Showing 156001 words to 159000 words out of 261165 words
Chapter 53 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
su kwana dan ALLAH”. “A'a babu batun kwana ɗiyata, ai ba'a kwana gidan amarya, zasuzo dai zuwa dare su dawo, ki tabbatar mijinki da Anuwar sun haɗu dan munyi waya dashi ɗazun yace baya gida”. “Insha ALLAHU Ummu zanyi ƙoƙari”. “To shikenan, sai anjima na kiraki kinji, kidage da shiga ruwan zafi karkiyi son jiki”. Kunyace ta kamani, a raina ina tunanin kodai shine ya sanar mata..... “Kina jina” magarta ta maidoni hankalina. “Eh Ummu”. “Bawai ina nufin ki shiga ruwan zafi idan babu abinda ya faru ba, tunda nasan kina fashin salla, bakuma saina buɗe miki abinda nake nufiba, ayita haƙuri danshi zaman aure haƙurine, allah yay miki albarka”. Hawayena na share nace, “Amin Ummu nagode”.
Rashin ganinsa a ɗakin ya sakani jin daɗi bayan na ajiye wayar, cikin dauriya na gyara ɗakin tsaf, na fito ɗaukar kayan shara naga Nabeelah, sosai naji daɗin ganin nata, itace tace nabar sharar ita zatayi, ban musa mataba na shiga nai wanka da sake gasa jikina sosai, hakan ba karamin nutsuwa ya ƙaraminba. Koda na fito saina koma ɗakina nai shiri, ina cikin shirin Nabeel
ah ta kawomin abinci, dan tunda taga yanayina ta tambayeni lafiya nace mata banida lafiya duk sai naga jikinta yayi sanyi. Yunwa nakeji sosai shiyyasa na zauna naci abincin. ɗakinsa na sake komawa ɗaukar maganin dan naji daɗinsa, ina buɗe box ɗinne Nabeelah ta shigo da sallama da waya a hannu, a kunne kawai ta sakamin batare da tayi maganaba. Ɗagowa nai zan tambayeta wanene? Muryarsa ta shiga dodon kunnena.
Saida na lumshe idanu na buɗe sannan na amsa masa sallamar tasa,
“Amarsu kin tashi?”. Ya faɗa cikin zolaya.
Jinai tamkar na nutse dan kunya, dukda bana gabansa, nai saurin saka hannuna na rufe fuskata ina murmushi da faɗin, “Nidai ALLAH a'a”. Ina jiyo sautin murmushinsa shima, yace, “Nidai nasan amaryata amaryace ƴar gaske, yaya jikin naki?”. Batare dana buɗe fuskarba nace, “Da sauƙi”. “Alhmdllh ai haka akeso, kinci abinci ko?”.
“Uhm naci”.
“Tom kisha magani ki sake kwanciya ki huta karki biyema surutun Nabeelah, Gimbiya ta kirani akan baƙi zasuzo kuyi sallama, zanyi ƙoƙari na dawo da wuri nima insha ALLAH. ga Sadiq nan zai kawo cefane Nabeelah tayi girki”.
“ALLAH ya dawo dakai lafiya to”.
“To nagode, amma mizan ɗan samune Noor-Jahan?”. A marairaice nace, “Mi kake so?”. yace, “Komai aka bani inaso mana”. Duk da ina tsananin jin kunya nace, “To rufe idonka”. “Na rufe ruf Matar Jay”. Yay maganar cikin sanyin murya kamar ba shiba. da saurin na yanke kiran ina dariya, ina gani ya sake kira naƙi ɗagawa, saima maganin na ɗauka na fita falo wajen Nabeelah.
Babu jimawa da zamanmu Sadiq ya kawo cefanan da yace, karon farko da zan fara girki a gidana dukda Nabeelah tace na barmata zatayi kar yazo ya gani yay faɗa, ban sauraretaba dan nima inason ƙarfafa jikina ai. Tare mukai girkin cikin nutsuwa da salon da Umm-Anum ta sake koyar dani, dan danan gidan ya kaure da ƙamshi, muka kammala tsaf muka gyara kitchen ɗin sannan.
Kusan ƙarfe uku na rana saiga su Anum, Anuwar, Abdul-Rahman, Abdur-raheem, Ameen, Meenal, Amaturrahman, Amatullah. Tuni muka rungume juna dasu Amaturrahman kamar mun shekara da rabuwa, su dai su Abdur-raheem dariya suketa mana.............✍
Inacan ina muku dogon page, kunanan kuna ƙwalama sunana kira😣😫, ku baku ganeba ne, duk randa nai posting da wuri to nayi typing ɗin dare ne ya kwana, idan kuma ban samu damar yiba dole sai randa zan tura nakeyi, ga aikin gida ga uzurorin rayuwa🤦🏻😓, gashi yanzu anzo gangara typing ɗin na buƙatar nutsuwata sosai, amma idan naga wani Comments ɗin har mamakin mai rubutashi nakeyi wlhy. ALLAH dai ya dafa mana kawai, duk ƙoƙarinka baka isa yima kowa yanda ya dace ba, ALLAH kaɗai ka iyama ɗan adam da halinsa wlhy😂🚶🏻🚴🏼.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/6, 9:21 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 44
Auntyn Alfindiki saƙonki ya iso gareni, alkairin ALLAH ya kai gareki a duk duniyar da kike, kema ALLAH ya tabbatar da addu'arnan da kikaimin a gareki, yanda kika soni domin ALLAH, kema ina roƙon ALLAH ya soki haka dear.
Godiya irin trillions dinan 😍😍😍😘😘😘😘
....................Duk yanda zan musalta muku kalar daɗin da naji na zuwansu bazaku fahimtaba, irina da suke gararanbar rayuwane kawai zasu fahimci kalar jin daɗin da mukanji idan mutane irin haka da baka haɗa komai da suba suna nuna maka soyayyar da naka dangin basa nuna maka irinta, abinda ya ƙarama farin cikin nawa armashi kuwa ganin harda matasan samarin ƴaƴan sarki masu zamani da lokacinsu a cikin gidana, kuma sun sake dani tamkar jininsu kona rayu a cikinsu ne. Abdul-raheem ne dai baida yawan fara'a da magana, amma shima bashi da wulaƙanci. Abincin kuma da aka jera musu zama sukai sukaci sosai har ana santi, Abdur-Rahaman harda cewa dama yunwarsa ya tara dan yazo yaci girkin amarya. Amaturrahman ta ɗauki filo ta saka masa waiji wai santi yakeyi. Nan take faɗa ya kaure tsakaninsu, ni wlhy dariyama suka bani, idan kana tare da triple ɗin Ummu dolene drama ɗinsu take baka dariya, shi Abdul-raheem baya magana, amma idan ya mulmulo baƙar magana ɗaya sai tayi kamar ta kar mutum dan takaici, shikuma Abdur-raham babu haƙuri saiya rama, Amaturrahman kuma zuga. Gefe kuma Ameenullah da Meenal ma cashewa akeyi, hakama Anum da Anuwar. Wannan caskalen nasu ne ya sake ƙara armashin hirar tamu da nishaɗi sosai. Kiran sallar la'asar ya saka samarin fita salla, mukuma mukayi a gida.
★★★★★★
Ana idar da sallar la'asar Jawaad ya baro station, kai tsaye anguwar su Hudah ya nufa, sadiq yay fakin dai-dai ƙofar gidansu Amina inda Jay ya bashi umarnin tsayawa. Jay daketa rubuce-rubuce batare da ya ɗagoba yace, “Sadiq yimin sallama a gidan nan”. “To Oga” Sadiq ya faɗa yana buɗe motar ya fita. Ƙofar gidan su Amina ya ƙwanƙwasa tare da yin sallama. Kusan mintuna uku Aminar ta fito sanye da hijjab tana amsa masa. “Assalamu alikum. Malam lafiya kuwa?”. Amsa mata sallamar Sadiq yayi, sannan ya nuna motar, “Dama oga ne yace aimasa sallama”. Cikin rashin fahimta Amina tace, “Oga kuma? Wanene kuma oga?”. Batajira amsar Sadiq ba ta fito zuwa motar, knocking glass ɗin tayi har sau uku, Jawaad da har yanzun hankalinsa na akan rubuce-rubucensa ya saka hannu ya sauke glass ɗin batare da ya ɗagoba. Amina taɗan zaro ido da ɗora hannunta saman baki, “Oh wlhy bansan kai bane Yaya Jawaad, ina yini?”. Ɗagowa yay ya kalleta da amsa mata, duk da fuskar dai babu walwala bai ɗaureta tamauba, “Mama na nan?”. Kanta ta jinjina masa, “Eh tana nan ka shigo”. “Okey” ya faɗa yana maida kansa ga abinda yakeyi. Juyawa tayi ciki ita kuma domin sanarma maman.
Sai da Jay yaja kusan mintuna huɗu sannan Sadiq ya buɗe masa motar ya fito. yana fitowa Amina na leƙowa dan sunji shiru, itace tai masa iso har cikin gidan, mama na zaune daga ƙofar ɗaki gefenta da tabarmar da aka shinfiɗa masa.
“Lale marhabin, yau angone a gidanmu?”. Ɗan murmushi Jawaad yay ya zauna a tabarmar yana faɗin, “Ayi haƙuri Mama bamuzo mun muki ya gajiya ba”. “A'a nikam ku riƙe ban gajiyar ku, dan an mana babban ya gajiya, ɗawainiya kan ɗawainiya Jawaad baka gajiya? Anyi hidimar azumi akayi ta salla shekaranjiya kuma saiga saƙo, ALLAH ya saka da alkairi ya jiƙan mahaifa kaji, ALLAH ya azurtaku da zuri'a tagari mai albarka”. Kan Jay a ƙasa yana ɗan murmushi yace, ”Amin mama”. Amina ta ajiye masa kunun ayar da sukayi ta sake gaishesa da tambayar Bilkisu.
Zama Jawaad ya gyara ya fuskanci mama sosai, “Mama wani taimako nazo kimin Please”. “Inajinka Jawaad, ka faɗa kanka tsaye, inhar baifi ƙarfinaba zan maka da izinin ALLAH”. “To nagode sosai Mama, nasan tun dawowar su Hudah ƙasarnan kike aiki a gidansu bayan rasuwar mijinki, sannan kaf anguwarnan da ƴan gidan nan suke mu'amularsu kawai, a zaman da kikai dasu nasan dolene zaki san abubuwa masu yawa dangane dasu, musanman ma akan duk wani ma'aikaci da yake aiki a gidan”. “Wannan gaskiyane Jawaad, dan mijina kansa kafin ya kwanta jiyyar ajali
Alhaji Ali ne ya koma masa kamar amini”. “Alhmdllh, inason sanin maigadin nan nasu ke da shi waye ya riga wani fara aiki?”. “Ya rigani farawa, danshi tunma ana gina gidan shine maigadinsa har aka gama suka tare”. “Okey, yanada mata ne?”. “Tunda nake da shi ban taɓa ganin iyalinsa ba, sannan ban taɓa jin ance yau ya tafi ganin gidaba, dan har tambayarsa nama taɓayi game da hakan lokacin inason bada wasu kaya sai nake tuntuɓarsa ko yanada iyali na haɗasu ya kai musu?. Sai cayaymin ai suna gida, daga wannan amsar ya shiriritar da zancenma gaba ɗaya. Nikuma ban sake tuntuɓarsa game da suba gaskiya”. Shiru Jawaad yayi yana nazarin maganganun Mama, kafin yaɗan huro iska da gyara zamansa. “Amma mama kin taɓa ganin wani abu dangane dashi na rashin gaskiya haka”. “Gaskiya ban taɓa ganiba, saboda shifa mutumne ma da baida yawan magana sam, kafin kaga firarsa da mutum tai tsawo akan daɗe, kodan ba abokina hirar nawa bane oho”. “Kukun gidanfa, yakai shekara nawa shikuma yana aiki dasu?”. “Shima tunda suka tare yake, a gidan na sanshi”. “Mai bayin fulawa fa?”. “Eto shine dai kafin shi kusan mutum uku sukai aiki”. “Miyasa suka bari to? Ko ba'a baku albashin daya dace ne?”. “Ai Jawaad idan ta yawan albashine babu wani mai aiki da zaiso barin aiki gidan Alhaji Ali, zan iya rantse maka a cikin dubu irinsa dake fita haƙƙin ma'aikacin gidansa da albashi mai tsoka sai an tona, sannan duk abinda masu gida zasuci kaima mai aiki zakaci, wulaƙanci da rashin tarbiyyar ƴaƴansa ne kawai matsalar ma'aikatan gidan, amma masu bayin fulawarnan da suka taɓa ajiye aiki wlhy bansan dalilinsu ba, dan daina ganinsu kawai mukai mudai koma sallama basuyi damuba”. “To amma baƙwa zaman mutuncine dasu har zasu ajiye aiki baku saniba?”. “Sosai ake zaman mutunci wlhy, dan wanda na tararma a gidan idan kaga yanda ya ɗaukeni tamkar uwa, amma daga zuwa ganin gida bamu sake ganinsaba sai wani mukaga an kawo”. “Zan iya sanin garinsu su duka biyun?”. “To gaskiya anan gizo ke saƙar dan na manta, amma zanyi ƙoƙari na tinano insha ALLAH”. “ALLAH ya bada iko to, drivern su fa?”. “Shima basu taɓa canjawaba”. “Kafin ku wasu sun taɓa musu aiki ne?”. “Akwai ƴammata biyu da suka fara musu aiki kafin mai gidana ya rasu mu fara”. “Miyasa suka bari? Kodan an sameku?”. “Wannan bansaniba kam Jawaad, nidai kawai nasan kafinmu wasu sunyi musu aiki, amma ai nasan kaima kasan duk waɗanan abubuwan tunda kana zuwa gidan”. Murmushi Jawaad yayi, “Sanin dazan musu bazai kai na wanda yake rayuwa dasu yini da kwana ba, Mama inason naji wani abu dangane da fyaɗen Amina, tana ina?”. Mama tai ɗan murmushi, “Oh ni, yanzunan Bilkisu bazata haƙura da maganarnanba? Abinda ya faru ya riga ya faru ai sai haƙuri kuma”. “Karki damu Mama, binciken yanada amfani, dan inma ba'aiba haka za'a cigaba da wulaƙanta rayuwar yara cike da zalunci, ita kanta Miemaa ɗin a zaman datai gidan anshayin farautar rayuwarta akan hakan ai”. Cikin tsagwaron mamaki Mama tace, “Bilkisun?”. “Eh wlhy Mama”. Mama tai sagade al'ajabi na neman kasheta, ta sauke nannauyan numfashi da faɗin, “Bilkisu akwai zurfin cikin tsiya, koda wasa bata taɓa faɗiba wlhy. Saima dagewa datai akan gano wanda yay ma Amina, to ALLAH ya ƙara tsarewa, tunda dai kuma basuci galaba a kantaba ai Alhmdllh”. Ta ƙare maganar da ƙwala kiran Amina.
Amina ta fito daga ɗakin tana amsa mata. Gurin da Mama ta nuna mata ta zauna, Jawaad ya kalleta da ƙyau. “Amina! Randa akai miki fyaɗe suwaye a cikin gidan can?”. “Yaya daga maigadi sai kuku”. “Ina mutanen gidan sukaje?”. “Yah Qaseem da Salman dai sun fita aiki, Momy kuma itada Aamilah ne suka fita, sannan Bilkisu tana makaranta ita”. “Wanene ƙarshen fita a gidan?”. Shiru Amina tayi alamar nazari, kafin tace, “Kamar Aamilah ce”. “Waye ya fara fita kuma?”. “Yah Qaseem”. “Waye ya fara dawowa?”. “Momy da Aamilah nidai na farka na gani bayan na farfaɗo” “Toke dama kina barcin rana a gidanne? Kokuwa a ranar kika fara?”. “Wani lokaci nakanyi idan nasan Mama ta fita dan karna dawo gida ni kaɗai. Da yake akwai ɗakin masu aiki sai nake shiga ciki na kwanta”. “Kafin ranar wani yataɓa miki maganar banza a gidan ne?”. “A'a
babu wanda ya taɓa”. “Mikikaci ranar a gidan? Ina nufin Abinci ko abinsha?”. “Banci komaiba bayan abincin safe, dana kammala aiki kuma saina zauna zanɗan huta, tunawa da wani sauran lemo dana ganine lokacin da zan saka wasu a fridge yasa na miƙe na ɗakkosa na shanye, daga haka ban sake sanin ina kaina yakeba sai farkawa nai na ganni cikin mummunar ƙaddara ”. Ta ƙare maganar da fashewa da kuka. Shiru Jawaad yay yana kallonta da nazarin maganarta. “Dama kina shan lemo a gidan kenan?”. “Eh inasha Yaya, dan indai ɓangaren Abincine ba'ai mana shamaki da komai, abinda sukaci muma shi mukeci babu hantara kuma ”. “Alamu sun nuna Dad baya gidan, lokacin kwanakinsa nawa da tafiya?”. “Eh kamar dai zai kai kwana goma inaga”. “Da yaushe ya dawo?”. “Kwana biyu dayin abun”. “Wane mataki ya ɗauka?”. “Da farko ya nuna damuwarsa, har ya bada kuɗi a kaini asibiti, amma daga baya daya fahimci yaransa ake zargi saima yayta faɗa ya kuma ja baya da al'amarin, yay mana korar kare da ƴan sandan da Yaya Sule ya ɗakko dan bincike”. “ALLAH ya ƙyauta to, ai kinyi karatu ko?”. “Eh nagama secondary school”. “Kin amshi result ɗinki? Kuma yayi ƙyau”. “Eh Yaya, credit ɗina taƙwas”. “Masha ALLAH, ki shirya gobe idan ALLAH ya kaimu Sadiq zaizo ya kaiki wani waje, saiki tafi da takardun, jeki abinki”. Tashi amina tayi tana masa godiya da addu'oin gamawa da rayuwa lafiya ta koma ɗaki.
Jay ya maida hankalinsa ga Mama, “Mama bara na wuce, zata iya yuwuwa kiga na sake dawowa. nagode sosai”. “Babu komai wlhy Jawaad, ALLAH ya saka maka da alkairi, bara kaga na ɗakko maka ɗanyar awara da nayi ɗazun da safe ka kaima ɗiyata dan tana sonta sosai”. “To mama ALLAH ya saka da alkairi, ita Amina yaushe zataje mata ne?”. Mama dake murmushi tace, “zuwa satin sama zatazo insha ALLAH, kusamu yanzu kuma ku huce gajiya basai an dameku da hayaniya ba”. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba.
Koda Jay ya baro gidansu Amina family House ɗinsu ya nufa, yay ƙoƙarin shishshiga ko ina ya gaishesu da musu godiyar hidima har wajen Mama Atika data amsashi sama-sama, daga baya kuma ta koma lallashinsa akan ya saka ɗan-fir'auna ya saki Shahudah kodan son da take masa ya maidata ɗakinta. Yana wannan murmushin nasa na rainin hankali yace to zaiyi hakan tai musu addu'a. Daga haka ya baro sashen nata ya leƙa yaga jikin Mama Badiyya da sai godiyar ALLAH kawai, zaman asibitin ne anyi har angaji an maidota gida, amma kullum lkitanta na zuwa dubata, su Uncle Sulaiman kuma tsaye suke akan al'amuranta basa wasa da ciwon mahaifiyar tasu da aka rasa kansa. Daga nan ya shiga sashensa ya ɗauki wani akwati ya fito suka fice daga gidan.
Hankalinsa kuma yay gida gaba ɗaya, duk da yaso zuwa ya duba ɓaleru sai wani gefe na zuciyarsa yafi ƙwaɗaita masa wucewa gidan, koba komai yana da ƙyau yaje yaga halin da ƴar mutane take ciki, ya kamatama ace yau a gidan ya yini ya bata dukkan kulawa da tattali, amma muhimmancin aikin nan daya saka gaba dole ya daure ya fito ɗin.
Bayan sun iso gidan Sadiq ne ya kwasar masa kayan ya bisa dasu a baya, suna zuwa ƙofar falon ya amsa, duk da yasan suwaye sukazo gidan hakan bai hanashi jin kishi ba saboda jin dariyar maza. Ya murɗa handle ɗin ƙofar ya shiga falon da sallama ciki-ciki. Su Abdul-Raheem duk suka amsa masa suna miƙewa tsaye domin girmamawa a garesa, Ameen yazo ya amshi kayan hannunsa duk suna jera masa sannu da zuwa banda Anuwar da tun shigowar Jay yay mutuwar tsaye, su kansu su Abdur-rahman duk baki suka saki suna kallon Jawaad sai kuma su koma su kalli Anuwar dan yau suka fara ganin Jay su. Jin yanda falon yay wani irin tsitt lokaci gudane ya saka Jawaad da tun shigowarsa gabansa ke wata irin faɗuwa ɗagowa ya kallesu. Idonsa ƙyam ya sauka akan Anuwar tamkar wanda magana ɗisu ya janyo. A take kansa ya shiga wata irin juyawa tamkar mai ganin hajijiya. Amma kasancewarsa gwanin dakiya sai ya dake ɗin ya kafe Anuwar kawai da kallo kamar zai haɗiyesa da idanun.
Anuwar da bazai iya jurewaba kansa ya riƙe da hannu biyu ya koma zaune daɓar saman kujera. Cikin rawar jiki Anum ta ƙarasa gabansa tana faɗin, “Bana faɗa makaba kace ƙ
arya nakeyi, kagani ko tamkar kai, Anuwar wlhy bari kaji yay bagana muryarku iri ɗaya ne shima. Anuwar da ya kasa bama Anum amsa ya wani rinƙa fisgar numfashi da ƙyar yana sake matse kansa cikin hannayensa yana jujjuyashi. “Anum kaina zai fashe, innalillahi wa'inna ilaihirraji'un, wash ALLAH kaina......”