Showing 174001 words to 177000 words out of 261165 words
Chapter 59 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
lallai sarauta ba ƙarya bace. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi, ya amsa min da kulawa tare da sakamin albarka.
Sai da suka fara shiga shi da boss da ya riƙema hannu da dogaransa biyu kacal sannan muma muka shiga. Da yake waje na musamman aka bamu sai naji kamar mu kaɗaine a jirgin, acan ƙasan raina cike nake da ɗoki da fatan dacewa akan abinda zamuje dominsa.
____________________________________
Gaba ɗaya hankalin Momy a tashe yake da duk wanda yake cikin gidan Dad a yau, ba komaine sanadin wannan tashin hankalinba kuwa sai zuwan ɗan fir'auna gidan da far1ar safiya ya tafi da Shahudah. Kusan ƙarfe takwas yazo gidan, lokacinma babu wanda ya tashi sai ma'aikatan gidan kawai, daga Shahudah harsu Momyn ma babu wanda nake tunanin yayi sallar asubahi, sabuwar mai aikinsu na tsaka da sharar falonsu ya shigo. Da ɓacin rai ta kallesa zatai magana, sai dai yanayinsa ya sakata haɗiye abinta a cikin rai ta koma zare idanu. Ya zabga mata harara cike da gadararsa yace, “K rakani ɗakin matata”. Cikin ƙarfin hali tace, “Matarka kuma? Anan gidan?”. yay mata kallon tara saura kwata ya ɗauke kansa, “Baki da labari kenan?”. Kafin ta bashi amsa sai ga Aamilah da muryar ɗan fir'auna ta sakata tashi a firgice, dan sam shi baya magana a hankali.
Idanu ta zaro zata koma da gudu ya daka mata tsawa, “K dan tsohonki dawo nan!!”. Bata da ikon jayayya, dan haka ta dawo ta tsaya tana rurrufe ƙirji da hannu kasancewar rigar barcin jikinta bata kirki baceba. Yi yay kamar bai fahimci abinda takeba, yace, “Ina matata?”. “T.. Tan tana barci a ciki”. tai maganar tana nuna masa saman benen. “Kaini”. Yay maganar yana yin gaba. Binsa ta farayi a baya tana hararsa, tai wata zabura daya juyo, baibi takanta ba yace, “Wuce gaba”. Kamar zata fasa ihu haka taji, amma dole ta haɗiye abinta a rai tai masa rakkiya har ƙofar ɗakin Shahudah.
Tana kwance ɗai-ɗai tana barcinta ac na kaɗata suka shiga. “Tasheta” ya faɗa yana kallon Aamilah. Jikinta na rawa ta shiga tashin Shahudah, daƙyar ta tashi, tana ganin Aamilah ta hau hararta, sai dai ganin ɗan fir'auna tsaye ya sakata watsakkewa.
“Sannu da tashi ƴar hutu. Ke shirya mata kayanta”. Idanu Aamilah ta zaro, ya daka mata wata mahaukaciyar tsawa da ta sakata fashewa da kuka tana bashi haƙuri, a take ta buɗe Wadrobe ɗin Shahudah ta fara zuba kayanta a cikin a kwati, shikuma yahau tattare kayan kwalliyar saman mirror. Ita dai Shahudah tayi mutuwar zaune, dan binsu kawai take da kallo ko sau ɗaya ta kasa magana.
Momy da mai aikinsu taje ta kirawo tana fitowa falo ɗan-fir'auna na fitowa daga ɗakin Shahudah riƙe da hannunta tana tirjewa da kuka tana kiran Dady da Momy, Aamilah na biye dasu da akwati. “Kai wai wane irin mahaikacine ne? Gidan ubanwa zaka kaimin yarinya? Sakarta dan ubanka!!”. Ko kallon Momy baiyiba yaja Shahudah ƙeeyyy!! sukai waje, Aamilah na biye dasu tana hawaye. Binsu momy tayi takai hannu zata riƙe Shahudah ya zaro bindiga a ƙugunsa, “Wlhy kina taɓata saina tsiyayar miki da jinin hannu, inbanda rashin mutunci da raini, an ɗauramin aure amma kun maidani ɗan iska kamar wani gwauro, ke lokacin da aka ɗaura aurenki da surukina ba ranar aka kaiki kika tareba ya kwashi gararsa, saini dan an maidani wani sha ka tafi sai safa da marwa nake tsakanin titi da gida, to daga yau ta ƙare, kwa biyota da sauran kayanta, ga oga can an basa matarsa shi yanata watayawa ƙilama mun samu ɗa, amma ni ambarni hagaga da baki kamar tsohon amalen raƙumi. Motsoow, aikin banza kawai. Ke muje ƴar farata yau nima ango nake mai lokaci”.
Sunaji suna gani ɗan-fir'auna ya tura Shahudah a motar da yazo da ita bus, ya shige abinsa ya tada yabar anguwar. Kuka momy da Aamilah keyi kamar ransu zai fita, Salman yana daga jikin Window ɗakinsa duk abinda akeyi yana gani amma yaƙi fitowa, saida ɗan fir'auna ya wuce da Shahudah sannan ya fito yana murza ido da tambayar abinda ya faru shi a dole barci yake baiji komaiba.
Kuku ne ya masa bayani dan sun ɗauka da gasken barcin yake bai jiba.
Daƙyar momy ta iya samun Number Dad ta faɗa masa komai, hankalinsa yay masifar tashi, yay kiran commissioner of police dan yayi report amma bai ɗauka ba, ya kira I.G shima wayarsa switch up, duk ya rikice ya rasa wazai kira, daga ƙarshe ya yanke shawarar kiran Jay, amma shima wayar tasa dai switch up. Tashin hankali kenan wanda ba'a saka masa rana, karan farko da yaji nadamar barin Qaseem barin ƙasarsa. Haka yayta bige-bige waya bai dace ba, wasu aƙi ɗauka, wasu suƙi shiga. kansa gaba ɗaya ya kulle ya kasa fahimtar wannan ruɗaɗɗen al'amari, yama za'ai ace shi kamarsa yana kiran wayoyin waɗanan mutanen amma babu mai wucewa, wasu kuma sunƙi su ɗaga masa ma. ‘Mi hakan ke nufi?’.
Muma wannan amsar muke buƙatar ji Dad😥.
__________________________________
Mun sauka Saudia lafiya, inda akazo da zuƙa-zuƙan motoci akai mana tarba ta girmamawa, Aunty Mahfuzah da mijinta da ƴaƴansu biyu. Nazata wannan karonma gidansu Aunty Mahfuzah zamuje, sai naga an kaimu wani wajen daban.
Ba boss ba koni a ƙage nake da son ganin Umm-Anum wlhy, sai dai shi jarumin naku ya dake kamar babu komai a ransa. Ni kaina ta yadda yake komai a sanyaye na fahimci komai ya kwance masa, hatta da wanka da ƙyar na samu yayi sannan mukaci abinci, kasancewarsa maicin abinci sosai sai gashi ya tsakura kaɗan ya tashi, nata marairaice masa da lallashi akan ya ƙara amma ya girgiza min kai, daga ƙarshe ma sai ya tashi ya shige bedroom ɗin ya barni a falon.
Raina gaba ɗaya sai ya sake jagulewa, na ajiye abincin nima na tashi na bisa ciki, kwance na iskesa saman gado a rigingine yana kallon p.o.p ɗin da aka ƙawata saman ɗakin dashi, ga fitulu masu ƙyau da ɗaukar hankaki, na daɗe tsaye a bakin ƙofa amma baiko motsaba balle nasan yasan na shigo, kaina na girgiza inaji a raina dolene nayi wani abu koyaya na dawo da kuzarinsa koda ba dukaba, dukda nasan ba sauƙi zan samoba haka na cije na ƙarisa gaban gadon, kwanciya nayi a gefensa na ɗaura kaina saman ƙirjinsa ina kallonsa, abin mamaki baiko motsaba fa, yatsana manuniya na ɗaura saman lips ɗinsa na fara zagayawa a hankali. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya da buɗe lumsassun idanunsa a kaina, gira na ɗage masa, na ɗan juya ƙwayoyin idona alamar “Yaya dai?”.
Murmushi ya ɗanyi da gyara kwanciya ya juyo sosai muna fuskantar juna, hannunsa ya ɗaura saman gefen fuskata muna kallon juna cikin ido, sai dai yaƙi cewa komai, sai busamin numfashinsa kawai yake saman fuska kamar yanda nima nawa ke sauka akan nasa.
“In baka wani labari”. Guntun murmushi ya ɗanyi, ya buɗe baki daƙyar yace, “A kanki kawai”. Murmushi nayi har haƙwarana na fitowa, na ɗaura hannuna nima akan fuskarsa ina ɗan murza gashin sajensa daya fito kaɗan da ƴan yatsun. “Bara na baka labarin farkon girkina”. Kansa ya ɗagamin yana lumshe ido. Na gyara kwanciyata sosai ina sake shigewa jikinsa, “Innata zataje anguwa sai ta barmin girki tace nayi kafin ta dawo, amma komai zan zuba na tabatar Innar Firdausi na a wajen, dan bata taɓa barina nayi girki ba, sai dai idan tanayi ta dinga sani na zuba abu harmu gama. Ni sarkin rawan kai inason na bama Inna mamaki tasan na iya girkin nima, sai kawai nahau hidima batare danama innar firdausi magana ba, da yake ita kuma tana ɗaki sai batasan hidimar da nake ba. Shinkafa da wake aka barmin nayi, kasan mina fara zubawa bayan na saka kayan miya, mai?”. Kansa ya girgizamin alamar a'a. Nai ƴar dariya, “Karfa kace zakamin dariya to”. “Ɗan kaɗan zanyi” ya faɗa a hankali. “Tab to na fasa gaskiya”. Da sauri yace, “Yi haƙuri wasa nake bazanyiba”. “Tam, in gaya maka na tsaida ruwan abinci bayan nayi komai dai-dai ɓangaren soya mai, kayan miya, da tsaida ruwa, na kawo magi da gishiri duk na zuba, saida ya tafasa saina zuba shinkafa...” cikin ɗan zaro ido yace, “Waken fa?”. Ƙaramar dariya nayi, “Yo waken sai da shinkafar tai rabin dahuwa sannan na wankesa na zuba na saka albasa na rufe inata murmushi ni na kammala komai, har wani imagine yanda Inna da Babana zasu kwashi girki nake a raina.
Kasa daurewa Jawaad yayi ya shiga ƙyalƙyala dariya sosai, dukda naji daɗin ganin yana dariya saina saka hannuna kan bakinsa zan rufe ina kumbura fuska ni a dole naji haushi. Hannuna ya riƙe zai janye naƙi, nai azamar hayewa kansa na danne da ƙyau yanda bazai cireba, “Kafayi alƙawarin bazakayi dariya ba?”. Dagewa yay ya cijemin hannun, nai saurin janyewa ina fashe masa da kukan taɓara duk da dai da gaske naji zafin. “Ni ALLAH saina rama” na faɗa ina kai bakina kan hannunsa daya riƙe ɗayan hannuna. Take muka fara kokawa, shi yana dariya ni kuma ina saina rama da kukan da babu hawaye. Ba'akai dogon zangoba lissafin ya canja salo, duk kuma yanda naso ƙwatar kaina a hannunsa sai hakan ta gagara, yayi yanda yakeso daga ƙarshe ya koma lallashina kamar yanda ya saba.
“Wai har yanzu fushin ne?”. Ya faɗa yana jawoni jikinsa. Sake tura baki nayi, nace, “Kuma indai mukaje gidan Umm-Anum bazan dawo nanba”. “Sai mu kwana tare a can ai”. Yay maganar yana ɗauremin gashi na daya gama gyarawa. Ɗagowa nai na kallesa, nace, “Dawa ɗin?”. Ya nuna kansa da ɗan yatsa. “Tab kayi ƙato da yawa bazaka kwanar mata a gida ba”. Ranƙwashi ya bani a kai mai zafi. Na dafe wajen idanuna na cika da ƙwalla. Ɗauke kansa yay tamkar baiganiba.
★★★★★★
Duk yanda muka kai da zumuɗin ganin Umm-Anum a ranar dai bata yuwu ba, sai washe gari wajen goma na safe. Ni da Ummu da amintacciyar baiwarta muka farayin gaba akan su boss sai daga baya zasu biyomu shi da Takawa da mijin aunty Mahfuzah. Duk da bansan yaya manufar tsarin nasu yakeba hakan yamun.
Tarbar da akai mana kawai zai tabbatar maka da ansan da zuwanmu, sai dai bawai da tunanin har dani ba, dan bayan Umm-Anum sun rungume juna da Ummu irin gaisuwar larabawa tana ɗagowa ta ganni, baki ta saki da mamaki, “Amaryan kwana takwas ne a saudia kuma?”. Kaina a ƙasa nidai ina murmushi ban iya bata amsaba, sai Ummu ce ta bata amsa ƙasa-ƙasa, bansan mitace mataba naga dai sunyi dariya.
Yanda Anum ta rikice da ihun murna zai tabbatar maka itama batayi tunanin dani a zuwan ba, ta rasa inda zata saka ranta dan daɗi, tabi dukta katantaneni da labarai, ganin banga Anuwar ba nace mata, “Ina Yah Anuwar?”. Ɗakinsa ta nuna da hannu. “Tunda muka dawo ai baida lafiya, dafa jiya zai kona ƙasarku wai yayi mantuwa, shinefa Umm-Anum tace masa ai Ummu ma zatazo ya faɗa abinda ya manta ɗin tazo masa da shi. Ni nasan bawani mantuwa da yayi, so yake yaje ya ƙara ganin mijinki kawai Umm-Anum ta ɓata masa shiri, shinefa yaketa fushi da kowa a gidan tun jiya, yau ko makaranta yaƙi yaje”. Tausayinsane ya kamani, sai dai bancema Anum komaiba game da zuwan boss.
Munyi kusan zaman awa biyu sannan Anuwar ya fito, wani irin taka burki yayi yana waro idanu waje. muryarsa har rawa take wajen faɗin, “Wai dama dake akazo?” ya ƙare maganar yana murza idanunsa da hannu. Murmushi nai masa hakama Ummu, cikin tsokana tace, “Dama kana gidan amma ko tarba babu Anuwar?”. Kafin yace wani abu Umm-Anum tace, “Fushi yake dan ya shirya ƙaryan komawa ƙasanku na ganosa na hana”. Kallonsa mukai da ga ni har Ummu, ya wani ɓata fuska da narketa a shagwaɓe. Dariya nayi kaɗan ina ɗauke kaina. Ummu tace, “Kaga manta dasu Anuwar kaji, lokacin da zamu rama yana zuwa ai”. “Yauwa Ummuna” ya faɗa yana zama kusa da ita ya gaisheta. Nima gaishesa nayi. Cikin hikima yaketa tambayata ina mijina? Da tsokana nikuma nake bashi amsar yana can mun baro. Da nace haka sai ya ɓata fuska ya ɗauke kai. Har raina sai nakejin tausayinsa, dan bamusan mi ALLAH ya ɓoyeba a al'amarin nasu da har suke masifar ƙulafucin juna irin haka.
Bayan sallar zuhur Abbun su Anum ɗin ya dawo gidan, sai da ya zauna suka gaisa da Ummu sannan yake sanar da Umm-Anum gasu takawa nan a falon baƙi a shirya musu abinci akai. Da yake dama tasan da zuwan nasu saita hau shirya komai yanda ya dace, sai dai kallo guda zakai mata ka fahimci kamar a rikice take. Daga ƙarshe ma saita zauna tana mai dafe kanta. Aunty Mahfuzah ce tai azamar ƙarisawa gareta ta dafa ta, “Umm-Anum lafiya kuwa?. Kanta ta nuna mata da hannu alamar yana mata ciwo, Ummu da Aunty Mahfuzah suka kalli juna dansu su Ummu sun sanar dasu komai dama. Addu'a Aunty Mahfuzah tai mata sannan taɗanji ya sassauta mata, amma data miƙe sai tace jiri take gani.
Anuwar ya fita salla bai dawoba, Anum da Bilkisu kuma suna ɗaki suma tunda suka idar da sallar basu fitoba, dan haka basu san wainar da ake toyawaba su.
A falon baƙi Takawa ne zaune da mijin Aunty Mahfuzah abokinsa, sai Jawaad dake zaune a wani irin yanayi mai wahalar fassara, idanunsa sun kaɗa sunyi jazur, ya jingina da kujera saboda jin yanda ƙirjinsa ke wani irin mahaukacin bugu, ga jinin jikinsa sai tsitstsinkewa yake. Takawa ya kafesa da idanu na wasu ƴan mintuna cike da nazari kafin ya sauke gajeren numfashi yana maida dubansa ga Abu-Siddiq, shima ɗin dai kallon Jay yakeyi tun ɗazun cike da nazari, dan tun haɗuwarsu da Abunsu Anuwar gaba ɗaya yanayin Jawaad ɗin ya sake canjawa, shi kansa Abbun su Anuwar ɗin rikicewa yay jikinsa ya hau rawa saboda ganin tsananin kamar Jawaad da Anuwar ɗin, farine kawai Anuwar ya ɗara Jawaad. Duk da daman Takawa yay masa bayanin komai tunma kan suzo ƙasar hakan bai hanashi shiga gigita da ruɗani ba, sai dai baice komaiba bayan gaisuwar daya zauna sukayi, shine ya fita ya sanarma Umm-Anum ɗin da zuwansu shi kuma ya sake dawowa.
Sam ya kasa haƙurin daina kallon Jawaad dake kwance cikin kujera idanunsa rufe, ba barci yakeba amma sam tunaninsa da hankalinsa basa tare da duniyar mutane, da za'a tambayesa wanene shi a wannan lokacin, bazai iya bada amsar komaiba. A wannan yanayin Aunty Mahfuzah da ma'aikatan gidan suka shigo suka shirya abinci gasu takawa.
Duk yanda sukaso Jawaad yaci abinci sam ya kasa, daga ƙarshema yace musu kansa ke masa ciwo, kuma yana ganin jiri, wannan magana ta sake rikita Abbun su Anuwar, dan a irin halin daya baro Umm-Anum kenan itama a cikin gida. Shine yayma Jawaad addu'a, kafin ya sakashi dole cin abincin, gurasa ɗaya yaci da ƙyar ya tsame hannunsa. basu sake tilasta masaba dan sun fahimci bayama cikin hayyacinsa kamar.............✍
Ku lallaɓa da wannan, yau na tashi banajin garin dai-dai nima😩
Gaskiya a rage sakama Jay ido da yawafa ƴan Wattpad😂, dan kunfi kowa iya gulmar Jay na kula, su ƴan Telegram ƴan blue House ne, Yah Qaseem ɗinmu sukafi sama ido da Aunty Hudah🙄😣.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/14, 5:27 PM] HASNA✍🏻: Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 49
..............Kamar yanda Umm-Anum ta saba duk sanda takawa yazo Saudia ya kanzo har gidan su gaisa, domin dai a halin da take ciki su kaɗai takema kallon ƴan uwa, su kaɗai ta sani a yanzu sai mijinta sai ƴaƴan guda biyu, ta mance ita wacece? Ƴar wacece? Daga ina take? Daga ina ta fito?. Wani lokaci hikimar UBANGIJI kan sakata kawo wannan tunanin a zuciyarta, musamman ida tunaninta ya karaɗe ko ina a cikin duniya ta ga babu wanda ta sani sai ƴan Masarautar gagara badau, sai mijinta da danginsa dake anan, hakan kan ɗaure mata kai, sai dai duk yanda taso ta furta da baki kota tambaya bata iyawa. Idan hakan ta kasance takan zauna tasha kukanta ta share hawayenta.
Yauma kamar yanda ta saba ɗin haka ta ƙimtsa ta fito cikin shirin zuwa gaida takawa, idan da Ummu yazo sukanje tare, idan kuma da amaryarsa ne tare itama suke zuwa, sai idan shi kaɗaine yazo sai taje tare da Anum su gaida shi ko Aunty Mahfuzah idan ta shigo. Yau kam sai suka ɗunguma gaba ɗaya, ita, Anum, Ummu, Bilkisu, sai Anuwar daya shigo gidan babu jimawa shima, dan tunda ya fita salla sai yanzu yake dawowa saboda baisan da Takawa sukazo ba balle yay tunanin harda Jawaad.
Sallama sukai a ƙofar ɗakin aka amsa musu da ga ciki, tare da basu izinin shiga, jikin Umm-Anum sai tsuma yake tanata dai ƙoƙarin dannewa da karanto addu'a a zuciyarta. Anum da Bilkisu ne suka fara shiga, sai Ummu sai Umm-Anum, sai Anuwar a ƙarshe. Jay na kwance a kujera idanunsa a lumshe tamkar mai barci, sai dai shigowarsu