Showing 102001 words to 105000 words out of 261165 words

Chapter 35 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1124

arziƙinsa, a gaba ɗaya jarin idan zaka dinƙuleshi waje ɗaya bazai wuce na naira dubu goma sha biyarba, wataƙil ma na zurma da yawa. Dalilin kamewarsa na janye kansa da ga ƙasƙancin bara ne ya ja hankalin mafi yawan telolin anguwarmu zuwa sayayyar kayan ɗinki a wajensa. Sai mahaifiyata da ke saida kayan kuka, kuɓewa busashshe, kayan ƙamshi harda daddawa domin kare mana mutunci itama. Gidan da muke gidan hayane mai ɗauke da ɗakuna kusan arba'in, dan irin dogon gidannan ne da akan jeranta ɗakuna reras da ga farkon baranda zuwa ƙarshe tamkar gidan karuwai, ba wani faɗine da gidan ba, amma kowa iyakar mu'amularsa a ƙofar ɗakinsa ne da bazata gaza taku goma ba, babban kicinne guda ɗaya a gidanmu dake a farkon shigowa gidan wanda ya gama cuɗewar baƙi saboda mafi yawancinmu girkin icce mukeyi, masu arziƙin cikinmu ne keda lasisin dahuwar abinci saman gawayi, can da ga ƙarshen gidan kuwa banɗakine guda biyu, na kashi da wanka, wanda suka ɗaine duk yawan mutanen gidan ke shiga, shiyyasa mafi yawanmu zaki samu kowa da fo ɗinsa na kashi a ɗaki ko ƙaramin botikin fenti, da safe idan bakai azamar tashi kai wanka ba to fa ka tabbata ƙila sai dare ko goshin magriba zaka samu damar yinsa, shiyyasa da yawanmu mukan jera kwana biyu babu wanka.
Tunda na taso a gidan na ganmu, hakama mafi yawan waɗanda suke gidan haka na tashi na gansu, dan har takai mun wuce ƴan zaman haya sai dai ƴan uwa.  mahaifina da mahaifiyata duk haifaffun garinne, kuma dukkan danginsu suna ciki suna rayuwa, hasalima akwai masu arziƙi a ciki. Sai dai kowa yasan halin zuciya irin ta wannan zamanin, inhar baka da shi to kaida banza duk ɗaya kuke, kai tsaye ma ake mantawa da kai a cikin dangi. To ballema irin iyayena da suka kasance n

akasassu, inhar za'a iya mantawa da mai ƙafafu da hannu da idanu saboda talauci ya masa katutu ta yaya kake tunanin ba za'a manta da musakan iyayena da bayan rauni da ALLAH ya jarabcesu da shi na halittar jiki harda talauci ba?. Ni kaɗai iyayena suka haifa a duniya, nima an jima ba'a sameninba, sai da ga baya ALLAH ya azurtasu da samuna matsayin ƴa ɗaya tilo a garesu, duk da talaucin iyayena da kasantuwarsu nakasassu ni ƴar gatace, dan gwargwadon iko iyayena tsaye suke a kan bani tarbiya, nakanje makarantar gwamnati kamar yanda sauran ƴaƴan gidanmu ke zuwa, hakama ina zuwa islamiyya. Sai dai aduk lokacin da aka buƙaci wani abu da ga makaranta da yafi ƙarfin ƙarfinmu hankalin iyayena kan tashi da ni kaina, wannan yasa da yawan lokuta karatun nawa ke kwan gaba kwan baya, dan kuwa ƴan ajinmu sunsha tsallakewa gaba su banni da maimaita aji saboda rashin kuɗin abu idan an buƙata tamkar ba makarantar gwamnati ba. Badan bani da ƙoƙari bane, a wannan ɓangaren ma ina sahun farko na gwarzayen yara masu ƙwaƙwalwar karatu da fahimtarsa, sai dai rashin kuɗi ke daƙileni a kulum..........................

          Tunda Bilkisu ta fara bama Jay labarin rayuwarta idanu kawai ya kafeta dashi ko ƙyaftawa bayayi, ko sau ɗaya bai katseta ba har saida takai aya, fuskarta shaɓe-shaɓe da haye ta juyo tana kallonsa. “Wannan itace asalin Bilkisu da take gabanka, mai rawa da bazar Dad, badan shi ba babu mai sanin wannan BILKEESUN bare ya bibiyi tarihinta, Yah Jawaad, bazan bijirema aurenkaba, dan har yanzun bansan asalin ƙullashi ba, sai dai kasani rashin auren Yah Qaseem tamkar butulcine daga alkairan Dad a gareni, ya ɗaukeni a lokacin da kowa ke ƙyamata, ya mini gata a lokacinda masu gata ke gudun raɓata, ya tsaftace rayuwata a lokacin da datti mai ciwo ke lulluɓe da ita, shin baka ganin ya cancanci fiye da auren jininsa a gareni koda kuwa matarsa bata ƙaunata?”.
           Jawaad dake kallonta idanu jazur ya ɗauke kansa daga gareta a karo na farko, murya a dakushe yace, “Bazan musa miki cancantar Dad da abinda yafima haka daga garekiba, sai dai ni Jawaad Abdul-Aziz Yusif nace bai cancanci samun sadaukarwar komai daga gareki ba”.
        Sosai nai masifar waro idanu ina ture bargon da naketa faman rufe jikina dashi da, nama manta boss ne a gabana, dan haka cikin zafin rai nace, “Kai wanene da kake tunin Dad bai cancantaba? Yaushe ka sanni harda zaka iya aza mizanin cancantarsa da kalaman son sakamin shakku da baƙantasa a gareni, y.......”
         “Yah isheki!!”. Ya faɗa cikin daka tsawa yana ɗaga hannu tamkar zai makeni. Baya nai da sauri ina mai rumtse idanu dan nama sadaƙar mazgenu zaiyi.
      Jawaad ya rintse hannun da yakai zai maketa yana lumshe idanunsa tare da danne lip ɗinsa na ƙasa da haƙori tamkar zai hudashi, kusan sakan ashirin suna a haka kafin shi ya fara buɗe nasa idon da hannun yaja goran ruwa dake bed side drawer yasha, ahankali abinda ya tokare masa maƙoshi ya faɗa, ya maida jikinsa ya jingina da gadon yana ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa.
      Nima jin bai makeninba yasa na buɗe idanuna, karan farko a rayuwata da nakejin zafinsa, miyasa yakeson aibantamin Dad ɗina bayan shine yaymin gatan da har shiɗin ya shiga cikin jerin masu sanina....?
          Jay daya ji ƴar nutsuwa tazo masa ya sauke numfashi daɗan ƙarfi, batare da ya juyo ga bily ba yace, “Ina su Firdausi da iyayenta?”. Kamar bazan tanka masaba sai dai nace, “Tun randa na baro gidan bayan kwaɗama Jazuga abu ban sake waiwayarsa ba saboda inajin tsoro, Nima babban burina a yanzu sanin halin da suke ciki, musamman dana yawaita mafarkinsu a kwanakinan”. 
         “Miya hanaki waiwayarsu bayan lafawar abubuwa?”.
         Kallonsa nai da mamaki, nace, “Taya za'ai batun kisan kai ya iya lafawa? Kasheshifa nayi da wannan hanun nawa”. Nai maganar ina mai fashewa da kuka da nuna masa hanun nawa.
        Murmushi naga yayi, dukda dagani kasan na takaicine hakan bai hanani jin ciwoba. Ya juyo sosai yana kallon hannuna da nake nuna masa, sai kuma ya ɗauke kansa. “Wace anguwa su Uwargida suke?”.
      “Harna baro gidan bansan anguwarba nima”. Baice komaiba ya sauka daga gadon,

saurin ɗauke idona nai daga garesa ganin gajeren wandone a jikinsa wanda iyakarsa rabin cinyarsa. Bai sake cemin komaiba tsahon lokaci yanata safa da marwa a ɗakin, nidai gittawarsa kawai nake iya hangowa ban yarda na ɗago na sake kallonsa ba. Yazo gabana ya tsaya, hakan yasani ɗagowa na kallesa a tsorace, “Wa bincikenki ya nuna yayma Amina fyaɗe?”. Wani irin muguwar bugawa ƙirjina yayi akan wannan tambaya batare da nasan dalilin hakanba, maimakon na bashi amsa sai kawai na fashe da kuka.
      Tsura mata idanu kawai Jay yayi cike da mamaki? Yanzufa ta bashi labarin komai tiryan-tiryan, amma ya mata tambaya ta saka masa kuka. A dake yace, “Qaseem ne?”. Kasa bashi amsa nai saboda wani irin juyawa da kaina keyi tamkar ana bugamin guduma, da sauri nakai hannu biyu na riƙesa ina faɗin, “Ya ALLAH kaina”.
      Babu shiri Jawaad ya durƙusa a gaban gadon ya tarota ganin zata faɗi, saurin kwantar da ita yay ya kama kan ya riƙe cikin hannunsa yana janye nata hannun, addu'a ya shiga yimata jin kan ya ɗauki wani mugun zafi maiban mamaki, ga jikinta ya ɗauki wani irin rawa. Cikin matuƙar sarƙewar halshe take faɗin, “Kamin addu'a, kamin addu'a dan ALLAH, kaina zai fashe, wayyo kaina”.
           Tsahon lokaci yana mata addu'a har tai shiru, jikinma ya daina rawar da yakeyi, bai dainaba cigaba yay da mata har saida yaji zafin kan ya ragu sosai barci ya ɗauketa kafin ya miƙe, alwala yaje ya ɗauro yazo ya saka dogon wando ya kabbara salla.
       Kusan ƙarfe uku da rabn ta farka, nama manta a ina nake sai dana gansa a zaune da alkur'ani a hannu sannan na tuna. Yunƙurawa nai na tashi da ƙyar dan jikinna kam ciwo yake min, nima alwalar na ɗauro nazo bayansa na saka wani abin sallar na tada.
    Jay duk yanajin motsinta, sai dai baiyi maganaba saboda karatun da yakeyi.

      UBANGIJI mai rahama da jinƙai sai ya bama Bilkisu da Jawaad damar raya wannan dare da ibada har akai kiran sallar asubahi.

★★★★★★★

             Tunkafin ya dawo sallar asuba na gyara ɗakin na wanke har toilet, ina cikin gyaran falon saman ya shigo, dauriya kawai nakeyi dan wani irin barci nakeji fiye da zato, batare dana kallesa ba nace, “Ina kwana”. “Lafiya, waya saki wannan aikin?”. Kaina a ƙasa har yanzu nace, “Babu kowa”. Gaba yay yana faɗin, “Ki barsa iya nan kizo ki shirya na ajiyeki inada ayyuka da yawa yau”. ban iya cewa komaiba harya shige, dubana na maida ga agogon falon, ƙarfe shida da minti talatin da huɗu. Ƙarasa mopping ɗin nayi da sauri-sauri.

      Yanda tai gyaran gadon sai ya kasa daina kallonsa, da ƙyar ya iya ɗauke idanunsa, abu ya ɗauka ya fita daga sashen gaba ɗaya yana jaddadama Bilkisu tai wanka kafin ya dawo.
          Kayan sharan naje na ajiye na nufi ɗakin, a gaggauce nai wankan dan banason yazo ya iskeni, babban tawul da yafi kowanne girma na ɗauro na maida hijjabi jikina na fito, ina isa gaban mirror yana shigowa da sallama, ALLAH ya soni ban cire hijjabinba, na amsa masa kaina a ƙasa. Ledar hannunsa kawai ya ajiye saman gado ya nufi toilet yana faɗin, “Ga kayan da zaki sakanan”.

        Sauri-sauri na shirya cikin doguwar rigar dake cikin ledar ruwan sararin samaniya, sai sabon hijjab har ƙasa fari tamkar wata matar liman, na fita dan bana fatan ya fito ya samini a ɗakin.

___________________

             Misalin ƙarfe bakwai da mintuna arba'in Bilkisu da Jawaad suka fito daga sashensa.
     Addu'a naketayi a raina ALLAH yasa karmu haɗu da kowa, ALLAH kuwa ya amsa min ma muna fitowa ashe motar da zamu fita na a kusa. Da kansa ya buɗemin na shiga, sannan ya maida ya rufe ya zagaya mazaunin driver. Bazan ɓoye mukuba banason tuƙinsa, dan na kula ya iya zuga gudun tsiya a hanya. To amma babu yanda na iya.
      Haka muka tafi babu mai cema wani uffan a cikinmu, sai dai naji daɗi sosai yanda naga mun nufi masarauta kai tsaye. Yauma kamar ranar a ƙofar farko ya tsaya, waya ya ɗauka yay kira. bayan ya ajiye wayar ya juyo yana kallona.
          “Ya sunan anguwar da kuka zauna?”. kaina a ƙasa nace, “Bankaura”. “Zaki zauna a gida yau sai gobe idan ALLAH ya kaimu zaki koma aiki, ki dage da addu'a, kina dai ganin duk abinda ke faruwa”.

Kaina na jinjina masa nace, “Insha ALLAH, amma dan ALLAH miyasa jiya kace ban cancanci nai sadaukarwa ga Dad ba?”.  
      Shiru kamar bazai tankaba, kusan sakan biyar sannan ya juyo yana kallona, “Lokaci zai nuna mana komai, babu abinda zaki iya fahimta a yanzu sai ruɗani, kije idan lokaci yay zaki sani”. Kafin nace wani abu su Amaturrahman da Amintacciyar baiwar gimbiya sun fito a mota. Gaishesa sukai cikin girmamawa, ya amsa shima fuska aɗan sake yana faɗin, “Kucema Ummu ga amanarta nan ban ciba”. Dariya Amintacciyar baiwar gimbiya tayi tana faɗin, “Jiya kam ai tayi faɗa tamkar ta ari baki anƙi maido mata ƴarta”. Murmushi Jay yayi kawai yana ɗan kallon gefen da Bily take suna magana da Amaturrahman kafin ya ɗauke kansa.
         Sallama yay mana ya tafi, Muna shiga daga ni har Amaturrahman barci muka kwanta dan shi nakeji fiye da komai a yanzun.
               

__________________________

         Jay yana ajiye Bilkisu Office ya nufa, ayyukane fal kansa har baisan da ina zai faraba, yana zama abinda ya farayi shine bige-bigen waya, a kiran farko Umarni ya bada a nemo masa gidan da Bilkisu ta sanar masa sun zauna da iyayenta a Anguwar Bankaura, tare da ainahin maigidan da halin da gidan yake ciki yanzun. Kira na biyu kuwa Ainahin gidansu Baba makaho inda aka haufesa yasa a binciko masa shikuma a Anguwar Tudin Jarƙasa.
       Sunyi zaman awa biyu shida su Aliyu, duk da yaga ɗacin ran da Rose takeyi baibi takanta ba, bayan sun kammala ta buƙaci yin magana dashi, ca yay mata bashi da lokaci yanzun kam saita bari wani lokacin. Cike da takaici ta riga kowa fita. Haka ya cigaba da rage akainin gabansa.
         Misalin sha biyu yabar station zuwa Barrack ɗin sojoji da suka fara zuwa jiya kafin su tai jejin nan, ya samu ganawa da Lieutenant General a tsaitsaye dan ya iskesa yana shirin fita, ya sanarmasa wajen baba ƙaura yazo. Lieut G ya saka wani soja yayma Jay rakkiya har gidan da baba ƙaura yake zaune a cikin Barrack ɗin.
           Baba ƙaura ya tarbi Jay da murmushinsa mai tsayawa mutum a rai, bayan sun gaisa ya sake yima Jawaad ta'aziyya. Jawaad yay masa godiya akan gudunmawar da ya basu jiya. Fuska ɗauke da murmushi baba ƙaura yace, “Yaro bani nayiba ALLAH ne yayi”. “Hakane baba” Jawaad ya faɗa cikin sake tabbatarwa. shiru suka ɗanyi na wasu sakanni, baba ƙaura yace, “Mike tafe da kai?”. Ɗagowa Jay yay ya kallesa da ƙyau, ya tsufa sosai sai dai yana tare da ƙarfinsa, bashi da tsaho sosai sannan shiba wada bane, ya risinar da idanunsa yana faɗin, “Maganganunka na jiya baba na kwana juyasu a rai, sai dai har safiyar yau ban iya samo amsar ko guda ba, baba mika sani a kanmu?”. Murmushi baba ƙaura yay idonsa akan Jawaad, yace, “Yaro bansan komai a kanku ba, hasalima jiya na fara ganinku a iya tsahon rayuwata, kowane irin mutum a duniya yanada baiwarsa, ni tawa baiwar kenan, fahimtar wasu abubuwa daga mutane, akwai mutane masu irin wannan baiwar tawa da yawa a duniya, sai dai mafi yawansu sunfi zaɓar aikata saɓon ALLAH da tasu damar, sai kaga mutum ya zama ɗan tsubbu ko naɗama kansa wani girman da zai halakar da mutane daga barin ALLAH, ko ya maida baiwar tasa ga zalunci da neman duniya. wlhy kaji na rantse maka bansan komai daya shafekuba face abinda UBANGIJI ya bama idanuna ikon gani tattare daku jiya.....”
      Cikin jinjina al'amarin baba ƙaura Jay yace, “baba ko zamu iya sanin abinda ka fahimta ɗin?”
       Murmushi Baba yay da faɗin,  “Yaro minene sunanka?”. Jay yace, “Jawaad”. “Masha ALLAH, malam Jawaad bawani abune na gani a rayuwar kuba, domin kuwa ƙaddarar da duk ke cikin rayuwar kowanne ɗan adam wannan ɓoyayyen sirrine daga taskar ALLAH, abinda ALLAH ya bani ikon gani tattare daku kawai shine rayuwarku na ɗaure da wani al'amari mai girma, sannan kunada taurari masu ƙarfin haske da suka hana duhun dake zagaye daku tasiri, dan har na waccan yarinyar sunfi nakama haske, abinda nazarina ya bani bayan faruwar abubuwa a dajin nan shine akwai sihiri mai ƙarfin gaske jingine da jininku, su wanene sukai muku? Miye dalili? Saboda mi? Daga yaushe ne? Shine ban saniba sai abunda ALLAH yasio sanar daku nan gaba”.

      Cikin ɗaurewar kai Jawaad yace, “Amma miyasa kanema sanin sunan mahaifinta?”. “Saboda duhun dana gani biye da bayanta yafi naka rintsi”. “Duhu kuma baba?”. “Ƙwarai duhu ɗana, amma da sannu zai yaye insha ALLAHU bisa rahamar ALLAH, shawarar dazan baku shine ku dage da addu'a da sadaka musamman a cikin wannan watan mai albarka na Ramadhan da zamu shiga nanda kwanaki uku idan munada rabon kaiwa. Kunika ciyar da bayin ALLAH fiye da yanda kukeyi a baya, ku saka dubunnan marayu farin ciki fiye da yanda kukeyi a baya, ku kaima UBANGIJI kukanku fiye da yanda kukeyi a baya, sannan a daren jiya naga wani haske dake nesa da kai na tunkaroka, sai dai yana nesa dakaine, bansan tayaya zakaje garesaba koshi yazo gareka”. Da sauri Jay ya kalli baba ƙaura, “Baba ko hakan nada nasaba da mafarkin da nake mai sarƙaƙiya?”. “ALLAH kaɗai yasan gaibu Jawaad, amma tun yaushe ka fara mafarkin?”. Jimmm Jay yay alamar tunanin, yace, “Baba idan har ban mantaba na farayinsa a daren da muka dawo daga wata horaswa daga ƙasar America ne, shekara kusa ɗaya kenan, sai da danayi sau ɗaya ban sakeba sai a watanan nan naketa maimaitawa, bayan ɗaurin aurena da ita sai kuma ya canja salo”. “Ikon ALLAH,to shidai mafarki sirrine yaro, sannan akwai abinda yake ishara daga UBANGIJI a cikinsa, akwai wanda shaiɗanu ke jinginuwa a cikinsa, akwai wanda keda alaƙa da saka abu a rai, to amma kozan iya jin wani abu daga mafarkinka?”. Babu musu Jay ya faɗa masa na farko da wanda yay a ƙarshe washe garin ɗaurin aurensa da Bilkisu bayan sallar la'asar. Baba ƙaura ya daɗe baice komaiba, yanata juya abun a ransa amma bai samu wani hasken da yake buƙataba, ya ɗago ido ya zubama Jay na tsahon lokaci kafin ya janye, “Alƙar jini a cikin jini yanada nasaba da kamar kun haɗa jini kenan nidai a nawa ɗan sanin da UBANGIJI ya banifa, amma sanin gaibu sai ALLAH”. Sam Jawaad bai fahimci komai daga kalaman baba ƙauraba, dan a iya saninsa babu ta inda yakeda dangantaka da Bilkisu sai ta wajen su Hudah..... Baba ƙaura ya katse masa tunani da cewar, “Sarƙaƙiyar dake ɗaure da rayuwarku tanada nasaba da wani zalincin mai tushe daga wasu jininku, UBANGIJI shikaɗai yasan sirrin dake ɓoye dai, amma a mafarkinka mutum kake gani yana sanar dakai kokuwa?”.
      “Da farko dai bana ganin kowa, amma daga bayan nan mace nake gani, gashi na santa a mafarkin, sai dai dana tashi fuskarta saita ɓacemin, duk iya hasashena bana tunota”.
      “To UBANGIJI shi kaɗai yasan dalilin sirranta maka ita a zahirin taswurar zuciya, kuje kucigaba da addu'a, ALLAH bai manta da al'amarinku ba. Ga wannan gadalin (maganin), karkaji komai sanine daga abinda ALLAH ya sanar dani nima, saboda bibiyarta da ake ana tsoratar da ita dalilin abinda ke hannunta nasu ALLAH bazai basu damaba insha ALLAH, a zubashi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login