Showing 21001 words to 24000 words out of 261165 words

Chapter 8 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1098

gama fita sannan na zama ƙarshe.
          Jikin motar da mukazo na hango rose tsaye, ta wani haɗe fuska, shi kuma yana daga gefe waya a kunnensa, hannunsa ɗaya a aljihun farin wandonsa, ido muka haɗa nai saurin janye nawa nidai, dan sam banyi zaton sashen da nake yake kalloba ma, a raina ina mamakin yanda duk sanda zan saci kallonsa nakan kama idanunsa a kaina shima, sai naji haushi na balla masa harara ta gefen ido duk da baisan inaiba.
     Duk tsaye mukai muna jiran ya kammala, kusan mintuna uku kafin ya sauke wayar ya tako wajen motar da rose ke tsaye, muma duk muna kusa, ya kalli Hafiz yana faɗin, “Yanzu yaya za'ai kenan?”.
         Hafiz yace, “Boss inaga ku koma Office, ni da rose da Aliyu zamuje can anguwar mu sake bincikawa, maybe mu samu wani a gidan yanzun”.
     “Okey hakan yayi” yay maganar yana yunƙurin buɗe motar, dole Rose data cika fam da haushi ta mat

sa, har zai shiga ta katse hanzarinsa da faɗin, “Boss nikam da sun wuce, sai na biku, zan ɗauka wayata dana manta a office, zan bisu a baya tunda nasan anguwar”.
       Ɗagowa yay yana kallonta fuskarsa babu walwala, ya janye idanunsa a kanta batare da ya bata amsaba ya maido kaina dan duk kallonsu mukeyi, “Mimaa! Shiga mota muje, ke kuma ki bisu kubiya ta station ɗin tare sai ku ɗauka wayan ku wuce”.
     Duk da naga idanunsa a kaina suke sai ban fahimci dani yakeba saboda sunan daya ambata, gashi har yayi shigewarsa motar.
      Jabeer dake kusa dani yay murmushi, “Dake yake fa, kije kutafi”.
    Kaina na jinjina masa kawai ina murmushin ƙarfin hali da sake juya sunan a raina, ‘Mimaa;? To wannan sunan kuma daga ina haka?’. Na ƙarasa zan shiga gaba, sai dai rose taƙi matsawa a wajen, na kalleta nace, “Zan shiga ciki maa”.
    Shiru bata motsaba, bakuma ta tanka minba..............✍


Rose yau kinga idi wajen bily team, dama hauhinmu sukeji😥🤐.


Asha weekend lafiya😜😑😉🤗🤗.




ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[11/30/2020, 1:00 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Page 8

.............Jawaad dake kallonsu daga ciki yay murmushi kawai yana girgiza kai, dan ya fahimci wani abu daga Rose ɗin. hannu ya miƙa ya buɗe murfin ɗayan gefensa, Hafiz dake ta wajen tsaye yace, “Kinga mai sunan Momcy zo tanan”.
      Amsa masa nai da “to” na nufi can duk da a raina banso hakanba dai, sai dai haka kawai naji inason bama shegiyar rose ɗinnan haushi yanzun, dan na kula sam bata ƙaunata dai, su mutanen duniya dasun ganka shiru-shiru saisu dinga ɗaukarka sakarai ko bakasan abinda kakeba, indai nice kuwa tasa kanta a ramin damisa wlhy. Ina shiga Hafiz ya rufe murfin, gimba yay ma mota key, bansan yanda aka ƙare da rose ba mukabar gidan bayan oga Jabeer ya shiga gaba bisa umarnin Boss da yay masa magana.
   
           Har muka isa station oga Jabeer da gimba na hira, amma ni dashi kamar mun haɗiyi kwaɗo. Yanda na takurama babu abinda nake buƙata kamar mu iso na sauka nidai. koda gimba ya tsaida motar ban fitaba saida duk suka fita, baiko kalli kowaba a cikinmu yay gaba abinsa zuwa hanyar office ɗinsa, Jabeer ne kawai ya kalleni fuskarsa ɗauke da murmushi yace, “To mai sunan mom sannu da ƙoƙari, ki ƙara ƙaimi da jarumta dan aiki da boss sai jarumi na gaske”.
       Duk da ban fahimci zancensaba nai murmushi ina ɗaga masa kai, sannan nace, “ngd” a ƙasan raina kuwa ina tunanin wai sunan wa? gareni suketa wani boyen suna.
    Murmushi yay shima, ya nunamin cikin motar yana faɗin, “Karki damu babu godiya a tsakaninmu, ki tattara masa tarkacensa kibisa office dasu, ai kinsan office ɗin ko?”.
          Tamkar na fasa ihu haka naji, amma sai na daure nace, “Ban taɓa shigaba dai, amma na sani”. Yace, “To Alhmdllh saiki kaimasa ni na wuce office ”. Kaina na jinjina masa batare da nace komaiba, shima yay murmushi kawai ya wuce abinsa.
    Duƙawa nai na tattaro wayoyinsa da tab da wasu takardu daya bari sai bindiga da keys da bansan kona miyeba, sai ƙamshi suke tamkar suma turaren ake fesa musu, ledar takeaway ɗinmu gimba ya bani, ban musaba na amsa, dan duk zatona duk shi zan kaimawa, sallama nai masa na nufi hanyar da zata kaini office ɗin da kaya riƙi-riƙi saikace wata ƴar gudun hijira, danma na barma gimba ledata akan idan na fito zan karɓa dukda yacemin gida zaije. Sai da na hau lifter domin office ɗinsa na hawa na uku ne, sai saƙawa da kwancewa nake ina zancen zuci, na iso shataletalen da ya raba hanyoyi uku na offices ɗinsu, ɗaya nasan hanyar dazata sadaka da offices ɗin su B.G ne, wanda suke a hawa na ƙarshe, sai kuma ɗayar hanyar bansan offices ɗin suwayeba a wajen, sai ɗayar hanyar da naga ya fito ɗazun, nan na nufa kai tsaye, dogon corridor ne da ƙofofi jere kusan goma, hakan yasa na fara bi ina karanta rubutun saman gudun kuskure, sai da naje na bakwai sannan naga an rubuta Captain Jawaad A yusif, inada tabbacin nanne, dan tunda aka gayamin cikakken sunansa bantaɓa mantawaba koda a second ɗaya ne kuwa. Sai da na daidaita kaina da sake ƙarfafa zuciyata da ke neman faso ƙirjina ta fito sannan nai knocking har sau uku, amma banji an amsa maniba, nai jim kusan na minti ɗaya kafin na ƙara yin knocking ɗin kamar mai tsoron a jita, nanma shiru, nakai hannu zan sake aka amsa mani. Ajiyar zuciya na sauke a hankali kafin na tura ƙofar da sallama na shiga, office ne da ya amsa sunansa office, dan kuwa yayi ƙyau, babu wasu tarkace komai kuma tsaf, ga mayen turarensa ya kama office ɗin haɗi da freshener mai daɗin ƙamshi, sai suka bada ƙamshi na musamman, kallo ɗaya naima inda yake zaune a kujerarsa ta office na duƙar da kaina, shima kuma bai kalleniba, baikuma cemin komaiba, yanata rubuce-rubucensa hankali kwance tamkarma baisan wani ya shigoba. Jinai tsayuwar ta isheni, dan haka na gyara kaɗan ina yamutse fuska, batare dana ɗago na kallesa ba nace, “Sir gashi inji oga Jabeer”.
      Jay da tun ɗazu ya daina rubutun ya kwantar da bayansa jikin kujerar kawai yana kallonta da jinjina shegen miskilancinta ya lumshe idanunsa ya buɗe a lokaci ɗaya, sai faman goga ƙasan biron hannunsa yake a jikin laɓɓansa, ko motsi baiyiba ballanta ya amsa mata. Tsabar miskilancin yarinyarne kawai ke bashi mamaki, ya ɗan taɓe baki t

are da maida kallonsa ga Computer ɗin dake kan desk ɗinsa, bironsa ya ajiye yana lafe jikin kujerar ya fara sarrafa keyboard ɗin Computer ɗin.
          Ƙaran danna keyboard da najine ya sakani ɗago idanuna nai masa kallon second 2 na janye, karan farko a rayuwata dana sake jinjina wulaƙancin mutuminnan, ‘kenan bazai tanka mani ba komi yake nufi?’ na ambata a zuciyata ina maijin takaicinsa. Satar kallonsa na sake yi sai muka haɗa idanu, da sauri na janye nawa ina tura baki gaba batare dana san nayima hakanba.
     Sautin fitar ƙaramin tsakinsa ya sakani saurin sake kallonsa, yako dallamin harara alamun har yanzu idonsa a kaina suke, “Kin zama bodyguard ɗinane shin?” yay maganar a hankali kamar baison yi.
       Kaina na girgiza masa, duk da bani da tabbacin kallon nawa yake har yanzu, takawa nai zuwa gaban tebir ɗin na ajiye kayan harda ledar abincin, ban kallesaba bai kuma tankaminba na juya zan fita.
      “Zonan”
Na tsinkayi umarninsa. Juyowa nai kaina a ƙasa batare dana kallesa ba, “Zauna” ya sake faɗa a daƙile. ‘Kai nikam na shiga uku da wannan mutumin’ na ambata a zuciyata ina mai jina a matuƙar takure, zuciyata sai faman harbawa take da sauri-sauri. Shiru office ɗin ya sake ɗauka na kusan minti ɗaya, sai ƙarar keyboard da yake dannawa kawai kake ji. Knocking ƙofa akai ya bada izinin shigowa, matashin sauriyi ma'aikacinmune ɗauke da takardu a hannu, kallo ɗaya nai masa na ɗauke idona, duk da shi na lura sai kallon mamakin ganina a nan ɗin ya keyi, har takai boss ya daka masa tsawa.
      “Kallon mutane aka turoka yine!?”.
     Cikin sauri da ladab yace, “Sorry sir”.
      Banji ya tanka masaba, danni kaina a duƙe banma ɗagoba, sai sautin siririn tsakinsa naji kawai, shidai saurayin sai faman nanata kalmar haƙuri ya keyi kusan sau huɗu kafin ya fara masa bayani akan takardun hannunsa, banji ya tankaba, hakan yasani satar kallonsu, gani nai ya miƙa hannu ya amsa takardun yana dubawa, kafin ya ɗago ya kallesa da sake miƙa masa ta kardun yana faɗin, ”Ka kaisu office ɗin Lieut..; Richard, kace ya duba, zuwa anjima sai yazo dasu ina nemansa”. “Okey sir” ya faɗa cike da girmamawa kafin ya amsa ya fita ko sau ɗaya bai sake gigin kallon sashen da nakeba.
        Ɓoyayyen numfashi na sauke bayan ficewarsa, saima naji yaɗan bani tausayi........

     “Bani malt.. A cikin fridge”. maganarsa ta dawo dani hayyacina, miƙewa nai ina ɗan dube-dube a office ɗin danson gano fridge ɗin, shi kuma yaja ledan abincin ya buɗe, ganin fridge ɗin da nayi bayansa kaɗan ya sakani nufar wajen, kasancewar ƙaramine madaidaici yasa saida na sunkuya, malt ɗin ne kawai a ciki da coc... nidai na ɗakko abinda ya sakani tare da kofin dana gani a saman fridge ɗin kusan guda shidda saƙale jikin wani ƙarfe mai ƙyau, gabansa naje na ajiye ina haɗiye yawu da ƙyar, dai-dai yana buɗe takeaway ɗin gasashen naman kaza daketa ƙamshi, ina ajewa nabar wajen na koma inda na fara zama a ɗaya daga kujeru biyun dake gaban tebir ɗinsa, ganinai kawai ya turo naman gabana, na ɗago na kallesa muka haɗa ido, kuma tamke fuska yay ya nunamin naman. Tamkar zan fasa kuka nace, “Nifa na ƙoshi, azumima nakeyi”. Banza yaymin tamkar baima jiba, ya ɗauki gwangwanin malt ɗinsa ya ɓalle hancin ya kai baki, kafin ya ajiye ya maida hannunsa kan keyboard ɗin Computer ya cigaba da daƙilarsu. Mun kwashi kusan minti uku a haka, bai tankaniba, nikuma banci namanba dukda ƙamshinsa ya addabeni.
     kamar daga sama naji yace, “Karki bari na sake miki magana, kiyi ki fitarmin a office”.
      Batare dana shiryaba bakina ya suɓuce wajen faɗin, “Toni nacefa azumi nake, sokake na karya azumina ne?”.
       Tunda ta fara magana ya dakata daga daƙilar Computer'n ya zubama laɓɓanta idanu da kumatunta da take ɗan kumburawa, sai da takai aya sannan ya janye ya maida ga abinda ya keyi batare da ya nuna yamaji mita faɗaba.

         A matuƙar takure nake gaba ɗaya bugun zuciyata da numfashina sun dawo a maƙoshina, kaɗan nake jira na amayota kowama ya huta, yaƙi kulani, sannan yaƙi cemin na tafi, ganinfa yama manta dani saina miƙe abina na nufi hanyar ƙofa, bai tanka maniba har saida na kama ƙofar zan

buɗe sannan yace, “An taɓa karyaki?”. Cak na tsaya, ni ban fitaba, ni ban komaba, bamma iya sakin mariƙin ƙofarba saboda yanda furucinsa ya daki ƙirjina, sai da na shaƙi iska na fesar sannan na juyo a hankali ina kallonsa, kauda kaina nayi saboda ganin shima niɗin yake kallo, ya wani haɗe fuska tamkar hadarin tsakkiyar ogusta.
        “Idan kika bari na sake miki magana ki kuka da kanki”.
      A yanda yay maganar da tsananin kaushi sai tsoro ya sake tsirgamin, dama dai ƙarfin hali nake kawai, dole na dawo na zauna ina sake haɗe fuska dan nikam gaskiya an sakama rayuwata ido, komawa nai kujerar dana tashi na zauna. Ina zama shikuma yana miƙewa ɗauke da wasu takardu ya fice daga office ɗin abinsa batare da yace dani komaiba. Na sauke nannauyan numfashi ina kallon naman, bani da zaɓinda ya wuce nacin kawai kodan ya barni na tafi, na ɗauki cinya nakai bakina ina ambatar bismilla, ɗanɗanon naman da laushinsa ya sakani lumshe idanuna, ko ba'a faɗaba dama namannan zaiyi ɗankaren daɗi ai, ban ankaraba na laƙume cinyar na sake ɗaukar wata tsoka irin ta haƙarƙarinan, (Damafa inaso shegen gulma ne. Lol) ina gab da cinyeta aka turo ƙofar da azabar ƙarfi aka shigo, a tsananin razane da ganin wanda ya shigo ɗinne ya sakani miƙewa babu shiri ina kallonsa. Shima idanunsa ya zubamin tamkar zai cinyeni da su.
         “Ubanmi kikeyi nan Bilkisu?!!”
Idanuna na lumshe saboda tsawar tashi ta rasha kunnuwana, na buɗe a hankali kansa, cike da dakiya na zubasu a kansa nace, “Yah Qaseem miya faru?”.
       Wata malalaciyar harara ya zubamin kamar zai juye idanunsa ƙasa, ya fara takowa inda nake, taku baifi ukuba tsakaninmu ya rage aka buɗe ƙofar office ɗin aka shigo. Ni da shi duk kallon ƙofar mukai, sai dai shi a take ya janye nasa idon yana jan uban tsaki. Nikam numfashi na sauke a ɓoye dan koba komai na samu kuɓuta daga wannan yunƙurin na yah Qaseem da bansan mi zuciyarsa ke kissima masa yaminba.
         Jay da ya shigo kuwa kallo ɗaya yay musu ya ɗauke kansa ya taka zuwa ga kujerarsa ya zauna.
       A mamakina sai naga yama cigaba da daƙilar Keyboard ɗin Computer ɗin hankalinsa kwance kamar baisan damuba. Shima yah Qaseem ɗin bai tanka masaba ya kalleni yace, “Wuce muje”.
     Jawaad daketa danne-dannensa batare daya ɗagoba yace, “Kai ka kawotane?”. Dogon tsaki yah Qaseem yaja yana damƙar hannuna da faɗin, “Miye na azarɓaɓi ƙaramin tsagera, ai zan dawo kanka idan na gama da ita”. Ya ƙare maganar da fisgar hannuna muka nufi ƙofa. Jinake tamkar na kurma ihu, ‘Nikuma wannan wace fitinace na shigo ciki haka?’..........
      “Wlhy kika fita daga office ɗinan saina saɓa miki kamanninki!”
      Muka tsinkayo kakkausan furucin boss yayinda yah Qaseem ya murɗa ƙofar zamu fice. Bani kaɗaiba hatta da yah Qaseem ɗinma tsayawa daga yunƙurin fitar yay, ya juya yana kallonsa, nidai kaina a ƙasa na gaza kallon kowa a cikinsu, addu'ar ALLAH ya kuɓtar dani daga tsakaninsu kawai nakeyi a raina, dan bansan wazan bijiremawaba? Wakuma zanma biyayya ba?. Yarfar da hannuna yah Qaseem yay ya nufesa, zafin da najine ya sakani durƙushewa a wajen ina sakin siririyar ƙarar azaba.
      Qaseem daya ƙarisa gaban Jawaad ya bugi tebir ɗin gabansa har wasu abubuwan na faɗuwa, “A matsayinka na ubanwa zaka saɓa mata kamannin?”. Ko motsi Jawaad baiyiba balle ya kalli Qaseem, aikin gabansa kawai ya cigaba dayi hankalinsa kwance. A kausashe Qaseem ya sake maimaita tambayar tamkar zai mari Jay ɗin. Ɗago idanu Jawaad yay ya zubasu akan Qaseem, cike da gadara yace, “Qaseem fitarmin daga office!!”.
     “Anƙi a fita, kayi duk abinda kaga zaka iyayi” Qaseem ya maida masa amsa a zafafe shima.
     Jawaad bai sake magana ba, ya miƙe ya nufi Bilkisu dake durƙushe tana hawaye saboda hannunta dake zugi.
     
        Tsayuwar mutum kawai naji a kaina, cikin bada umarni yace, “Tashi”. Miƙewa nai babu musu, na saci kallonsa, ganin shima kallon nawa yakene yasa na janye nawa ina goge fuska, kafin ya sake wata magana yah Qaseem yazo ya shiga tsakkiyarmu, ”Wuce muje” ya faɗa yana nunamin hanya, haushin murɗamin hannu da yayne yasa naƙi motsawa. Ganin naƙi motsawarne ya sake hasalashi ya

ɗaga hannu zai saukemin mari.
         Rufe idona nai da sauri naja baya saboda masifar firgita da nai da ihun da yaymin akai, na ƙanƙame jikina ganin ya ɗaga hannu zai makeni, shirun da naji yasani ɗago kaina kaɗan naga miya hanashi dukan nawa da yay niyya.. Saurin waro idanu nai waje ganin boss riƙe da hannun Yah Qaseem da ya ƙara kumbura sai hura dogon hancinsa yake.
       “kika fita saina karyaki a office ɗinan Miemaa” boss yay magana a dake  kamar yanda na fahimci halittarsace yin magana kai tsaye koda a gaban wa yake. Saurin duƙar da kaina nai saboda tsatstsareni da yay da idanu, nai baya daga kusa dasu cike da tashin hankalin sakani tsakkiya da sukai.
        yah Qaseem ya fisge hannunsa dake cikin na boss ya kai hannu zai damƙoni ina ƙoƙarin matsawa. Cikin matuƙar zafin nama boss ya fisgi yah Qaseem ɗin gefe, hakan sai ya bani damar mannewa a bango na sake musu kuka kawai, dan zuciyata bazata iya ɗauka ba.

          A cikin tsagwaron fushi Qaseem ya damƙi wuyan rigar Jawaad zai shaƙeshi, “Amma kasan zan iya illataka ko?”.
     Murmushi Jawaad yayi yasa hannu ya ture hannun Qaseem dake damƙe da wuyansa, cikin halin ko in kula yace, “Ka illatanin mana Qaseem, kai wai wace irin banzar zuciyane da kai haka? Mace zaka ɗaga hannu ka daka?”. A matuƙar masife Qaseem yace, “ina ruwanka? Miye matsalarka?” baki Jawaad ya taɓe yana watsa hannayensa da ɗage kafaɗa yace, “Banda” ya ƙare maganar da juyawa zai koma kujerarsa. Saurin maidoshi baya Qaseem yay, hakan ya saka Jawaad tsayawa sai dai bai juyo ya kalli Qaseem ɗinba, ƙoƙarin danne zuciyarsa yake dan bayaso su raba hali gaban yarinyarnan kamar yanda ya kula Qaseem yana buƙata. Cikin nunashi da ɗanyatsa Qaseem yace, “Wannan ya zama na farko kuma na ƙarshe da zaka sake saka Bilkisu! cikin lamarinka, itaɗin matar dazan aurace, ya rage naka ka kiyayi ko kaci gaba”.
       Rumtse idanu Jawaad yayi saboda jin yanda Qaseem ya ambaci sunan mahaifiyarsa gatsal, ya juyo a hankali yana kallon Qaseem cikin ido, cikin ƙunar zuciya yace, “Ko wacece ita a wajenka baya gabana, sai dai kai kasani baka isa hanani sakata aikin dana gadamaba tunda har tazo station ɗinnan a ƙasana, kasa a ranka yanzu aka fara wasan kuma, ina gargaɗinka Ka kiyayi  kai hannu kan mace da nufin duka”. ya ƙare maganar a wani irin yanayin rainin wayo. Hakan sai yay masifar sake fusata Qaseem, a tsawace yace, “Matsayinka na ubanwa?”..............✍
     

Qaseem team & Jawaad team banda faɗa kuma 🚴🏼🏋🏼🤼🏼😂😖.

Ina Bil-Qas team nidai😜🤫🤸🏼.

ALLAH ka gafartama iyayenmu🙏🏻
[11/30/2020, 1:01 PM] HASNA✍🏻: Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 9
............A matsayinka na ubanwa?” cewar Qaseem a fusace.
Cike da rainin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login