Showing 177001 words to 180000 words out of 261165 words
Chapter 60 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
falon ya saka ƙirjinsa wani irin mahaukacin bugu irin wanda tunda yake a rayuwarsa zai iya rantsuwa bai taɓa jiba, ya buɗe idanunsa a hankali zuciyarsa na wani irin masifaffen tsitstsinkewa. Akan Bilkisu da Anum da suka zauna gefen Abbun su Anuwar ya fara saukewa, ya maida kan Ummu da itama ta zauna a kujerar da takawa yake zaune, sai Anuwar dake tsaye tamkar gunki idanu a ware yana kallon Jawaad, da alama dai yayi sumar tsayene na bazata. Ya maida kallonsa ga dattijuwar mace data juya masa baya suna gaisawa da takawa, tana sanye da baƙar abaya ta naɗe kanta irin naɗin larabawa. Jiyay gaba ɗaya jinin jikinsa na wani bada zuuuu!! Zuuuu! Zuuuu, bazai iya daurewa har saita juyo garesa ba, a matuƙar ɗokance yake da son ganinta duk da cike yake da fargaba da tsoron kar hasashensu ya zama kuskurene kuma ba itaɗin bace ba. Ya miƙe a hankali ƙafafunsa na harharɗewa, yayinda bugun zuciyarsa da fitar numfarfashisa ke fita a matuƙar guje. Miƙewarsa tai daidai da miƙewar Umm-Anum itama fuskarta ɗauke da murmushi sun gama gaisawa da takawa tanason komawa kusa da mijinta ta zauna sai a ɗora firar, dauriya kawai take itama tana danne halin da take ciki. Lokaci ɗaya sukai tsaiii! Suna kallon juna, kallo mai wahalar fassara ga ma'abocin yinsa da wanda ke kallo, kallo mai saka razani da firgici da ban mamaki, kallo mai ɗarsa tausayi ga duk wanda idanunsa zai iya sauka a kansu shima.
Ƙafafun Jawaad sun kasa ɗaukar gangar jikinsa, Mahaifiya ta wuce gaban wasa, jini ba ƙarya bane musamman irin na uwa da ƴaƴa, ko shekara dubu yay baigantaba saiya gane, shekarun data barsa bazai yuwu ya iya manta fuskartaba musamman da ya zam yana kallonta a hoto a koda yaushe, manyanta kawai da ƙiba da haske ta ƙara na alamun girma da jin daɗi. Ƙasa ya zube bisa gwiwoyinsa jikinsa na rawa, kansa na wani irin Masifaffen sara masa tamkar zai tsage gida biyu, cikin rawar harshe da kwararowar hawaye bisa kumatunsa yace, “Ummuna!”.
Umm-Anum dake tsaye cikin mawuyacin hali da ruɗanin zuciya da gangar jiki idanunta kafe akan Jawaad ko ƙyaftawa batayi ta ɗaga hannu da ƙyar tana mai nuna shi da yatsanta manuniya jikinta na wani irin rawa, mai kama da Anuwar ɗinta! Wanene shi? Da ga ina yake? Ya akai kamaninsa da Anuwar ɗinta?! Mutum ɗaya tasan duk duniya yana kiranta da wannan sunan, sai dai wanene? A ina yake? A yaushe ne kuma?. Bakinta rawa yake amma ta gaza furta komai, sai tai luuuu baya zata faɗi.
Wani irin wawan miƙewa Jawaad yayi ya tarota jikinsa, dai dai da zaburowar Anuwar shima yana ƙoƙarin tarota, sai kawai hanunsu ya haɗe waje guda suka tallafota a tare......
Zumbur suma ƴan falon duk suka miƙe tsaye, banda Takawa kawai da ya dake abinsa duk da shima jikin nasa duk yay saƙwat. Da ga can Anum ta ƙwala kiran sunanta cikin kukan da takeyi tun farkon durƙushewar Jay a gaban Umm-Anum. Bilkisu ma hawayen takeyi.
Abin tausayi da tashin hankali daga Jawaad har Anuwar kuka suke suna faman girgiza Umm-Anum da kiranta, Jay na faɗin, “Ummuna! Ummuna Please, Ummuna ki buɗe idanunki ki ganni, nine Jay-p ɗinku ke da Abbah, karkice ba hakaba dan ALLAH, dan ALLAH Ummuna zuciyata zata buga ki tashi ki ganni kicemin da gaske kece ba gizo idanuna keyiba, ba mafarkin dana sabayi bane, ba tunain danake dulmiyawa bane, ki tabbatarmin a zahirance kece tare dani Ummuna, kitashi kiga Jay-p ɗinku yazam Jay-p ɗin gaskiya, Dan ALLAH Ummuna karkice baki ganeniba karkice baki sanibaaaaa”. Yaja (a) ɗin ƙarshe da fashe da wanu irin kuka maiban tausayi da tsuma zuciya yana mai kife fuskarsa saman tata.
Anuwar shima kukan yake yana faɗin, “Umm-Anum ki tashi da ALLAH, ki tashi ki faɗamin shiɗin ɗan uwanmu ne da gaske, wlhy inajin ƙaunarsa mai zafi a raina irin wadda ban taɓama wani mahaluki irinta ba, jinake tamkar zan iya rasa numfashina sabida shi, Umm-Anum dan ALLAH kice shiɗin jininmu ne Ummu”.
Duk wanda yace baiyi hawayeba a parlorn nan ƙarya yake, hatta da Takawa saida yasa handkherchief ya tsane hawaye, Abbun su Anuwar ya saka gefen mayafinsa da larabawa ke sakawa saman kai ya share nasa hawayen, kafin ya taka a hankali shima ya durƙusa a gabansu ya ɗago kawunansu ya rungume a ƙirjinsa yana shafa kansu, fuskarsa ɗauke daɗan murmushi ga ƙwalla da suka sake cika idanunsa, a hankali yakai bakinsa saman kan Jawaad ya sumbata, kafin ya maida akan Anuwar shima ya sumbata. Cikin harshen turanci ya shiga lallashinsu da kalamai masu sanyi. Suna cikin haka Ambulance ɗin da Abbu-Siddiq ya kira asibiti ta iso, mata ma'aikatan asibitine suka shigo su huɗu, da taimakon su Jawaad da har yanzu jikinsa ke a sanyaye suka kamata aka ɗaura a gadon gungura mara lafiya, ma'aikatan asibitinne suka fita da ita, Jawaad da Anuwar suka take musu baya suma. Bilkisu da Anum ma miƙewa sukai da sauri sukabi bayansu. Duk miƙewa suma sukai domin binsu, amma sai Abbun Anuwar yace Abu-Siddiq ya maida su Takawa masauki su huta. Noƙewa Ummu tayi akan ita dai zatabi bayansu itama. Takawa baice komaiba suka fito gaba ɗaya, su Jawaad harsun wuce, su Bilkisu ma basu iskesu ba suna tsaye suna jiran fitowarsu Ummu, Ummu, Aunty Mahfuzah, Bilkisu, Anum suka shiga mota ɗaya suka bisu. Abbunsu Anuwar kuma dasu Takawa suma suka tafi a mota guda.
Da taimakon su Jay da suma suke a motar Ambulance ɗin aka fidda Umm-Anum zuwa cikin asibitin, abinka da inda kasan darajar ɗan adam, dan danan likitoci sukai mata caa da taimakon gaggawa, yayinda Anuwar da Jawaad ke tsaye aƙofar ɗakin da aka shiga da ita kowanne cike da tsantsar damuwa, kaɗan-kaɗan saisu ɗago su kalli juna, sai dai kowanne ya kasa magana ma ɗan uwansa ko sau ɗaya, dan harsunansu sun musu nauyi, burinsu kawai suga farfaɗowar rabin numfashinsu masoyiyar zuciyarsu mahaifiyarsu abin alfaharin kowa da tinƙaho.
A wannan halin su Bilkisu suka ƙariso suka iskesu, da ga ita har Anum idanunsu sunyi luhu-luhu saboda kuka, Ummu duk tana riƙe da hannayensu. Idanu kawai Jay ya zuba musu amma bai iya cewa komaiba, sai Anuwar ne ya bama Ummu amsar tambayar da tayi akan ina Umm-Anum ɗin. Isowar su Abbu suma ya saka aka basu wajen zama, domin su Abbu sun kasance zuri'a sananniya mai daraja a ƙasar saudia musamman cikin birnin makka, nagartattun malamaine hafizan Al-Qur'ani mai girma, sunada manyan makarantu na addini da cibiyoyin magunan musulunci da suke badawa da sunansu ya zagaye lungu da saƙon birnin na makka da kewaye da saudia ke alfahari dasu a ɓangarori da dama na ƙasar.
Anuwar da Jawaad dai sun kasa zama, sai da Abbu ya kamosu duk ya zaunar tare da zama tsakkiyarsu. Jawaad shi kaɗai yasan irin matsanancin ciwon da kansa ke masa, amma ya daure ya jure, sai dai ta jijiyar kansa data mimmiƙene kawai zaka iya fahimtar yana cikin mawuyacin hali. Hannu Abbu ya ɗaura akan Jawaad ɗin daya kwantar da bayansa jikin kujera ya lumshe idanunsa, hakan ya saka shi buɗe idanun da suke jajur ainun, addu'a ya fara karantowa yana tofa masa a kan nasa, Jay ya maida idanunsa ya lumshe jirin da yakeji na ƙara ƙarfi a cikin idanunsa. Luuuu ya kwanto jikin Abbu alamar shima dai koya suman kokuma wani abun dai daban, saurin ɗagosa Abbu yay yana girgizashi, amma ina numfashinsa yay ɗaf daga ƙirjinsa. Saurin miƙewa Anuwar yay shima jiki na rawa, hakanne ya jawo hankalin sauran suka fahimci abinda ke faruwa. Bilkisu ta cusa kanta cikin cinyoyinta ta sake fashewa da kuka mai tsuma rai. Hakama Anum ƙanƙame Ummu tai ta fashe da kuka tana faɗin, “Ummu shima yayi kamar na Umm-Anum”. Rungumesu Ummu tayi a jikinta daga ita har Bilkisu itama tana ƙoƙarin haɗiye hawayenta, ‘wannan wane irin tashin hankaline haka?’. Ta faɗa a ranta cike da tausayin wannan ahali.
A take shima Jawaad aka ɗaukesa zuwa ɗakin kusa da Umm-Anum aka shiga bashi taimakon gaggawa domin ceto numfashinsa.
★★★★★★
Saida sukai zaman awanni biyu cikin kuka da tashin hankaki sannan suka sami labarin farfaɗowar su, atake duk murmushi ya suɓuce musu, Bily ta saka gyalenta itama tana share hawaye kamar yanda Anum keta faman yi. Ba'a basu damar shiga ba dan duk ance suna buƙatar samun hutu musamman ma Umm-Anum da jikinta ya manyanta.
Da wannan albishir ɗin suka sami ƙwarin gwiwar tafiya yin sallar la'asar da lokacinta yayi, kowa ya shiga miƙama UBANGIJIN al'arshi kukansa dan shine masanin duk wani sirri dake a binne tare da rahama ga bayin da aka zalunta kuma suka jurema jarabawar rayuwa batare da nuna ƙosawarsu ba. Sosai yin sallar ya ɗan basu ƙwarin gwiwa suka dawo asibitin, Abbu ya roƙa takawa akan suje su huta haka nan tunda ance sun farfaɗo ai. Daƙyar Ummu ta yarda, Bilkisu kam ƙasa tai da kai tana hawaye alamar batason tafiya. Takawa yay murmushi da yima Ummu alamar a barta anan ɗin da ido.
Hakan kuwa akayi, bayan sun shiga sun duba su Jawaad da Umm-Anum suka tafi akabar Bilkisu da Anum da Anuwar anan, sai Aunty Mahfuzah, takawa kuma da Ummu da Amintacciyar baiwar Ummu da Abu-Siddiq suka tafi, sai Anuwar da Abbu suma suna nan. Suma dai bayan wucewar su takawan duk sai suka shiga suka dubasu suka sake fitowa suka zauna zaman jiran farkawarsu da musu addu'oi.
Kasa haƙuri Abbun su Anuwar yayi yaɗan farama Bilkisu wasu tambayiyi game da Jawaad da ita kanta, danshi tabbas yana kallon wasu abubuwan na Bilkisu masu mugun kamanceceniya da Umm-Anum, tafiya, murmushi dama abubuwa da dama tun a wancan zuwan nata, hakan sai yasa kansa ya ƙara kullewa ya shiga tambayarta ko auren zuminci akai musu ita da Jawaad?. kanta a ƙasa ta bashi amsa da “A'a”. Ya tisa (a'a) ɗin nan ta bilkisu a ransa yafi sau dubu, dan shidai gaskiya bai yardaba akwai abinda ita Bilkisun bata saniba maybe, musamman yanda yake mata tambayoyin da amsoshin da take bashi. Anuwar dai da Anum da Aunty Mahfuzah na binsu da kallone da saurarensu.
A haka lokacin sallar magriba yayi itama suka tashi suka gabarta, sun dawone suka iske Jawaad ya tashi, Abbu ne yace Bilkisu kawai ce zata shiga, badan Anuwar da Anum sunso ba suka haƙura.
Tunda na shigo ɗakin idanuna a kansa suke, shiko nasa a lumshe tamkar mai barci har yanzun, yana kwance ne, amma yanzu an ɗago gadon sama ta wajen kanshi yanda kwanciyar ta bada style kamar yana a zaune. Na cigaba da takawa a hankali na ƙarasa garesa, Zama nayi dai-dai saitin fuskarsa tare da ranƙwafawa na sumbaci goshinsa, hawayen da suka cikamin ido suka ziraro suka ɗiga akan fuskarsa. Buɗe idanun yayi a hankali tare da riƙo hannuna cikin nashi, kallon cikin ido mukaima juna, wasu hawayen suka sake silalo mani na tausayinsa, abinda ban taɓa gani daga garesaba sai yau, (kuka) Boss ne gwanin dauriya da shanye abu yay kuka, kai mahaifiya dabance a rayuwar kowanne ɗan adam, mahaifiya tafi gaban wasa, mahaifiya mutum mafi daraja sama ga komai ga ƴaƴa. Na ayyana a raina ina matsawa jikinsa na kwantar da kaina a ƙirjinsa ina fashewa da kuka, dan nima haka kawai sai naji ƙaunar tawa mahaifiyar da kewarta, Innata gatana, innata abar alfaharina da tinƙahona harma da taƙama a dukkan daƙiƙa ta rayuwata.
Jawaad da shima wasu zafafan hawayen da babu zato suka silalo masa ya ɗaura duka hannayensa saman bayanta ya rungumeta a jikinsa. Sunkai tsahon lokaci Bilkisu na kukan da shashsheka ta kasa ɓoyesa, Jawaad na kukan zuci da hawaye masu zafi da raɗaɗi. Buɗe ƙofar da akaine ya saka Bilkisu saurin ɗagowa dan ta zata su Abbu ne, shima babu musu ya saketa ta miƙe yana share hawayensa, itama nata ta shiga sharewa da bakin mayafin jallabiyar. Nurse ɗin daya shigo ya nema afuwarsu, dan ya jima yana sallama da knocking babu amsa, hakanne ya sakashi shigowa direct, dan tun daga can waje ta cctv'n da suke amfani dashi na ganin duk wanda ke a sashen da suke kula da shi ya gano ruwan da suka sakama Jay ya ƙare har jininsa ya fara zuƙa yana komawa cikin robar ruwan, shikam sam baima luraba saida Nurse ɗin ya kama hannunsa yana cirewa sannan suka gani shi da Bilkisu. Idanu taɗan ware waje na alamar mamaki, shikam sai ya lumshe nasa idanun ya maida bayansa ya jinginar kamar yanda yake da.
Nurse ya kammala komai sannan ya fita su Abbu suka shigo duba Jawaad ɗin. Sannu sukaita jera masa da addu'oi, shi kuma yana amsa musu da kai dan harshensa ya masa nauyi sosai har yanzu baijin zai iya furta wata kalma ga kowa idan ba Umm-Anun ba. A rikice Nurse ɗin dake tare da Umm-Anun ta shigo tana sanar musu ta farka itama amma bata cikin hayyacinta.
Rige-rigen fita aka dingayi a tsakaninsu, dan hatta da Jay ba'a barsa a baya ba shima. Tashin hankali kenan, yanda Nurse kusan biyar ke riƙe da Umm-Anum zai baka matuƙar tausayi, a take duk suka rufu a kanta banda Abbu dake tsaye kawai yana kallon yanayin nata cike da nazari, ajiyar zuciya ya sauke kafin yayma Nurse ɗin Umarni akan su sallamesu zasu koma gidan ciwon nata addu'a yake buƙata. Basu musaba dan sunsan shiɗin babban likitane mai bada magungunan musulunci wanda akema ɗakko marasa lafiya daga wata ƙasa mai nisa a kawo garesa balle matarsa kuma.
A take aka shirya musu maidata gida. Hankalin Jawaad yay matuƙar sake tashi ganin mahaifiyarsa ta koma cikin asalin halin hauka kamar yanda tabar gida a wancan lokacin, su kansu su Anuwar ɗin hankalinsu a tashe yake dan basu taɓa ganin Ummunsu a wannan irin halinba, sundai san tanada wani rashin lafiya da takan fita hayyacinta lokaci-lokaci amma basu taɓa sanin dalilin motsawar ciwon nataba suma, da kuma Abbu ya dage kanta saita dawo normal kamilar mace. Anuwar yasha tambayar Abbu amma bai taɓa sanar masa komaiba sai yace lokaci na zuwa da zai sani.
Da isarsu gida Abu-Siddiq da Abbu suka rufi kan Umm-Anum da karatun Al-Qur'ani mai tsarki, hakanne ya ja hankali su Jawaad suma duk sai suka ɗaura al'awa suka zauna sunayi su duka har Bilkisu da Anum, kai harma da ama'aikatan gidan da Aunty Mahfuzah da yaranta itama dukda ƙanana ne ba'a barsu a baya ba. A hankali Umm-Anum ta fara lafawa daga bige-bigen da takeyi, ta buɗe idanunta dake jajur tamkar garwashin wutane a cikinsu tana binsu da kallo. Ba ƙaramin tsorata idanunta suka basu ba, amma hakan baisa sun dakataba suka cigaba, maidawa tai ta sake lumshewa tare da kwanciya jikinta na wani irin masifar rawa, sai kuma ta fashe da matsanancin kuka. Turaren magani Abbu ya tashi ya kunna, hayaƙi ya fara fita yana baje ɗakin. Wani irin gunjin kuka ta fara maiban tsoro tana magana cikin muryar da dagaji kasan ba tata bace. “Ku daina ƙonamu, dan ko zaku shekara dubu kuna ƙonamu bazamu bartaba, zamu gama jiyyane a jikinta batare da mun bar aikinmu ba, alƙawarine rubutacce zamu kasance da ita har ƙarshen rayuwarta, dan haka kuma bar wahalar da kanku babu inda zamuje, bazamu taɓa saɓama shugabanmu ba har abada dan shima bai taɓa saɓa manaba bisa umarninmu...!!”. Sam su Abbu basu sauraresuba suka cigaba da abinda sukeyi, hakama su Anuwar basu fasa nasu karatunba, yayinda Abbu ya cigaba da zuba magani kala-kala na hayaƙi a cikin Burne. Tun suna ihu har suka koma kuka da magiyar a daina ƙonasu kar'a halakasu suba laifinsu bane sakasu akayi. Zuwa wani lokaci kuma sai tayi shiru sai uwar zufa take tamkar an jiƙeta da ruwan zafi. Abbu bai dakata da abinda yakeba har saida yaji ta kirayi sunansa cikin sanyin murya. Ajiye abinda ke hannunsa yayi ya ƙarasa gareta ya ɗago, faɗawa tai jikinsa ta fashe da kuka mai ban tausayi. “Abu-Anuwar yau cikin mafarki naga wani abu maiban mamaki da al'ajabi, naga mai kama da Anuwar wanda tabbas inada alaƙa dashi”.
Tashi Abu-Siddiq yay ya fita dan ya basu waje.
Abbu dake shafa bayan Umm-Anum yana murmushi yace, “Ba mafarki kikeba zahiri ne”. Zumbur ta miƙe zaune tana kallonsa, sai kuma tai saurin dafe kanta da taji ya sara mata. Kamata yay ya kwantar yana faɗin, “Kiyi haƙuri ki kwanta ki huta zuwa anjima ko da safe idan ALLAH ya kaimu sai muyi magana, Alhmdllh nafahimci mun samu wani haske saɓanin da da bama ki taɓa makamancin wannan maganarba”. Umm-Anum dai batace komaiba hannunta na dafe da kanta, ahaka barci mai nauyi yay awon gaba da ita, dukda anata kiraye-kirayen sallar magriba bai hanataba.
Sai da ya tabbatar barcin ya ɗauketa sosai sannan ya fito falo, Bilkisu da Anum yace su shiga suyi salla a ɗakin dansu dinga kula da ita, shi kuma suka fita tare da su Abu-Siddiq salla masallaci. Tunda suka fita salla Abbu ya fahimci Jawaad bayajin daɗi, dan daya kama hannunsa sai yaji zafi alamar zazzaɓi na neman rufesa. Baice komaiba sukai salla suka zauna har isha'i itama suka gabatar sannan suka koma gida. Har lokacin Umm-Anum nata barci, su Bilkisu da suma suka idar da salla suna zaune sun zuba mata idanu cike da damuwa.
Sashin baƙi Abbu yasa aka gyara, aka kaima su Jawaad abincinsu can, Abbu yace Anuwar yaje ya raka Jawaad itama Bilkisu Anum zata rakota.
____________________________________
★★★★★★★★★★★★★★★★★★★
____________________________________
Duk wani masoyin su Momy hankalinsa a tashe yake akan ɗauke Shahudah da ɗan fir'auna yayi, abin ɗaure kai da ban mamaki shine duk yanda ƴan sanda suka bazu nemansa basu samu koda mai kama da shiba, dai-dai da wayarsa an kasa samunta ta kowanne yanayi, dama ita Shahudah tata wayar na nan bai bari ta ɗauka ba, duk kuma inda ake tunanin samun ɗan fir'auna anje babu shi babu abokansa.
Hankalin kowa ya ƙara tashi, Momy kuka take kawai tana zazzagama Dad masifa ta waya akan ya dawo ita tashin hankalin nan yamata yawa, sannan ya saka Qaseem ya taho shima. Shidai lallashinta kawai yakeyi dan shima hankalin nasa aiba a ƙwance yakeba, yana matuƙar ƙaunar Shahudah fiye da zaton mai hasashe, shi da yake nesama dasu ya fisu tashin hankalin. A ranar ya sanarma Qaseem ya shirya ya koma gida zuwa gobe saboda halin da ake ciki. Qaseem dai ya amsa da “to” dan zuwa yanzun bai iyama Dad musu akan komai, duk abinda yace yayi