Showing 108001 words to 111000 words out of 261165 words

Chapter 37 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1131

maida hankalinsa ga tuƙin.
Asibiti suka fara zuwa wajen Doctor Ballo Warzu, cikin girmama ya tarisu yana tambayar jikin Bilkisu?, mafi yawan amsarsa Jabeer ne ya bashi ita, sai da suka gama gaishe-gaishensu sannan Jay yay masa magana akan abinda ya kawosu, da tambayar miya faru bayan tafiyarsa?. Labarin komai Dr Bello ya basu, Jay ya dafe kai cikin takaici.
Shi dai Dr Bello haka kawai komai Jay yayi ƙyau yake masa da burgesa, haka ALLAH ke sakama bawa ƙaunar wani batare da wata manufa ba, yay murmushi yana kallonsa, “Karka damu abokina na haƙura indai nine, bansan ɗan uwanka bane dana barsa tun a ranarma baza'a kai hakaba saboda kai, naga rashin hankalin nasa ne yayi yawa shiyyasa naga gara aɗau mataki, amma yanzu kam yaci darajar mai daraja”.
Fuskar Jay ɗauke da guntun murmushi yace, “Nagode Doctor ALLAH yabar zuminci”. Shima Doctor godiya yaymusu, ya kuma rakosu har inda motarsu take, sai da yaga fitarsu sannan ya koma office yana kiran babansa a waya.
★★★★★
Tunda suka shigo police station ɗin aketa basu girma, kai tsaye office ɗin d.p.o suka nufa, inda acan ɗinma dai suka tarbi juna da girmamawa kafin a ɗaura da gaisuwar mutunci. Jay da kansa yayma d.p.o bayanin abinda ya kawosa, ya kuma nuna masa lawyer'n Qaseem ɗin da ya shigo a bayansu dan shi isowarsa kenan. A take anan aka kashe magana babu zancen zuwa kotu sannan aka kawo musu Qaseem. Babu abinda akai masa, dan ko hararsa babu wanda yayi tunda aka kawosa gurin saima girmamawa, ko kayansa ba'a cire masaba, sannan ba'a haɗashi da kowaba a cell.
Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Jay, kowa ya ɗauke nasa fuska a tamke, Jay ya fara miƙewa ya fice abinsa, hakan yasa Qaseem jan tsaki, rai a ɓace ya kalli d.p.o yace su maidashi cikin cell ɗin. Duk kallon mamaki suke masa, Jabeer da yasan wasan ya dafa Qaseem ɗin yana magana a hankali, kamar Qaseem ɗin bazai yardaba sai kuma miya tuna oho masa ya nufi hanyar fita Jabeer da lawyer ɗinsa suka take masa baya.
A jikin mota suka iske Jay tsaye yana magana da Engineer ɗin da zai masa gyaran gidansa da Bilkisu zata zauna. Suna isowa yana ajiye wayar dan sungama. Sake ma juna kallon ido cikin ido sukai shi da Qaseem, cikin ɗacin rai Qaseem yace, “Miyasa ka cironi? Minene haɗina da kai?”. Murmushin rainin wayeo Jay yay masa yana lasar lip ɗinsa na ƙasa, yaɗan ɗage gira cike da salo dukda idanunsa na cikin glass ne, hannayensa duka cikin aljihun wandonsa suke, Yace, “Inada business da kaine shiyyasa”. Wani kallon banza Qaseem yayma Jay shima, yace, “A kasuwa ka ganni?”. Jay ya sake murmusawa tare da ciro hannunsa yaɗan sosa gefen girarsa da ɗan yatsa yana karyar da wuya, “Karkai taurin kai, akwai tagomashi mai yawa da riba”. Qaseem yaja tsaki ya motsa zaibar wajen yana faɗin, “Zanyi maganin tsagerancinka ne yaro kwanan nan”. Cike da rainin hankali Jay yace, “Ai zuru batacin zuru, sai dai a haɗu ai zuru-zuru. Nabaka nanda kwanaki bakwai kacal zaka nemeni da kuɗinka ma”. Qaseem yay wata dariyar kai banzane ya wuce motar lawyer ɗinsa batare da yabama Jay amsaba....
Jawaad yay wani lalataccen murmushi yana zare gilashin idonsa, sai da Qaseem ya shiga motar sannan ya maida glasess ɗinsa yay salute ɗin motar da faɗin, “YANZUN MUKA FARA”. (Bari na ƙarasa maka jikan Yusufa🤣. WASAN😉).
____________________________________
Ƙarfe sha biyu da wasu mintuna na farka, ni kaɗaice a ɗakin, na sauka daga gadon ina addu'a da miƙa, naji daɗin jikina sosai gaskiya, rashin barci ai masifane. Wanka na shigayi, amma abin mamaki sai nai karo da Jini, cikin mamaki nace, “Jini kuma? To duka yaushe ma nai wankan tsarki? Kofa sati biyu banyiba”. Mamaki tamkar zai kasheni nai wanka na fito. Ina shiri ina juya al'amarin cikin raina. Shigowar Amaturrahman ne ya sakani juyawa na kalleta. Tai murmushi da faɗin, “Amarya saifa wani Shining kikeyi miye sirrin ne?”. Murmushin yaƙe na mata kawai bance komaiba, itama tai dariya kaɗan, “Kefa tuni na lura irin Marwah ce, muskilanci ya muku yawa, idanma an zauna hira daku daga eh sai uhm sai a'a kuka ƙware yi, badai haka za'aje anama Yayan namu dunɗun dunkum ba kamar hadarin maraice?”. Bansan sanda na ƙyalƙyale da dariya ba babu shiri, dan harga ALLAH taban dariya musamman yanda tayi da fuska sanda zatai maganar. Ta ɗagamin gira da cewar, “Ko kefa, gashi na sakaki kin dara, ki shirya muje Ummu na jiranki, yau dai tace sai taga ƴarta”. Naji daɗi a raina, sai dai ina ɗanjin tsoro-tsoro, nice yau zan gamu da Sarauniyar gagara badau gaba ɗaya, ni Bilkisu ɗiyar baba makaho da Asiya gurguwa, ALLAH sarki duniya, duk abinda kaga ba'a gani saboda ƙanƙantarsa wataran zai fito kowa ya gansa saboda girmansa, wataran kuma sai tsufa ya sakayashi, a ƙarshe mutuwa ta ɓoyesa. Tsaf na shirya da taimakon Amaturrahman cikin siket da riga na atanfa da sukaimin ɗas a jiki, dukda dai basu kama jikina ba, duk yanda tasi hanani na saka gyale kasawa nai saida na saka sannan muka fito.................✍
Barkanmu da dawowa, ina fatan kunyi weekend cikin ƙoshin lafiya😉😘😘😍😍😍😍.
Masu kira akan zasu sayi ƘWAI CIKIN ƘAYA!! bafa shi ake tallaba, muna tallar buks ɗinmune guda goma na zafafa gasunan, duk wanda bai sayaba ya motso ya saya karya bari romon daɗi ya wucesa🤗🤗🚴🏼

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300

Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/22/2020, 6:53 PM] HASNA✍🏻: ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 34
...................Katafaren falone daya amsa sunansa falo, komai yaji iyakar ji fiye da tunanin mai hasashe, ga wani sassanyan ƙamshi mai kashe lakkar jiki da tsaida gudun jini na tashi, lallai wannan baiwa ta isa a kirata sarauniya, ta haɗu tama gaji da haɗuwar, ga kwarjini irin wanda kowa yasan masu mulki dashi. Tana kishingiɗe ne amintacciyar baiwarta na gefenta da alama hira sukeyi, dan fuskokinsu dukansu ɗauke suke da murmushi, sai bayi biyu kawai a falon, ɗaya na tausa mata ƙafafu ɗaya na yanka mata tufa a ƙaramin filet. Sallamarmu ta sakata maido fararen idanunta kanmu, da sauri Amaturrahman ta tareni tana faɗin, “Gaskiya Ummu sai kin biya”. Murmushi Gimbiya Munaya tayi mai ƙayatarwa, cikin nutsatstsiyar muryarta tace, “Amaturrahman kin maidani kakarki a gidannan, nakula kema auren kikeso”. Da sauri Amaturrahman ta matsa gefe tana tura baki gaba da faɗin, “Ni ALLAH banason aure ina tare dake da Abbu da Mommah”. Dariya hadiman sukayi, nima dai murmushi nike, dan saita tunomin da Nabeelah. Gimbiya Munaya dake murmushi ta miƙomin hannunta da yasha adon jan lalle, “Kinga ɗiyata manta da wannan zo naji ɗuminki kinji”. Jikina har rawa yake saboda yanda tamin tamkar mahaifiya, na taka a sannu cikin nutsuwa gareta, durƙusawa nai kaina a ƙasa, ina faɗin, “Barka da rana Ummu”. Ina jiyo fitar sautin murmushinta, ta ɗora yatsunta saman haɓata ta ɗago kaina, “Nagode da wannan girmama ɗiyata, ALLAH yay miki albarka kinji, kiyi haƙuri da rashin ganina tun zuwanki”. Murmushi na mata ina ƙasa-ƙasa da idanu, dan bazan iya kallonta kamar yanda take kallona ba, nace, “Babu komai Ummu”. Murmushi ta sake yi, tare da zaunar dani sosai, ta sallami bayinta guda biyu, daga ni sai Amintacciyar baiwarta da kuma Amaturrahman data koma can cikin kujera tana kumbura wai ance za'a mata aure. itafa ta rantse bazatai aure tabar Ummu da Abbu ba. (Kujimin ƴa, to itama munayar ai sunƙumota Galadima yay daga gabansu hajiya innaro😂).
Cikin nutsuwa da hikima Gimbiya Munaya kejan Bilkisu da hira, abin gwanin sha'awa, babu wani nuna ƙyara ko izzar mulkin kasancewarta ƙasan ƙasa da ita, haka gimbiya Munaya take, bata yarda ƙasƙantar da waniba a rayuwarta, tace tasan ciwon ƙasƙanci, bazataso yima waniba, ita tasan wahalar da zuciyarta tasha lokacin da suke ƙarƙashin mulkin mallakar Innaro a gidansu. (hajiya innaronmu ta mutumci kwanciyarki lafiya cikin ƙasa matar Faruku😂🤗, karkimin fatalwa da daddare kuma yasin😤).
Yanda Sarauniya ta iya hira har bansan sanda nake bata duk amsar data buƙata daga gareni ba, har takai munyi zurfi sosai a hirar fiye dazaton mai hasashe, kiran sallar zuhur ne ya tashemu, muka koma ɗakinmu domin yi, nidai banyi yunƙurin yiba tunda naga jini a jikina dukda dai kaina a ƙulle yake.
Muna cin abinci kira ya shigo wayar Amaturrahman, ɗaukata cike da zumuɗi tana faɗin “Meenal kun tahone?” bansan mi akace mata daga canba naji cike da murna ta sake cewa, “Wlhy da gaske nake tana nan har sai lokacin tarewarta”. Daga inda nake ina jiyo ihunsu, itama ta miƙe tana rawa da ihu. Nikam mamaki suke ban, Amaturrahman irin tsagwaron izza da mulkinan na ƴaƴan sarakuna sam batayi, ko kiga tana wulaƙanta bayi tana takasu yanda takeso, abinda kawai na fahimta tarbiyyace daga iyayensu hakan, An nuna musu bayin gidansu mutanene tamkarsu masu daraja da mutunci, shiyyasa sam basa tozartasu.
Ban tambayeta su wayeba muka cigaba da ƴar hirarmu, dukda nifa dauriya kawai nake hankalina ya rabune kashi-kashi. Ba'afi mintuna talatinba saiga ƴammatan ranar da muka taɓa haɗuwa a Saloon tare da su Amaturrahman ɗin, Meenal da Amatullah, ashe tafiya sukayi shiyyasa ban gansuba tunda nazo. Suka rungumeni cike da murna, ni harma mamaki suka bani, gasu suma da shegen kauɗi, aiko yinin yau dai kaina har ciwo yake saboda surutunsu, amma zamana dasu ya ɗeben kewa sosai, sai nake ganinsu kamar su Ummie. Muna tare Zuhrah ta kira waya, yanda sukaji muna waya da ita tana tsokanata Amatullah ɗiyar Buzaye mai cike da sirrin ƙyau ta fige wayar ta saka a hansfree kowa yanaji, a cewarta suma yanzu ai ƙawayen Zuhrah ne, duk ƙawayena sun zama nasu suma.
Abin mamaki da daddare saina nema jini na rasa, baƙaramin ɗaure kaina al'amarin ya sake yiba, ni a ƴan kwanakinnan sam bama na ganema kaina, daga wannan al'amari ya wuce sai wannan, ALLAH na gode maka da wannan jarabawa, ya rabbi ka bani ikon cinyeta, ka ƙaramin haƙuri da juriya.

(Amin Sakwara🚴🏼)
____________________________________
“Nifa wannan wasan naku dariya yake bani kaida Qaseem Boss, gashi yanzu Mami ta sake tunzura komai ya ɗau zafi, shi bazai yarda da ƙaddara bane ba?”. Murmushi Jay yayi baice komaiba, sai ƙoƙarin saka waya da yake a kunne. Daga can Abbati yay sallama. Amsawa Jay yay suka gaisa. Yace, “Ina fatan yau zaka tashi aiki da wuri dan inason ganinka, banason kuma a wuce yau saboda muhimmancin zaman”. Daga can Abbati yace, “Babu damuwa, ai kama yanka akan gaɓa, dan inason na shigo namaka ta'aziyya dama, zan shigo bayan magriba da safe sai na wuce”. Jay yace, “Kai malam nifa yanzun ƙattai sun daina kwanarmin a gida inada iyali”. Ba Abbati ba hatta da Jabeer dariya ya kwashe da ita harda ƙyaƙyƙyewa, Jay ya mangarema Jabeer kai tareda ranƙwashi mai zafi, yace, “Kaima ɗan iska na wayar zan kamaka ne, masu zuwa lahira da ido ɗai-ɗai”. Bai jira amsar abbati ba ya yanke wayarsa. Jabeer dake sosa inda Jay ya ranƙwashesa yana tuƙi yace, “Oho dai, ai sa idon namu mai lasisi ne, ni nama taɓa ganin munafukin soyayya irinka?, ALLAH zan cema sarauniya karta bar Mami ta tare har sai kazo da kanka ka furta kana SO da hawaye”. Taɓe baki Jay yayi da kwantar da kansa jikin sit ya lumshe idanunsa, a hankali yace, “Idan namata ciki a waje saiku barta ta tare ɗin, koku bari saita haihu kukaita da ƴar ko ɗan”.
Jabeer dake ƙumshe dariya yace, “Ainasan kai waliyyine bazakai hakanba”.
Shiru Jay yay tamkar bazai tankaba. Sai kuma zuwa can ya zubama Jabeer ɗin harara ya ɗauke kansa.
Kasa daurewa Jabeer yay ya kwashe da dariya yana dukan sitiyari. Jawaad yay guntun tsaki da faɗin, “Kaifa wani lokacin baka da man kai, ka isheni fa”. Jabeer dake dariya yace, “Baka da amsa yanzu, sai mun isa inda zan saida wannan jaridar tukunna”. Banza Jay yay masa bai sake magana ba, saima kansa daya sake kwantarwa jikin kujerar yay luf.
Gaba ɗaya a wannan yinin Jay yayisa cikin aiyuka, Baibar Office ba sai bayan sallar isha'i, haka ya tashi a gajiye, gida ya wuce kai tsaye dan Abbati harya kirasa ya sanar masa ya iso, ada idan zasu haɗu A.Y street suke haɗuwa, yakan daɗe bai kawo aboki family house ɗinsuba sai idan ta kama dole, to a yanzu wancan gidan a hargitse yake dan amma fidda komai na cikinsa aiki akeyi tuƙuru da sauya fasalin abubuwa.
Tare suka shigo da Abbati dake ɗauke da jikkar Jay ɗin a hannu, basu zauna falon ƙasaba saboda yay datti sosai, suka haye sama, anan yabar Abbati shikuma ya shige bedroom dan yaɗan watsa ruwa. Ya sauke idanunsa akan gadonsa ya lumshesu yana maijin wani iri, jiya iyanzu suna nan tare. Wasu abubuwan data dingayi ya tuna, babu shiri murmushi ya suɓuce masa, aransa mamaki ma yake yanda take matsoraciya ya akai ta shiga aikin nan? Bashi da mai bashi amsa dan haka ya nufi bayi, bai wani jimaba saboda yanaso su tattauna da Abbati ya kwanta da wuri, yay shiri cikin kayan barcinsa farare tas masu taushi wandon har ƙasa. Dama ya sayo musu abinda zasuci a hanya, hakan yasa yana fitowa ƙasa ya sauka ya ɗakko filets ya dawo inda Abbati ke zaune yana kallo. Sake gaisawa sukai, Abbati na juye kajin a filet Jay kuwa na daga can wajen D/table yana haɗoma kansa Shayin da shansa ya zame masa jiki yanzun, takai har idan baima shaba bayajin daɗi.
“Ni ina nawa shayin?” cewar Abbati. Hararsa Jay yayi ya ɗauke kansa ya maida ga tv, “Sai kazauna tunda ni matarkane na kawo maka”. Abbati ya miƙe yana faɗin, “Kazama matata aiban moreba Yasin, ina zani da gabjejen ƙato kamarka”. Murmushi kawai Jay yayi ban sake tankawaba, saima shayinsa da yakesha hankali kwance har Abbati shima ya dawo ɗauke da nasa.
Bayan sun sake gaisawa sukai jimamin rasuwar Gimba sosai sannan Jay ya ɗora da faɗin, “Bana babu Gimba, dama shike tsaye akan rabon kayannan na azumi Abbati, narasa wazan ɗauka yay aikinan, gashi ya kamata ace tun jiyama aka fara rabonsu kamar yanda marigayi yakeyi”. Abbati yace, “ALLAH sarki rayuwa kenan, ALLAH ya gafarta masa, lamarine na mutane sai addu'a, sam bama tsoron ALLAH, wanda ya bada baiji ƙyashiba sai kaga masu rabawa sun zama azzalumai, amma kuma wai da an tashi zagin shugabbani suma sunada bakin jefa nasu”. Jay yace, “Humm, ai Abbati ɗan adam barshi yanda ka ganshi kaji, lokacin daka bashi zuma ya lasa zai sanar maka da daɗi yama gode maka, amma da saɓanin hakan ya gitta kafi kowa muni a idonsa. Manta da wannan maganar muyi wadda ta fita muhimmanci. Yanzu dai kafinma akai ga mahanar fidda kayan, kayan abincinmu da zamu saida sunada yawane?”.
“ALLAH na tuba boss ai suma ɗin dai kamar ƙyautarne, tunda ana saida musu ne bisa farashi mai matuƙar sauƙi, duka stores ɗinmu cike suke da kayan abinci kamar kowacce shekara, idanma munada ƙarancin wani abu to manja ne gaskiya”.
“Karka damu, batun manja nayi magana da Jessica ɗazun, insha ALLAH zuwa jibi zai iso, inason linka kayan da ake rabawarne, to da nayi tunanin sayen waɗanda muke dasu a ƙasa, sai dai ɗazun kuma wani tunani yazo mani, gara mu saya hannun ƴan kasuwa, shikuma namun mu saida musu akan farashin da aka saba ɗin bisa ƙaramar riba”.
“Banƙi ta takaba Jay, amma kaima idan ka sayi namun ai zaka samu sauƙi, dan naga wannan karon abubuwan sun taso da yawa, ga maganar gyaran gida naga ka saka, hidimar aure ta wuce wasa ai”. Ɗan lumshe idanu Jay yay yace, “ALLAH zai rufa asiri Abbati, muyi hakan kawai, inason zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu a kammala siyayyar, dukda guri ya ƙure zuwa jibi sai a fidda kayan, kayanmu kuma da za'a saida yakamata kuma ku fiddasu ai”.
“Eh dama munyi dasu Labaran gobe idan ALLAH ya kaimu za'ai baja koli, shiyyasama nace zanzo na sameka yau ɗin, zan ɗauki hutun sati guda wajen aiki insha ALLAH muga an raba kayan yanda ya kamata mabuƙata sun samu”.
“Nagode sosai Abbati, nayi magana da Alhaji Garba yadi, amma Jabeer ne zai tsaya nan ɓangaren shi da su Aliyu dan aikin yamaku yawa kuma, inason wannan shekarar insha ALLAH muhaɗa da tufafi wa ƙananun yara suma, ni kuma inason hankalina ya tsaya wajen gyaran gidannan ne”.
Cikin jin daɗi Abbati yace, “ALLAH ya saka maka da alkairi ya ƙara buɗi, ALLAH yasa baɗi iwar haka muna nan muna shagalin sunan babys ɗinmu. Murmushi kawai Jay yayi baice komaiba. Sun cigaba da tattaunawa har kusan 12 sannan suka kwanta, Abbati a ɗakin baƙi da Jay ya shiga ya taimaka masa suka gyara, shikuma ya koma ɗakinsa ya kwanta.

WASHE GARI.
Washe gari Jay suka koma garin su Gimba, ta'azziya suka sakeyi, shima kuma aka sake masa dukda wasu harda munafunci dan sun dasa ƙananun magana akan Jay ɗan ƙungiyar asirine, shine yakai Gimba ma aka shanye nasa. Kasancewar shi mutumne mai saurin fahimtar abu kafin su baro garin ya karanci abubuwa masu yawa daga mutane, ya kuma saka an bincika masa inda ɓaleru yake ta hanyar iyayensa da basusan dawan garinba. Zuwa Azhar suka baro garin.
Tunda suka dawo daga garin su gimba aiki yake babu hutu, kiran sallar la'asar ne kawai ya tadashi, bayan an idar office ya dawo ya ɗora daga inda ya tsaya. Zamansa baifi da mintuna goma ba Hafiz dake ɗauke da takardu a hannu ya shigo office ɗin da sallama..
Batare da Jay ya ɗagoba ya amsa masa. Hafiz ya zauna a ɗaya daga kujerun gaban tebirin yana faɗin, “Yauwa boss ga file ɗinan na gama tattare komai, abinda ya rage mana kawai yanzun shine bin sawunsa kawai, kaga dai dukkan abinda muke buƙata mun riga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login