Showing 198001 words to 201000 words out of 261165 words
Chapter 67 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
to bara naje mu cigaba da namu aikin muma, dama dan naga yaya aikin ke tafiyane shiyyasa”.
Ficewa tai, ni kuma na sauke ajiyar zuciya da lumshe idanu na buɗe lokaci guda, hannuna dafe da ƙirjina. Yanzu kam a fili na fara karatun alkur'ani mai girma cikin suratul baƙara, na sake ɗaga katifar da kwalin, baƙin maciji na gani kwance idanunsa jajur, sai tukunyar ƙasa a gefensa an ƙulle bakinta da jan ƙyale. UBANGIJI mai rahama da ƙari, sai ya sakamin dakiyar zuciya da ganin nasa, nama cigaba da karatuna ina sake danne al'ajabi na, baya ya ringa ja daga gaban tukunyar, ganin haka sai na cigaba da karatun nima, sai kawai naga ya sulala ya shige wani rami a jikin bangon wanda bansan tayaya aka ƙirƙiresa ba. Cikin rawar jiki na ɗauka tukunyar na fiddo, ina cigaba da addu'a, sai dai ƙirjina wani irin mahaikacin bugawa ya keyi tamakar zuciyata zata faso ta fito, maida kwalin da katifar nayi, na fito falo da tukunyar jikina har yanzu rawa yake, sai da na leƙa falon ƙasa na tabbatar babu kowa sai tv kawai dake magana sannan na fito cikin sanɗa, addu'a nake jikina kuma na wani irin tsumar rawa, ina ficewa a falon naji muryar cikin masu aikin na faɗin, “wanene ya fita?”. Innalillahi na faɗa ina ƙara sauri, baba maigadi yana hangoni ya taso, na tsaya bayan wata mota inata waige-waige, isowa yayi gareni cikin sassarfa, na miƙa masa tukunyar ina magana da rawar murya matuƙa, “Baba, ka kirashi yazo ya amsa yanzun, bara naje na ƙarasa aikin da aka sani karsu fahimci wani abu”. Kansa ya ɗagamin kawai, na juya da gudu na koma, nai saurin daidaita yanayina lokacin dana shiga falon, hajiya na iske tsaye, ta zubamin ido cike da kallon tuhuma. “Keda kike aiki a sama mi kuma ya sakko dake ƙasa larai?”. Da ƙyar na iya ƙaƙalo yawu na haɗiye ina murmushin ƙarfin hali, “Hajiya wani yana na gani ta tagan ɗakin (Window) shine fa na zagaya dan na share sai naga ashe da nisa ta waje”. Dariya naga ta tuntsure dashi tana girgiza kanta, “Banda abinki larai ba a sama kikeba? Ki barsa akwai yaron dake sharewa zaizo ya share ranar weekend”. Kaina na ɗaga mata, ta juya kicin ɗi
n ni kuna na nufi saman benen ina godema ALLAH da ya rufamin asiri. Sai dai jikinafa har yanzu wani irin tsuma yakeyi, ga Masifaffen ciwon kai da alokaci ɗaya ya saukarmin. Haka na daure na koma ɗakin, canma na iske laila tsaye tana ƙarema ɗakin kallo, da masifa ta hauni akan ina naje? Kenanma tana fita nima na fita tunda ga shi nan ko gadon ban kammala gyarawa ba. Haƙuri na bata duk da zamuyi sa'anni da ita, na faɗa mata kamar yanda naima hajiya bayanin share yana. Tsaki taja min tana faɗin, “Malama kiyi sauri ki gama inada wajen zuwa”. Kaina na ɗaga mata kawai a sanyaye na hau gyaran gadon, yanzunkam tsaye tayi a kaina harna kammala aikin, hakan bai dameniba tunda naci nasara, na saka turaren wuta muka fito tare ina dafe kai saboda ciwon da yakemin.
★★★★★
Jawaad na tsaka da aiki a office, sai dai rabin hankalinsa duk yana ga Bilkisu, tunda ta tafi basuyi ko waya ba, sai dai baba na faɗa masa tana cikin ƙoshin lafiya ya cigaba da mata addu'ar nasara. Wayarsa da tai ring ya duba, ganin baba ne yay saurin ɗagawa babu ɓata lokaci. Ko gaisuwa baba bai jira sunyiba yace, “Duk inda kake ka taho nan yanzun, yarinyarnan ƴar albarka tayi nasarar ɗakko tukunyarnan gata a hannuna ma”. Zaram Jawaad ya miƙe tare da wancakalar da takardun gabansa, bai saurari ɗaukar komaiba ya fice, key ɗin motar ya amsa a hannun Sadiq yace ya zauna ya jirashi dan da kansa zai tuƙa motar.
Gudu yake na tashin hankali kamar titin nasane shi kaɗai, tsabar karya samu cinkoso ma sai ya ringabi ta wasu hanyiyin daban yana ratsema duk titin da yasan zai iske go-slow. Acan bayan layin suka haɗu da baba maigadi daya fito daga gidan akan yaje salla, da yake anata kiraye-kirayen sallar magriba ne. Miƙa masa kawai yayi batare da sun tsaya doguwar magana ba, “Maza kaje ka fasata Jawaad, karka tsaya ɓata lokaci”. “To baba, amma matata fa?”. “Kaje itama zan fiddota yanzu dana koma, dan tabbas akwai haɗari babba Alhaji ƙarfe takwas zai sauka ƙasarnan, duk inda yake a halin yanzun kuma nasan yaji a jikinsa an ɗauka tukunyar nan.............✍
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻
[1/22, 9:04 AM] HASNA✍🏻: Page 55
.................“Baba bazan iya barin anguwarnan ba sai da ita”. “Bazai yuwuba Jawaad, kaje itama insha ALLAH lafiya zata fito, dana koma yanzu zan fiddotane itama”. “Baba kaima fa bazai yuwu ka zaunaba, dan zamanka akwai haɗari Sadiq zaizo ya ɗaukeku tare, kaje ka haɗa duk wani abunka mai muhimmanci”. “To shikenan ɗana, ALLAH yay maka albarka sai ya zo”.
CIKIN JIRGI
Tun ɗaga gadon farko da Bilkisu tayi jikin Alhaji kokino ya bashi, to amma yasan akwai mai tsaron wajen koma waye tsautsayi ya kaisa sai dai gawarsa. Sai dai kuma ƙarfin gwiwarsa ta sare lokacin da yaga zoben dake a hannunsa yana canja kala zuwa baƙi, gabansa yay matuƙar faɗuwa, gashi babu damar kiran waya, a take komai nasa ya fara kwancewa lokacin da zobe tsafinsu ya shiga hasko masa abinda bilkisu keyi, sai dai ALLAH ya hanashi ganin fuskarta sam sai duhun inuwarta kawai yake gani harta ɗauki tukunyar data ɗauki tsawon shekaru a jiye babu wani mahaluki da ko yatsansa ya taɓa taɓata, sai maman yara da idanunta suka gani itama kuma saida ya sakata tai nadamar hakan, tanama can cikin nadamar ma (Masu karatu Alhaji kokino fa baisan yanzu maman yara bata wajen yaransa ba, dan randa ƴarsa ta saka masa maganin barci koda ya farka a washe gari har an maida masa wayoyinsa, babu wata kuma alama da Jawaad ya bari dazai iya zarga, shikuma da yasan babu wani mahaluki da zai iya masa makamancin haka sai bai kawo komai a ransaba, a washe garin ya bar ƙasar batare da yayi waya da yaransa akan komaiba. ALLAH kuma ya hana shaiɗanun dake taimaka musu fahimtar komai balle shugaban nasu na dodon tsafi damar sanar masa.
Gaba ɗaya ya jiƙe da uwar zufa sharkaf kamar ana masa wanka da ruwan zafi, jiyake tamkar ya rikito jirgin ƙasa dan tsabagen tashin hankalin da yake a ciki, gashi sauransu kusan awa ɗaya da rabi kafin ma su sauka. Lallai wannan ko wanene a cikin gidansa sai ya ƙarar da dukan ahalinsa bama shi kaɗaiba.
Jawaad kam kai tsaye gidan Alhaji babba ya nufa, sun fito masallaci kenan sai ganin Jawaad ɗin yayi ya fito a mota, sai dai yanayinsa yay masifar ɗaga hankalinsa. Tambayoyi ya shiga jera masa, Jay dai bai amsa masa ko gudaba a ciki ba, “Baba wannan ba lokacin amsa tambayoyi bane”. Ya faɗa yana nufar cikin gidan da tukunyar a hannunsa dan da duk a wajen gate suke inda Jawaad ɗin ya faka motarsa. Alhaji babba da ciwon ƙafa ya matsamawa a kwanakin nan ga yawan mafarke-mafarke da faɗuwar gaba da yake yawanyi yabi bayan Jawaad jiki a sanyaye, iskesa yay tsaye tacan bayan ɗakunansu ya ɗaga tukunyar zai fasa bakinsa ɗauke da addu'a. “Kai wai minene kake haka? sai kace wani matsafi?”. Jikake “Tassss!” Jawaad ya buga tukunya da ƙasa.
Fashewarta tayi dai-dai da faruwar abu uku a zahiri, biyu a ɓoye.
Na farko shine saukar jirgin da alhaji kokino ke a ciki bisa ƙasa. Na biyu mummunar faɗuwar gaba ga duk masu alaƙa da tukunyar, na uku faɗuwar Umm-Anum dake a kicin tana dafama Abbu shayi da yake a gidanta yake yau. Na baɗinin kuwa daga can fadar shaiɗancinsu ya faru.
Wasu irin mugayen layune manya-manya guda uku a ciki, sai ƙananun allurai da wasu irin abubuwan surkulle da baisan minene ba shima, sai ruwan kuwa da suke ciki na jini ne sai wani uban wari ya keyi maiban tashin hankali, Alhaji Babba ya waro idanu waje jikinsa na rawa da toshe hancinsa da hannu yace, “Muhammad minene wannan? A ina ka samoshi ni Nuhu?”. Taga-taga Jawaad yay zai faɗi idanunsa a matuƙar jazur, Alhaji babba yay saurin riƙosa. Atare suka sauke ajiyar zuciya, da sauri Jawaad ya zare hanunsa daga na Alhaji babba ya nufi cikin gidan, hankalin Alhaji babba sake tashi yayi, ya kalli tukunyar da kayan ciki ya kalli hanyar da Jawaad yabi, ya juya zai bishi sai gashi ya fito ɗauke da ashana da gallon ɗin fetur na Genretor. Akan kayan ya zuba ya ƙyasta musu wuta. A take gidan ya ɗauki wani irin mahaukacin ƙauri mara daɗin shaƙa, sai ƙananun motsi kamar ana guje-guje, suka hau waige-waige suna dafe kunnuwansu da hannu da sauri, sai kuma aka fasa kuka da wata irin murya mara daɗin saurare. Ana ƙwalla kiran sallar isha'i gidan kuma yay tsitt dan masallacin idan aka kira salla kakanji tamkar a cikin gidan akeyi tsabar kusancin da suke dashi. Jagwab Jawaad ya zauna a ɗan dakalin da aka shuka fulawoyin gidan, ya dafe kansa yana karanto hasbinallahu wani'imal wakil. Sai kuma ya miƙe zumbur saboda tunawa da bilkisu da baba, lallai duk inda Alhaji kokino yake yanzu jirginsu ya isa sauka ƙasarnan. “Baba ina zuwa ya faɗa yana nufar gate cikin zafin nama. Sake binsa da kallo Alhaji babba yayi harya fice.
Jay ya buɗe mota zai shiga saiga drivern gidan Ummah babba ya kawo Batool, baiko kallesu ba duk da ɗaga masa hannu da takeyi ya buɗe motarsa ya shiga tare da yin reverse yabar anguwar da mahaukacin gudu kamar zai tashi sama.
★★★★
Tun ina ɗaukar ciwon kai wasa har ya fara neman fin ƙarfina, dan idanuna sun fara rufewa bana ganin abu da ƙyau, innalillahi wainna'ilairraji'un naketa ambata da sauran addu'oi. A wannan halin lariya ta shigo ta sameni ɗaya daga masu akin gidan. “Larai kije inji hajiya”. Gabana ne ya faɗi, dan a tunanina kodai ta gane wani abune?.
A babban falo na iskesa tsuggune ita kuma tana daga tsaye da hijjab jikinta alamar salla tayi, “Haba dai baba, ai bai kamata ace a darennan zata wuceba, gashi bamu tanadar mata komai ba, kacema wanda yazo ɗaukar nata yayi haƙuri sai da safe sai ya dawo su tafi”. Baba da gabansa ke faɗuwa yace, “To hajiya banƙi ta takiba, amma da anyi haƙuri sun tafin dai babu damuwa, idan ta gama kwanakinta a can ɗin saita dawo nan ta ƙara miki kwana ɗaya daga nan saita wuce”. Shiru tai kamar bazata amsaba, sai kuma tace, “To shikenan na amince da wannan shawarar taka, bara na basu ko kuɗin motane, amma dan ALLAH fa kartaƙi dawowa”. “Insha ALLAHU zata dawo Hajiya”. Kallona tai da ɗan murmushi, “To larai kije ki ɗakko kayanki anzo ɗaukarkine”. Kaina na ɗaga kamar banason tafiyar jikina a sanyaye, ta nufi sashenta ni kuma na nufi ɗakin da aka saukeni na ƴan aiki, ƴar bakko ɗin kayana na ɗakko na fito bayan nama sauran sallama, kaina ne kemin ciwo sosai, dauriya kawai nakeyi.
Dubu biyar hajiya ta bani, nai mata godiya da cewar ai zan dawo na sake mata kwana biyu kafin na tafi, da haka mukai sallama. Muna fitowa daga cikin gidan ana yin horn a ƙofar gate. Wani irin Masifaffen faɗuwa gabana yay, shi kansa baba mai gadi a take ya diririce, saurin nunamin ɗakinsa yay yace na shiga ciki, shi kuma yaje ya buɗe gate ɗin.
Drivern Alhaji kokino ya danno kan motar da sauri, kamar yanda baba ya saba duk sanda ya shigo gidan zaije su gaisa kafin ya shige, yanzunma hakan yayi, sai dai sama-sama Alhaji kokino ya amsama baba maigadi, yay ciki da masifar sauri tamkar zai tashi sama. Drivern ya kalli Alhajin ya kalli baba maigadi yana faɗin, “Anya kuwa lafiya gidan nan yake yau? Tunfa a filin jirgi yake azalzalata kamar wanda akace gidansa naci da wuta”. Baba maigadi yace “kadai bisa da jikkar ka dawo”. Yana ganin drivern shima ya shige yay saurin nufar ɗakinsa, jikkarsa daya gama haɗawa Bilkisu ta haɗo da tata ta fiddo, ƙofa ya buɗe mata ta fice da sauri shima ya rufa mata baya, suna fitowa Jay na isowa wajen, da sauri bily ta buɗe gaba ta shiga baba kuma ya shiga baya, jan motar yay da gudu yabar anguwar.
Da gani har baba muka sauke wata nannauyar ajiyar zuciya. Sai kuma naji hawaye na gangaromin a fuska a hankali, kife kaina nayi saman jakunkunanmu dana shigo dasu kawai na cigaba da kukana, babu wanda yay magana a cikin motar har muka iso, sai sheshshekar kukana kawai.
___________________________________
Ɓangaren Alhaji kokino kam koda ya shigo falon sama yay cikin sassarfa, sam bayama jin sannu da zuwan da ƴaƴansa suke masa harda ma matar tasa. Kaɗan ya rage babbar rigarsa ta taɗesa ya faɗi a step na bakwai, yay azamar riƙe ƙarfen ALLAH ya soshi bai faɗinba.
Matarsa da abin ya girmi kanta tuni ta take masa baya da hanzarinta, sai dai tana zuwa ƙofar ɗakin sai ta jita a datse alamar ya kulle kansa. Duk da bayau ya fara mata hakanba sai taji na yau yay mata zafi, ta shiga buga ƙofar tana ambatar sunansa amma ko tari bataji yayi ba. Tana nan tsaye hankalinta a matuƙar tashe ya buɗe ƙofar da ƙarfi ya fito, jikinsa sai ɓari yakeyi.
“Alhaji lafiya wai?”. Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cayay, “Wanene ya shigarmin ɗaki?”. “Alhaji ban gane wannan tambayarba, wanene zai shigar maka ɗakin bayan ni?......” “K!! Bansan iskanci, uban wanene ya shigarmin ɗaki?!!”. Yanda yay maganar tamkar zai haɗiyeta da mugun hargagi kuma sai duk ta firgice, jikinta na rawa ta shiga girgiza masa kai, “Alhaji babu wanda ya shiga wlhy sai ni, sai ko jikar baba maigadi da nasa ta gyara maka saboda aiki yamin yaw.....” wani irin wawan mari ya ɗauke fuskarta dashi jikinsa na rawa. “Sau nawa zanmiki gargaɗi akan saka wani yaymin gyaran ɗaki a gidan nan?!!”. Yanda jikinsa ke karkarwa dolene ya bama mai kallo tsoro, tunda take da shi ko sanda yay auren amaryarsa yana mata wulaƙanci saboda asirin waccan bai taɓa ɗaga hannu a kantaba ko murya irin haka, gashi gaba ɗaya tama lura baya a cikin hayyacinsa, mike damun mijinta haka ne? Mi Larai ta aikata masa a ɗakin da ita bata ganiba? dan yanzu ta shiga ta gama haɗa masa ruwan wanka ta kuma ƙara Air Fresheners a ciki bayan ta shirya masa abinci a dining....
Cikin wata gigitacciyar tsawar ya kuma cewa, “Ina yarinyar take?!!!”. Share hawayenta tayi ta nufo ƙasa tana kiran larai, shima biye yake da ita yana baza idanu da babbar riga yaga ta ina larai zata ɓillo?. Sai dai tun kafin su sakko ƙasan ma ƴaƴansa da ma'aikatan gidan harsun bazu nemanta suma.
“Momy wlhy fa Larai bata gidan nan”. A rikice hajiya tace, “Ban gane bata gidan nanba, yo ina zataje?”. Kafin wani cikinsu ya bata amsa Alhaji kokino yace, “Wai ita laran ƴar gidan uban wacece? Da ga ina kuka samota?!!”. “Dady jikar baba maigadi ce” laila ta bashi amsa a tsorace.
“Maigadi?!!” ya faɗa a wani irin zazzaro idanu, kafinma wani yace wani abu tuni ya fice daga falon zuwa gate, driver kawai ya iske akan bench a zaune yana ƙoƙarin zuba abincin da aka kawo musu daga cikin gidan. “Kai Mati ina maigadi?!”. Yanda Alhaji yay maganar ne ya saka driver sakin plate ɗin abincin ƙasa a tsorace, “Alhaji lafiya kuwa?”. “Ina tambayarka maigadi kana tambayata kafiya?!”. “Ayi haƙuri Alhaji, yana bayi inaga, nima dana fito ban gansaba, nasan dai bazai wuce banɗaki ya zagaya ba”. “Ƙwanƙwasa masa maza ya fito” tashi driver yay ya nufi cikin ɗakin maigadi, sai dai yana taɓa ƙofar toilet ɗin da nufin bugawa sai kawai yaga tama buɗe da kanta, ya leƙa babu alamar mutum, kai da ganima ba'ayi amfani da ruwaba yanzun dan bayin a bushe yake ƙamas. fitowa yay da sauru yana faɗin, “Wlhy bayanan ashe”. Shaƙosa Alhaji kokino yayi yana faɗin, “Idan baya nan dan ubanka ina yaje?!” sosai hankalin kowa ya ƙara tashi, dan ya koma musu tamkar wani zararre. Jikin driver sai rawa yake dan yaji shaƙa, Alhaji kokino ya wullar dashi gefe ya shiga ɗakin da kansa. Hakan yasa Hajiya ta sake take masa baya duk da a tsorace take. Abun mamaki duk kayan baba maigadi babu su, sai abinda ba'a rasaba waɗanda sam basu da wani muhimmanci ga mai su. A yanzune hajiya ta fahimci lallai akwai abu a ƙasa kenan. A fili tace “Mi hakan ke nufi to?”. Cikin tsananin tashin hankali Alhaji kokino yace, “kezan tambaya Nafisa, shikenan kin kasheni Nafisa, taya za'ai har wani ya kawo baƙon ido gidan nan kai tsaye ki yarda da shi harki bashi damar shigarmin ɗaki?!!”. “Wlhy Alhaji ni....” hankaɗeta yay gefe batare da ya jira ta ƙarasa faɗaba, ya fice da saurinsa yabar mata ɗakin, kuka mai tsuma rai ta fashe da shi a ranta tana mamakin miyasa baba maigadi zaiyi haka? Shekaru nawa suka ɗauka tare bai taɓa cutar da suba sai a yanzun? shin minene maigadi yasa Larai ta aikata ne? Ta tuno fitarta ɗazun lokacin da take mata tambaya akan ina taje ita da aka saka aiki? Tabbas ba cikin nutsuwa larai ta bata amsa da cewar yana ta fita sharewa ba, amma da yake bata kawo komai a ranta ba sai bata zargeta ba.
SAUDIA
Hankali tashe Anum ta ƙwala kiran sunan Abbu da Anuwar dake falo suna jiran shayi, har rige-rige. isowa suke cikin kicin ɗin, ganin Umm-Anun yashe a ƙasa yay masifar ɗaga hankalinsu, Anuwar ya tallafo kanta ya aza bisa cinyarsa yana mai fashewa da kuka, Abbu ne yay ƙarfin halin komawa ya ɗakko goran ruwan zam-zam ya dawo, a hannu ya zuba ya