Showing 234001 words to 237000 words out of 261165 words
Chapter 79 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
muna sonki, idan kika tafi abin zai mana yawa Mom, idan kika tafi wa zamu kalla muji daɗi”. Ya ƙare maganar da kife kansa bisa fuskarta yana cigaba da kuka, shi kansa bai taɓa sanin shi rago bane mai rauni irin haka ba sai a yau, gani yake kaf duniya babu wanda ya kaisa shiga ruɗani da tsananin tashin hankali.
Har Jawaad daya ja motar ya fice daga station ɗin Qaseem nata kuka rungume da Mom. A haka suka isa General hospital, inda suka tadda ƴan jarida da jama'ar gari cike anan ma, har takai da ƙyar ƴan sandan da aka zuba ke control ɗinsu. Burin kowa yaga gawarwaki da mutanen da aka ƙwato wajen su Dad. A haka dai aka samu shiga da Mom ciki da ƙyar. Darajar waɗanda suka kawotan yasa akai mata amsar gaggawa da miƙata wani ɗaki.
Motar su Umm-Anum na shigowa asibitin ana shiga da Mom ciki, gurin a cinkushe yake da mutane, hakan yasa suka rasa hanyar da zasubi su shiga balle susan ta inda zasu fara. Aunty Batool ce tai tunanin kiran Jawaad, dan haka ta ciro wayarta daga bag ta fara nemansa, harta tsinke bai ɗaga ba, bata gajiba ta sake kira, nan ɗinma dai harta tsinken bai ɗagan ba. Kanta taɗan dafe zatai magana sai idanunta suka sauka akan Jawaad dake magana da wasu police su uku da alama suna masa bayani ne akan yanayin da asibitin yake ciki na cikar mutane da ƴan jarida.
“Alhmdllhi ga yayanmu ɗin canma ai”. Dukansu inda take kallo suka kalla, kafin wani ya samu yin magana Anum da Nabeelah suka nufi inda yake, sai dai kafin su ƙarasa aka dakatar dasu a tsawace. Bayani Nabeelah keson ma police ɗin daya tsaidasun amma yaƙi saurarenta, hakan yasa ta fara masa magana da tsiwa dan sun roƙesa amma yana neman cin zarafinsu ma. Hayaniyarsu ta jawo hankalin Jay ya juyo. A bazata yaga ƙannensa, ya ɗan ɗaura hannunsa na dama saman goshinsa da keyi tamkar zai tsage saboda azabar ciwon kai. Da sauri ya kalli police ɗin da suke tare yana nunasu Anum ganin wancan ɗan sandan da suke tare ya ɗaga hannu zai mari Nabeelah amma ta duƙe. “Kaga, cemasa ya barsu suzo”. Amsa masa yay da to, yana nufar inda su Nabeelah suke, yay saurin riƙe hanun ɗan sandan daya sake ɗaga hannu zai mari Nabeelah dan bakinta yaƙi mutuwa saboda haushin baƙar maganar daya faɗa musu dan sunce su ƙannen Jay ne wajensa zasuje. A harzuƙe ɗan sandan ya juya zaiyi magana sai yaga ogansu, saurin gyara yanayinsa yay zai masa bayanin abinda ya faru tsakaninsa da yaran sai yaji ogan nasa yacema su Nabeelah suje wajen Jay ɗin. “Oga kasan mi sukayimin kuwa?”. Murmushi yay masa da ɗan buga kafaɗarsa, “Komi sukai maka kayi haƙuri. ƙanen yallaɓai Jay ne”.
Da kaushin murya Jawaad daya tsare su Nabeelah da rikitattun idanunsa yace, “Miya kawoku nan?”. “Uh...Uhm Yayanmu bamu kaɗai bane, Ummu ce tace a kawota wajen Alhaji babba”. Nabeelah ta bashi amsa tana laɓewa bayan Anum idanunta cike da tsoro.
Da sauri Jay ya hau waige-waige, saiko idanunsa suka sauka akan Batool da su Ummah da suma kallonsu sukeyi. Batare da ya sake cewa komaiba yabar wajen zuwa inda su Batool ɗin suke.
Umm-Anum data rage a mota bata fitoba hango Jay ya nufosu ta fito da ƙyar dan jikinta duk babu daɗi, kallo ɗaya zakaima idanunta kuma kasan tayi kuka sosai, dan sun kumburi sun kumayi jaa.
Sauri riƙeta Jawaad daya ƙaraso yayi, ya taimaka mata ta tsaya akan ƙafafunta sosai tana sauke ajiyar zuciya, “Ummuna miyasa kuka fito? Kallafa ƙafarki ta kumbura?”. Maimakon ta bashi amsa sai tambaya ta jefa masa, “Ina Bilkisu?”. “Amma Umm......” “Ni dai ina yarinyata nace maka?”. Numfashi ya sauke da ɗan ƙarfi yana lumshe idanu sai kuma ya buɗe lokaci ɗaya, “Tana ciki Ummuna, sun saka mata drip ne saboda ta suma acan, amma inama ganin ƙila ta farka yanzun dan tun ɗazun Dr Bello ya sanarmin ta farfaɗo”. “Alhmdllh, babana fa”. Yanzu kam ɗan murmushi ya mata da sumbatar hannunta, “Shiyyasa naga idanunki sun kumbura ko Ummuna, kinyi kuka?”. Kansa ta dungure tana ƴar hararsa, yay murmushi da kama kunnuwansa alamar na tuba.
★★★★
Sun fara shiga ɗakin da aka kwantar da Bilkisu, kamar yanda Jawaad yay hasashe sun iske ta farka, tana zaune jingine da filo wata Nurse na bata abinci da takeci da ƙyar dan warin asibitin yay masifar addabarta, farkawarta amanta biyu saboda warin asibitin, yanzu ma Dr Bello ne da kansa yasa aka kawo mata abincin dan taci tasha magani kafin Jay yazo ya ɗauketa kamar yanda ya sanar masa.
Gaba ɗaya tayi wani zuru-zuru, idanunta sunyi masifar kumbura da ƙanƙancewa, sannan sunyi jajur a ciki. shigowar su Jay yayi dai-dai da zaburarta ta sakko a gadon saboda tahowar amai, Nurse ɗin ta ajiye tray'n abincin da sauri tana ƙoƙarin kamota amma tuni takai toilet. Duk rufa mata baya sukai cikin tashin hankali, sai dai duk a ƙofar bayin sukaja birki, Jay da Nurse ɗin ce kawai suka sami damar shiga. Sosai hankalin Jay ya tashi ganin yanda bily ke yunƙurin amai tamkar zata amayo hanjin cikinta, Nurse ɗin na riƙe da ita tana jera mata sannu da shafa bayanta. Matsowa yay kusa da ita shima ya ruƙo hannunta. Da ƙyar aman ya tsagaita, ya taimaka mata da kansa ta wanke bakinta, sai numfashi take saukewa a wahale, kwantar da ita yay a ƙirjinsa tausayinta mai tsanani yana ratsashi, a ƙasan ransa kuma tunani yake ‘mi taci haka?’.
“Ka kaini gida, banason warin asibitin nan”. Ta faɗa murya can ƙasan maƙoshi tana sake lafewa a jikinsa da shaƙar ƙamshin turarensa da yake ɗan dawo mata da nutsuwarta. Ɗago kanta yay ya saka fuskarta cikin tafukan hannunsa suna kallon juna, “Mi kikaci haka?”. Ya faɗa cikin tashi daskararriyar muryar yana raba idanu akan fuskarta tamkar zai gano abinda ke damunta anan ɗin. Matsawa tai zata sake kwanciya a jikinta tana faɗin, “Banci komaiba, warin asibitinne banaso nidai”.
“Jawaad yaya dai?”. Ummah ƙarama ta faɗa kafin ya samu damar sake tambayar bily.
Da sauri naja baya daga jikinsa dan na manta bafa mu kaɗai bane, bango na dafe saboda jikina babu ƙarfi. Ban iya fahimtar amsar daya bataba dan hankalina baya a garesu, tadai riƙe hannuna ta kamani muka fita sunata jeramin sannu.
Jay da duk damuwa ta sake lulluɓesa ya fita domin son ganin Doctor dan yazo ya duba Bilkisun ko akwai wata matsala data sakata aman ne.
A ƙofar ɗakin sukaci karo da Dr Bello da Nurse ɗin dake tare da bilyn, da alama itace taje tai kiransa. Fuskar Dr Bello washe da murmushi ya miƙama Jay hannu, “Dadyn baby ai bansan ka shigoba ma”. Duk da Jay bai fahimci sunan da yay kiransa da shiba sai yaɗan saki fuska kaɗan amma ba murmushi yayi ba, yadai sassauta ta daga cinkushen da take. Doctor bai gajiyaba ya sake faɗin, “Dama sister ce ke sanarmin madam na amai, wannan babyn da alama soja ne, dan nakula zai wajiga madam da yawa tun yana ɗan ficit”. Yanzunkam dai sosai Jay ya kallesa da alamar tambaya, sai dai ya gaza cemasa komai. Lura da hakan da Dr Bello yayne ya sakashi yin murmushi suka ƙarasa shiga ɗakin da Bily take, inda su Umm-Anum suka zagayeta sunata jera mata sannu, kanta na'akan cinyar Ummah babba.
Sai da ya gaisa da su sannan yayma bilyn sannu, kanta taɗan ɗaga masa kawai alamar amsawa, ya sake kallonta da murmushi ganin tanata faman rufe hannci, juyawa yay ya sake kallon Jay dake tsaye hannayensa duka a aljihu shima yana kallon bilyn. “Congratulations dear Friend, madam na ɗauke da babien mu ɗan sati shida. Ma'ana tana ɗauke da ciki ɗan wata ɗaya da sati biyu”.
Babu shiri Bily ta janye hannunta daga saman hanci tana waro idanu waje, ganin duk yanda suka zuba mata ido suna murmushi yasa taji kunya, saurin juya baya tayi taja gyalen Ummah babba ta rufe fuskarta ƙirjinta na wata irin bugawa da sauri-sauri.
Su Ummah kam fuskokinsu washe da murmushi sunata jerama UBANGIJI godiya da kirari, gaba ɗaya sai damuwar da suka yini da ita ta ɓace ɓat. Ubangayya da tunda aka fara cakwakiyar nan babu mai cewa yaga haƙorinsa a waje a take ya saki wani lallausan murmushi yana mai lumshe idanu, duk wata damuwarsa sai yaji ta gudu, farin ciki ya mamaye gurbinta. Dariyar su Ummah ce ta sakashi buɗe lumsassun idanunsa dake jajur, yay murmushi a karo na biyu yana girgiza kansa ganin iya shegen da Anuwar keyi shi da Anum da Nabeelah. Ya dage sai rawa yake yana waƙar larabawa shi a dole yayi ɗa ko ƴa, yayinda Anum da Nabeelah ke tayashi.
Cikin dariya Ummah ƙarama tace, “Yarona dama haka kake da iya shege ina ganinka wani ustazu?”. Umm-Anum dake murmushi tana kallon Bily da duk abin nan da ake taƙi kallon kowa tace, “Kaɗanma kika gani indai Anuwar ne, dama can Ustaz ɗin da babu Ustazai ne”. Dariya su Ummah da Batool da Dr Bello suka sanya, Jay dai murmushine har yanzu a saman fuskarsa, kunyar iyayensa ta sakashi dakewa abinsa yanata dai kallon bilyn ta ƙasan ido.
Aunty Batool tace, “Lallai ta maganar Doctor babyn nan namu soja ne, inba soja ba wannan gumurzu da akashawo amma ko gezau baiyiba saima nuna kansa da yayi wa duniya”. Sosai nanma suka sanya dariya, Dr Bello yace, “Gaskiyarki Sister kam, ALLAH dai ya inganta, kema saiki daure kiyi aure ki samo mana namu”. Duk kallon Doctor sukai banda Jay da Bilkisu dake ɓoye, Batool ta zuba masa harara. Shiko murmushi yayi abinsa yana sosa ƙeya waishi yaji kunyar su Ummah. Cike da tsokana Anuwar yace, “Su Aunty Batool kodai-kodai gidan Doctor zamu ɓulla ne?”. Duka takai masa ya kauce yana dariya, Doctor Bello ya kama hannun Anuwar yana faɗin, “Yauwa ɗan ƙanina tayani yaɗa manufa”. Yay maganar suna ficewa daga ɗakin.
“A to mukam wannan indai na ƙwaraine ai bashi zamuyi Batool”. Umm-Anum ta faɗa tana kallon Batool ɗin. Ƙasa tai da kanta batace komaiba. Ummah ƙarama tace, “Yayah wlhy bansan ko Dr Bello da wata matsalaba, mutum kirkine ɗan manyan mutane, sai dai babansane ɗan rigima, amma shima bawai ta ashsha ba”. “Ato Alhmdllh, bara nazo na fara shirin aurar da ɗiya kenan”. Murna Nabeelah da Anum suka fara, ita dai Ummah babba batace komaiba, hakama Jay uffan baice ba, yayi kamarma baya a ɗakinne, idonsa gaba ɗaya yana akan motsin matarsa.
★★★★★★★
Koda suka baro ɗakin da bily take da sallama daga Doctor gaba ɗaya sai suka nufi ɗakin da aka kai Alhaji babba, daga shi sai baba maigadi a ɗakin, jikin Umm-Anum har rawa yake, sai da Batool ta riƙeta, cike da sassarfa ta ƙarasa gaban gadon da Alhaji babba ke a ƙwance an saka masa na'urar taimakon numfashi, sosai jikinta ke ɓari, ta durƙushe ƙasa tana kamo hannunta cikin nasa da fashewa da kuka tana kiran sunansa. “Baba kaine haka? ka tashi baba kaga BILKEESUN ka, nadawo gareku baba, baba ka buɗe idanunka ka kalleni dan ALLAH kozanji sassauci babana farin cikina” ta ƙare maganar da ɗaura kanta a gefen hannunsa tana kuka mai tsuma rai. Suma su Ummah hawayen sukeyi har Bily, Batool da Nabeelah da Anum. Anuwar ma hannu ya saka ya ɗauke nasa ƙananun hawayen tare da ƙarasawa ya durƙusa ta ɗayen gefen kakan nasa daya fara gani a yau karan farko na rayuwarsa, Anum tazo kusa dashi ta tsugunna itama tana ɗaura hannunta akan na Anuwar dake riƙe dana Alhaji babba. Jawaad dai yana kallonsu, sai dai bazaka taɓa fahimtar yanayinsa ba, kamilar fuskarsa ta shanye komai.
A hakanli Alhaji babba yaɗan motsa hannunsa dake riƙe a cikin na Umm-Anum, saurin ɗagowa tai tana kallon hannun, ya sake motsashi a karo na biyu tare da kansa. tsitt ɗakin yay duk suka zuba masa ido. Sake motsawa yay fiye dana farko, sai kuma ya buɗe idanunsa a hankali ya sake maidawa ya rufe saboda nauyin da sukai masa, sake buɗewar yayi a karo na biyu, dishi-dishi ya fara hango Jawaad dake tsaye daga can ƙofar ɗakin yana facing nashi, ya ɗan kafesa da kallo tamkar dai yanason gano wanene?. takowa Jay yay a hankali zuwa gaban gadon, ya tsaya kusa da Umm-Anum tare da ɗan ranƙwafawa yanama Alhaji babba murmushi, hannu ya saka da kansa ya cire masa na'urar da aka saka masa. cikin magana a hankali yace, “Tsoho mairan ƙarfe!”.
Karan farko Alhaji babba yay wani ɗan murmushi kaɗan da sake motsa hannunsa sai ya jisu duka biyu an riƙe. “Babah!” Umm-Anum ta kira sunansa cikin sanyin murya. Cikin wata irin faɗuwar gaba Alhaji babba ya juya saitin inda yaji muryar da bazai taɓa mantawaba a rayuwarsa, to kodai mafarki yakeyine har yanzun? Ya ayyana a ransa yana ware idanu akan Umm-Anum dake kallonsa tana murmushi da hawaye.
Ya mata kallon kusan minti ɗaya kafin ya sake juyowa ya kalli Jay, sai kuma ya kalli Anuwar da Anum, ya sake maidawa ya kalli Ummah ƙarama da babba da Batool, Bilkisu da Nabeelah, cike da ƙarfin hali ya yunƙura zai tashi zaune dan ba'a ƙaramin ruɗani ya tsinci kansaba. Saurin riƙesa Jay yayi yana girgiza masa kai. Alhaji babba ya kalesa cikin muryar dake nuna bashi da lafiya yace, “Jawaad mafarkin dana sabane ko? Yo inba mafarkiba a ina nikam zanga mahaifiyarka ido da ido irin haka? Dan ALLAH kaga karka tadani a barcin nan barni nayi tayi ko ALLAH zaisa itama Rahmah da Maryam da Amina da Adamu zasuzo gareni duk mu haɗu anan”.
“Baba ba mafarki ka ke ba, Bilkisun ka ce a gaske gabanka, nice na dawo gareku, ni ce ban mutuba baba”. Umm-Anum ta faɗa tana rushewa da kuka. Ai yanzunkam babuma wanda yaga sanda Alhaji babba ya tashi dingangan zaune yana riƙo hannun Umm-Anum cikin nasa duka, jikinsa sai rawa yakeyi, hannunsa ya ɗaura saman idonsa ya murza, ya kai kuma kan fuskarta ya shafa. Tabbas ba mafarki yakeba Bilkisun sa ce a gabansa, bilkisun daya rasa kusan shekaru ashirin dashida, bilkisun daya fidda rai da gani a wannan duniyar dukda yana tsananin ƙwaɗayin hakan. “Bilkisu dama kina raye?”. ya faɗa da tsananin rawar murya.
“Ina raye baba, ganima ALLAH ya ƙaddara sake haɗuwarmu, na godema UBANGIJINA daya saka ka kasance mai tsahon ran da zan dawo na tadda, da ace na dawo baka raye bazan taɓa daina yima mutanen nan munanan addu'oi ba har randa numfashina zai yanke”. Fashewa Alhaji babba yay da kuka, ya kamo kan Umm-Anum ya ɗaura saman cinyarsa ya rungume yana sake fashewa da kuka mai ban tausayi da tsuma rai.
Da ƙyar Jay da Doctor suka samu damar lallashin Umm-Anum da Alhaji babba, harma dasu Ummah dasu Bilkisu, sai dai fa Alhaji babba ya tubure akan ya warke a sallamesa ya tafi gida, anyi lallashin duniya yace sam baisan wannanba wlhy shifa bazai kwana a asibitin nanba koma mi za'ayi.
Ganin ya rikice musu harda hawaye Jay yace Doctor ya basu sallama kawai, sai su sami likitan dazai dinga zuwa gida yana dubashi babu damuwa. badan Doctor yasoba ya basu sallama.
Jay da Anuwar ne suka kama Alhaji babba aka kaisa har mota, yayinda itama Ummah ƙarama ke riƙe da Bilkisu da keta dauriya da ƙarfafa jikinta dukda batajin daɗinsa sam, sai dai ƙasan ranta wani irin farin ciki takeyi da barin asibitin da zasuyi. Motar ta musu kaɗan, dan haka suka shiga ta Aliyu da suka iso asibitin babu jimawa suma dan an ƙaro jami'an tsaro cikin asibitin saboda mutane dake neman kawo ruɗani, acewarsu sunason suga gawawwakin da waɗanda aka samo da rai ko akwai ƴan uwansu a cikinsu.
Jay bai bisuba, cikin asibitin ya sake komawa inda Qaseem da Salman ke tare da Mom wadda ta farfaɗo amma sun mata allurar barci mai ƙarfi dan jininta ya hau sosai, Doctor ma yace badan ALLAH ya taƙaita mata wahalaba irin wannan faɗuwar da tayi zai iya sakawa ta kamu da paralysis. Sai da suka ɗanyi magana da Qaseem da shi kansa idan da za'a bashi gadon an taimakesa sannan Jay ya fito. Daya fito ɗinma wajen su Jabeer ya tsaya sukai magana sannan ya amshi key ɗin mashin ɗin ɗaya daga cikin jami'insu yabi bayan su Alhaji Babba.
_____________________
Dr Tayyeb Hospital
_________________________
Shahudah dai suma tai a wajen, sai da cikin ƴan matan family ɗin wata tai ƙarfin halin shafa mata ruwa sannan ta kawo numfashi, hakama matar Uncle Nasir ita sai dama aka bata gado, ƴaƴansa nata kuka maiban tausayi da saka zukatan mai kallonsu rauni. Kosu Uncle Sulaiman sai da suka share hawaye dan tsananin tashin hankali. A yanzun kam sun fahimci zaman asibitin sam bazai yuwu a garesuba, dan haka suka tattara inasu-inasu suka nufi gida, dan anma hana kowa shiga wajen Mama Badiyya dama, ba'ason ai mata wata hayaniya ko kaɗan.
Sun iso gida suka iske waɗanda suka bari anan cikin matsanancin tashin hankali suma, ciki harda Mama Atika da tafi kowa shiga ruɗani ganin halin da babba ɗanta yake a ciki da surukinta, tayi bala'in yin wujiga-wujiga da ita tamkar wata taɓaɓɓiya, dan sai surutai take, fitsari kuwa ba'a magana, tayisa a zane sau babu adadadi batare da tasan yanama zuba ba. Sai da ƴan asibiti suka isone suka fargar da ita halin da take ciki.
Tabbas bayyana irin kalar ruɗanin da wannan ahali suke ciki ɓata lokacine, sai dai na bama kowa gari ya ƙiyasta a ransa. Gashi an turo jami'an tsaro sun zagaye sashen Uncle Nasir ɗin babu mai shiga kamar yanda akaima gidan Dad shima.