Showing 219001 words to 222000 words out of 261165 words

Chapter 74 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1154

aka kawo.
                “Baka da hankali ne!!!? Wace riba kake tunanin samu a kashe kanka da zakayi Qaseem? Kaifa musulmine! Taya zaka bari tunanin aƙidar yahudu da nasara har takai mizanin tasirin zama a zuciyarka irin haka? kai ƙoƙarin salwantar da rayuwarka da kanka!!! Kasan kuwa hukuncin wanda ya kashe kansa a addinin musulunci?. To sunansa KAFURI!!! kuma wlhy WUTACE zata zama sakamakonsa!!!”. Jay ya faɗa yana huci da nuna Qaseem ɗin da hannu.
        A zabure Qaseem ya hankaɗa Jawaad yay baya yana faɗin, “Bani da hankali Jawaad, wlhy da gaske na haukace, tabbas na haukace, minene amfanina idan na zauna a raye a wannan duniyar da babu komai a cikinta sai ruɗani?!!” ya finciko rigar Jay jikinsa na rawa, hawaye na zuba masa babu ƙaƙƙautawa, “Idan ka hanani kashe kaina mi kakeso nayi Jawaad? Wacce irin amsace dani da zan bama duniya akan mahaifin da nake kallo babu kamarsa a da? Matsayin suruki kawai ya taɓa amsawa a gareka amma akai maka gugar zana da halayyarsa yanzun, to inaga ni da yake mahaifina!!, da wane idanun kakeson na sake kallonsa Jawaad?! Dan ALLAH na roƙeka ka barni na kashe kaina na huta!!”....  Ya ƙare maganar da wani irin kuka mai tsuma zuciya da ya saka jijiyoyin kan Jawaad sake mimmiƙewa shima hawayen na taruwar masa a idanu. Jawo Qaseem yay ya rungume a jikinsa suka fashe da kuka a tare.....😭

(Kai jama'a, wlhy zuminci ya wuce gaban wasa komai lalacewarsa😭😭)

        
            Dalilin go-slow da Mom ta riska a hanya yasa ta iso station ɗin a wahale cikin dogon jinkiri, da kutsa-kutsar shiga cikin ƴan jarida ta samu shiga ciki da ƙyar, inda shigar tata tai dai-dai da harbin harsasai biyar da Qaseem da Jawaad sukayi. Da wannan ruɗanin da jama'a suka shiga ta samu damar bin ayarin su Sir Ahmad zuwa office ɗin Qaseem dan ta sani, bata fahimci can su Sir Ahmad ɗin ke yunƙurin zuwaba saida taga sun isa tare da su inda itama ta dosa.
     Itace farkon shiga office ɗin, sai tai tsaye turus tana kallon Qaseem da Jawaad dake rungume da juna da dauraren kalamansu.
         “Qaseem hakan ba mafita bane ɓata ne, ba'a samun hutu da saɓon UBANGIJI bisa ganganci, ka daina irin wannan tunanin”. “Dolene nayi Jawaad, ƙo Bilkisu da tazo a ƙarshen ƙaddarar kunyarta nakeji balle kai da sauran mutane, nayi nadamar kasancewata jininsa wlhy Jawaad”.

        Da sauri Momy tazo ta fincike kafaɗar Qaseem ta matsar da shi baya daga jikin Jawaad, batare da ta tsaya ta gama fahimtar matsalarba, jin sunan bilkisu kawai da tai a bakin Qaseem ya sakata harzuƙa da fassara matsalar akan bilkisun ne komai ke faruwa ma kawai, hawaye na zirar a kumatunta tace, “Qaseem wai mi kakeyi hakane? akan tsintacciyar mage, kake wannan hanƙoron da tura mana ƴan sanda gida saboda cin zarafinmu? Akan butulu da ya wulaƙanta ƴar uwarka har kake iƙirarin mahaifinka ya shirya tarwatsaka? TSINTACCIYAR MAGE! YARINYAR DA MUKA ƊAKKO A TSAKKIYAR RANA! YARIYAR DA......”
        
            “Da haɗin bakinki kenan mijinki ke aikata komai!!” Qaseem ya faɗa cikin matsanancin fushi tamkar zai haɗiye Mom, baya tai da sauri jikinta na rawa, cikin rawar murya tace, “Qaseem anya kana cikin hankalinka kuwa? Miya samu kanka? Ko an sauya mana kai ne?”.
       “Komai ma ya sameni fiye da yanda tunaninki ke baki ke da shi. Tun bansan kaina ba ke da shi kuketa nunamin banida wani maƙiyi a duniya sama da Jawaad, Why?. Mom! Nace Why? Shiɗin baɗan ɗan uwanki bane?, shi ɗin ba mijin ƴarku bane? Miya aikata mai zafine wai a gareku da har yau ban taɓa saninsa ba ni?......”
      “Qaseem!!” Mom ta faɗa cikin tsawa tana fashewa da kuka.
        Cikin ficewar hayyaci Qaseem yace, “Eh ki kira sunana koma sau dubune, gaskiyace bazan taɓa fasa faɗaba, to idanma baki saniba yanzu zan sanar miki, idan kuma kin sani bara na maimaita miki. Ita wannan tsintsiyar magen da kike magana MIJIN naki ya tsintota daga ranar ne dan ya jefata cikin abinda yafi ranar zafi, cikin wuta yay niyyar jefa mata rayuwa saboda cimma burinsa, mahaifinane shi amma nasha zarginsa da aikata abubuwa marasa ƙyau a cikin gidan nan, amma da naso ɗaukar mataki saina gaza hakan, na tabbata dukkan ƴan aikin da akai raping a gidannan shine yay musu.....”
      Tsawa Mom ta daka ma Qaseem jikinta na matuƙar rawa, “Qaseem!! Mahaifinka zaka ƙullana sharri irin wannan saboda Jawaad da Bilkisu?”.
        Da ƙarfi Qaseem ya daki tebir ɗinsa, kayan sama suka tarwatse, ya matsa gab da Mom yana nunata da ɗan yatsa ƙirjinsa na sama da ƙasa na kumburar zuciya. Ya cigaba da faɗin, “Tun kin nuna bakisan komaiba bara na faɗa miki to, tun lokacin da akaima ƴar matarnan Amina fyaɗe a cikin gidanmu na gaskata hakan a cikin raina, domin kuwa lemon da aka ajiye ta sha lemo ne da kaf gidan nan shi kaɗaine ke shansa, hakanma yasa ba'a ajiyesa a fridge ɗin kitchen sai na falonsa kawai, ko a falon ƙasa inhar baya ƙasar kwashewa kike ki maida masa sama, to tayaya akai ranar yaje kitchen har yarinyar ta gani ta ɗauka ta sha bayan shi mai shan ma baya nan? Abu na biyu sai da na ɗauki kwalin lemon a bola naje nai bincike akan ɗan sauran cikinsa na gane magani ne mai ƙarfi aka saka a ciki kuma a ƙalla ya kai kwanaki biyar da zubawa, abu na uku na zauna nayi dogon nazari da tunani harna gano ainahin maganain da akai amfani da shi, sai kuma kwatsam na tunano na taɓa ganin maganin a wajen Dad amma a wancan lokacin sai ya gayamin na ciwon bayane dan na gansa da shine a bazata, da yake kuma ban kawo komai a rainaba sai ban amsa na karanta ba a lokacin. Tun daga wannan ranar na fara bibiyar al'amuransa, sai dai abin mamaki bana iya cewa komai akan dukan abinda zan gani. to bara nama faɗa miki abinda baki saniba, a dukkan tafiye-tafiyensa cikin kashi uku biyu bayinsu yake ba, idan yace yabar ƙasarnan tafiyar sati biyu to kwana huɗu ko sati guda ya keyi ya dawo, da wannan makircin nasa yake amfani wajen aikata laifi a rasa wanene keyi a gidan, Mom ya kamata kiyi tunani da hankalinki, a dukka masu aikinmu uku da akai Raping a gidanmu duk sai baƙya nan ake aikatawa, kuma da anyi washe gari ko kwana biyu dayi Dad yake dawowa.......”
       Ƙasa Mom ta zube tana kallon Jawaad dake tsaye kawai yana kallon tamkar wani gunki, tun fara maganarsu baice komaiba bai kuma motsa ba. hawayene ke kwarara a idanun Mom tamkar an buɗe fanfo.
       Qaseem ya nuna Jay da faɗin, “Kayi haƙuri Jay ka gafarceni, zan faɗi wani abu a kan matarka duk da bata a wajen nan, tunda Bilkisu tazo gidanmu ban taɓa jinta a zuciyata da sunan soyayya ba, sai dai ina sonta matsayin ƴar uwata kawai. Amma tun randa na farka a barci naga Dad tsaye kaina a cikin ɗakina naji duk duniya babu wadda nakeso sama da yarinyar nan, ga wata sha'awarta mai tsanani inaji wadda inhar zata kasance kusa dani sai naji inason taɓa mata jiki, abin mamaki duk wannan sha'awar tata da nakeji ban taɓa jin zan iya lalata mata rayuwaba, ni dai kawai burina na taɓa jikinta ko nayi kissing ɗinta na rungumeta shike nan. Da ya ke kuma yarinyace mai tarbiya ko hannunta bata yarda na taɓa sai ta nunamin ɓacin ranta. Kuma saifa ina a kusa da itane nakejin hakan, amma da zarar bama tare da juna ni mantawama nake da ita gaba ɗaya. A daren da Dad ya fara shigo mata ɗaki har aka tsoratamu da ƙara a gidannan nine na fara fitowa, ni duk zatona mai gadine wani abu ya sama, shiyyasa nai gate kai tsaye, ina isowa maigadi na buɗema Dad ƙofa ya fita a gidan....”
          Dafe kai Jawaad yayi da sauri zuciyarsa na wani irin matsanancin harbawa da sauri-sauri, duk da Dad yake zargi dama hakan bai hanashi jin maganar tai masa nauyiba a ƙwaƙwalwa da zuciya....
         “Ƙwarai kuwa Dad” Qaseem ya bama ya sake maimaitawa yana kallon Mom cikin ido, “A tunaninki mai aƙidar kar ƴan uwansa su raɓesa ne zai ɗakko budurwa kamar bilkisu ya ajeta gidansa dan ya ƙyautata mata rayuwa kawai? Aini tun washe garin da aka kawota gidannan na ganta kuma akai min bayanin zuwanta nasan akwai manufa a zuciyarsa game da ita, sai dai narasa ta wace hanya zan kuɓutar da ita? Wannan mijin naki da kike ji da gani ramin bushiyane daga shi sai ƴaƴansa, ke kuma matarsa kura ce kema daga ke sai ƴaƴanki. Bara na sake maimaita miki shine keta bibiyar rayuwar marainiyar ALLAH akan fyaɗe har cikin gidan aurenta, da yaga bazai cimma burinsa cikin sauƙiba shine ya tafka mana asirin da har nai maganar shirya aurenta duk da a zuciyata sam ba haka bane ba. A gaban duniya ya nuna cewa ya ƙyautata mata rayuwa, zai kuma aurama ɗansa jininsa ita, amma sai ya zagaye ta bayan fage shi da ɗan uwanki Uncle Nasir suka zurmaki a ciki da ɗauraki a dukkan hanyoyin da suka gama tsarawa, ke kuma kika hau saboda baƙya son aurenmu bisa naki gurɓataccen tunanin na jahilci da son zuciya. Kuka ɗakko hayar ɗan fir'auna akan ranar ɗaurin aure za'a aura mishi ita, ni kuma zaɓinku, daga baya sai ace mistake aka samu, shi kuma dama kunbiyasa akan karya sake ya saketa duk bala'in da za'ayi har sai ƙura ta lafa an kaita gidansa. sai shi Dad yaje ya cika burinsa a kanta kawai batare da kowa yasan hakanba har ke kanki. Sai dai UBANGIJI ba azzalumin sarki bane, sannan shi yana dubi da ƙyawawan zuciyoyi masu tsoronsa da biyayya a garesa, ashe Jay ya saka ana bibiyar dukkan al'amarinsu basu sani ba..........”
         Zubewa Mom tai ƙasa kawai tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma rai tare da riƙe kanta da ke juya mata. Jawaad yay mata kallo ɗaya ya ɗauke kansa da mai dawa kan Qassem. Murmushi mai ciwo da ƙunar zuciya Jay yay yana tura ɗayan hannunsa cikin aljihu, ɗayan kuma ya dafa kafaɗar Qaseem sukaima juna murmushi. Takawa ya sakeyi gaban Mom ya tsaya har lokacin fuskar tasa da murmushin, ya durƙusa a gabanta yana haɗiye ɗacin daya tokare masa maƙoshi, “Har yanzu ke uwace a gareni Mom, yayar mahaifina, duk da ina zargin kina cikin waɗanda suka tarwatsa masa ahali”.
Da sauri Mom ta ɗago tana kallon Jay, ta shiga girgiza kanta tana hawaye, “Jawaad dan ALLAH kar kaimin wannan mummunar zargin, mi Abdul-aziz zaimin niko a duniyarnan da har zan tarwatsa masa a hali?......”
Miƙewa Jawaad yayi yana ɗage kafaɗa da taɓe baki, “Wannan amsar a gaban alƙali zaki badata Mom ba ananba”.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un ni Aysha wannan wace irin ranace”. Mom ta faɗa tana fashewa da wani irin kuka.
Qaseem da yakejin kamar ace yau ɗin ranar barinsa duniya ce yace, “Momy wannan ranace ta tonon silili, ranace mafi muni da a garemu bisa ga son zuciyar mijinki, rana ce da duniya suka san wanene shi? Mom Dad ya cutar da rayuwarmu, kaicon dukiyar da zata kasance haramtacciya ga mai ita, ki kalla yanda ake nunasu cikin ƙasƙanci dan ALLAH, wace riba sukaci? Wane alfahari suka barmana muyi? Wane tunƙaho da taƙama ya rage mana kuma?”.
Mom da batasanma wainar da ake toyawaba game dasu Dad sai yanzu da Qaseem ya nuna mata a tvn office ɗinsa a take ta ƙwalla ƙara ta zube yaraf a sume.
Jay daya fice ƙofar office ɗin ya tsaya dansu Sir Ahmad tuni suka bar wajen ganin maganace data shafi family ya dafe kansa da rumtse idanunsa da masifar ƙarfi, dan yaji dukkan abinda Qaseem ɗin ke faɗama Mom, ya kuma tabbatar ƙarar tata nada nasaba da ganin abinda ya farun.


___________________________
Dr Tayyeb hospital    
_______________________

Kamar yanda ƙarar kai kawon jirage ta ɗauki mafi yawan mutanen dake cikin asibitin haka ta ɗauki tasu Anuwar dake zaune jigum-jigum suna jiran farkawar Umm-Anum, dan Dr Tayyeb ya sake shiga ya dubata, ya kuma musu bayani akan su kwantar da hankalinsu da ruwan da aka saka mata ya ƙare zata farka normal insha ALLAH.
Aunty Batool ce ta fara miƙewa ta leƙa ta Window'n da suke a kusa da shi, da ɗan mamaki ta juyi tana kallonsu Ummah da faɗin, “Anya kuwa yau garin nan lafiya yake? Helicopters nefa na sojoji keta yawo wannan ƙarar da mukeji”.
“Helicopters kuma? To miya faru kuma?”. Ummah ƙarama ta faɗa tana miƙewa itama ta leƙa. Tabbas kuwa zancen Batool gaskiyane, dan har wasuma dake cikin asibitin sun fara fita waje. “Gaskiya garin nan babu lafiya kam”. Ummah ƙarama ta sake faɗa tana nufar ƙofa.
Da sauri su Anum sukabi bayanta harda Batoul da Anuwar ma daya bisu a ƙarshe shi da Ummah babba, sai dai Ummah babba na gabansa.
“Ya salam”. Anuwar ya faɗa da sauri saboda karo da sukaci da wani bawan ALLAH dake ƙoƙarin shigowa shi kuma Anuwar ɗin yana yunƙurin fita. A kusan tare suka buɗe baku zasu bama juna haƙuri sai hakan ya gagara kowa ya cak a tsaye baki buɗe jiki na tsuma. Idanun Uncle Sulaiman tamkar zasu faɗo ƙasa dan ruɗani da al'ajabi, cikin sarƙewar harshe yace, “Ja...waa...” sai kuma ya gaza ƙarasawa ya girgiza kansa yana haɗiye yawu da ƙyar.
Shiko Anuwar wani irin yamutsawa jininsa keyi da kansa, ya kafe Uncle Sulaiman da kallo tamkar ya samu television ɗin kallo. A haka Shahudah da sauran ƴammatan family ɗin sa'anninta suka iso wajen suma zasu koma ciki. A take duk sukaja wani wawan birki suna kallon Anuwar.
“Kai!!”
Shahudah ta faɗa daɗan ƙarfi tana matsawa gab da Anuwar da binsa da kallo daga sama har ƙasa tana zagayashi. Nannauyan numfashi Anuwar ya sauke da ɗan lumshe idanu ya kalato busashen yawun daya rage masa ya hadiye da ƙyar da raɓawa ta gefen Uncle Sulaiman zai wuce. Caraf Shahudah ta riƙo hannunsa jikinta na rawa. “Kai dan ALLAH wanene kai?”.
“Muhammad Anuwar Abdul-aziz yusif tafida”. Wata murya dake a bayansu ta basu amsa saɓanin shi Anuwar ɗin da sukaima tambayar. Juyawa sukai da azabar sauri har Uncle Yusif na neman zubewa ƙasa wajen rawar jiki.
“Hajiya Mariya, kinsan mi kika faɗa kuwa?”. Uncle Sulaiman ya faɗa yana ware idanunsa akan Ummah babba data basu amsar.
Murmushi mai ciwo Ummah babba tayi tana kamo hannun Anuwar ɗin cikin nata, “Alhaji Sulaiman ai ko baku sami wannan amsarba ya kamata kuyi tunanin hakan direct tunda wanda ya mutu baya dawowa ai ko? Kuma koda ace yaya nada rai ai bazai zauna a wannan ƙuruciyarba tunda har Jawaad daya bari matsayin ɗa ya wuceta”.
“Haj....h...ha..hajiya mariya kin sake sakani a ruɗani wlhy, a ina Abdul-aziz ya samu ɗa bayan Jawaad kuma?”.
“Biyoni da zakayi shine kaɗai zai baka amsar dukkanin tambayoyinka”. Ummah ta faɗa tana murmushi da kama hannun Anuwar suka nufi corridor ɗin da ɗakin da aka kwantar da Umm-Anum yake.
Ba Uncle Sulaiman kawai ba, hatta su Shahudah bin bayansu sukai, yayinda wasu a cikinsu kuma suka nufu kaima iyayensu rahoto.

Dr Tayyeb na ƙoƙarin fitowa daga ɗakin da Umm-Anum take dan ya sanarma su Ummah su shiga an cire mata drip yaci karo da Ummahn dake riƙe da Anuwar. Murmushi ya ɗanyi yana ja baya ya koma cikin ɗakin da juyawa ya kalli Umm-Anum dake kallonsu da murmushi yace, “Yauwa hajiya, dama zan sanar muku ku shigo ta tashi normal Alhmdllh, dan zama mu iya sallamarku kamar”.
Kafin Ummah tace wani abu Uncle Sulaiman dake a bayansu cikin tsananin kiɗima yace, “Bilkisu!”. Da sauri Umm-Anum ta maida dubanta gareshi, sai kuma taɗan waro idanu waje itama tace, “Yayah Sulaiman!”. Cikin matuƙar rawar jiki ya afka cikin ɗakin, babbar rigarsa har tana neman taɗesa Dr Tayyeb yay azamar tarosa yana faɗin, “Subahanalillhi, Alhaji yi a hankali”.
Duk da Umm-Anum batajin ƙwarin jikinta hakan bai hanata sakkowa daga saman gadon ba. Sakkowar tata kuma tayi dai-dai da faɗowar Uncle Uwaisu da sauran ƴan gidan su Jawaad ɗakin.
“Wlhy itace da gaske!!” Uncle Uwaisu ya faɗa yana jan birki da ɗaga hannaye sama tamkar wani zararre.... Kafin wani a cikinsu ya samu damar sake tofa tashi Nabeelah ta kutso tsakkiyarsu jikinta na rawa, “Ummah! Ummah!! Ummah!! Ku kalla television, ku kalli abinda ya faru dasu Yayanmu a wajen ƙwato Alhaji babba, m....m..matsafa Ummah, wlhy matsafa suka gano acan.....”
Uncle Sadiq ne yay azamar rarumar remote ɗin television ɗin ɗakin ya kulla, anko haske dai-dai inada ake fiddo su Uncle Nasir daga cikin gidan daga su sai jajayen ƙyallaye, Jawaad na rungume da Alhaji babba yana shafa masa ruwa a fuska za'a sakashi cikin helicopter shi da wasu a cikin waɗanda aka ceto.
A take ɗakin ya ruguntsume da tsananin tashin hankali da ruɗani,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login