shigo, dan yasan zai samu nutsuwa sosai..............✍
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.[11/30/2020, 12:57 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 14
Guys ɗinan anya kunaso na mutu da idanuna?, kusan words dubu uku nakeyifa a kullum amma sai naji kuna farautar ƙari🤔, aradu inason ƙulla shekara ɗari da idanuna kuyi haƙuri😂🤣😂. Ga zaɓin lokacin posting, 11pm ko kuma 6am. Waɗanda naga sunfi rinjaye sai abi ra'ayinsu. Amma masu cewa dama Jay yana dariya?? nima kun bani dariya wlhy sosai, waye baya ya dariya a duniya, sai dai idan bata kamaba😂. Harda ƙyaƙyƙewa zakuji yayima wataran🚴🏼🚴🏼👌🏼.
Ina muku fatan alkairi😍😘😍😘😘😘.
................Zagayen gidan gonar suka farayi suna hira mai daɗi da mutunta juna, sashen dabbobin da ake kiwo da sashen da ake noma, sashen kaji, kifi, su talo-talo, zabi, agwagi, kajin gida, zomaye, harda tantabaru, sai sashen itatuwan fruits, komai yana tafiya yanda yake buƙata, sun nufi inda Jawaad ya gyara shima suke fidda yankakkun kaji dasu zabbi da sauran duk nau'in ƙananun dabbobin da ake kiwo a wajen ana packaging nasu a ledoji a shiryasu a wasu robobi manya masu haske domin masu sari dake kaiwa birni, hakama ƙwan kaji da zabi dana talo-talo, sai inda ake tace tsaftatacciyar madarar shanu kuma ana sakawa a galoli shima, kowacce galon da adadin litar da take ci, da inda ake shirya dukkanin nau'in kayan itatuwa suma. Abin dai dolene ya burge mai kallo da ƙayatarwa sosai. Sai da suka shiga lungu da saƙo, ya kuma gamsuwa da yanda komai ke tafiya, yana ta ma ma'aikatan jinjina da sake basu ƙwarin gwiwa, inda yaga kuskure kuwa cikin hikima yake musu gyara ba yanda zasu fahimci gazawarsu ba, yanda yake tafiyar da al'amarinsu na ƙara masa girma a idonsu sosai da daraja. Bayan sun kammala zagayawa suka yada zango ƙarƙashin bukkar bunu da tasha gyara domin hutawa, gefenta kuma anyi ɗan gini mai 2 bedroom kawai, domin idan yazo da shirin kwana nan yake kwana ko gidan baba maigari, hirarsu suka cigaba dayi cikin nishaɗi, lokaci-lokaci Jay yakan amsa waya, wadda ta shafi aiki kuwa yakan tashi ya koma gefe idan ya gama ya dawo. Da rana sai ga abinci lafiyayye daga gidan baba maigari an aiko musu, harda fura mai ƙyau da tasha damu. Yini guda anan suka yisa, Jawaad yaji matsalolin jama'ar garinsa waɗanda zai iya kawo gyara da iya ƙarfin aljihunsa yace zaiyi, dan dama ya daɗe bai zoba kusan wata uku. wanda sukafi ƙarfinsa kuma zasu haɗa hannu domin neman taimakon wanda zai iya musu, Jawaad ya gaji mahaifinsa a abubuwa da dama, komai nashi na al'ummane, dukiyar da mahaifinsa ya bari bata rufe masa ido ya zama asharari ba, sai ya ɗora kyawawan aiyukansa akan wanda mahaifinsa ya fara, tare da nasa da ya ƙirƙira shima, yanda yake rayuwarsa a sauƙaƙe bazaka taɓa tunanin an tara masa irin wannan dukiyarba, dan ko iya gidan gonarnan ai al'amarine babba, balle kuma akwai wanima bayan wannan, bayan sauran abubuwa da shima nasa ƙoƙarin.
Bayan sunbar gidan gona gidan baba mai-gari suka koma, sun samu zama dashi da manyan gari suka tattauna akan maganar da sukai a gidan gona na abokansa, sai bayan sallar magriba Jawaad ya baro ƙauyen cike da tsaraba daga jama'a, duk da sunsan yanadashi hakan baisa suji ƙyashin ƙyautata masa da ni'imar da suma ALLAH yay musu ba. A hanya ya tsaya yay sallar isha'i kafin ya ƙarisa gidan Umma ƙarama. Tayi murnar ganinsa ita da yaranta, ya sauke mata tsarabarta anan da ɗibar mata wadda mutane suka bashi yay mata sallama ya tafi dan bai jimaba sosai, daga nan sai gidan Ummah babba, gidansu Nabeelah kenan, nanma sunyi murnar ganinsa, inda suka fara faɗansu shi da Batool kamar yanda suka saba, itama dai tsarabar ya ajiye musu ya tafi, a gida ya yada zango, kasancewar kowa ya shige sashensa shima nashi ya shige akan da safe zai fiddama kowa nasa kason, sauran ya kaima kakansa nasa shima, sai nasu Hafiz.
WASHE GARI LAHADI.
Washe gari lahadi, na tashi da burin abubuwa da dama, dan da daddare na samu Dad da yah Qassem ya kirashi, na faɗa masa zanje na gaida Inna zainabu yace naje sai driver ya kaini, na sanar masa zanhau napep saboda zan fara zuwa wajen aiki da aka sakani kafin naje canɗin idan na fito wajen saloon. Ina kammala gyaran ɗaki nai wanka, na fita nai breakfast sama-sama na koma ɗaki nai shiri. Doguwa
r rigace na saka ta Material baƙa da ratsin fari, ta zaunamin ɗas a jiki, gashi ta