Showing 51001 words to 54000 words out of 261165 words

Chapter 18 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1111

hannunta ke gab da kaiwa jikin Bilkisu da batasan Rose ɗin na kantaba ma, dan barci take cikin kwanciyar hankali da jin daɗi, harma ta manta a inda take kwance.
        A firgice Rose ta janye hannunta tare da ɗago idanunta da juyowa domin tabbatar da abinda take zato, ilai kuwa shine fuska a murtuke babu alamar wasa tattare dashi balle sassauci, ya saki hannunsa dake harɗe a ƙirjinsa yana cigaba da watsa mata wani mugun kallon daketa tsitstsinke jijiyoyin jikinta da hanjin cikinta, “Mi kike shirin yi da?” ya faɗa muryarsa cike da tsanarta irin wadda bata taɓa ganiba a gareshi. Da ƙyar Rose ta haɗiye ɗan yawun data tattaro a maƙoshinta, tace, “Ni babu abinda zanyi, kawai dai na shigone na ganta anan kwance____” “Shine zaki tada ita saboda a kanki take kwance?”. Yay saurin ƙarasa mata zancen data ɗakko yana tsatstsareta da idanu. Fuska ta sake tsukewa cikin tsananin kishi tace, “Ni wlhy yarinyarnan batai minba”. Wani banzan kallo sama da ƙasa yay mata ya ɗauke kansa yana faɗin, “Saiki kasheta ai”. Kamar zatai kuka tace, “Amma boss wai miye haɗinka da ƙwailar yarinyarnan? dako mace bata gama zamaba ma”. Tsaki yayi ya juya zaibar wajen yana faɗin, “Duk abinda ke ranki shine tsakaninmu, kozaki hana?”. Tamkar rose zata fasa kuka tabishi da kallo, yana zama Su Hafiz na shigowa da sallama, hannun Aliyu ɗauke da leda mai tambarin gidan abinci, duk kallon Rose sukai ganinta tsaye tamkar gunki tana kallon Jawaad da tamkarma baisan da itaba, ga fuskarsa a matuƙar ɗaure alamun zuciyar na kusa, mai tsautsayi ya taɓa a fashe masa ita. Hafiz ne ya fara janye idanunsa daga kan Rose ya sauke akan Bilkisu dake kwance tana barcinta lulluɓe da rigar Jay, har yanzu ko motsi bataiba dukda ihun da yayma Rose ɗazun, kafin suma su Jabeer su lura da ita. Babu wanda yace komai a cikinsu, shi kuma Jay baiko ɗago yama kallesuba balle su saran zai tanka.
       Aliyu ya matsa inda Jay yake ya ajiye ledar yana faɗin, “Ga abinci, kasa munje munata jiranka a wajen ashe kai kanama nan ka manta damu Boss”. Ɗago ido Jay yay fuska a yatsine ya harari Aliyu batare da yace komaiba, shi dai Aliyu zama yay abinsa bai kulashiba, Jabeer ma yaja kujerar kusa da Aliyu ya zauna yana haɗiye dariyarsa, dan ya lura Rose suman tsaye tayi a wajen kokuma ta samu gushewar hankaline na wasu mintoci.
       Hafiz yay guntun tsaki yana harar Rose, “Ke kuma lafiya kika wani tsaya ƙiƙam kamar wata dogariya?”. Numfashi Rose ta kawo cikin dawowa hayyacinta, ta watsama Hafiz harara kafin ta nufi ƙofar fita batare data tankama kowa a cikinsu ba, jikinta sai rawa yakeyi. Tana fita Jabeer ya kwashe da dariya, duka Hafiz yakai masa ya duƙe, Jay ya galla masa harara da faɗin, “Dilla malam miye haka?”. “Me nayi ni?” cewar Jabeer dake rama harar da Jay yay masa, ya cigaba da faɗin, “Kai ka dace da wannan tambayar baniba boss, sai neman haukatar da yaran mutane kake kana wani cijewa, gwara idan son yarinyarnan kake kafito ka sanarma duniya ka kuma shiga cikin ƴan takara ko Rose ta dawo hankalinta, kuma ka kwana da sanin Qaseem son yarinyarnan yake, yasin ka tsaya kallon ruwa ƙwaɗone zaima ƙafa, saboda gida ɗaya suke kwana suna tashi, dan a ruwa kake kusa da kada malam”. A fusace Jay da dama kaɗan yake jira ya miƙe, ƙofa ya nunama Jabeer yana huci, “Tashi ka fita a office ɗinan Jabeer kafin nama rashin mutuncin da bazaka taɓa mantawaba, banason wasan banza kaima ka sani ko”. Miƙewa Jabeer yay yana taɓe baki, yasan fitar tasa shine mafi alkairi dan Jawaad a wuya yake, shikuma idan yay zuciyar da har ɓacinta ya fito a muryarsa kai nesa dashi yafi komai alkairi, idan ya huce da kansa zai nemeka yay maka bayani harma daban haƙuri idan yasan yamaka abinda bai daceba. Ficewa Jabeer yay yana murmushi da girgiza kai. Jawaad ya koma ya zauna yana ƙwafa, sai kuma ya miƙe ya nufi toilet yabar su Hafiz dake binsa da kallo.
       A sanyaye Aliyu yace, “Sonta yake amma kamar shima bai fahi

mci hakaba Hafiz”. Cikin damuwa Hafiz ya bama Aliyu amsa da cewar, “Na daɗe da fahimtar haka Aliy, ba fahimtace baiyiba kuma shima, sarƙaƙiyar dake cikin al'amarin yarinyarne yake sakashi ƙoƙarin haɗiyewa, sai dai kuskuren daya kasa tunawa shine, ba kowanne irin SO bane yake haɗiyuwa lokacin da ake buƙata, wani koda ka korashi da ruwan haƙuri dana juriya a maƙoshi yake tsayawa ya tsaida dukkanin muhimman al'amuranka wucewa cikin zuciya da ƙwaƙwalwa,  ni kaina na waiga ta kowacce kusurwa bashi da wani magoyin baya akan al'amarin yarinyarnan sai sashe ɗaya, shi kuma baida wani ƙarfin iko akan hakan”. ajiyar zuciya Aliyu ya sauke mai ƙarfi yana dafe kansa, sai kuma ya ɗago ya kalli Hafiz dake kallon inda Bilkisu take, yace, “Minene mafita yanzu Hafiz? Jay yana buƙatar mace a kusa dashi sosai ta kowanne ɓangarema kuwa, yarinyarnan kuma tanada mafi yawan nagartar data dace ta zame masa abokiyar rayuwa, mizai hana mu bashi shawarar ya sanar mata ABINDA KE RANSA”. Numfashi Hafiz ya sauke yay shiru na wasu sakkani yana nazari da bubbuga yatsansa akan baki, ya kalli Aliyu yana kaɗa kai, “Aliyu ita kanta yarinyarfa bamuda wani ƙwarin gwiwar samun goyon bayanta, dan tayi nisa wajen son ɗan uwanta, sannan bana tunanin zata iya barin Qaseem kodan halaccin mahaifinsa a rayuwarta ta ɗauki waninsa, shiyyasa nace maka akwai sarƙaƙiya takowacce kusurwa, Kasan Jabeer yanada fiƙira akan irin waɗannan al'amuran, sai dai shi matsalarsa saka wasa a dukkan lamarinsa, bansan lokacin da zai dinga kallon abu mai muhimmanci a muhallin daya dace ba, amma mubari zuwa weekend sai muyi zamana musamman akan maganar”. Cikin gamsuwa Aliyu yace, “Shikenan ALLAH ya kaimu”. Fitowar Jay daga bayi fuskarsa jiƙe da ruwa ya sakasu yin shiru, babu wanda yace dashi komai yazo ya zauna a kujerarsa, Hafiz ne ya fara miƙewa yana faɗin, “Bara muje zuwa anjima ma dawo muyi maganar idan ka samu lokaci”. Kai kawai jay ya ɗaga amma baice uffanba.

      Fitar su Aliyu babu jimawa Dad ya iso station ɗin su Jawaad, ba'a bashi damar shigaba saida ya kira Jawaad a waya, tamkarma Jawaad bazai ɗauka wayarba sai wani tunani yazo masa a rai, hakan yasa bayan wayar ta katse yabi bayan kiran Dad shi ya kirashi. Koda ya sanarmasa yana gate sosai mamaki ya kasheshi, amma sai yabama securitys ɗin umarnin a rako Dad office ɗinsa, shaf ya manta da Bilkisu dake kwance tana barci.
        Bai nunama Dad komaiba yay masa tarba ta mutuntawa, bayan sun gaisa ya bashi ruwa Dad ya fara magana cikin karyar da murya. “Jawaad”. Yanda ya kira sunansane ya sakashi ɗaga kai ya kallesa, ya amsa da “Na'am”. “Jawaad wajenka nazo gwiwoyina a ƙasa da tarin magiya da roƙon da idan kamawa tai na duƙa a gabanka zanyi hakan. Dan ALLAH ka tausayama Mamana ka dubi al'amarinta, bazan musamaka ba akan ita mai laifice damu kanmu, sai dai ince dan ALLAH mu manta da baya domin ta shuɗe, wlhy ina mai tabbatar maka duk wautar dake kan Mamana a yanzu babu ita, dan ta gurzu da horonka, ka tausayamin kodan ciwon dake tare da ita na hawan jini da likita ya sanar mana, badan tanada sauran shan ruwaba faɗuwar da tai jiya a gidanku likita ya tabbatar mana da sai ta kamu da paralysis, wlhy yarinyarnan tana sonka fiye da yanda kake zato ko tsammani........” Jawaad da kansa ke ƙasa yace, “Kayi haƙuri Dad ban katsekaba, da Huda na min irin wannan son da bazata guji haɗa zuri'a daniba, yakamata mu fahimci Hudah ta huce sahun ƙuruciya yanzun, bai kamata ace duk abinda yazo zuciyarta tai tunanin aikatashi shine mafi dai-dai a rayuwarta ba, sannan kuma abinda takeso ace dole saita samesa, dolene duk inda akwai take wataran za'a samu babu. batason haihuwa yanzun miyasa ta yarda tai aure? Bata shirya zama kamar kowacce macen aureba miyasa ta zaɓi muyi aure? A ganina da sai ta bari sai lokacin da duk ta shirya waɗan nan, Dady ni bahaushene, uwata bahaushiyace, mahaifina bahaushene, dukkanin dangina hausawane sai fulani, addinina shine musulunci, addinin iyayena da dangina duk musuluncine, tayaya Hudah take tunanin zan biye mata na ajiye dokokin UBANGIJINA na ɗauki son zuciyarta?, tayaya take tunani zan ajiye al'adun yarena dana tashi

cikinsu na ɗauki ra'ayinta data aro a wajen wasu?, ai duk duniyar da zan shiga dady ina alfahari da abubuwannan guda biyu, YARENA ADDININAH, banajin kunyar nuna kaina a gaban kowanne mahaluki da tambari kasancewata musulmi, dan rahamace babba a gareni da wofantar da ita babbar asarace da bata da madadi duniya da lahira, a duk duniyar dana shiga zan kira kaina bahaushe, koda wanda nake tare dashi baitaɓa jin sunan yaren hausa ba ma zan tabbatar masa da yaren ya fara saninsa a lokacin kuma nai masa AlFAHARI dashi saboda yarena ne, shine harshen da UBANGIJINA yafi ganin ya cancanta na fito a ciki ya zama abin maganata, to mizaisa na ƙyamacesa saboda yaren wasu da ko za'a kashesuma basusan nawa ba, wlhy Dady idan ka cire LARABCI daya kasance yaren MANZON ALLAH (S.A.W) to babu wani yare da yakai muhimmancin dazan fifitashi sama da yarena na HAUSA, duk yaren da kaji yafita a harshena saɓanin LARABCI da HAUSA to inayinsane saboda lalurar mu'amulla da mutane badan ina kallonsa a saman nawaba. Kayi haƙuri Dad mubar wannan maganar kawai, ku tayamu addu'ar ALLAH ya bama kowa dai-dai da ra'ayinsa ni da ita, dan nikam Hudah tafi ƙarfina”.
          Jikin Dad duk yayi sanyi da maganganun Jawaad, dan kuwa dukkan abinda ya lissafa matsalace mai tushe da shima yanada kaso mafi yawa wajen ƙirƙirarta ga ahalinsa, to amma yanzu bata wannan akeba, matsalar mamansa itace gaba da komai. Ya nisa cikin girgiza kai da raunana murya fiye da farko yace, “A karo na babu adadi Jawaad zan kuma cewa kayi haƙuri, ina mai tabbatar maka a yanzu zaka sami mamana a yanda kakeso kuma kake buƙata”.
            Shiru Jawaad yay yana mai kallon Dad cike da tausayi, dan yasan shine ginshiƙin ruguza gidansa wajen sakaci, gashi a yanzu abinda ya raina yayi gawurtar da al'amarinsa yafi ƙarfinsa amma shi baima fahimtaba, cike da girmamawa yace, “Kayi haƙuri Dad zanzo gida na sameka idan na tashi aiki insha ALLAH, wannan maganar bata nan baceba, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. Shiru Dad yay ya kasa tashi, dan gani yake tamkar Jay yawo da hankali zai masa, saboda yasan taurin kan yaron da kafiya idan ya juyama abu baya, tun yana yaro ya fahimci wannan shegiyar halayyar tattare dashi, shiko buƙatar ƴaƴansa bai haɗata da komai a wannan duniyar ba. A bazata Jawaad kawai sai yaga Dad tsuggunne gabansa yana faɗin, “Jawaad dan girman ALLAH karka wofantar da maganar n....” da sauri Jawaad ya miƙe jikinsa har rawa yake ya tanƙwaɓe wayarsa dake kan desk ɗinsa ta faɗi ƙasa, baibi takantaba ya kama hannun Dad yana faɗin, “Ya ilahi, Dad dan ALLAH ka tashi, minene kakeyi haka? Wlhy na tabbatar maka zanzo muyi magana a gida” da ƙyar Jawaad ya samu Dad ya tashi tsaye, gaba ɗaya al'amarin yana neman birkita masa ƙwaƙwalwa, wane irin ubane Dad? Wane irin kalar mugun so ne wannan yakema ƴaƴansa? Abin yayi yawa matuƙa, kowanne iyaye nason ƴaƴansu amma na Dad yana neman wuce hankali. Shidai Jawaad sai ya koma lallashin Dad ɗin ya samu suka fita yay masa rakkiya ya tafi, gaba ɗaya kansa a cinkushe yake, harma ya fara masa wani masiffen ciwo tacan ciki.

        Koda ya dawo office da shashshekar kukan Bilkisu ya fara cin karo, tun shigowar Dad ta farka, dukkan maganganun da Dad sukai da Jawaad kaf ta jisu, takuma fahimci kaso mafi yawa na dangane da matsalar data raba aunty Shahudah da mijinta, Dad ya bata tausayi matuƙa gaya yau, babban mutum kamarsa da ya haifi ɗan da yafi Jawaad amma yake tsugunawa a gabansa domin kawai farin cikin ƴarsa, wanne irin makahon so ne haka Uncle ɗin nata kema zuri'arsa?, a ganinta lokaci yayi da zata bada gudunmawarta ga Dad ko ƴar kaɗance......
      Jawaad tsaye yay a ƙofa hannunsa duka biyu cikin aljihun wandonsa ya zuba mata ido, ransa a dagule yake, sannan ita kuma baisan ma'anar kukan nataba balle inda ya dosa, hakanne ya sakashi jan wani shegen tsaki ya cigaba da takowa cikin office ɗin batare daya sake kallonta ba. Har cikin zuciya da ruhi tsakinsa ya taɓa Bily, hakan ya sake jawo gudun ruwan hawayenta babu ƙaƙƙautawa, ta cigaba da kukanta na tsawon wasu mintuna shi kuma yana cigaba da aikinsa tamkarma baisan da zamanta a office ɗinba. Dan

kanta taji kukan ya isheta ta share hawayenta ta tashi ɗauke da rigarsa a hannu ta nufesa. A tsorace zuciyarta take, amma wani sashe na bata ƙwarin gwiwa akan abinda take shirin yi. Gaban Jawaad taje ta durƙusa kanta a ƙasa. Jawaad da yaƙi ɗagowa ya kalleta dukda yanajin motsinta ya cigaba da aikinsa.
         Karan farko a rayuwar Bilkisu data shirya ambaton sunan Jay a harshenta harma da ƙarfin halin furtawa a gabansa, sai dai tayi imanin bazata iya ambaton sunansa da kallonsaba a yau, dan haka ta duƙar da kanta tana durƙushe akan gwiwoyinta, rigarsa riƙe a hannunta ajiye akan cinya, tace, “Yah Jawaad!.…….”
     Cak Jay dake rubutu a wasu takardu ya tsaya tamkar wanda aka tsaida da remote, shi bai kalleta ba, kuma bai cigaba da abinda yakeba, saima lumshe idanunsa da yay yana sauraren sarawar da kansa ke masa da harbawar jijiyoyinsa harma da gudun jininsa daya tsinke a lokaci ɗaya. Bilkisu daba kallonsa takeba ta cigaba da faɗin “Dan girman ALLAH Yah Jawaad kayi haƙuri karka wofantar da magiyar Dadynmu, wlhy ni shaidace aunty Shahudah na matuƙar sonka, duk da bansan ainahin matsalarkuba inada yaƙinin zaka iya amfani da son da take maka ka canjata, matsalar da duk kake ganinta da ita ƙirƙirarriyar matsalace dakeda tushe a gareta tun tana tsumman haihuwa, ba laifinta bane ita kaɗai haka ta tashi taga kanta itama, bata isa banbance baƙi ko fariba a buƙatar jin zafi saboda an nuna mata hakan shine dai-dai da rayuwarta kuma nasararta, Mahaifina yasha faɗamin, {Bilkisu, aduk lokacin da zama ya haɗaki da mutane ki fara nutsuwa ki fuskanci halayyarsu da tsarin rayuwar da suka rayu, dan babu wata zuciya dake gogayya da ƴar uwarta akan hallayya iri ɗaya, lokacin da k tarbiyyarki ta baki dai-dai a wajen wani shi kuskurene, abinda yake kuskure a yaƙininki a wajen wani dai-dai ne, idan har kika kasance cikin mutane masu fahimtar ilimin duniya ina mai tabbatar miki zaki zama nasararki sama data kowa koda ace ke kaɗai kike kallon kanki a wannan nasarar,  daga lokacinda ilimin sanin hallayar ɗan adam ya dawo tafin hannunki inada yaƙinin zaki gyara ɓarna da yawa, domin zakibi mutum da halinsa ki ɗorashi akan hanyarki mai nagarta batare dashi yasan ya afkaba ma, munzo zamanin da halin ɗan adam dashi ake cinsa da yaƙi bada takobiba, zauna dame ƙinki da zuciya ɗaya, ƙyautata masa kuma da yaƙinin neman sakamo wajen mai badawa ba ga shiba, koda shi a kullum zai kasance mai bibiyar bayanki da sharri, karki zama mai damuwa da zama gwana a duniya, dan wani lokacin nasarar duniya faɗuwace gamai ita, koda idanun duniya na kallonsa a saman kowa, mai kuma sa'a fiye da kowa}, Yah Jawaad ba soyayyarka kawai aunty Shahudah ke buƙataba, a yanzu tafi buƙatar ka jingina da soyayyar tata ka ɗorata a hanyar tsira domin kaikaɗaine zata iya saurara, saboda girmamaka a matsayin gwaninta, na yarda dakai ta kowanne fanni koda banida ilimin sanin ɓoyayyun halayenka, ina sake roƙonka a matsayin Yaya ba shugabana a wajen aikiba, dan ALLAH ka ceto rayukan bayin da zukatansu suke a rufe ruf akan sanin gaskiya da makomar bin hanyarta, yahudanci da nasaranci duhune, wannan duhun kuma shike mamaye da jama'ar gidanmu, sai dai hasken ruɗani da gushewar banbance mai tsafta ya hana ijiyarsu ganin kowanne tsani sai wanda suka hau, kullum fatana ALLAH ya kawo musu drivern dazai fidda rayukansu a kwale-kwale saboda ni nayi ƙanƙanta ƙarancin matsayin yin wannan jagorancin, kaiko inada yaƙinin zaka iya, domin son da sukema aunty Shahudah gyaruwarta tamkar gyaruwar kaso mafi yawane daga ahalin gidan, ciki kuwa harda Dad da tuni ya fahimci gaskiya, sai dai ƙarfin riƙonta a garesa da tafi ya hanashi nunawa ko a fuska, ya gwammaci ya haɗiyeta a rai yacigaba da rainon ƴaƴansa tamkar ƴaƴan agwagi da basa bin uwa sai dai ita ta bisu” na ɗago kai a karo na farko tunda na fara maganar na kallesa, sai dai a mamakinna shi ba ni yake kalloba, gashi yayi kicin-kicin da fuska irin yanda ban taɓa ganiba a tun sanina dashi, na raya a raina saitna dire abinda na fara, dan haka nace, “Dan ALLAH Yaya Jawaad ka yarda a maida aurenku da aunty Shahudah a karo na b....i...y...u.”
         A yanda y

a juyo ya sauke rikitattun idanunsa a kainane yay masifar hargitsani na ƙarasa kalmar ƙarshe da ɗai-ɗai.............✍

Tab wlhy badaniba nayi nan, idan ya huce na dawo na ƙarasa muku yanda aka ƙare🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼🚴🏼kuma bily addu'ar fitowa lafiya itama, dan inaga ba'a taɓa karyata ba😂🤣.

Barkanmu da dawowa, inafatan kowa yayi weekend cikin ƙoshin lafiya?.😍😍[12/1/2020, 12:26 PM] HASNA✍🏻: Bilyn Abdull 📚:
Telegram link group ɗinmu kenan, dan wasu sunata tambaya cewa ya zasu shiga, indai kana tele to kawai ka antaya MASARAUTAR BILYN ABDULL tanan.

https://t.me/joinchat/TIsXYRvhtri2kQ9E4x7w6g


Page 19

................Idanunsa sunyi masifar kaɗawa sunyi jajur, batare da yace dani komaiba yaymin nuni da ƙofa alamar in fita, kasa koda motsi nayi, sai hawaye dake cigaba da ambaliya a kumatuna tamkar an buɗe fanfo.
          Cikin matuƙar kaushin murya da tsawa na tsinkayi furucinsa cikin kunnuwana, “Miemaa! niɗin sa'anki ne ko?!”. Da sauri na shiga girgiza masa kai jikina na rawa saboda harga ALLAH na matuƙar tsorata da yanayinsa. Ya sake faɗin, “Tashi kifita a office ɗinan kafin naimiki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login