Showing 6001 words to 9000 words out of 261165 words

Chapter 3 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1094

firgita.
     Saura kaɗan su takemin ƙafa, nai azamar sunkuyawa na ɗauki bindigarsa data faɗi, banyi zato ko tsammanin zan iya abinda nake yunƙuriba, amma cikin amincin UBANGIJI koda na harba sai harsashin ya sauka akan tayar motar ta baya.
     Tangal-tangal motar ta fara, hakan kuma ya sake hargitse wajen da ihun mutane. Kuma harbin ɗayar tayar nayi, hakan ya saka motocin dake gefenta, sukuma suka bigi fitilar dake a tsakkiyar titi ta tsaya cak.
          Gaba ɗayansu suka fito kuma lokaci ɗaya, dukansu sanye cikin baƙaƙen kaya, gaba ɗayansu bindigace a hannayensu, hatta da wanda na bugama hannu da ƙofa na ɗauka tashi yana tare da wata, hannunsa dana buga sai faman jale-jale yake tabbacin na jimasa ciwo.......
         Da ƙarfi naji an fisgi hannuna, dai-dai shigar ihun Ummie cikin kunnena tana faɗin “Bily!!! harsashi!!”..................✍🏻


ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 3

...............Shuuuu yazo ya wuce sai jikin glass ɗin wata motar bus.
Saurin kallon wanda ke riƙe da hannuna nayi, gabana yay masifar faɗuwa saboda cin karo da nai da fuskar da ban taɓa tunanin gani a wajenba ko tsammani, ya sake fisgar min hannu muka duƙe bayan wata mota saboda tahowar wasu harsasan huɗu kanmu.
Cikin matuƙar fusata ya girgizamin hannu yana faɗin, “K shashasha ki dawo hankalinki!!”.
Yanda yay maganar da wata firgitacciyar muryace ta dawo dani duniyar mutane, amma hatta da kunnuwana da sun doɗe baki ɗaya ko ƙarar harbin banaji.
Ya jefamin wata bindigar a jiki, cikin zafin nama na cafeta.
Sosai Jawaad yaji mamakin salon na bilkisu, sai dai babu wannan lokacin a garesa yanzun, dan haka ya maida hankalinsa akan abinda ke gabasu.
Wajen ya sake hargitsewa da musayar wutar harbe-harbe, kowa burinsa ya kare kansa, mutane kam bamuda tabbacin halin da suke ciki a yanzu.
Bazan iya tantance muku halin dana tsinci kainaba a ciki a wannan lokacin, amma ni kaina nasan na zama jaruma mai ban al'ajabi..
Kowa ya jigatu a wajennan. Bagamu jami'an tsaronba baga ƴan ta'addaba, balle kuma jama'ar gari da suka fimu shiga ruɗani da tashin hankali. Sai dai abin farin cikin shine mutum biyune suka haɗu da tsautsayin harbi a farar hula, ɗaya a ƙafa ɗaya a hannu, amma Alhmdllh babu wanda ya rasa ransa sai a cikin ƴan ta'addar da aka harba a ƙirji. Mun sami nasarar cafkesu baki ɗaya, su biyarne, ɗaya ya mutu, ɗaya naji masa ciwo a hannu, sai raunika da sauran suka samu da wasu a cikinmu harda ni da gilashin wata mota ya yanka a hannu.
Wannan shine karon farko dana taɓajin mummunan rauni makamancin haka a rayuwata, sai dai lokacin dana jisa ruɗani baisa na maida hankaliba dukda inajin wani masifaffen zafi da raɗaɗi na ratsani, a cikin ƴan uwana kuma babu wanda ya lura sai da ƙura ta lafa, zuwa sannan na zubar da jini sosai, harma takai ina ganin jiri a idanuna, dama gashi inajin yunwa sosai. Rose da hankalinta ya fara kaiwa kainace ta iso gareni da hanzari, dan tuni hayaniyar mutane data ababen hawa data cika wajen ta fara yima kunnuwana nisa, duhu ya fara mamaye idanuna, hakama numfashina sai tattarewa yake waje guda yana dunƙulewa a cikin ƙirjina, abinda kawai zan iya tunawa shine taroni da tai na faɗa jikinta, daga haka ban sake fahimtar komaiba daga duniyar mutane.
★★..::..★..::..★..::..★★
A hankali nake buɗe idanuna da sukaimin masifar nauyi, naɗan motsa kaɗan ina cije leɓe kafin na samu nasarar buɗe ido da ƙyau. ‘Asibiti kuma?’ na ambata a hankali ina waige-waige da kallon ɗakin dana buɗe ido na ganni cikin bazata. A saman hannuna dake naɗe da bandegi na sauke ganina, sai yanzune abinda ya faru yake ƙoƙarin dawomin a zuciya, a hasashena zan iya cewa jiya kenan abin ya faru, dan yanzu dai ranace ƙwanyar na fahimta, idan kuma ban mantaba ƙurar jiya ta tashine da yammaci har zuwa duhun mangariba, kenan a cikin asibiti na kwana?.
Bani da amsar tambayar tawa, kamar yanda babu alamun akwai mai amsa mani ita a kusa, dan babu kowa a ɗakin sai ni kaɗai.
Na ɗauki tsawon wasu mintuna da bazan iya ƙididdige yawansuba sallamar Ummie ta riski kunnuwana, nakai dubana gareta yayinda take ajiye madaidaicin kwandon data shigo dashi a hannu,
“Bily ashe kin tashi ma?”
Tai maganar tana matsowa daf dani. tare da taɓa hannuna da naji ciwon. murmushi nai mata, kafin na buɗe baki a hankali ina bata amsa da “eh”. Zama tai a kujerar gaban gadon, tana murmushi, tace, “Kai Alhmdllh, bily kin bala'in rikitamu jiya, wlhy mun zata bazaki sake buɗe ido ki ganmu ba”. Da tsagwaron mamaki nace, “Miyasa?”. Tai ƙaramar dariya tana miƙewa, “karki damu zan baki labarin komai, yanzu dai bara na kira Doctor danya dubaki, daganan kici abinci ko, dan tun kiran sallar farko na tashi domin na haɗa miki shi”. Kaina kawai na iya rausayarwa gefe ina binta da murmushi, tare da tarin ƙaunar da nake jinmu tamkar jini guda.
Ba'a ɗauki wani dogon lokaciba Doctor yazo, yaymin tanbayoyi kafin ya bama Ummie Umarni akan ta taimakamin nayi wanka ga bayi nan, idan na kammala naci abinci nasha magani, zuwa yamma ƙilama su sallameni tunda sunga komai normal.
Da taimakon Ummie na sakko a gadon, sai yanzune na kuma fahimtar a ɗaki na musamman nake, kuma ni kaɗaice a ciki, na kalli ledar jini dake rataye a ƙarfe cikin mamaki, Ummie data lura saita bani amsa da faɗin, “Ke aka ƙaramawa, dan sanda muka iso jininki ya zuba da yawa, amma Doctor yace babu wata damuwa a hakan, idan an ƙara miki zai amfaneki, idan kuma ba'a ƙaraba bazaki cutuba, sai dai boss ya dage akan a ƙara miki jinin dole, anbuƙaci gwada su oga Hafiz koza'a samu na ɗaya a cikinsu yay dai-dai da naki, amma sai boss ya hana a gwada kowa, a cewarsa jininsa yana rukunin da zai iya bama kowa, dan haka a ɗeba nashi, kowa yasha mamakin furucinsa, amma bawan ALLAHN nan ya fuske abinsa, babu ma wanda ya samu ƙofar kawo masa wargin tambayar dalilin hakan, daga ƙarshe dai jininsa aka ɗiba aka saka miki.......”
Lokaci ɗaya nai masifar zabura da zaro idanuna waje, har ina bige hannuna mai ciwo, hakan ya sakani cije lip ɗina na ƙasa kafin nace, “Jininsa fa kikace?”.
Sosai ta ƙyalƙyale da dariya, “Wlhy karkiji wasa, jinin Boss ne ke gauraye da naki suna aiki a kowacce kafar jijiyarki a halin yanzu”.
“Na shiga uku ni Bilkisu” nai maganar ciki yanayin ta ƙaremin. Dariya Ummie ta cigaba dayi, dan na lura sam bata fahimci tashin hankalin da nake a cikiba da gaske, ban sake iya maganaba har taimin rakkiya cikin toilet ɗin ɗakin dake tsaf babu datti, ga ruwan ɗumi ta haɗa mani kuma.
A cikin dabaru nake wankan gudun karna jiƙa hannun dake naɗe da bandeji, sai dai zuciyata sam bata tare da hankalina, sai faman juya maganar sakamin jinin Boss da Ummie tace anyi nakeyi, haka kawai naji hawaye masu ɗumi suna sauka bisa kumatuna, bansan na mineneba, sannan bansan dalilin zubar tasuba, sai dai wani gefe na zuciyata na danganta saukarsu da ganin kamar bankai matsayin da za'ace jinin wannan bawa ya gaurayu da nawaba, da kuma zaka tambayeni dalilin faɗar haka a lokacin bazan iya cewa komaiba balle yin fashin baƙi. Haka dai na kammala na fito, da taimakon Ummie na kimtsa cikin kayan da tazomin dasu, ta shafa min mai harda ƴar hoda fara ta sakamin dan karna zauna fuska na ƙyalli, na zauna a saman gadon jingine da filo ita kuma ta haɗamin tea, tare da zubamin farfesun kan rago daketa ƙamshin kayan yaji.
“Ummie ƴan gidanmu kuwa sun sani?”.
Sai da ta miƙamin tea ɗin kafin tace, “Eh, tun jiya da daddare sukazo ai, Daddy, Mom sai Aamilah da Shahudah da Salim, lokacin bakisan inda hankalinki yakeba, anama ƙara miki jinin ne”.
Kaina na gyaɗa mata sannan na amshi kofin, cikin suɓucewar harshe nace, “Sanda sukazo Boss na nan?”.
Tsareni tai da kallon tuhuma, ni kuma na basar cikin kauda mata shakkun dake neman yin ƙutse a ranta, fahimtar hakanne ya sakata daidaita yanayinta itama, tace, “A'a sun tafi lokaci harsu Oga Aliyu, ni kaɗaice kawai, saboda nima Daddy ne yace na jirashi shida Mami zasuzo su dubaki saisu tafi dani, tunda Doctor yace basa buƙatar kowa ya zauna dake”.
Bansan miyasaba sai kawai naji zuciyata tamin daɗi da rashin haɗuwar tasu, na cigaba da shan tea ɗin a hankali, Ummie ce ta kuma maido hankalina gareta da faɗin,
“Ammafa kin bala'in burgeni jiya wlhy Bily, wai dama baki da tsoro ashe?”.
Murmushi nayi kaɗan ina lumshe idanuna tare da muskuta zamana yanda zanji daɗi sosai, “Ummie ba tsorone banda shiba, wani lokacin tsoro da kansa yana jin tsoron mai tsoronsa, sai dai ba kowacce ƙwarin gwiwa ke fahimtar da hakanba, a duk lokacin da kikejin tsoron abu to kawai ki tunkareshi koda kina tunanin zaki halaka ne, ina mai tabbatar miki shi wannan abin tsoron shine zai koma tsoronki, da gaske daga jiya na ƙarajin ƙarfin gwiwar yima ƙasata aiki bakin rai bakin fama , alƙawarin danai da izinin ALLAH bazata tashi a banzaba, daga yanzu zan cigaba da tunkarar kowanne irin abin tsoro daka iya tsoratar da al'ummar ƙasata koda zai sakani fuskantar ƙalubale, bani da kowa sai kaina Ummie, akwai irina da yawa a faɗin duniya, waɗanda sukafini shiga gararin rayuwa da buƙatar jin ɗumin duniya a dalilin rashin majingina ta iyaye, wadda mutuwa ta nisantasu, kokuma iyayen na raye ƙaddara ta nisantasu, sai dai ita duniyar ta juya musu nata bayan saboda bata buƙatar nasu ɗumin, waɗanda kuma keda kusanci da duniyar suna hantararsu saboda basu da buƙatar taimakonsu koda da nuna tausayawane, irina da sukasan wannan zafinne kawai yakamata ace suna iya tunawa dasu da waiwayensu a lokacin da suka sami damar ƙutsawa jikin duniya ta ƙarfin tsiya. Na shiga aikinnan ne domin ALLAH, zanyi hidima wa ƙasata domin ita ƙasata ce, zan rungumi marayu irina domin ƴan uwanane, zan kare haƙƙin ƴan ƙasata domin suɗin ahalinane, nabar kallon allon tsoro a gabana a yanzun, allon jajircewa kawai nake burin cinmawa insha ALLAHU, abokan tafiya kawai nake buƙata, waɗanda basai naje farautarsuba, da kansu nakeso suzo gareni, hakkane kawai zaisa na tabbatar da sun cika sharuɗɗan abokan gwagwarmaya dai-dai da yaƙar tsorona, jiya ta wuce, yanzu a yau muke, abi mafi muhimmanci shine mu fiskanci gobanmu idan muna cikin masu rabon gani”.
Sosai Ummie keta faman jinjina kai da dogon bayanina da bani da tabbacin zai zama abin fahimta ga kowa har ita kanta, wani zai iya kallonsa ta fuskar ƙuruciya, wani yace rashin hankali na mata, wani yace wauta ta mara gata, wani yace zaƙewa ta ƴaƴa mata masu san nuna daidaita kafaɗunsu da maza, hakan bazai dameniba a duk yanda fahimtarka ta baka, abinda na sani kawai zuciya sirrin mai ita kawai takeji, duk bin diddigin ma'abocin kusanci koya kasa kunnuwa bazaiji komaiba sai bugawarta, idan kuwa har mun yarda gaibu sunanta gaibu, to yazama tilas muyi imani da hankali koda bama ganinsa a zahiri saita yaƙini kawai.
“Maganganunki irin na mutanene masu himma bilkisu, sannan masu duba gabansu mizatazo dashi, bawai yau ɗinsu kawaiba, da jiyansu data shuɗe ta zama tarihi, tun haɗuwata dake ta farko na fahimci kinada wata baiwa ɓoyayya da bakowa ALLAH ya bama ilhamar hasasotaba, daga lokacin kuma da muka kasance ma'abota kusanci na tabbatar da zamu ribantu da junanmu, sai dai taki ribar da zamu samu saita ɗara tamu muhimmanci da amfani a garemu, k.......”
“Sam ban gamsu da bayanankiba Ummie” na faɗa cikin ɗaga mata hannu saboda yanda ta kwararo zance.
“Miyasa kikace haka Bily?”.
“Banason faɗa kice na maida hannun agogo baya, mubar zancen kawai watarana ma ƙarasa, mizai hana kije wajen Doctor kimasa maganar ya sallamemu haka, banason zaman asibiti a rayuwata”.
kafin Ummie ta samu damar yin magana aka turo ƙofar aka shigo da sallama, Dad ne, hakanne ya sakani faɗaɗa murmushi akan fuskata, saurin tashi tsaye Ummie tayi ta bashi kujerar da take zaune akai, kafin ta gaidashi cikin girmamawa. Nima gaidashi nai, ya tambayeni jikina cike da kulawa. Naji daɗin ganinsa sosai, nakumaji daɗin alhinin daya nuna akan halin dana tsinci kaina, sai dai nayi ƙoƙarin daƙile alwashinsa na buƙatar nabar aikin, danshi kam ya fara tsorata dajin cewa wannan aikin namu da gaske bai dace da ɗiya mace ba, musamman ma irina da nake yarinya ƙarama.
Cikin murmushi da girmamawa a garesa nace, “Dad addu'arku kawai muke buƙata, idan har zamu cigaba da sakawa a ranmu mata basu dace da irin kowanne aikiba saboda matsalolin cikinsa, to lallai yankinmu bazai daina fuskantar koma bayaba, hakama sauran mata masu tasowa bazasu daina fuskantar ƙalubale na daƙile burinsu akan kansu da ƙasarsuba”.
Sosai Dad yay murmushi, ya shafa kaina da cewar, “ALLAH yay miki albarka kinji, lallai tunaninki ƙyaƙyƙyawane Bilkisu, ALLAH ya kiyaye gaba to, nabiya ta wajen likita, ya baki sallama yanzu haka, sai dai ya tabbatarmin daga office ɗinku an turo ɗaukarki, ɗan aiken na hanya kuma, dan haka ni zan wuce, dama daga nan airport na dosa”.
“Dad badai har zaka sake wata tafiyar ba?”.
Murmushi yaymin mai ƙayatarwa yana jinjina kansa, “Hakane bilkisu, masu iya magana nacewa na kwance baiga gariba, muma addu'arku muke buƙata tamkar yanda kuke buƙatar tamu kinji, wannan karon kuma bazan jimaba, dan sati ɗaya kacal zanyi, idan na wuce hakan kuwa bazan zarta gomaba”.
“To Dad ALLAH ya tsare hanya, ya kuma bada nasarar abinda za'a fita nema mai albarka”.
“Amin ɗiyata, nagode sosai”.
Itama Ummie tai masa addu'a, ya amsa mata da kulawa kafin ya ajiye mana kuɗaɗe masu kauri ya fice daga ɗakin”.
Koda Dad ya fice fuskarsa ɗauke take da murmushi tare da ɗunbin tausayin yarinyar a ransa, shidai haka kawai ALLAH ya dasa masa ƙaunarta a zuciya, yaɗan juya ya kalli ɗakin yay murmushi kafin ya cigaba da tafiya........
Gaff sukaci karo da mutum, Gimba yay saurin fara jero kalamun ban haƙuri a gareshi. Batare da Dad yay masa wani kallon arziƙiba yace babu damuwa, yay wucewarsa. Binsa da kallo Gimba yay cikin wani tsagwaron mamaki da juya abinda ya gani a cikin zuciyarsa, sarai ya gane mahaifin matar Boss ɗinsace ta da, kuma mijin Gwaggonsa, afili yace, “To mikenan? Mi yazo yi nan? Minene ma'anar wannan kallon da yayma ɗakin nan? Minenema haɗinsa da ɗakin?”. Bashi da mai amsa masa wannan tambayoyin, dan haka yaja bakinsa ya tsuke dan bai dace ya shiga abinda babu ruwansaba, Boss na yawan masa nasiha da kiyaye abinda ba huruminsaba koda a inane, kuma koda akan minene.
A ɗaki kuwa bayan fitar Dad yabo Ummie ta shiga jero masa, yayinda Bilkisu ke tayata tare da ƙara buɗe ƙyawawan halaye na Dad waɗanda Ummie batasan da suba. A haka gimba yay sallama a ƙofar ɗakin, sai da na suturta jikinna kafin mu bashi damar shigowa, dukda bamusan shiɗin waneneba.
Mun gaisa da juna cikin girmamawa, sannan ya kora mana bayani akan cewar Boss ɗinsa Jawaad ne ya bada umarnin yazo yakaimu gida dan an bani sallama.
Kallon juna mukai ni da Ummie, kowanne baki a hangame, sai dai bamu da damar bin ba'asi akan wannan umarnin, dan kuwa dai yana sama damu, mizaisa mu tuhumesa da abinda bamu da bakin zarensa. Haka muka shiga kimtsawa har Doctor ya shigo, ya ƙara mana bayani akan yanda zan kula da cuwon saboda gudun karya zarta haka, tare da kwanakin da zan ringa zuwa asibitin domin tabbatar da ingancin kulawar da nake bashi.
___________________________
JAWAAD
___________________________________
Zaune suke a office ɗinsa su huɗu, aminan juna kenan da sukejin kansu jini guda, sannan abokan amanar juna masu taruwa wajen magance matsalolin juna da ƙarfin zuciya dana aljihu.
Sunyi nisa cikin tattauna abinda ya faru a yammacin jiya ne, domin dai da gaske Jabeer ne ya haɗa cinkoson jiya da gangan saboda son cimma burin kama tsagerun da suka biyo, amma sai suka ɓace musu, ganin zasu rasa wannan damarne Jawaad ya bama Jabeer umarnin nuna ƙwarewarsa kasancewarsa masani sosai ta ɓangaren na'ura mai ƙwaƙwalwa.
A take kuwa ya nuna gwarzantakar tashi, ya haɗa cinkoson da su Bilkisu suka riska saboda tabbacin nan kaɗaice hanyar da masu laifin zasubi su tsira da wuri, ita kuma Bilkisu tayi tarar aradu daka akan abinda bata da tabbaci.
Aliyu ne ya fara faɗin, “Maganar gaskiya na daɗe banga jarumar mace mai ƙarancin shekaru irin yarinyarnanba, a yanda labari ke fitowa da ga bakunan mutane na yanda ta tari motar mutanen da suka fara ganin farkon al'amari da yanda ta tunkari mutanen zai baka tabbacin da gaske tanada kaifin zuciya akan aikinta”.
Cikin jin jina kai na tabbaci Jabeer yace, “Lallai maganarka tana akan gaskiya wlhy Aliyu, nifa abindama ya sake birgeni da ita shine, dukda mugun ciwon da taji, amma saita dake dan tabbatarma da duniya lallai ita ma'aikaciyar tsaroce ta gaske ba ƴar burgaba”.
Fuska shimfiɗe da murmushi Hafiz yace, “Sosaima kuwa Jabeer, dolene ƙaimin yarinyar ya burge kowa, dan kuwa da ƙwaƙwalwa tai amfani wajen fahimtar motar tana da alaƙa da rashin gaskiya, ta kuma nuna himmarta na sadaukarwa koda hakan na nufin zata cutu a wajensu, ta cancanci kowanne irin jinjina ga hukumarnan tamu, musamman idan akai la'akari da shigowarta cikin aiki jiya-jiya kawai, bana tunanin kuma an taɓama fita da ita wani aiki makamancin haka koda sau ɗaya”.
Duk wannan zance da suke faman zubawa akan yabon Bilkisu da jinjina himmarta Jawaad na zaune shima a cikinsu, yana sanye cikin baƙaƙen suit kamar sauran da a kullum suke ƙara masa kwarjinin kasancewarsa ma'aikaci, sai dai ya cire rigar sama, yana zaune ne kawai da baƙin dogon wandon da rigar ciki mai dogon hannu kalar kore mai haske, maɓallan rigar uku a buɗe, hakanne ya bayyana singlet ɗinsa kaɗan fara tas, yaci zanzaro, ya tsuke ƙugunsa da belt kalar shirt ɗinsa.
Abinda zai baka mamaki ko tari bai yiba akan maganar, baima nuna ya fahimci mi suke tattaunawarba sam, yana zaune ne ƙafa ɗaya kan ɗaya tamkar wani basarake, kansa sunkuye yanata faman danne-danne a cikin tab... ɗinsa ta kamfanin Apple, sam fuskarsa babu wata walwala, kuma ba'a tsuke take sosaiba.
Aliyu ne yakai dubansa garesa, tare da faɗin, “Ka fuskanci abinda muke tattaunawa game da yarinyarnan kuwa Jay?”...............✍

ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.Typing📲

ƘWAI cikin ƘAYA!!

Bilyn Abdull ce🤙🏻

BOOK TWO

Page 4
...............Shiru tamkar bazai tankaba, kusan sakanni sha biyar kafin yay magana batare daya bar danne-dannen tab... Ɗinba balle ya kallesu, “Wace yarinya kenan?”. Yay tambayar cikin nuna halin ko'in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login