Showing 135001 words to 138000 words out of 261165 words

Chapter 46 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete

17 Dec 2024

1151

tsinkayi muryarsa ƙasa-ƙasa saitin kunnena, da sauri na juya garesa dan a bazata maganar tazomin. A karo na biyu muka sake haɗa ido, sai dai yanzun duk yanda naso janye nawa kamar ɗazun hakan ya gagara, kallo yakemin irin na tsakkiyar idonnan tamkar zai haɗiyeni dasu, bazan iya jurewa ba, amma na kasa janyewa dan tamkar yamin ɗaurin goro ne da mayun idanun nasa da a yau suke farare tas babu sirkin ja alamar dai baya tattare da ɓacin rai. Da ƙyar na samu nai ƙoƙarin yin ƙasa da kaina zuciyata na wani tsitstsinkewa tare da jinin jikina. Amma a bazata saijin tattausan hannunsa nai ya taro haɓata ya sake ɗago fuskar, tuni zuciyata ta sake wani zallo tamjar zata faso ƙirji ta fito, Farfar na farayi da idanuna da suka cika taf da ƙwalla lokacin da ya matso da fuskarsa daf da tawa har munajin saukar numfashin juna, lumshe idanun kawai nayi ganin bani da wata mafita kuma, ya kawo bakinsa daf da nawa.
Yanda jikina ke tsuma zai tabbatar maka a matsanancin tsoro nake da yanayin, tsigar jikina duk ta miƙe.
Jay dake kallon yanda bily ta rikice ya saki lallausan murmushi tare da goga hancinsa kan nata, murya can ƙasan maƙoshi yace, “Matsoraciya kawai, darajar matata tafi ƙarfin nayi kissing ɗinta anan wajen yariya, hakan bazai taɓa yuwuba sai a fadata insha ALLAH. badan girman alƙawari ba da bazan taɓa bari ki shiga wajen nanba, ni kaɗai yafi cancanta na shaida wannan ƙyawu naki a cikin gidana. Ina ƙara maimaita miki bana son rawa”. Ya ƙare maganar da ɗaura yatsansa babba saman lips ɗina ya kwashe ɗan lipstick ɗin da aka samin.
Wata irin kunya naji ta lulluɓeni mai haɗe da tsoro da ɗan haushin gogen lipstick da yayi, nai ƙasa da kaina ina ɗan kumbura da faɗin, “Toni nama iya rawan ne ma.........”
Saukar ɗalli kawai naji a saman laɓɓana mai azabar zafin, na ɗago idanuna da suka cika da ƙwalla a kansa. sassanyan murmushin mugunta ya sakarmin har dimples ɗinsa duka biyu na loɓawa, ya ɗage kafaɗunsa yana ɗage gira ɗaya da taɓe baki alamar ni naja.
Kafin wani ya ƙara magana a ciki

nmu akai knocking glass ɗin motar, sauke gilas ɗin yayi, oga Hafiz ne yay masa magana akan mu fito. Banji amsar da ya bashiba, baice min komaiba nima ya fice, ina ƙoƙarin gyara alƙyabata nima na fita naji an buɗe ƙofar ɓangarena, na ɗago dan ganin wanene muka haɗa ido ashe shine ya zagayo tanan, hannunsa na dama ya miƙomin yana wani ɓata fuska da kallona ƙasa-ƙasa, a kunyace na ɗora nawa ya taimakamin na fita nima, hannunsa na haggu yasa yaja hular alƙyabar ya sake rufemin fuska da ƙyau.
Ina jiyo wani cikin baƙin abokansa na faɗin, “Sarakin kishi muma ba kalla zamuyiba ai bar wahalar rurrufe mata fuska”. banji ya bashi amsaba sai dariyar da sauran sukayi. Inajin irin zafin da nakeji a duk lokacin da ya raɓu jikina, sai dai yau kaɗan nakejinsa cikin amincin ALLAH, dan haka nai jarumtar daurewa tamkar banajin komai ina addu'a cikin raina har muka shige abokansa da ƙawayena na biye damu a baya cikin ƙyaƙyƙyawan tsari babu wata hayaniya.
Muna shiga da aunty Batool dake ƙofar tsaye tana jiranmu muka fara cin karo, ta shiga feso mana wani farin abu mai ƙyalƙyali da ƙamshi, masu hotuna kuwa nata ƙyalla mu.

Sauran mutanen duk suka miƙe idanun kowa na kan amarya da ango dake cike da birgewa, yayinda ƴanmatan family ɗin su Jay sukejin zafi a zukatansu dajin takaicin bilkisu da tazo daga sama tai musu wuf da shi, sai irinsu Rose da kallo ɗaya zakai musu ka hango tsagwaron kishi da tsanar bilkisun a cikin idanunsu. MC kuwa na zubama amarya da ango kirari. yayinda Ali jita ya sake gyara maƙogwaron nan nasa na zinari ya fara baitocin girma ga amaryar ƙamshi bilkisu mai gadon zinari cikin waƙarsa mai taken Bilkisu gimbiya.

(Bara naɗan raira muku kaɗan saura wani yace ban iyaba😣😚. lol)

🎸🎸🎶🎶BILKEESU zan faɗa dan ALLAH, mata ku bani dama duka.
bilkisu gimbiya.
BILKEESU mai gadon zinari waƙarki ta fita haka.🎸🎶🎶
BILKEESU sai gani sai nuni, kowa ya tabbata duka.🎸🎸🎸🎺🎺
BILKEESU gimbiya an baki, mata su dakata duka.🎸🎸🎺
BILKEESU sanya alƙyabar ki kaya mayalwata haka.🎸
Bilkisu gimbiya.
BILKEESU za'a yiwa fada, ai mata fifita haka. 🎸
Jita kaja muje nai waƙar Bilkisu masu girma haka.🎸
Mata ku rausaya Ali jita nine na baku dama haka🎸🎶🎶
Komai yanada rana a gane dama tanada dama haka, Bilkisu gimbiya.
Giwa ki rausaya BILKEESU ALLAH ya ƙara baiwa haka.🎸🎷🎷
Komai yaje ya dawo BILKEESU ku za'a tabbatarwa haka🎸
Ganga irin ta girma a miki waccan a mata garwa haka.🎸
BILKEESU za'a baiwa Number komai daren daɗewa duka
Bilkisu gimbiya
BILKEESU sannu mata irin na zamanin ɗebe kewa duka.🎸🎸
Kinsha aradu kinsha yasin, kin samu arziƙi duka.🎸🎷🎸🎷
Kin tsallakema tarkon maƙiya, ga ɗan abin biki haka.🎸
Kinzam sarauniya a cikin mata bar munafuka haka.
Bilkisu gimbiya🎸
Ga zamani da daɗi wannan al'amarinkine duka🎸🎸🎸
Tsarki na zuciya bilkisu ya baki ɗaukaka haka.
Kinsa kara a hanya BILKEESU wazata tsallakane🎸
Komai kina tunani Bilkisu baƙya abu daka haka🎸
Bilkisu gimbiya
Ga ilimi da halin girma, ALLAH ya ɗaukaka haka.........🎸🎷🎸🎷🎸🎺🎺🎺🎺

(Kunema sauran kuji na gaji😂😜)

“Mawaƙin nan dolene yaci ƙyautar mota”. Oga Aliyu dake bayanmu shida matarsa ya faɗa yana ƴar dariya.
Murmushi naga boss yayi a hankali lokacin da yake kama kafaɗuna yana zaunar da ni a ɗaya daga kujerar guda biyu da aka tanada danmu. Ni kaina waƙar tamin daɗi sosai, hakan ya sakani sakin murmushi da banyi niyyaba. Jay yaɗan lumshe idanu ya sake buɗewa a kanta sannan ya zauna a nashi mazaunin shima.

Babu ɓata lokaci aka fara gudanar da abinda ya tara mutane, an buɗe taro da addu'a kafin ai kiran Ummie tazo ta bada tarihin amarya a taƙaice, Hafiz ma ya bada tarihin ango tare da ɗorawa da shaƙiyancin randa suka fara gane Jawaad ya kamu da son amaryar tasa. Yanda yake faɗar wajen dole ya saka mutane dariya, masu baƙin ciki kuwa suka shiga zuba tsaki suna haɗiyar zuciya. Bily kanta sai da ta murmusa dukda tasan ba haka bane tunda ita

dai bai taɓa ce mata yana son nata ba, ɗagowa tai da nufin satar kallonsa sai suka haɗa ido, dan shima kallonta yake ƙasa-ƙasa idanu a narke.
Cike da salo ya wani ɗagemin girarsa ɗaya, maida kaina nai ƙasa zuciyata na motsawa. Ban sake gigin kallon sashen da yakeba nima na maida hankalina ga kallon mawaƙa da suketa baje fasaharsu cikin daɗaɗan waƙoƙi da duk an raira baitocinsune da sunayenmu. Umar m shariff, Ado gwanja, Nura m inuwa, Naziru Ahmad, Hamisu breaker, Isa ayagi, Abdul D one, kai abunfa ba'a magana, ƴan uwa da ƙawaye da abokan ango nata casar rawa, duk yanda mc keta magiya da roƙon amarya da ango su fito filin rawa ya hanani ko motsi, duk wanda ke buƙatar mana liƙi sai daifa yazo nan inda muke zaune ya liƙa mana ɗin, amma ko sau ɗaya bamu shiga filin rawarba.
Lokacin da Anum da Nabeelah suka hawo domin yima su Jay liƙi ba ƙaramin faɗuwa gabansa yayiba, itama ɗin dai sai da ta ɗora hannunta a ƙirji alamar gaban nata faɗuwar ya keyi, dama tun sanda su bilkisu suka shigo saida gabanta ya faɗi, jikinta a sanyaye ta liƙa masa kuɗin shi da bilyn suka sauka ko jin surutun da Nabeelah keyi bataiba. Duk bilkisu na kula da yanayin da boss da Anum ɗin suka shiga, dan harta sauka yana binta da kallone.
Tun ɗazun nake wuwwula idanu ko zanga Yah Anuwar, haka kawai nakeji a raina bana son su haɗu da boss yanzu anan, to bammaga su Abdur-raheem bama. Da hannu na yafito Anum, ta taso zuwa gareni. Cikin magana ƙasa-ƙasa nace, “Ina Yah Anuwar?”. Tace, “Tab aishi bayason bidi'a, da wahala idan zaizo wajen nan, amma bakiga yanda mijinki ke kama da Yah Anuwar ba? Nifa dana kallesa gabana sai ya faɗi wlhy bilkisu”. Murmushi na mata da cewa, “Karki damu zamuyi magana amma ba anan ba”. Kanta ta ɗagamin ta koma wajen zamanta. Ina kallon irin kallon tuhumar da boss kemin nai kamar ban ganiba, dan rashin zuwar Anuwat ɗin yasa naji hankalina ya kwanta.
An buƙaci mu fito domin yanka cake. Ganin bai motsaba nima nai zamana, Ina jiyo fitar guntun tsakinsa alamar bayason yi, ni kaina bason nakeba, dan duk a takure nake matuƙa. Sai da Jabeer yazo yayta roƙonsa da ƙyar ya amince muka miƙe zuwa gaban cake ɗin da yay masifar ƙyau.
Mun yanka cake tamkar yanda tsarin yake, ni na fara cira ɗan guntu da zan saka masa a baki cike da jin matsananciyar kunya, dan da ƙyar na iya control ɗin tsumar da jikina keyi nakai hannuna bakinsa, hannun nawa ya riƙe shima muka saka masa gaba ɗaya wanda na ciroɗin kasancewar ɗan ƙaramine a baki. Ina ƙoƙarin janye hannun ya maidashi cikin bakinsa ya tsotse yatsun biyu dana ɗauki cake ɗin dasu suka ɗan ɓaci kaɗan. tafi hall ɗin ya ɗauka. Jinai tamkar na nutse dan kunya.
Shi kam Maimakon ya ciro ya bani kamar yanda nai masa sai ya lakato ya samin a saman hanci kawai dan wulaƙanci, ban gama fita daga takaicin salon nasaba naji saukar numfashinsa kan fuskata, kafin na sami damar magana ya lashe wanda ya lakatamin ɗin da bakinsa. tafin yanzun kam har yafi na ɗazu, dan yanzu harda waƙar Ali jita aka sake saki ta Bilkisu gimbiya. Ƙasa nai niyyar duƙewa dan kunya yay azamar riƙoni jikinsa, sai kawai na ɗora kaina saman ƙirjinsa ina sakin murmushin jin kunya, shima ya ɗaura hannunsa ɗaya saman bayana yana ɗan bubbugawa.
Da ƙyar mc ya samu hayaniyar ta lafa, zamu koma wajen zamanmu aka dakatar damu. Jabeer ya fara bayani kamar haka....
“To jama'a kowa sai ya buɗe idanu domin dai zamuga wasan manya ne, kunsan daga amaryar har angon jarumaine a filin daga”. Ya nuna bindigu guda biyu dake saman wani table duk an buɗesu, “Kuna dai ganin bindiga guda biyu ajiye ko? To munason ango da amarya su haɗasu cikin minti ɗaya yanda suke, wanda ya fara gamawa yana da ƙyauta ta musamman”.
Ni abinma dariya ya bani, hakan yasa naɗan murmusa, batare da tunanin zanyi nasaraba muka ƙarasa, sai da oga Jabeer ya irga uku sannan duk muka fara ƙoƙarin haɗawar cikin hanzari, ina kammalawa nai saurin ɗagowa na nunasa da bindigar fuskata a ɗaure, dai-dai da shima ya nunani data hannunsa fusakarsa babu wasa. .
Wani irin ihu hall ɗin ya ɗauka da tafi. Murmushi ya saki tare da tanƙwa

ɓe hannuna bindigar tai ƙasa ya caɓe cikin hannunsa, nai ƙasa da kaina ina murmushin nima dan naji kunya.
Duk da kusan tare muka gama ni aka bama ƙyautar dai dan nina fara nunasa da bindigar, wajen zamanmu muka koma, muna zama mc ya fara sanar da babban saƙo daga ƙannen ango na musamman Princes, sunce a basu wannan filin su kaɗai, dan ga waƙa ta musamman daga garesu da suka tanada domin amarya da ango. tsit hall ɗin yayi kowa ya buɗe kunne yaji ya kuma ga waɗanan ƙannen ango na musman da kowa ke ƙyautata zaton ƴaƴane daga masarauta.
Matasan samari masu ji da jini a jika da wautar ƙuruciya, Abdul-Raheem, Abdur-rahman, Ameen, suka miƙe, dan da gaske Anuwar bai zoba (su ustazu🤐 lol). sunsha ƙyau harsun gaji cikin shadda kalar sararin samaniya, kansu tsaye mazaunin ango da amarya suka nufa, yayinda Hamisu breaker ya miƙe ya fara raira musu waƙar........
Ashe da rai yake sanki jaruma bada zuciyatai ba, komai ruwa da iska akanki jay baza ya daina kewa ba, tunda dai ya samu zarrar samunki baza ya tanka kowaba, shi baiga mai hararaba, balle ya waiwaya baya. Indai a kankine zaya jure wahalar zuwa garin nisa, da an taɓaki ajirasa danko tilas yazo ya ɗau fansa..........

(Man kaina ya tsiyaye dole mukoma wajen breaker ya ƙarisa🚶🏻😫)

Breaker na fara raira waka sukuma suka farke ƴan dubu-dubu suka fara zubama Jay da bily liƙi, gaba ɗaya hall ɗin ya yamutse da hayaniya, masu ɗaukar video nayi a waya masu hotuna nayi, masu yima breaker liƙi nayi masu yima ango da amarya dasu Abdur-raheem nayi. Daga hakafa aka tafi casun ƙarshe.
Alhmdllh taro ya tashi lafiya kowa cikin farin ciki, anci ansha kowa yayi haniƙan banda amarya da ango, dan ko ruwa bily batasha a wajen nanba har aka tashi, haka shima Jay ɗin.

★★★★★

Ana tashi aka fice dani daga wajen, ganin mun barsa acan ba'a mota ɗaya zamu tafiba kuma farin ciki ya kamani, dan nazata dai masarauta za'a maidani. Sai dai ana sakani mota naji suna faɗin daga nan gidan amarya za'a nufa, idan anje ana kaita mutane su fito dan ba zama za'aiba dare yayi shabiyu saura.
A take zuciyata ta shiga tsitstsinkewa, hawaye suka fara gudu a kumatuna, dan nama manta da wata kwalliyar fuskata, ALLAH bansan wannan shirin suka shirya ba, duk zatona sai gobe idan ALLAH ya kaimu ganin bamuyi sallama da Ummu ba a masarauta. Tun ina kuka a hankali har ya bayyana fili. Lallashina Mah-mah take tayi da sakemin nasiha ƙasa-ƙasa har muka isa, dazan fita a motarma sai da ta sakani nai addu'a, hakama da zan saka ƙafata a falon, kaina lulluɓe yake da alƙyabba banajin komai sai ƙamshin fenta da ya haɗe dana turare dana sabon kaya ya bada yanayi na musamman.

An miƙa amarya Bilkisu ɗakin mijinta, inda basu wani ɓata lokaciba dan basufi mintuna ashirinba aka saka kowa ya fita ya shiga mota, dama wasu sun wuce gida daga wajen dinner, acewarsu zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sazo suga gidan amarya da ƙyau.
Cikin mintuna ƙalilan gidan yay tsit, motocin duk sun juya, Aunty Batool kawai aka bari, itama zata ɗan zaunane kar abar Bilkisu ita kaɗai kafin Jay ya shigo. Bayi ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi da turaruka masu ƙamshi tazo ta tada bily da har yanzu take kuka. “Kukan ya isa haka amarsu, tashi ki daure ki watsa ruwa dan wannan kukan naki nasan ya ɓata kwalliyar”. Ban musa mataba dan inada buƙatar yin wankan kasancewar a yanayin da nake ciki. Alƙyabar ta taimakamin na cire kawai ta fita ta barni, ban zauna jan jikiba dan tace nai sauri boss zai iya shigowa koda yaushe, bai kuma dace ya iskeni a haka ba. Wanka na shiga nayo sauri-sauri na kimtsa jikina na fito, harta kwashe kayan dana cire ta ajiye min riga da zani na atanfa. Shiryawa nai a gurguje, ina kammala saka kayan tana shigowa. Tace, “Yauwa kinga ai hakan yafi, bara aɗan gyara fuskar”. Bance komaiba nidai taɗan shafamin fauda da lipsgloss a baki kaɗan sai turarurruka data fesheni dasu ta bani babban gyale na yafa tare da sake feshe ɗakin da Air Fresheners masu daɗin ƙamshi.
Inda ta zaunar dani ta matso tana murmushi, “To Amarsu angonki ya shigo, bara naje hasu Aliyu can na jirana zasu

saukeni a gida, mu kwana lafiya ALLAH ya huta gajiya”. Hawayen da suka ziraromin na share, nace, “Aunty Batool dan ALLAH ki kwana anan mana, kingafa dare yayi”. Murmushi tayi tana riƙe haɓa, “Inani ina kwana gidan amarya, kinga nayi nan”. Hawaye masu ɗumi ne suka sake gangaromin, na zame na kwanta inayin kayana dan jinake ma duk haushin kowa nakeji, ni banason auren a maidani gidan Dad kawai na cigaba da zamana hankalina kwance.


__________________________

Lokacin da shagali ke gudana a gidan Dad tashin hankali suke fuskanta, dan kuwa dai Salman ne ya gano hotunan biki na yawo a yanar gizo waɗanda ke wajen dinner nata ɗorawa, kunsan mutane da waya a hannu tamkar abu na cizonsune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login