Showing 111001 words to 114000 words out of 261165 words

Chapter 38 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1168

mun gama samunshi”.
Jawaad ya ɗago yana ɗan bubbuga pen ɗin hannunsa akan laɓɓa, takardun da Hafiz ya ajiye ya ɗauka, sai da ya gama dubawa sannan ya sake ɗagowa ga Hafiz ɗin, “Kamar ba komai ne anan ba ai Hafiz, Rose ta baka dukkan bayanan dake hannunta ne? akwai kuma bayanan Restaurant ɗinan shima ban gansaba anan?”. Hafiz yace, “Oh sorry, wlhy nama shafa'a sosai, na gidan cin abincin nan kamar suna hannun Mami ne fa, jiya naso amsa, sai kuma na iske batazoba, bara na amsosu, saina haɗo dana hannun Rose ɗin”. Dakatar dashi Jay yayi ta hanyar ɗaga masa hannu. “Rose ta fita ita da Aliyu, Miemaa Kirata ta kawo, nima akwai aikin dana sakata ma ita da Dawood shi ya kawo nasa ita shiru kakeji”. Miƙewa Hafiz yay zuwa gaban landline ɗin office ɗin yana faɗin, “Bara muji to kota kammala duka”. Jay baice komaiba ya cigaba da aikinsa, yayinda Hafiz yay waya department ɗin su Bilkisun. Baifi mintuna goma da ajiye wayarba akai knocking ƙofar.
★★★
Tunda nazo office ban gansaba, ban kuma je inda yakeba, ina namu office ɗin na duƙufa dukkan ayyukan dake gabana, sai hirarmu da bata ƙarewa ni da Ummie.
Kasancewar jinin dana gani jiya tun a daren na nemesa na rasa yasa dukkan sallolina yau nayisu batare dana sake ganinsa ba kuma. Mun fito sallar la'asar kowa ya koma kan aikinsa. Nayi nisa sosai akan aikin da nakeyi saƙon kira daga office ɗin Boss ya sameni. Dukda nasan dalilin kiran sai da gabana ya faɗi, dama tun ɗazun Dawood ya sanarmin ya kai masa aikin daya sakamu tare saura ni yake jira. Miƙewa nai na tattare files ɗin guda biyu na fita.
Da sallama na shiga office ɗin bayan nayi knocking an bani izinin shiga, naɗanji sanyi ganin akwai Oga Hafiz a office ɗin, shinema ya amsan sallamata, dodon nawa kam bai ko ɗagoba, gaba ɗaya hankalinsa nakan Computer, inama shigowa ƙarar danna keyboard ɗinsa ce ta fara tarata, yanda yake dannawar da sauri-sauri yasa akejin ƙararsu sosai. Da fara'a oga Hafiz ya tarbeni, na gaishesa ina miƙa masa file ɗaya a cikin biyun dana shigo dashi tunda nasan dama shine wanda zan baiwa. Ɗayan kuma na matsa tebirin boss na ajiye, murya a sanyaya nace, “Barka da yamma”. Batare daya ɗagoba yace, “Barka” ya cigaba da aikinsa. Duk da yanda yaymin ɗin haka na sake dannewa nace, “Gashi na kammala, sai dai result ɗin sayin hannun nasa ɗin bai fitaba”. Dakatawa yay daga abinda yakeyi ya ɗago min manyan idanunsa da a yau suke farare tas, sai dai sunɗan kumburo alamar cike suke da gajiya, sauri janye nawa nai lokacin da sautin muryarsa ta fara isowa cikin kunnena. “Wakika kaimawa?”. Yay maganar har yanzu idanunsa a kaina dan inajin yanda suke shiga ɓargona. Cikin nutsuwa ta nace, “Sir danaje office ɗin Umar bayanan saina gamu da Hashim”. Cikin kaushin murya yace, “Hashim! Kina nufin shi kika bamawa!?”. Yanda yay maganar ya sani ɗagowa na dubesa da sauri. Dan masifa har fararen idanun nan dana gani yanzu sun sirka da ɗan ja, na kula da yashiga ɓacinrai zakaga idanunsa sun sauya kala. A ɗarare na ɗaga masa kai kawai. Uffan bai sake cewaba ya ɗauki wayar landline yay kira.
Hafiz da duk yana zaune yana kallonsu ya kalli Bilkisu, “Mami garin yaya kika bama Hashim bayan bashi akace ki bamawa ba?”. Kaina a ƙasa nace, “Wlhy ni bansan akwai matsalaba ne, na fito shikuma zai shiga office ɗin shine yake tambayata ko lafiya? Nikuma nace masa wajen Umar nazo, shine yace bara ya ajiye masa anjima saina dawo na amsa, to kafin na koma ɗinne kuma mukai fitar ranar, jiya kuma banzo office ba, ɗazun nakoma amsowa danna tattare komai shine Umar ɗin ya sanarmin bai bashiba, amma ya fita idan ya dawo zai tambayesa koya mantane”
Hafiz ya ɗan girgiza kansa da faɗin, “Ki ringa kula kinji, duk wanda ba'ace kibama abububa kidaina bashi, wannan aikin namu da kike gani kowa takansa yakeyi, shiyyasa zakiga a komai ana taka tsantsan, bara ni naje wajen Hashim ɗin da kaina Boss”.
Jawaad ya dangwarar da kan wayar a ƙasa saboda yakasa samun Umar ɗinma, bai cema Hafiz komaiba harya fice.
Kansa ya dafe cike da takaici, ya miƙe tare da tura kujerarsa baya da ɗan ƙarfi ni harma na tsorata, yay taku ɗaya biyu kafin ya juyo yana kallona, yanda ya matso daf dani yasani maida kaina ƙasa, yaɗan buga tebirin da faɗin, “Wai sai yaushene zaki daina bani ciwon kai ne yarinyarnan? Wataran saina sauya miki kamannin fuskarnan taki maikama data mage idan baki dawo hankalinki ba” yay maganar da yunƙurowa kamar zai makeni. Baya nai da sauri, cikin zafin nama na tura kujerar na miƙe tsaye, dan yanda ya fusato ɗinan nasan iya makeni zaiyi ɗin.
Jay da takaici yake neman shaƙema numfashi yace, “Zonan, idan kuma kika bari ni nazo saina karya ƙasusuwanki”. Idanuna cike da ƙwalla na kallesa ina tura baki, kafin na samu damar bashi haƙuri yace.
“Ni kike murguɗama baki?!”.
Saurin ɗagowa nai ina ƙwalalo idanu waje, kujimin sabon sharri, ni yaushe na murguɗa baki dan ALLAH jama'a?. ganinfa da gaske ni yake nufowa fuska a ɗaure sai na fara ja baya, bai fasa biyoni ba kamar yanda ban fasa tafiya da bayaba ina yarfe hannu, jinai tamkar na saki fitsari, yayi bala'in ɗaure fuska yanda na tabbatar yau idan ya kamani sai ya karyanin da yake faɗa. cikin sarƙewar harshe nace, “Ni wlhy ban murguɗa maka baki ba fa Sir, kuma ALLAH bani da lafiya ma”. Nai maganar dai-dai na dangane da bango, shikuma ya iso daf dani.
Ina rufe baki ana turo ƙofar, ido huɗu mukai da Rose, kafin bakina ya iya sake furta wani abu naji an fisgoni na faɗo saman ƙirjin mutum.............✍

ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻[12/23/2020, 2:52 PM] HASNA✍🏻: ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO



Page 35
.................Rintse idanuna nai da azabar ƙarfi, a duk lokacin da jikinsa ya taɓa nawa nakanji tamkar na taɓa wuta, daga randa mukaje ɗakko gawar Gimba kuma sai na rage jin hakan, sai dai sam banason yace zai taɓani, amma a mamakina yau sai naji tamkar an azani bisa wutar. A take jikina ya fara karkarwa saboda azabar da nakeji, cikin gangarowar hawaye bisa idanuna nace, “Boss dan ALLAH ka matsa, wlhy jikinka tamkar wuta nake jinsa”.
Yanda ta ƙare maganar da fashewa da kuka tana neman silalewa ƙasa yasaka Jay ja baya cikin ɓacin rai, dan shi kalamanta zafi sukai masa a zuciya, cikin kaushin murya yace, “Qaseem ne kawai idan ya taɓaki baƙyajin zafi tunda shi kikeso?”. Idanuna na shiga lumshewa ga zufa sai karyomin take a jiki saboda azabar da nakeji, na shiga girgiza masa kawai, “Kaimin addu'a, fatar jikina jinake tamkar ana ɗayemin itane”. Yanzu kam da mamaki yake kallonta, dan yanda jikinta ke wani irin karkarwa da zufar da takeyi ta cancanci a fahimceta, kalaman baba ƙaurane suka faɗo masa cikin rai, addu'ar ya shiga karantowa yana tofa mata, idanunsa harsun ƙaɗa sunyi jazur saboda yanda yakeji a cikin ransa, gaba ɗaya yakan rasa wane tunani zaiyi akan lamarinnan, idan ya zurfafa tunaninma sai kiji kansa ya fara matsanancin ciwo, dole yake ajiye batun ya shiga wata sabgar badan kuma al'amarin baya cikin ransa baneba. Ahankali Bilkisu ta shiga sauke numfashi, zufar na tsafewa sanyin ac na ratsata, kusan mintuna goma suna a haka.
Rose da tunɗazun tai sumar tsaye tai Luuuu zata faɗi saboda wata hajijiya data rufe ganinta. Da sauri Hafiz da isowarsa kenan dasu Jabeer ya tarota. tai ƙoƙarin ƙwacewa jikinta na rawa zata sake danna kai cikin office ɗin idanunta na zubar hawaye Hafiz yay saurin sake fusgota, cikin tsawa-tsawa yace, “Rose! Minene kikeyi hakane?”. Wasu irin zafafan hawayene suka shiga rige-rigen sake gangaro mata saman kumatu, ta tsare Hafiz da kallo, hannu na rawa ta nuna ƙofar office ɗin Jay, “Boss fa rungume da yarinyar nan”. Cikin takaici Hafiz yace, “Idan ya rungumeta sai akai me? Ba matarsa bace! matarsa ce ita halalinsa, ke kanki shedace akansa, inda Jay yana harkar mata ke zai fara lalatawa ai” ya ƙare maganar da balla mata harara yaja tsaki ya juya yabar wajen.
Da sauri Rose ta maida kallonta ga Jabeer da Aliyu. Tace, “Kunajinfa miyace, miyasa Hafiz baya ƙaunata?”. Ɗan murmushi Jabeer yay yana girgiza kansa, “Hafiz ba ƙaunarkine bayayi ba, gaskiya ya faɗa miki, Mami matar Jay ce yanzun”. Daɓar Rose ta zauna ƙasa tana faɗin, “Jesus, shikenan na mutu Jabeer, yaushe akai musu auren?”. Duƙawa Aliyu yay gabanta cikin taushin murya yace, “Baki mutuba Rose, kisama ranki haƙuri dan ALLAH karki tada hankalinki kinji, ALLAH ya rubuta itace matarsa, kema naki mijin nanan zuw.......” “Aliy daina faɗamin maganar banza kaji, ni boss zai yaudara, dama tunda naga yarinyarnan na shige masa nasan zatai abinda yafi haka, nasan asiri tai masa kawai”. Ƴar Dariya Jabeer yay shima ya duƙa gabansu, “Rose na faɗa miki gaskiyar magana? Boss shike bin Mami ba ita ke binsa ba, tunda muke da ita bata taɓa nuna wanima a cikinmu ya taɓa koda birgetaba, shi kansa farautar soyayyarta yake amma sam taƙi bada ƙofar hakan, kullum ma nunawa take ita batama taɓa fahimtarsa ba, itaɗin mace ce mai AJI!, shine babban maganin asirinta akan zuciyar Boss, yakamata ki fahimci yana son mace mai suna mace, ma'ana mai Ajiiii!!”. ya ƙare maganar cike da salon iskanci yana salute ɗinta, miƙewa yay tare da mata nuni ta miƙe dan tayi sagafene tana kallonsa da fassara maganganunsa sala-sala.
Sam Jay baiga Rose ba, Bily kanta data ganta halin data shiga yasa tama manta da ganin nata, ruwa ya ɗakko ya bata, babu musu ta amsa, yanda tasha ruwan sosai har mamaki ta bashi, ta miƙa masa kofin tana godiya, baice mata komaiba sai nuni da yay mata data tashi takoma kan kujera.
Nima ina buƙatar hutawar, dan haka na tashi na koma saman kujerar na zauna tare da lumshe idanuna.
Sosai nakeji a jikina kallona ake, ina buɗe idanu muka haɗa ido dashi, ɗauke kansa yay tamkar baniɗin yake kallonba, nima na janye nawa a raina ina jinjina yanda ya ƙware a iya kallon mutum.
Babu wanda ya sake shigowa office ɗin har aka kira sallar la'asar, shine ya fara shiga ya ɗaura alwala sannan yace naje nayi nima, lokacin dana fito tsaye na gansa, bance komaiba na nufi hanyar fita yana biye dani.


Daƙyar Aliyu ya lallaɓa rose suka bar ƙofar office ɗin Jay, kuka take rurus cin ƙarfinta, a zuciyarta tana ayyana matakin gaggawa da zata ɗauka akan Bilkisu nan bada jimawa ba, bazai yuwu tazo jiya-jiya ta samu abinda ita ta kashe shekaru masu yawa tana bibiyaba, dolene kodai ita ta samu, kokima su rasa gaba ɗaya. Da wannan ƙudirin tabar office yau.
Yau tare dashi mukabar office, a ƙasan raina cike nake da tuhumar ina Yah Qaseem ya shiga? Sam bana ganinsa a office tunda na dawo, mike faruwa dashi ne? Inason tambayar boss inajin tsoron buyaginsa. Munyi nisa a tafiya batare daya kalleniba yace, “Jazuga bai mutuba”. Da wani irin matsanancin sauri na juyo na kallesa, harma na manta dawa nake na kafesa da idanu ko ƙyaftawa banayi”. “Malama idanun nan sunmin yawafa”. Kumbura fuska nai na ɗauke kaina jin abinda yace, sai kuma na kasa haƙuri naɗan sake kallonsa na risinar da kaina, cikin zumuɗi nace, “Dan ALLAH da gaske boss?”. yace, “Mun fara ƴar wasane dake?” kaina na girgiza masa dukda nasan bani yake kalloba. Shiru bai sake cewa komaiba, har muka isa masarauta, dukda inason jin ƙarin bayani haka na daure na danne a raina, idan taƙamarsa jan aji gidan ya taras.
A cikin ran Jay wani irin haushine ke cinsa, mamaki da takaicin miskilancinta yake, yayi shirune yaji kozata tambayesa cigaba labarin amma yanda yay shiru itama ta tsuke baki, shikuma inhar ba ita tanema jin yanda akaiba bazai faɗa mataba. Babu wanda ya sake yin magana tsakanina da shi har yasamu guri yay fakin gab da sashen gimbiya, dan yanzu shi babu shamaki an bashi damar shigowa cikin masarauta a duk sanda yaso. Yunƙurin buɗe motar nai ya riƙo hannuna. Daƙyar na iya danne abinda nakeji na kallesa, ganin ni yake kallo sai nai ƙasa da kaina, sakarmin hannu yay yana faɗin, “Saiki jira na gama tunda ba tauneki zanyi ba”. Nidai bance komaiba, ya miƙa hannu sit ɗin baya ya ɗakko leda viva sabuwa. “ga wannan, duk yanda zakiyi amfani dasu na rubuta miki, Karkiyi wasa Miemaa, dan ina buƙatar matata a kusa dani” yay maganar ahankali yana kafeni da idanu, saurin sadda kaina nai dan naji wata irin bahaguwar kunya ne. Jay dake kallonta yay wani lallausan murmushi da cigaba da faɗin, “dolene ta hanyarki zan gano bakin zaren matsalarmu, hakan kuma bazai yuwuba kai tsaye sai da taimakon UBANGIJI”. Kaina a ƙasa nace, “Insha ALLAHU zanyi Sir”. “ALLAH ya tabbatar”. Ya faɗa batare da ya da ɗauke kansa daga gareni.
Nima saina fita a motar ɗauke da ledar da bag ɗina, ta sashensa na zagaya na sake masa godiya sannan na shige, tuni an amshi kayan hannuna tun fitowata a motar.
Jay daya kafeta da kallo ta cikin mota yaɗan lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya lokacin data shige. Shima fitowar yayi. Masallacin masarauta yay salla har isha'i, kafin ya samu damar ganawa da gimbiya a tsaitsaye. Yamata bayanin abubuwa da dama a gurguje, itama ta sanar masa ƴar firar da sukai da Bily da abinda ta fahimta. Duk yanda taso yaci abinci ƙinci yay yauma yaymata sallama ya wuce.
__________________________
Tun daga wannan ranar gimbiya ta sake jan Bilkisu jikinta, riritata take tamkar uwa da ƴa, gefe ɗaya tana koya mata dabarun rayuwar aure cikin hikima kamar yanda itama Mommah tai mata gata, sannan a hankali take fahitar wasu abubuwa daga Bilkisu ta cikin hira. Magungunan da Jay ya kawo mata Amintacciyar baiwar gambiya tsaye take akan Bilkisu dan ganin tayisu kamar yanda ake buƙata, ga maganin sanyi shima da ake bata acewar gimbiya shine matakin farko.
Kullum da safe driver zai kaita office da yamma idan an tashi Jawaad ya ɗakkota ya maidota, dukda babu wata hirar arziƙi a ciki, yakuma daina raɓarta koda wasa, yanzu sam basama haɗuwa sosai a station ɗin saboda baya zama aiki yaymasa yawa, su kansu yana wajigasu da ayyukan sosai.
A haka aka shiga wata mai albarka na ramadhana, manya da ƙananun yara harma da tsaffi kowa ya tashi da wannan ibada a baki cike da ɗoki da fatan kammalawa lafiya. Yayinda Bilkisu ke kallon ikon ALLAH wajensu gambiya dangane da alkairin da ake fita dashi domin talakawa. Abin sai ya birgeta, a cikin ranta tana fatan kwatantawa taji idan zata iya watanara, sannan har yau da take nufar sati na biyu a masarautar bata taɓa gamo da Sarki Sameer ba, Safah ta sanar mata yaje saudia hutawa shida amaryarsa da suke kira Ammi, sai azumi yaje tsakkiya zai dawo sukuma su tafi Umarah



★★★★
Jay da muƙarrabansa sunyi busy matuƙa, ga aiki ga aikin sa kai gana hidimar bayin ALLAH duk ya haɗama kansa, burinsa ya kammala abubuwa da yawa cikin watannan, baya neman Bilkisu ne dan yana tausayinta sosai, ga azumi ga rana dan ruwa bai zaunaba sosai, gani yay ta rame masa a kwanakinan sosai sai tai haske kuma.
Abin mamaki Rose kuma saita shiga ja baya dasu, har takai saida Jay yamata magana da kasa, ranar kam dai yaga taɓara da iyayi, gashi yanaji da azuminsa. Shidai ya lalaɓata kawai dan yana buƙatar nutsuwa baison hayaniya.
Tuni yasa ana bibiyar masa bayan Ɓaleru duk inda ya sanya ƙafa batare da shi ya saniba, bayason kamasa a cikin watannan mai albarka shiyyasa yay tamkar ya manta da al'amarinsa, ga jikin ɗan-fir'auna da har gidan su Shahudah suka ɗauka ya mutu na nata sauƙi da warwarewa.
__________________________
Kwanci tashi babu wahala wajen UBANGIJI azumi yakai tsakkiya, a daren sha bakwai sarki Sameer da Amaryarsa suka dawo, anyi murna da dawowar tasu sosai, dan ranar kam kowa ya shaida hakan a masarautar gagara badau, ranar gimbiya da kanta taima Takawa abincin buɗa baki a kicin ɗinta na sirri da babu mai shiga sai ita saiko Amintacciyar baiwarta. Tunda ta tafi ɓangarensa su bily basu sake jin ɗuriyartaba sai washe gari, sai a randa za'a ɗau azumi na sha takwas ne suka ganta, shima dan tasaka a kira mata bily ne.
Cikin girmamawa na gaisheta kamar yanda na saba, fuskarta ɗauke da murmushi ta amsa min tare da kamo hannayena cikin nata. “Ɗiyata dama nasa a kiramin kene saboda zaku wuce Umrah gobe idan ALLAH ya kaimu ke da su Amaturrahman, an kammala miki komai insha ALLAH” Dama Boss ya sanarmin tun shekaranjiya, sai dai na nuna mata farin cikina sosai akan hakan itama tamkar bansan da tafiyarba, nakuma mata godiya. Ta cigaba da faɗin, “Naso ace tun farkon azumi kika tafi, sai dai mijinki ya sanarmin hakan bazai yuwuba saboda aikinki, dan akwai wata auntyna matar yayan abokin Takawa tanada makaranta ta musamman domin koyar da amare, ana gyaran jiki da komai a ciki, koya girki da dukkan dabarun zaman aure, itama ƴar nan ƙasarmu ce, dalilin ƙaddara ta shigo rayuwarmu, mun kaita domin neman magani sai yayan abokin Takawa yace shifa yayi mata, wannan shine dalilin zamanta a can itama”. Fuskata ɗauke da murmushi nace, “ALLAH sarki”. Itama murmushi tayi, “Yanzu dai yayi dukkan cuku-cukun daya dace a wajen aikinku insha ALLAH keda nan sai saura kwana biyar tarewarki, inason naga kin zama cikakkiyar mace mai amsa suna mace a fadar mijinta, mijinki babban mutumne sannan yanada wasu sirrika dake kaɗai zaki fahimci kayanki anan gaba, shiyyasa nakeso a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login