Showing 243001 words to 246000 words out of 261165 words
Chapter 82 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
da suka sakko a tsakkiya, yasha gayu cikin farar shadda ƙal harda babbar riga, fuskarsa fayau alamar gyaran fuska yasha a ciki, sai baza ƙamshi suke su duka ukun. Ido muka haɗa da boss mukaima juna murmushi.
Sune suka fara fita, mu kuma muna biye da su. Lokacin har motocin guda uku zuƙa-zuƙa sun gama shigowa, sauran kuma duk sun tsaya a waje alamar bazasu samu waje ba dan habar gidan batacin mota fiye da bakwai. Akwai kuma ta Batool, boss sai na Alhaji babba guda biyu.
Abu-Siddiq ne ya fara fitowa, sai Abbu. Da gudu Anum ta nufi Abbu ta maƙalƙalesa, shima ya tarba ɗiyarsa cike da ɗoki da kewa duk da shekaranjiya suka rabu. Mota ta biyu, Gombiya munaya sai mai martaba Sarki Sameer Saifudden cike da izzarnan tasa da kwarjinin girma da mulki, a take dogarai suka fara jera masa kirari tare da lulluɓe gaban motar har saida ya fito. (ALLAH ya taimaki ɗan autan jimina gagara ɗaukar shaho. Ɗawisu sarkin ado, hadari sa gabanka inda kakeso, kaga dutsen cikin ruwa bakasan ana rana ba, kainuwa dashen ALLAH. Ɗan sarki, jikan sarki, baban sarki kuma insha ALLAHU). Duk da sarauta da mulki na wannan sarki yana girmama duk abinda ya kasance a gabansa, ma'ana wanda yasan ya girmesa a shekaru, dan haka koda Alhaji babba da su jay suka ƙarasa gabansa ƙasa ya rissinar da kai alamar girmama ga Alhaji babba. Dan ya tabbata a haife zai haifesa.
Sosai Alhaji babba yaji daɗin wannan girmamawa har fuskarsa ta bayyana.
Ba'a ɓata lokaci ba akai musu jagora zuwa babban falon baƙi na Alhaji babba da yasha gyara da ƙamshi, an kuma shirya musu abincin karin kumallo.
Gambiya na riƙe dani sai faman taɓa jikina take da tambayata mike damuna. Nidai kaina a ƙasa nake faɗa mata babu komai, kawai gajiyace, da yake ita bata bi su takawaba muna tare da itane sai Ummah ƙarama ke faɗa mata ai ta samu jikane. A take Ummu ta rikice da murna ta rungumeni a jikinta kai kace niɗin jininta ce da gaske. Hakan ya ƙara saka kimarta da mutuncinta gasu Umm-Anum dama duk wanda yake a wajen.
Daga haka mukai zaman yin breakfast, inda Ummu ta saki jikinta sosai kodan dama can ta riga ta saba da Umm-Anum ne oho. Sai dai kowa yaci ya ƙoshi Alhmdllh sannan su Nabeelah suka gyara wajen, bandani da Umm-Anum ta hanani tashi, a cewarta na zauna na huta haka nan.
★★★★
Acan falon baƙi kam Abbu kasa sakewa yay yaci abinci saboda nauyin Alhaji babba da yakeji, hakama takawa da ƙyar yasha haɗaɗɗen shayin da Umm-Anum taima dahu na musamman saboda tasan shi da Abbu suna matuƙar son shayin, dan idan takawa yaje can sosai yake shansa, sai farfesun kan rago da shima yana matuƙar sonsa.
Alhaji babba babu ruwansa, mutum ne mai sakewa da jama'a dajan na ƙasa da shi a jiki, dan haka yayta jansu da hira hardai suka saki jiki da shi, musamman Abbu daya fahimci shine surukin nashi kodan nannoƙewar da yaketa famanyi.
__________
Bayan kammala cin abinci dukanmu muka ɗunguma falon baƙi inda su takawa suke kamar yanda Alhaji babba ya bada umarni, muna gama zama sai ga kira ya shigo wayar boss, tashi yay ya fita, mintuna baifi uku ba ya dawo ya sanar da cewar su Uncle Sulaiman ne. damar shigo da su Alhaji babba ya bada.
Tunda suka shigo falon idona ya sauka akan aunty Shahudah sai kaina ya ɗaure, bawai alamunta na nuna bata tatare da damuwa bane, bakuma shigartace ta bani mamaki ba dan dama nasaba ganin abinda ma yafi hakan, yanda take ta faman shigewa jikin Boss da shi hankalinsama baya kantane ya bani mamaki, inajin lokacin da take faɗa masa wai tanason magana da shi. Banji ya bata amsaba, baima kalleta ba naga yabar inda take ya nufi kusa da Alhaji babba ya zauna.
Harara ta watsomin tare da jan tsaki ta koma kusa da kakarsu ta zauna dan tsallakawa inda boss yake dai babu dama na sani. ɗauke kaina nayi tamkarma ban gantaba, dan ni bata gabana wlhy.
Sai da aka fara buɗe taro da addu'a kamar yanda addini ya koyar, kafin kowa ya fara magana Umm-Anum ta kalli Alhaji babba, cikin girmamawa ta roƙesa dan ALLAH tanason idan da hali a kawo Dad da Uncle Nasir da Alhaji kokino gidan kafin ita dai tace komai, dan tanason ta maimaita dukkan abinda ta sani a gabansu gudun karma ace ta musu ƙazafi.
Kowa kallon Boss yayi, dan ansan dai wannan aikinsane. Kansa ya girgiza yana gyara zamasa, “Bani da wannan damar, domin case ɗinsu babbane, sai dai........” sai kuma yay shiru yana ɗan kallon sashin da Takawa yake. Murmushi sarki Sameer daya fahimci inda ya nufa yayi, baice komaiba ya ɗauka wayarsa ɗaya a cikin wayoyinsa, ɗan danne-danne yay kafin ya ajiye, da alama dai text message ya tura. Babu jimawa kuwa wayarsa tai ƴar ƙara alamun shigowar saƙo. ɗauka yay ya duba, sai kuma ya ajiye yana kallon Boss, shima kallonsa ya keyi, Takawa ya jinjina kai alamar an gama. Murmushi Boss yay yana rissinar da kansa akamar girmamawa da jinjina.
Da ɗan lokacin jira ne Gimbiya tai amfani wajen basu labarin yanda akai su Takawa suka tsinci Umm-Anum, har kaita asibiti da maidata saudia, da maganin da aka nema mata, bata kai ƙarsheba aka iso dasu Dad kowanne a cikin ankwa. Gaba ɗayansu kansu a duƙe sun kasa kallon kowa dake falon saboda kunya, jami'an tsaronma dake a tare dasu basu bada damar kowa ya raɓi inda suke ba, dan cikin kuka Aamilah ta nufi Dad amma sai suka daga mata tsawa, hakama yaron Uncle Nasir autansa hanashi taɓa Abbansa akai, dole ya koma jikin mamansa yana kuka itama tanayi.
Gyaran murya takawa yay, a take falon yay tsitt, sai ƙarar ac kawai data taimakawa cinkushewar falon kakeji, dan falon yay matuƙar cika sosai. Hakan ya saka Jay miƙewa ya tada yaran da ƴammatan yace su koma falon cikin gida. badan sunso ba duk suka miƙe har bily. sai dai kuma Alhaji babba ya buƙaci Bilkisu ta dawo. a cewarsa zaman yanada nasaba da ita ita da Anum.
Dawo mukai muka zauna, dama a raina naji haushi ganin banda Shahudah aka kora sai mu, dan ƙin tashi tayi ita, duk da kuma harda ita ya nuna ɗin.
“Inaga kuka bashi bane ya dace ace munyi a wannan lokacin, haƙuri dayin amfani da lokacin zamuyi domin warware matsalolin dake a tsakkiya”. Takawa ya faɗa a hankali yana kallon kowa dake falon. Hakan yasa kowa ya sake nutsuwa aka sake maida hankali ga Gimbiya data cigaba da bada labarin Umm-Anum, bayyanar cikinta da kuma aurenta da Abbu da haihuwar Anum. Sai a yanzu Dad, Uncle Nasir, Alhaji Kokino sukama fahimci halin da ake ciki. Gaba ɗaya ganin Umm-Anum dajin ƙarin baya
ni game da ita daga bakin Matar sarki ya sakasu diriricewa, sai kallonta suke hawaye na kwarara bisa fuskokinsu. Uncle Nasir ne cikin kuka yace tabbas BA FARKON BA ƘARSHEN, da ace nasan da zuwan wannan rana da ban biyema yaudara ta azzalumai irinku ba Alhaji Sadi, yau gashi babu Abdul-aziz a duniya amma ina cikin tsananin kunya mai muni dako ƙaramin ɗana banason duba, mama kin bada gudunmawa, kema....” yay maganar yana kallon Mama Atika data duƙar da kai ƙasa tana hawaye. “Da baki zama mai hassada da ƙyashi ba da ban tsinta kaina a wannan halinba, da baki zama maison tafi kowaba da ban tsinci kaina a hakaba, tabbas ke uwace mahaifiya a gareni, amma tun daga jiya na farajin nadamar hakan, kaicon rayuwar da take ƙarewa da dana sani da ruɗani. kaicon jin daɗi da arziƙin da sakamakonsa yake zama wuta, inama nine Abdul-aziz...........”
“Bashi bane kai, bakuma zaka taɓa zama shiba azzalumi, mai maida hallaci da butulci”. Umm-Anum ta faɗa a harzuƙe idanunta sun kaɗa sunyi jazur da ɓacin rai.
Numfashi takawa ya sauke yana gyara alƙyabbarsa, yace, “Inaga mai makon wannan kace nace ɗin, mizai hana mutafi kai tsaye akan abinda ya taramu nan. Umm-Anum, mike faruwa?”.
Cikin soyewar zuciya Umm-Anum ta kalli Takawa da yay mata maganar tana haɗiye zafin da takeji a ƙirjinta, kafin ta maida dubanta ga jama'ar falon baki ɗaya. “Basai na maimaita ba kowa yasan wacece ni, ɗiyar wacece, sannan wanene ya kasance mijina a shekarun baya, gwagwarmayar da akasha kafin zamansa wani abu harma ya zama wani abun. Abdul-aziz mutum ne mai matuƙar son ƴan uwansa, bai haɗa sonsu da kowaba hatta ɗan da ya haifa, yanda yake ƙaunarsu al'amarin har tsoro yake bani, dan nidai nasan suɗin da wahala ace suna sonsa kamar haka. Sai dai kuma ban taɓa magana ba, dan hakan ba hurumina baneba. Halayyarsa ta samo asaline kuma da yanda mahaifiyarsa tai masa tarbiyya akan ƙyaunar ƴan uwansa da zuciya ɗaya. Abdul-aziz yanada abokai tunkan yazama wani abu, sai dai babu wanda yafi shaƙuwa da shi kamar Sadi Kokino duk da kuwa ya girmesa da shekaru masu ɗan tazara. tare sukai karatu tamkar yanda ya faɗa min, sannan kuma aminine a garesa bawai aboki kawai ba. Sadi ya taka matuƙar rawa a bikinmu dan a lokacin yafi Abdul-aziz abin hannu, saboda shi yana juya dukiyar da mahaifinsa ya rasu ya bar masane shi da ƙaninsa. Bayan aurenmu nasha zuwa gidansa wajen matarsa, hakama matarsa tana zuwa wajena sosai, a haka muka zama aminai sosai har ALLAH ya ɗaga darajar Abdul-aziz ya zama gwamna, wanda Sadi yana ɗaya daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka akan hakan har Abdul-aziz ya amince duk da baya buƙata. Harga ALLAH siyasar da Abdul-aziz ya shiga bata taɓa kwantamin a rai ba, sai dai nayi shiru ne saboda su Mama maryam da Baba duk sun amince masa, kuma shima naga ya karɓa, Alhaji kokino yana ɗaya daga cikin waɗanda sukaita nunamin muhimmancin mutane irin Abdul-aziz a cikin masu mulkin ƙasarnan, tun ina ganin suna tunzurashine kawai harna yarda dasu na shiga jerin masu masa addu'a. A haka ya kammala shekara huɗun farko a gwamna aka tsaidashi takarar shugaban ƙasa a bazata. Yaso ya bijire a lokacin kam, amma muka tsaya kai da fata ni da Sadi da Nasir da wasu a ƴan uwansu wajen roƙonsa ya tsaya tunda jama'ane suke buƙatar hakan. Haka ya haƙura dan darajar roƙon da mukai masa. An shiga hidimar kamfen da sauransu har dai gwamnati ta tsaya, Abdul-aziz ya zama shugaban ƙasa. Harkokin mulki sun fara zama da ƙafafunsu yanada watani huɗu, dan anyi naɗe-naɗe ga waɗanda ya dace, ciki harda Sadi wanda ya samu muƙami mai tsokar gaske, hakama Alhaji Ali. cikin amincin ALLAH suka fara fiddo ayyuka na cigaban ƙasa wanda ina ɗaya daga mashawartan na cikin gida. Ƴan ƙasa nata murna da nuna jin daɗinsu, sai dai kuma ga Abdul-aziz abubuwa sun fara canjawa, walwalarsa da kuzari duk sun fara raguwa, idan ya zauna sai kagansa zugum tamkar wani wanda abin duniya ya addaba. Abotarsa da Sadi kokino kamar ta fara ja baya, dan yawan zuwa da ya keyi gidan sai naga ya rage daga shi har Ali. A koda yaushe ya dawo gida yana manne da Jawaad kamar wani wanda za'a ƙwace masa shi. Idan na tam
bayesa mike damunsa kuma sai yace dani babu komai, ko yace, “Harka mulkin ƙasarnan sai addu'a Bilkisu, babu komai cikinsa sai baƙin tashin hankali, a zahiri kawai shugaban ƙasa yake amsa sunansa, amma a baɗini ɗaure yake tamau agun waɗanda ke zagaye da shi”. Nakan nema fashin baƙi akan wannan magana a duk sanda ya yita, amma sai dai yay murmushi kawai baya cewa komai. Tun ina ƙoƙarin tambayarsa ma harna daina, sai dai inata masa addu'a. Yana wata na goma da hawa mulki nakasa haƙuri nai masa tambaya akan Sadi da Ali, amsar daya bani itace kawai babu komai. Hakan yasa naji babu daɗi gaskiya. dan harna nuna masa. Mutum ne shi mai matuƙar sauƙin kai ga iyalansa. sai ya zauna ya dinga bani haƙuri damin nasiha akan wani abun barinsa a yanda yake yafi muhimmanci fiye da tonasa. Nanma dai haƙura nai na barsa badan naso hakanba, sai daga bayane na samu Mama maryam da maganar dan abin ya kasa barin zuciyata. A ranar yazo nan gidan, sai dai bansan mi suka tattauna ba, da ya koma gida kuma ban tambayesa komaiba”. Umm-Anum ta sauke numfashi da share hawayen dake gangaro mata, wanda su Bilkisu ma kukan suke a hankali. Ƙafarta mai ciwo taɗan miƙe da cigaba da faɗin,
“A daren wata juma'a dake dai-dai da cikar Abdul-aziz shekara ɗaya da wata ɗaya akan kujerar mulki sai yay baƙi bayan sallar isha'i, tunda naga har ya yarda zaiga baƙin na tabbata masu muhimmanci ne, dan a ƙa'ida shugaban ƙasa baya irin wannan zaman musamman ma da daddare, kuma a cikin gida, gidanma a falonsa. Inason tashi na bisa naga wanene Jawaad dake fama da zazzaɓi ya hanani tashi dan yanata faman kuka, haka na haƙura nai amfani da telephone nai kiran su Wasila dake ɗakinsu, dan suna a tare damune kowa ya sani. Rahma ce ta ɗaga wayan, a cewarta Wasila tayi barci. Umarni na bata akan tasaka akaima baƙin Abdul-aziz abin sha, idan kuma suna buƙatar wani abu sai a haɗa da shi. Ta amsamin da to na katse kiran. Kusan mintuna arba'in da yin haka harma na manta ina jiran shigowarsa ne kawai sai ga Rahma ta shigomin a wani iri. Faɗa na fara mata, dan basa shigowa ɗakinsa inba da wani babban daliliba. Cikin rudin da take ciki tace, Kiyi haƙuri Yayah, wlhy wani abune ya sakani a ruɗani, zomuje ɗakinki kiji dan ALLAH kada Yah Abdul ya shigo. Ban musa mataba nabi bayanta muka fita, ina goye da Jawaad da yay barci a bayana”.
(Yayah wai dan ALLAH mi su Alhaji Sadi keson Yah Abdull yayi ne yaƙi?). Ban ganemba Rahmah miya faru?. (Ruwan da kikace na saka a kaimusu saina iske ma'aikatan sunata faman aiki, kinsan kuma Yaya bason kowa yay masa aiki yake ba wani lokacin, shinefa na ɗauka da kaina nakai ruwan, to saina iske Yaya Nasir, Alhaji Ali da Alhaji Kokino tare da shi, sai dai kafin nai sallama naji wani furuci na Yaya Nasir daya saka bayan na gaishesu na ajiye ruwan na sake laɓewa, dan tundafa na shiga falon kan Yah Abdull a ƙasa alamun ransa a ɓace yake. Kinsan minaji kuwa?) kaina na jinjina mata a lokacin. (Ta cigaba da faɗin Yaya Nasir naji yana faɗin, “Amma dai Abdul-aziz kasan baka isa sanin sirrinmu ba sannan ka bijire mana, bafa wai dan bama sonka bane muke jawoka jikinmu, duk yanda kake tunanin mulkin ƙasarnan yafi ƙarfinka saika ɗaura ɗammarar da muke nuna maka, dan mulkin ƙasarnar baya buƙatar GASKIYARKA ko ƘWAZONKA balle son TALAKAWANKA”. Murmushi Yaya Abdull yayi yana girgiza kansa, cike da ladabi yace, “Yaya dan ALLAH mu ajiye maganarnan, indai nine kusa a ranku abinda naji na gani a can wajen na barsa wlhy, kuma har abada bazan taɓa furtashi ga waniba koda kuwa ace Bilkisu ce ko Mama ko Jawaad. Amma hakan bawai yana nufin zan barku kucigaba da zama akan wannan hakalarba, kuji tsoron ALLAH, karku.........” da sauri Yaya Nasir ya ɗaga masa hannu, “Bama buƙatar ji”. Murmushi Yaya Abdull yay kawai yaɗan girgiza kansa, “Shikenan Yaya na bari, ALLAH ya ganar daku gaskiya idan kunada rabonta. Sai dai gaskiya koda zan haɗe wannan maganar a cikina bazan iya barin Sadi ya cigaba da sarrafa mugan ƙwayoyi ana cutar talakawa naba, dolene kodai ka rufe kamfaninka na sararafa magunguna, kokuma ni nasaka kwamitin bincike a kansa ƙarƙashin hukumar lafiya.......”
a fusace Alhaji Ali (Dad) yace, “Mi kake nufi Abdul!? Kenan zaka iya mana SARAN ƁOYE (littafina na zafafa 2021🤗😋) kenan bayan kasan mu duka nan munada hannun jari a wannan kamfanin hatta da kai kanka ka sakama ɗanka hannun jari zaka aikata hakan kuma?”. “Babu wani maganar Saran Ɓoye Alhaji Ali, inda Saran Ɓoye zan muku da bazan fito na faɗa muku ba ai, sannan da kake maganar na sakama Jay hanun Jari a ciki ALLAH shine shaidata bansan abinda kukeyi a ɓoyeba kenan ai, nidai ABINDA KE CIKIN ZUCIYA ta (Littafin Rano a Zafafa 2021🤗😋) na fito na faɗa muku, dan ALLAH ya kukeson nayi? Ku kune garkuwata, a wannan tafiyar, amma kundawo kuna meman sakani cikin SIRAƊIN RAYUWA (Littafin Huguma a zafafa 2021🤗😋) kuma? Dama kun dafamin bayane domin kuyi amfani dani wajen cimma burinku ko mi? To wlhy! Wlhy! Wlhy!! Kunji sau uku, bazan taɓa cutar da talakawana danna faranta mukuba, bakuma zan taɓa nisanta kaina da UBANGIJINA saboda ku ba, sirrinku kuwa zan riƙe, domin wanda ya halicceku na kallonku, nayi imani da KIBIYAR AJALI.....(Littafin Miss Xoxo na zafafa 2021🤗😋) sulke baya tareta saita gitta wataran, duk abinda yay farko zaiyi ƙarshe. Karku sake zuwamin gida akan wanan maganar daga yau na rufeta, kuma har gaban abada bazata sake tashiba insha ALLAH”. Kallon tsoro suke masa sosai, Alhaji Kokino zaiyi magana Alhaji Ali ya hanashi, shinefa na taho ganin Yaya zai fito). Ajiyar zuciya na sauke da cigaba da kallon Rahmah tamkar a jikinta zan samu amsoshina, fassara maganganunta nake amma babu wadda na iya samawa fassarar data dace, haka na haƙura na barta ta tafi ɗakinsu saboda farkawar da Jawaad yayi baban yaji kukansa ya shigo. Ban tambayesaba a ranar sai bayan sati kusan ɗaya, sai dai ko uffan baice daniba balle na samu amsa, haka na cigaba da masa naci daga ƙarshe yace karna sake damunsa akan abinda bai shafeniba. Ranar haka muka yini ran kowa a ɓace ni da shi”.
Ta sake share hawayenta tana shaƙar numfashi da ƙyar, saida Gambiya ta bata ruwa tasha sannan ta cigaba.
Tun daga wannan lokacin na fahinci abubuwa sun ɗauki zafi tsakanin Abdul-aziz da su Sadi, sai dai yaƙi faɗa min komai duk yanda naso ji,