Showing 168001 words to 171000 words out of 261165 words
Chapter 57 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
naita addu'a da fatan su kawo tunda nai sallar asuba, sai da sukai laushi sosai sannan na tace tsaf na ɗauraye tukunya na zuba, ban kunna gas ɗinba tukunna na ɗib
a wake gwangwani biyu da rabi shima nai zaman dakawa aɗan turmina, sai da yaymin yanda nakeso sannan na cire na wanke shima nai markaɗan ƙosai, saida na tabbatar na haɗa komai sannan na kunna gas, ban rufeba tukunyar kunun ba gudun karya taso ya zube saboda gafin gyaɗa, na saka ludayi ina motsawa a hankali har yay zafi ya fara kauri, cikin amincin ALLAH baiyi ƙurnu ba yay ƙyau abinsa sai ƙamshin gyaɗa da kwakwa ke tashi, na sauke tukunyar a ƙasa danya ɗan huce kafin na saka madarar dana dama. Suyar ƙosan na fara wanda dandanan na gama kasancewar bawani yawane da shiba, na zuba madarar a kunun sannan na zuba ma maigadi muma na juye mana namu, saida na gyara komai tsaf sannan na fito da namu a Dining na maigadi ma na fito dashi na ajiye gefe. Baya a falon, dan haka naɗan gyara tunda babu wani datti na azo a gani na saka turaren wuta. Ina kammalawa yana fitowa, yay tsaf cikin ƙananun kaya sai baza ƙamshi yakeyi.
Baice dani komaiba ya ɗauki abincin maigadi ya fita, babu jimawa sai gashi ya dawo, lokacin ina a Dining ɗin ina ƙoƙarin haɗa masa nasa, kujera yaja ya zauna idonsa akan hannuna da har yanzu yake raɗam da ƙunshi.
“Duk a yaushe kikai wannan?” na tsinkayi muryarsa a bazata. Kallonsa nai na janye idanuna, nace, “Yanzun”. “Kinyi ƙoƙari, ALLAH yay miki albarka”. Murmushin daban niyyaba na saki sai naji duk fushin nawa yay ƙasa, a hankali nace, “Nagode”. Shima murmusawa yayi kaɗan da ɗaukar ƙosan yakai bakinsa, ya lumshe idanu da faɗin, “Uhhhmm”. Kallonsa nai dariya na cina, na ɗauki cokali nasa gefensa alamar waiji. “Yarinya ai ba santi nakeba” ya faɗa yana jan kofin kunun dana ajiye masa a gabansa sosai. “Nima ai bance santi kake ba”. “Kin taimaki kanki to”.
Murmushin na sakeyi ina ƙoƙarin haɗa nawa nima.
Nayi mamakin yanda yaci sosai, ya ɗauki tissue yana goge bakinsa damin almar komai zamm da hannu👌🏼. “Nagode to” nafaɗa ina murmushi. Zagayowa yay ta bayan kujerar da nake ya ranƙwafo ya sumbaci kumatuna duka biyu sannan yace, “Kin gama mallake Jay da komansa Miemaa”.
Hannu nakai na shafi fuskarsa ina faɗaɗa murmushina, dan naji yanda ya nuna jin daɗinsa da abincin.
ya zagayo ta gabana ya nunamin kuncinsa alamar na sumbata. Dukda inajin kunya haka na daure na sumbacesan kamar yanda yake buƙata. Sassanyan numfashi ya sauke da juyamin ɗayan, nanma dai yi nayi ina mamakin rashin kunyarsa. “Jazakhillah bi jannah” ya faɗa yana kamo fuskata cikin tafukan hannayensa, kafin nace wani abu ya manne bakinsa da nawa.
Yana saki na saka hannu na rufe fuska. yace, “Daga baya kenan. Bara naje Alhaji Babba na jirana zamuje wani waje”.
Miƙewa nai tsaye nima, “To dan ALLAH ka kira Nabeelah tazo ta tayani zama, ALLAH babu daɗi kaɗaicin”. “Baga wuta ba, kuma nima aiba daɗewa zanyiba”. Cikin marairaicewa nace, “Idan suka ɗauke fa, kumafa ni tsoro nakeji”. “Jami'ar tsaro da tsoro”. Ya faɗa yana jan hancina. Bai jira amsataba ya fice yana faɗin “Aimana addu'a”.
Da “ALLAH ya tsare” na rakasa inajin duk babu daɗi...................✍
Jiya kam Wattpad yay muku buƙulu, nayi typing tun dare zan baku na nemesa na rasa, wlhy sai sake wannan page ɗin nai cike da haushi, gashi dai sai dai kuyi maneji da shi😥.
ZAAFAFAN LITTATAFAI GUDA GOMA da sukazo muku cikin ƙyawawan tsari a baya har yanzu suna nanfa a kasuwa.
SAFIYYA HUGUMA tazo muku da;
ƊAURIN ƁOYE
ALƘAWARIN ALLAH.
HAFSAT RANO tazo muku da;
SAUYIN ƘADDARA
ƊAURIN GORO
MAMU GEE tazo muku da;
BURI ƊAYA
ƘAUNAR MU.
MISS XOXO tazo muku da;
KAIMIN HALACCI
IGIYAR ZATO.
BILYN ABDULL tazo muku da;
WUTSIYAR RAƘUMI...
GUDU DA WAIWAYE....
abin birgewa books ɗinan duk sun wanzune akan farashi mai rahusa, guda goma duka 1k ne, guda biya 500, guda huɗu 450, guda uku 400, guda biyu 300, ɗaya 200 gamai buƙata zai iya tun tuɓar wannan numban domin samunsu a documents dan an kammalasu.
Katin waya mtn za'a turaahi tanan. 09032345899
sai kunma masu tura kuɗi ta bank zaku tura tanan 0225878823
Hafsat Kabir Umar GTB.
Saiku tura shaidar biyanku ta wannan number 0803 081 1300
Sai kunzo😍😍😍😘.
ALLAH ka gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[1/12, 4:57 PM] HASNA✍🏻: Typing📲
ƘWAI cikin ƘAYA!!
Bilyn Abdull ce🤙🏻
BOOK TWO
Page 47
..................A harabar gidan suka iske Alhaji babba zaune alamar isowarsu daman yake jira, kafin ma Sadiq ya fito ya buɗema Jay shi harya buɗe da kansa ya fita, fuskarsa ɗauke da murmushi ya ƙarisa ga kakan nasa da tun shigowar motar gidan ya ajiye jaridar dake hannunsa. Cike da zolaya Alhaji babba yace, “Kai angon nanfa kamin wayo, gaskiya nima azo a nomin ƴar bana bakwai auren nan zanyi ko kaurin wuya na ƙara da jar fata”. Sosai Jay ya ƙyalƙyale da dariya, ya zauna akujerar robar dake gefen Alhaji babba yana faɗin, “Duk gasarka dai ba zaka samo cancaɗeɗiya kamar tawaba Alhaji, domin tawa fa ta musamman ce”. “Ni dai banason cika baki, kar nan da wata biyu inga ka faramin zarya a gida ehe”. “Ai bama zanyin ba, sai dai kai ka ringa mana saboda zuwa cin tuwo”. Dariya suka sanya a tare, Jay ya rissina ya gaidashi cikin girmamawa, kafin su miƙe cike da farin ciki. Sadiq da shima tuni ya fito a motar ya rissina ya gaida Alhaji babba. Cike da kulawa ya amsa masa tare da sanya masa albarka. Jawaad ya buɗema kakansa mota da kansa, sai da ya shiga ya maida ya rufe sannan ya zagaya inda Sadiq shima ya buɗe masa. Kasancewar tun fitowarsu Jay ya bama Sadiq address ɗin inda suka nufa sai kawai kaka da jika suka cigaba da hirarsu, yayinda Sadiq keta aikin tuƙi abinsa.
Tun a farkon shigowa layin Sadiq yay tambayar gidan Malam ɗan inna. Kasancewar sanannen gidane kuma anga mota mai ƙyau dan danan suka samu rakkiya har ƙofar gidan. Gidane irin da ɗin nan, dan daga ƙofar gidan zaka iya kallon babban zaure dake da ƙatan murfi ja wanda wahaka ta sakashi komawa mai roɗi-roɗin baƙi. Sadiq ne kawai ya fita, cikin alnajiran dake zazzaune bisa dakalin gidan wasu na karatu wasu na rubutu a alluna wasuma hirarsu sukeyi ya ƙarisa. Duk idanu suka zuro masa, ya ɗaga musu hannu alamar sannu sannan yace, “Ƙannena dan ALLAH ko malam ɗan inna na nan?”. Babban gardi dake karatu da sauri-sauri tamkar zai haɗiye harshensa ya dakata yana kallon Sadiq ɗin. “Malam baya nan, amma ba nisa yayiba”. Sadiq dake saurarensa yace, “To masha ALLAH, dama baƙine muke tare dasu gasu a mota, idan babu damuwa ko za'a aika wani ya kira mana shi ne?”. Gardin baice komaiba ya gyara zaman allonsa ya sakko daga dakalin, zauren gidan ya shiga, babu jimawa sai gashi ya dawo. “Ku shigo” ya faɗa kawai yana kallon Sadiq. Sadiq baice komaiba ya juya ga motar, a saitin Jay yay knocking glass ɗin, Jawaad da gaba ɗaya hankalinsa na'a tattaunawa da Alhaji babba ya juyi tare da sauke gilashin motar. “Oga yaronsa yace baya nan amma bai nisaba, yace kushiga ciki inaga zaije ya kirashi ne”. “Okay” Jawaad ya faɗa a taƙaice yana maida kallonsa ga Alhaji babba dake saurarensu.
Kusan a tare suka fito, a take dukkan almajiran dake wajen suka zubo musu idanu, sannu kawai suke musu babu batun gaisuwa, su dai suka shige cikin zauren dake ƙaton gaske, sai dai ko'ina mulmule yake da suminti, sai alluna masu yawan gaske dake jijjingine da kowacce kusurwa ta bangon zauren. Zama sukai a tabarmar da aka shinfiɗa, Sadiq dai dama bai biyosu ba sai Gaddin nan kawai. Saida yaga sun zauna sannan ya shige wata ƙofa alamar cikin gidanne, babu jimawa sai gashi ɗauke da kofin silba babba. ya ajiye a gabansu sannan ya gaishesu. “Bara naje na kirashi yana nan ƙasan layi suba wata mata mara lafiya”. Alhaji babba ne kawai ya amsa masa, ahi Jay ma dai kallon Gaddin yake cike da nazari.
Kusan mintuna talatin da fitar gaddin nan sai gashi ya dawo tare da Dattijo, daka gansa kasan akwai wahalar rayuwa tattare da shi, dan tsufan nasa yafi shekarun yawa a zahiri. Tun shigowarsa Alhaji babba ya shaidashi tsaf, dan kamanninsa na ƙuruciya duk suna a tare dashi, ya ɗan murmusa yana sake girmama buwayar UBANGIJI.
Sannu da zuwa shi dai malam ɗan inna keta zuba musu, ya zauna saman buzunsa dake fuskantar su Jawaad, shima dai kallon sani yakema Alhaji babba, sai dai ya rasa a ina yasan fuskar ne?. Hannu ya fara bama Alhaji babba suka far gaisawa, sannan ya miƙama Jawaad shima suka gaisa. Cikin ɗan tsantseni yace, “Sai dai kuma ban gane baƙin nawa ba duk da ina musu kallon sani sai dai na rasa a ina?”.
Murmushi Alhaji babba yayi yana gyara zamansa, yace, “To bazan musa makaba, sai dai nasan ƙila kamanni kake gani kawai. Da farko dai sunana Nuhu. wannan jikanane sunansa Jawaad, munzo neman wani bawan ALLAH ne mai suna Adamu”.
Malam ɗan inna ya kafe Alhaji babba da kallo, dan yanzukam ya gano ta inda ya kema Alhaji babban kallon sani, to amma abin tambaya shi wanene? Haɗiye wannan tambayar yayi a ransa, a fili yace, “To Adamu dai biyu ke garemu, ɗaya muna kiransa Ado, yanzu haka yana can balaguro kudu damu, shiɗin babban ɗanane, yanada iyalinsa duk suna man cikin gida tare damu, sai kuma ɗan ƴar uwata shima sunansa Adamu, amma ana kiransa Adamu makaho, shikam dai ALLAH yay masa rasuwa shekara kusan ta takwas kenan, matarsa ma ta rasu kafin shi”.
Su jay suna jira suji yace yana da ƴa sai sukaji yay shiru.
Alhaji babba daya haɗiye mamakinsa ya gyara zama yana faɗin, “Masha ALLAH, mu munzo neman Adamu makahon ne, ashema ALLAH yay masa rasuwa?”. “Tabbas ya rasu dalilin mota data bigesa”. Ƙwallar data cika idon Alhaji babba yasa bakin rigarsa ya share yana ɗan murmushi, “ALLAH ya gafarta masa shi da matar tasa”. Amin ya rabbi, da Alhaji ɗan inna suka faɗa a tare.
“Mahaifiyarsa fa ko ita tana raye? Sannan shi baibar zuri'a ba ne?”. Alhaji babba ya faɗa cikin ƙarfin hali.
Alhaji ɗan inna ya jinjina kansa, “Mahaifiyarsa ta jima da rasuwa, dan dalilin jinyane ma ya maidota gida saboda shekaru da dama ba'asan inda takeba ita da ɗan nata, sai kawai rana tsaka muka ganta tare dashi, adalilin jinya ya matsa suka dawo gida, dan shi makanta ta samesa ta idi ɗaya tun ƙuruciya dalilin ƙyanda, to ganin inda suke babu mataimaki sai ALLAH ya matsa mata harta faɗa masa tushenta suka dawo, kowa ƙin yarda ta raɓesa yay a cikin dangi, sai nine na bata masauki a gidana, na kuma riƙe shi Adamun tamkar sauran ƴaƴana har nai masa aure, bayan aurensa da shekara kusan huɗu ALLAH yay ma yaya Sa'a rasuwa. Shi adamun da anan cikin gidan nawa suke zaune shi da matar tasa mai suna Asiya, itama tanada nakasar ƙafa dan gurguwa ce. Daga baya kuma sai suka tashi”.
Kafin Alhaji babba yay magana Jay yay saurin faɗan, “Miye dalilin tashin nashi? Sannan kuma basu da yarane? Naji baka amsa wannan tambayarba”.
Malam ɗan inna yaja fasali yana sake gyara zamansa a karo na babu adadi. “Mudai a saninmu Adamu baida wasu ƴaƴa, amma kuma al'amarinsu dalilin wata ƴa ƙwallin ƙwal yazo ma mutane da ruɗani musamman lokacin da tai girma kamanninta da nashi suka fita. Tun aurensa da Asiya bata taɓa ko ɓatan wata ba a gidanan, danni da kaina nan nasha basu taimako akan hakan ko za'a dace, amma har bayan rasuwa yaya Sa'a da kusan shekaru uku babu wani bayani daga matarsa, hakanne ya saka muka fara masa kwaɗayin kozai ƙara aure. Amma ya murje idonsa yace baisan wannan zanceba shi yana son matarsa. Munta lallaɓashi akan inma kuɗin auren yakeji karya damu zamu haɗa muyi masa, tunda dai maganar ciyarwa daga iyalina ake basu abincin dare da rana, na safe kawai yake samowa da yake yana ƴar sana'arsa ta gyran tsummokara. Sam bai saurari kowaba, dama yaga an takura masa da zancen sai kawai rana tsaka yazo mana da maganar zai tashi ya samu ɗakin haya a wata anguwa dalilin abokinsa. Munsha mamaki sosai da al'ajabi, dan bamuyi zaton gatan da muke masa har yakai abin zafin da zaiyi tunanin yin nesa damu ba. Hakan ba ƙaramin sqkamu ɓacin rai yayiba ainun, musamman ma ni da nake ganin na taimakesu shiga mahaifiyarsa a lokacin da kowa ya gujesu. Cikin fushi nace yaje abinsa, amma karya sake tunawa dani matsayin ƙanan mahaiyarsa tunda ya zaɓi mace sama damu. Suma sauran dangi duk sukai masa wannan furucin.
Baiko nuna yaji ko ɗarba ya tattara matarsa daƴan komatsansu sukabarmu zuwa can nesa damu sosai. Tunda suka tafi bamu sakejin ɗuriyarsu ba sai bayan shekara biyu sukazo mana nan matar tasa da ciki ƙarami, da farko kowa yaƙi saurarensa, amma ni saina sauraresa ganin abin farin cikin da matarsa ke tare dashi, shima ya nema gafararmu dukda wasu a cikinmu basuce dashi sun yafe ɗin ba. Matarsa ta cigaba da rainon ciki lokaci-lokaci sukanzo gaishemu, hakama yaranmu sukan ɗanje musu, idan kuma sabga ta tashi matarsa na zuwa har cikinta ya shiga wata takwas. Rana tsaka yazo ya sanar mana wai tana asibiti babu lafiya, likitoci sunce ɗan cikinta ya samu matsala cireshi zasuyi dan rabin jikinsa a ruɓe yake, ma'ana dai bamashi da rai kenan, suna buƙatar kuɗaɗen da za'ai mata tiyatar, shi kuma na wajensa basu kaiba amma dan ALLAH mu ranta masa a hankali zai biyamu idan komai yay dai-dai. To mudai bai samu ko sisiba daga garemu, dan bamu dashi saboda kuɗin sunda yawa gaskiya, haka ya tafi. Mukuma anan mukai shiri domin zuwa mu duba matar tasa sai dai kuma mun manta bamu tambayesa asibitinba. Haƙura mukai muka zauna zaman jiransa kozai sauyo saiya kaimu. To adai ranar bai dawo ba sai washe gari mu mukaje can gidan da yake hayar muka tambaya, daga can akai mana rakkiya asibitin, tun kuma kafin muje an sanar mana ai anmata aikin an cire ɗan babu rai. Amma abin mamaki sai muka isketa da jaririyar yarinya a hannu. Babu wanda ɗunbin mamaki bai kamaba a cikinmu, har muka kasa haƙuri mukai magana tunda ita amma ce ɗa namiji aka cire mata kuma baizo da raiba. Amma sai cewa sukai ai jaririyar dake wajenau itace ƴar tasu, yaran ƴan biyu ne, ɗayane babu rai ɗaya da rai. Sam bamu yarda dasu ba, hakan yasa mukai fushimuka bar musu asibitin, munta sauraren muga Adamu ya biyi bayanmu yay mana cikakken bayani akan gaskiyar al'amari sai mukaji shiru, a haka har shekaru suka shuɗa yarinya ta fara girma, kowa dai yasan tabbas ƴarnan ba ɗiyar Adamu bace akwai abinda suka ɓoye dangane da samuwarta, amma kuma a zahiri ga wasu abu na kamanninsa na bayyana ga yarinyar, sannan idan ka nutsu da kallon yarinyar lallai zakaga wasu abubuwan na Asiya tattare da ita dukda sam batayo asalin fuskarta ta fulaniba dan Asiya farace tas kuma ƙyaƙyƙyawar gaske, wahalhalun rayuwane kawai suka ɓoye kaso mafi yawa daga ƙyawunta, wannan abu shine ya kawo mana ruɗani maiban mamaki wanda har a yanzu da kuke a gabana bamu fita daga cikinsaba, kuma har Adamu ya rasu shida matarsa basu taɓa faɗa mana komai daya shafi yarinyarba”.
Alhaji babba daketa sauke tagwayen ajiyar zuciya na tausayin gudan jinin nasa da son zuciya ya saka mahaifiyarsa nisantasu ya share ƙwallarsa, muryarsa a raunane yace, “Tabbas bakai dake bamu labarin nanba, hatta dani nan ka sake dulmiyani a ruɗani, taya za'ai kuna zargin ba ƴarsu bace amma kuma take kamanni dasu ta wasu abubuwan? Koni dana kalli hotonsa da yarinyar naga tabbataccen jini na haƙiƙa tattare da junansu, na tabbatar koda kutu akaje wannan yarinya za'a iya tabbatar da tasuce babu wani haufi a cikin hakan”. “Tabbas hakane Baba, sai dai mai warware ainahin gaskiyar lamari sai ALLAH sai kuma su da suka kasance da yarinyar, gashi kuma a yanzu duk basa a raye”.
Jawaad da baice ƙalaba, saima latsa waya da yakeyi, batare da ya ɗagoba yace, “Yanzu Kunsan inda yarinyar take ku?”. Yanda yay maganar babu wasane ya saka Alhaji babba da Malam ɗan inna kallonsa, dukda yasan kallon nasa suke bai ɗagoba, baikuma gyara fuskarsa dake a ɗaureba. Malam ɗan inna da duk ya daburce yace, “E.. e eto saurayi yarinyar dai tana gidan da ayka zauna”. Ɗago idanu Jay yay ya kallesa, “Kenan babu wanda ya ɗauketa a cikinku bayan rasuwar mahaifinta saboda kunaji a ita ba jininku bace bayan kuma UBANGIJI ya baku komai a bayyane tunda ya fidda kamanin iyayenta a jikinta?”. “Saurayi ba haka bane ba”. “To yayane?”. Kasa cewa komai malam ɗan inna yayi, sai zufa data jiƙe ta cikin babbar riga, shi dama tun shigowarsa bai hangi sauƙi da ga yaron nanba sam.
Ajiye wayar Jawaad yayi yana fuskantarsa sosai, “Malam da farko dai yanzun bara na fito maka a mutum, wannan da kake gani dai shine mahaifin Adamu makahon, mijin ƴar uwarka Sa'a wanda ta gudar masa da ɗa bisa son zuciyarta, ina fatan ka gane”..
Sallalami malam ɗan inna ya kwaso daga samaniya ya dire bisa ƙasa yana zare idanu jikinsa na ɓari, “Wai dan ALLAH da gaske kana nufin Mati ne? Dama kana raye? Adamu yayta nemanka ruwa a jallo amma ko labarinka bai taɓa samuba daga wani, dangi da duk muka sani a baya mun sakashi ya abi amma duk sun rasu bai samu ko guda ba a ciki”.
“Hakane Hamza, kasan idan UBANGIJI nason saukar da wata aya ga bayi saiya datse al'amarinsu ya ɓoyesa a rasa bakin zaren a dalilin ƙaddara, muduka ƙaddarace ta ɓoyemu dukda muna a cikin gari ɗaya, nima nasha bibiyar ahalinku dalilin son ganin ɗana ya dawo gareni, sai dai hakan bata kasanceba har gashi ƙasa ta rufe idanunsa, hakan jarabawace, dan tabbas tun daga Zazzafar soyayyar danaima Sa'a har zuwa zaman aurenmu da guduwarta da yarona duk jarabawace a garemu da wata hikima ta UBANGIJI, naso ace na sake ganinsa, naso ace na kwatanta sauke haƙƙinsa dake kaina matsayin mahaifi a garesa,