Showing 171001 words to 174000 words out of 261165 words

Chapter 58 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1137

naso ace shima ya tashi cikin ƴan uwansa da a yanzu sune suka zamema rayuwata haske, ALLAH ne yaymin komai da kaini matsayin da nake a yanzu amma ta dalilinsu ne, na yarda abinda kakeso bai zama lallai ya kasancema rayuwarka alkairiba, wanda kake ganin yay kutse ma rayuwarka sai kaga shine alkairin, naso Sa'a so mai tsanani, harnaso bijirema iyayena a kanta, sai dai itaɗin ashe ba itace abinda nake ma hasashenba, wadda iyayena suka auramin ina baƙin ciki da takaici, na ƙuntata rayuwarta a zamanmu sai tazama ashe itace abinda banyi zatonba, dan gashi yanzun albarkacin zuri'arta nakeci ita bata raye, wannan aya ce ga masu ZUCIYA irin tawa, ɗan adam shidai abinda akeso ya nema zaɓin ALLAH akan dukkan al'amarin sa ba wai son zuciyarsa ba”.
Sosai Malam ɗan inna keta faman jinjina kansa, Jawaad dai yana saurarensu amma bazaka taɓa fahintar yanayinsa ba sam, saida Alhaji babba ya gama share-sharen hawayensa sannan Jawaad ya ɗago ya sake kallon Malam ɗan inna, “Na biyu kuma zamuje da kai gidanda suka zauna danka nuna mana yarinyar, mu zamu ɗauketa mu riƙe, basai munsan gaskiyar yanda suka sametanba”.
Sosai ruɗani ya bayyana ga Malam ɗan inna, ya shiga matsar hawaye yana bada haƙuri da musu bayani akan suma basusan inda Bilkisu take zaune ba, amma kwanaki taɗan zazzo gaishesu, sai dai maganar gaskiya ko tazo ɗin basu wani sake mata fuska, danshi sau ɗayama ya taɓa ganinta, kusan shekara uku kenan ya kuma ja mata gargaɗi akan karta sake zuwa masa gida tunda basu da alaƙa da ita, dan saida ya titsiyetama yaji wanene ya nuna mata gidan kafin yaymata korar rashin arziƙi. to amma yaji kwanaki iyalinsa suna gulma wai tana zuwa wajen Ramatu, kuma ma har tayi aure kwana nannan ita Ramatun taje.
Kafesa kawai da kallo Jawaad yay ransa a matuƙar ɓace, ganin hakanne ya saka Alhaji babba riƙe hannunsa yana murzawa alamar lallashi, hannunsa ya zame ya tashi ya fice daga zauren.
Alhaji babba yay murmushi yana girgiza kansa, sannan ya maido kallonsa ga Malam ɗan inna da shima yabi Jawaad ɗin da kallo, “Haka yake yana da matuƙar zuciya, sai dai yanada kirki sosai, shine jikana na farko da ƙanwar Adamu mai suna Bilkisu ta wajen Amina kenan ta haifa, ɗan tsohon shugaban ƙasa da ALLAH yayma rasuwa Alhaji Abdul'aziz yusif tafida”. Idanu sosai malam ɗan inna ya zaro, cikin ɗan rawar baki yace, “Dama yarinyar wajenka ce matar marigayi A.Y tafida?”. “Hakane, gama yaronsu da ya bari nan”. “ALLAH maiyin yanda yaso, ALLAH mai hikima, lallai zaɓin ALLAH shine zaɓi kam bawai son zuciya ba, wanene zai iya mantawa da tsohon shugaban ƙasa Abdul-aziz Yusif Tafida a ƙasarnan ai saida azzalumi, adalin shugaba da har yanzu ba'a ƙara samun makamancinsa ba ma”. Murmushi Alhaji Babba ya dingayi jin ba'a manta da ɗan matarsa ba, surikinsa kuma uba ga babban jikansa. A take ya warwarema Malam ɗan inna gaskiyar al'amari dan gane da bilkisu harma aurenta da jikansa Jawaad, wanda a dalilin hakanne kuma yasaka su ma bincike har suka ganosu ta dalilin kamannin bilkisu da Adomu daya gani, da kuma ƴarsa data rasu Rahmah, wanda yake ganin bilkisu ta ɗakko kamanin Rahama ne saboda ƙarfin jini, to gashi sukuma sunmace basu yarda ADamun ta haifi bilkisu ba, to shi ina zasu kama su fahimci gaskiyar wannan ruɗanin ne. Al'ajabi ya sake kama Malam ɗan Inna har takaisa ga sharar hawaye, yayta ban haƙuri da neman afuwa ga alhaji Babba tundaga laifin da ƴar uwarsu ta zama sila har wanda suma suka tafka. Tarr syka fito har wajen mota yana bama Jawad da yay kicin-kicin da fuska haƙuri shima. Hannu kawai ya ɗaga masa da jinjina kansa, dan ransa a ɓace yake, kuma bayaso kosau ɗaya fushinsa yakaisa ga aikata abinda bai daceba ga dattijon da zaiyi sa'a da mahaifinsa, gashi koba komai akwai alaƙa.
Sun rabu akan zai faɗama sauran ƴan uwansa komai auzo kuma har gida su ƙara bada haƙuri.


Lallashin Jawaad Alhaji babba yay tayi cikin hikima, tun yana baɓɓata fuska na shagwaɓa harya sake yana masa murmushi, gida suka maida Alhaji babba, batare da sun shigaba Sadiq yay reverse suka sake barin anguwar. Daga nan inda ya ajiye ɓaleru suka nufa kuma.
Tun shigar Jay ɗakin da ɓaleru yake jikinsa ya fara ɓari, ya ajiye abincin da yake ci gefe yana zazzare idanu, da hannu Jawaad yay masa nuni da abincin alamar ya ɗauka ya cigaba da ci. Babu musu ɓaleru ya ɗauka teakaway ɗin yana cusawa kamar yanacin maɗaci saɓanin yanda abincin ya fara masa daɗi da farko.
Ɗauke kai Jawaad yay daga garesa, saida ɓaleru ya cinye abincin tas ya ajiye batare da yaci kifin cikiba, ”Shikuma wannan waka barwa?”. Jawaad ya faɗa yana tsatstsaresa da idanu murya a kausashe. Ɗauka ɓaleru yay da sauri ya hau ci, ALLAH dai ya taimakesa ƙaya bata maƙale masaba ya gama lafiya. Hannu yaje ya wanko ya dawo, ya maƙure jikin bango hantar cikinsa na kaɗawar tsoro, dan har yanzu baibar jin ciwon jikin dukan daya shaba ranar. Jawaad ya ajiye wayarsa yana kallon ɓaleru da ƙyau. “Ka shirya faɗamin gaskiya ko sai mun sake kalar wasan ranar?”. “Wlhy duk abinda kake buƙata inhar na sanshi zan faɗa maka oga”. “Tunani mai ƙyai” Jay ya faɗa yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya. “A gidan wa kake aiki?”. “Mr Gebrail”. “Waya sakaka ka ɗauki Gimba a mota?”. Inda inda ɓaleru ya nema farawa Jay ya daka masa tsawa, “Wlhy ko sau ɗaya kamin ƙarya saina karyaka a wajenan na ɗauraka”. Sanin Jay zai iya aikatawa yasa ɓaleru haɗiyar yawu muƙutt, “Uh.. Uh... Uhmm ni dai kawai wata safiya ne aka kirani da kwatanta mini shi, bammayi zaton shi bane saida naje zan ɗaukesa”. “Waye ya kirakan?”. “Mr Gebrail ɗin”. “Ina ka kaishi?”. “Wlhy acan titin ƙatshen gari ya tareni ya amshesa?”. “Kenan dama ka saba musu irin wannan aikin? Koma shi kake musu?”. “Oga Wlhy.....” “Amsa kawai nake buƙata, duk abinda yazo a saɓaninta kai kuka da kanka”. Kansa ya ɗaga da sauri yana karkarwa. “Shi da waye suke sakaka? Kuma wanene ya kaika aiki gidansa?”. “Ɓaleru ya share hawayen da suka cika masa idanu, “A anguwar da gidan drama ɗin nan yake yake gini, wataran yazo wajen shine ya ganni”. “Sai kawai yace zoga aiki na baka?”. “A'a nine da kaina naje na tambayesa saboda a lokacin aikin nake mema, to da yake ina ɗibo yashi daga can wani rafin dake ƙasan anguwar ina kawoma masu gini na saya, lokacin ana aikin gininsa kuma nine mai ɗebo musu yashin, sai naji yana tambayar Engineer ɗin ko yasan wani driver? Dan yanason ɗaukar driver, drivernsa ya ajiye aiki saboda tsufa, to ahinefa nace zanyi da yake na iya mota. Da farko yayi kamar bazai ɗaukeniba sai kuma ya bani key yace na gwada ya gani, a take na amsa na shiga motarsa naɗan zagaya wajen, a lokacinma bai amsa zai ɗaukeniba ya tafi, sai bayan kwanaki biyu harma na fidda rai sannan yazo yace ya ɗaukeni”. “Daga nan sai ya maidaka kidnapper ko? Har takai kuɗi ya rufe idonka aka haɗa baki dakai aka kashe abokinka ɗan garinku?”. “Wlhy oga bada ni aka haɗa baki aka kashesa ba, hasalima nima mutuwarsa kawai naji, wlhy tunda gimba ya rasu ban sake samun kwanciyar hankaliba, oga ina tsaka mai wuya”. “Ai bama ka shigaba tukkunna indai tsaka mai wuya ce. Ya akai ka tuƙa Alhaji Kokino ranar kuma?”. “Alhaji Kokino kuma? Wlhy ni bamma sanshi ba”. “Humm kana wasa dani ko?”. “Wlhy oga da gaske nake maka”. Jay baice komaiba ya ɗauka wayarsa, hoton da yay musu lokacin da traffic light ya tsaidasu ya nuna masa, ɓaleru yace, “Aiho, ai yaje office ɗin Mr Gebrail ne sakan kasuwanci sai motarsa ta samu matsa, shine drivernsa ya ɗauka ya kai wajen gyara, to bai dawo da wuriba shi kuma ya gaji da jiransa shine yace na kaisa gida, wannan shine dalilin da yasa ka ganmu tare”.
Kafesa da kallo Jay yayi cike da nazarin maganarsa, bai sake cewa komaiba ya miƙe, fitowa yay abinsa. Ɓaleru ya bisa da kallo, daka ganshi kasan a tsorace yake. Securitys ɗin dake kula da ɓaleru ya korama winning akan su kula dashi da ƙyau, duk kuskuren da aka samu sune zai fara hukuntawa. Daga haka ya shiga mota suka bar gidan.
Ganin lokacin sallar la'asar yayi saiya saka Sadiq tsayawa sukayi sannan suka ƙarasa gida.
★★★★
Bily na zaune da ƴammatan maƙwafta da suka shigo mata dan a gaisa asan juna ya shigo. Sannu da zuwa tai masa, suma suka shiga gaisheaa suna binsa da kallo tamkar wasu mayu. Kallo ɗaya yay musu ya amsa Sau ɗaya yay shigewar, miƙewa nayi, dan haka suma duk suka miƙe, sallama sukai man suka tafi, nai musu godiya nima sannan naje kicin na ɗauki kunun ayar da nayi na nufi ɗakin nasa. A bakin gado na iskesa zaune ya dafe kai, koda nai sallama bai ɗagoba yadai amsa mani. Naja ƙaramin table ɗin na ajiye. “Su wanene waɗanan?”. Ya faɗa batare da ya ɗago ba. “Nima ban sansuba, basu fi mintuna talatin da shigowaba, sunce min nan gidan maƙwaftan nan namu suke”. Amsar kofin dana miƙa masan yayi, yaɗa lumshe idanu sannan yasaka a bakinsa ya shanye gaba ɗaya alamar yanajin ƙishi sosai, kofin ya ajiye yana miƙewa, “Kidaiyi a hankali”. Ya faɗa yana cire maɓallan rigarsa. “Insha ALLAH zan kiyaye”. Na faɗa ina miƙewa.
Hannunsa ya miƙomin yana min nuni da rigar, dukda dai inajin nauyinsa haka na kama na taimaka masa muka cire, dan na lura shifa komai yafison ai masa. Na juya zan ajiye rigar naji kawai an kwasheni anyi sama dani, ina mamakin yanda ya ƙware da iya ɗaukar mutum babu ko ɗar, shi ko nauyina bayaji ma.
Ganin ya nufihanyar bayi nai saurin cewa, “Bandaɗe da yin wankaba fa ALLAH”. “Ke kika san wannan”. Ya shige toilet ɗin yana faɗa. Nidai balki naga ta kaina, inaji ina gani dole akai wankan nan, ni gaba ɗayama ya fara busarmin ido da salonsa. Haka mukai wankan muka fito, bayan mun kimtsa muka fita domin cin abinci.
★★★★★★★★
Yau kwanakinmu shida kenan da tarewa, zuwa yanzun bansan yanda zan lissafo muku abubuwan da boss ya koya minba, gaba ɗaya ya fetsarar dani, duk da dau bana fiddo zaƙewat dan akwai sauran lokaci, kunyarsa kuwa inajinta tamkar babu gobe, dan duk abinda zai sakani na masa inayi ina rufe idanu, mu'amular gadoce fa na kasa sabawa, dan duk sanda zaizo min babu fashi sai nayi kuka, har fargaba nake ya nuna buƙatarsa, duk da hutun amarci da aka bamu hakan bai hana boss aiki tuƙuruba a gida, ni kaina bai barni na hutaba, matan su Jabeer sunzo sun yinarmin, hakama su Safah an kawosu, Amina ma tazo ta yini randa matan su Jabeer sukazo, da yamma sai ga su Nazifa ma, maganar da muka tattauna ta sakani fahimtar sun shirya zuwanne dama, nayi farinciki sosai ganin maganar ƙungiya ta kankama, komai an kammala na shirye-shirye a satinan za'a fara fidda komi ta kafafen yaɗa labarai da yanar gizo kamar yanda aka tsara, dan aomuke mu fito da zafinmu, ga bikin Nazifa nata matsowa ita, dan ƙarshen wata mai kamawa ne.
Bayan tafiyarsu na gaji liɓis dan dan suma su Aliyun anan suka kusan yinar mana tare da boss, sauƙina ma basu bar gidanba saida suka tayani na gama komai tsaf gidan ya dawo normal, sanin ko nayi wanka idan ya dawo saina sake dole tare da shi dan kullum tare muke wankan dare sai kawai naƙiyi na dafa masa shayi na gyara fruit. Falonsa nakai komai sannan na shiga haɗa ruwan wanka, ina ciki kuwa ya shigo, sai kawai jinai an ringumeni ta baya. Murmushi kawai nayi na juyo muna kallon juna, murmushin shima yamin da kai hannu a.................🙄😣✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/13, 3:03 PM] HASNA✍🏻: Page 48

..............Murmushi shima yaymin da kai hannu a ƙuguna ya kuma matsoni sosai jikinsa, cikin raɗa yace, “Are you ready?”. Ɓata fuska nayi ƙwalla na cikamin ido na girgiza masa kai dan nasan inda ya dosa. Wata shaƙiyyar dariya yayi dajan hancina yace, “Kedai raguwa ce yarinyarnan”. “Ni dai wlhy naji koma miye ace ba raguwaba, kai dan bakasan wahalar da ake sha bane ai”. Bakinsa ya ɗaura a saman kunnena ya ɗan ciza yana dariya da faɗin, “Shiyyasa nake son maidaki jaruma”. Nai saurin ƙanƙamesa saboda tsigar jikina dake tashi, da sauri na mintsini damtsan hannunsa “Ai na fika jarumta”.
       Saurin sakina yay da faɗin, “Ouch!. Ke dai muguwace wani lokacin”. Gwalo na masa na shige cikin ruwan. biyoni yay ciki, “Yarinya kin taro match kuwa”. Saurin ɗaukar soso nai dana haɗama kumfa na saka masa a fuska, yay ƙoƙarin riƙe hannuna naƙi bashi dama, hakan yasa mukaita facal-facal da ruwan kamar wasu ƙananun yara.
     Sai da muka gama shiriritarmu sannan muka fito. Zama nai a kujerar mirror ina goge fuska yazo ta bayana ya tsaya yana miƙamin hannunsa.
        Cike da mamaki na kalli hannun nasa, wani ɗan ƙyaƙyƙyawan akwatine mai kama da diamond amma farine shi tas wannan, sai ɗaukar ido yake da ƙyalƙyali, ɗaga kai nayi na kallesa ta cikin mirror ɗin ya ɗaga min kai da lumshe ido. Yawu na haɗiye da ƙyar nasa hannu na ɗauki ɗan box ɗin inayi ina kallonsa, ganin idonsa a kaina yake har sannan sai na nutsu waje guda, jiki a sanyaye na buɗesa. Na waro idanu sosai waje da faɗin, “Woow!” dan ƴan kune ne masu ƙyau a ciki da zobe. Bansan sanda na juya na daka tsale na ɗanesa bama ni, ya riƙeni da hannu biyu yana dariya muka faɗa saman gadon, tattare kunya nai na ajiye gefe, cikin salonsa daya koyar dani na shiga sumbatarsa fiye da yanda ya koyamin nasa karatun. A take ya rikicemin, nima dai nasan na taro match ai dama, tunda a hannu yake, dan wannan boss ɗin da kuke gani hummm, baisan wasaba ta wannan fannin.
         Duk yanda na dawo kuma ina roƙo da magiya daga ƙarshe bai saurareni ba, sai da ya samu abinda dama yakema ƙulafucin. Daga ƙarshe ya barni da kuka😒 (Kinada matsala ɗiyarga🚴🏼. Lol)
         “Haba my sweet Miemaa na Mai gadon zinarina, kukan ya isa haka Uhimyim, kece kinzo da salon da ban taɓa zaton kin iyaba, ashe kina ɗaukar karatun dai-dai gwargwado”. Cusa kaina nai jikinsa ina ɗan kai masa duka. Ya riƙe hannayen duka yana sakin murmushi mai sauti, “To shikenan nama fasa zuwa dake ni kaɗai zan tafiyata saudian gobe idan ALLAH ya kaimu”. Da sauri na ɗago na kallesa hawaye shaɓe-shaɓe, “Dan ALLAH da gaske kake?”. Goshina ya sumbata yana murmushi, “Idan kin barmin kuka ba”. Saurin share hawayena nayi, yaymin raɗa a cikin kunne. Zabura nai da sauri inaja da baya, “Dan ALLAH ka tausayamin wlhy bazan iyaba”.  Jawoni ya sakeyi jikin nasa yana murmushi, ya sake min raɗa a acikin kunne, hakkane ya sakani yin luff a jikin nasa ina sauke tagwayen ajiyar zuciya, shiko yana aikin shafa bayana alamar lallashi.
        Saida ya tabbatar nabar kukan sannan muka je muka sake wankan, shirin barci mukai muka koma falo, gaba ɗaya ya sake rugurguzar dani da gajiya, ko iya zaman shan fruit ɗin banyiba na kwanta da ɗora kaina a cinyarsa sai barci. Buɗe ido kawai nai da asuba na gammu a kan gadon ɗakinsa.

            Kamar yanda ya faɗa bayan dawowarsa sallar asuba ya sakani muka shirya kaya akwati ɗaya kacal, da dukna ɗauka wasa yake wlhy, sai da naga dai da gaske yake sannan na yarda. Da taimakonsa na gyara gidan, na killace duk abinda ya dace da ya zam a kilkacen, abinda nasan zai iya lalacewa naci na tattaresa ya kaima maigadi da Sadiq da yazo zai kaimu airport. Mamaki bai nema kasheniba sai da muka fito zamu tafi, securitys ɗin hukumarmu na gani nata kaikawo, na kallesa amma sai ya ɗauke kansa alamar baya buƙatar kowace iriyar tambaya, dole naja bakina na tsuke dan a zauna lafiya tunda baya buƙata.
      Wani gida muka fara zuwa, saida muka shiga naga dattijon tsoho da naita son tunano inda na san fuskar amma na kasa hakan, ga kallon da ya kemin shima tsigar jikina har tashi take. Har ƙasa na tsugunna na gaidashi cike da girmamawa.
        Yanda ya amsamin da tsantsar kulawane ya sakani kallonsa, ya sakarmin ƙyaƙyƙyawan murmushi wanda a wajen Mahaifina kawai nasan irinsa, gabana yay wata irin yankewa ya faɗi har ina ɗan dafe ƙirji, “Babana”. Na faɗa a zuciya batare dana san maganar ta fito fili ba. Daga Alhaji babba har Jay kallon Bilkisu sukai.
    Nai saurin zama ƙasa danjin ƙafafuna suna neman gaza ɗaukata, wlhy da tsohon nan yay murmushi sai naga kamar babana ne, sake ɗagowa nai na kalleaa sai naga duk idanunsu a kaina suke. Boss yace “Yaya dai?”. Kai na girgiza masa da sauri alamar babu komai ina sake satar kallon tsohon ta gefen ido.
          “Tashi ki koma saman kujera”. Muryar tsohon ta daki dodon kunnena. “Nanma Yayi Baba” na faɗa muryata naɗan rawa.
     Murmushi yayi da har na iya jinsa daga inda nake, yace, “Amarya lallai kin iya tuwo, naga wannan ɗan dokar ya washe harda kaurin wuya ya ƙara”. Murmushi nayi kaina a ƙasa, sai boss naji yana basa amsa. “Idan yaji haushi gobe muje ɗaurin aurensa Miemaa, idan ya auro matarsa shima saita ringa masa yayi kaurin wuyan”. Dariya naji ya ƙyalƙyale da ita. Haka suka cigaba da tsokanar juna cike da birgewa, kafin suɗan tattauna. Banji ya faɗa masa ainahin mi zamuje yiba, hakan sai ya bani mamaki sosai. Kusan awar mu ɗaya da rabi a gidan sannan muka fito, daga nan sai airport.
                Farin cikine mara misali ya kamani lokacin da nai tozali da Ummu, ashe tare da ita zamu tafi harda takawa, ta rungumeni a jikinta tana yaba yanda nai ɓulɓul kamar yanda ta faɗa. Amintacciyar baiwarta nata mana dariya, banga takawa ba saida zamu shiga jirgi, ‘Masha ALLAH’ na faɗa a raina dan ganin cikakken mutum mai haiba da kwarjinin mulki,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login