Showing 195001 words to 198000 words out of 261165 words
Chapter 66 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
maka bayani shine ta wace hanya kake gani zan iya shiga gidan domin ɗakko abinda tace? Matsalar shine a ɗakinsa tace abin yake, ɗakinma a tsakkiyar ƙarƙashin gado”. Baba ya jinjina kansa yana gyara zama, “Wato ɗana, ba wai ɗaukar ko shigar bace matsala ma, dole al'amarin sai da lura, su shaiɗanun mutane irin waɗan nan al'amarinsu baya buƙatar fuska da fuska, kamar yanda suke ƴan yaƙin sunƙuru haka masu cinsu da yaƙi ya kamata su kasance suma”. “Hakane baba”. “Yauwa to kagani ni a nawama tunanin wannan aikin kam da mace yafi dacewa ta wani ɓangaren, wani ɓangaren kuma namijinne, ɗakinsa dai bazai shigu gareka matsayin namijiba cikin sauƙi”.
“Baba to mizai hana ni kawai naje”. Na faɗa kaina tsaye babu ko ɗar a raina. Shiru duk sukai suka zubamin ido. Cikin jinjina kai baba yace, “Shawararki kam abar dubawace, sai dai kuma ai bazai yuwu kije kai tsaye ba, sai dai mu duba wasu ƴan dabaru haka?”.
Kafin nayi magana boss yace, “Baba bazai yuwu taje ba, mudai sake wata shawarar”. Murmushi naga baba yayi kawai, cikin rawar murya nace, “Miyasa to? Yanzu idan bajeba wa zamuce zamu saka wannan aiki? Ni a ganina baba zai iya ya kaini gidan matsayin jikarsa, insha ALLAHU ni kuma zan ƙarasa sauran aikin inhar na shiga gidan dai da matsayin da zan iya shiga wasu ɓangarori shikenan”.
Shiru yay bai tankaba, baba yace, “ƴata idan mijinki baya so karki matsa, dan gaskiya wannan aikine mai haɗarin gaske, inaga zanje na ƙara tunanin wata hanyar, kuma sai ku sakeyi, yazam dai kafin safiya idan ALLAH ya kaimu ya muna da abinda muka riƙe, dan na tabbata nan da kwana biyu zai dawo daga tafiyar da yayi yau da safe. zan koma dan banason a farga da bani bane a gate ɗin”. Godiya mukai masa ya tashi yay masa rakkiya, ni kuma na koma ciki ina ƙunƙuni, dan insha ALLAH zanta lallaɓasa nikam harya amince naje nai wannan aikin da kaina. Ganin halin da maman yara take ba ƙaramin zaburar da zuciyata yayiba, na fahimci al'ummata na buƙatar jajurtattun mata irin su ma
man yara, wayasan shekarun data ɓata domin bibiyar wannan tukunyar? Amma gashi har tana a cikin magagin wahalar da aka bata bataji ta gajiyaba da son cimma ƙyaƙyƙyawar manufarta ba.
Jin an taɓani na sauke sassanyar ajiyar zuciya, kujera yaja ya zauna idonsa a kaina har lokacin. Kallonsa nai cikin ido ko gezau babu a karo farko na tarihin rayuwata, dukda bugun ɗari-ɗari da zuciyata keyi haka na daure na dake ban cire idanuna ba, “Kar kace a'a, dan ALLAH, mune ya dace muyi aikin nan basai mun saka kowa a ciki ba, sannan bamu da isashen lokacin zaman yin tunni ko binciken wanda zaiyi mana ma. ɗiyarsa ta ɗakko mana wayoyi ba shine ke nufin zata ɗakko mana wannan ba kuma”.
Gani kawai nai idanunsa na ƙyalli tamkar hawaye sun taru a ciki, ya girgizamin kai a hankali yana kauda kansa, hannunsa nai saurin kamowa cikin nawa, ya sake juyowa ya kalleni, nawa hawayen ne suka silalo a hankali saman kumatu, “Please yayanmu karkace a'a, nima ka barni nai hidima ga Umm-Anum kamar yanda tayi a gareni tun batasan wacece ni a gareta ba, har raina jin ahalinka nake a zuciyata da ɓargo, idan ka hanani yin wannan aikin zanji matuƙar zafi a raina bakuma zan daina jiba har na koma ga ALLAH, dan zanke ganin kamar ni ɗin dan ba ahalink.....”
Jawoni kawai yayi jikinsa ya rungumeni batare da ya barni na ƙarasa faɗa ba, da sauri-sauri zuciyarsa ke harbawa a ƙirjinsa, kamar yanda nima tawa keyi, cikin kuka na sake cewa, “Please Yah Jayyyy”.
Jawaad ya lumshe idanunsa a hankali yana wani cije lip ɗinsa na ƙasa da ƙarfi, “Jay” sunane da mafi yawan mutane ke kiransa da shi, bai taɓajin ambatar sunan da wani banbanci na daban ba ga mai faɗarsa sai yau a bakinta, musamman ma data ja “y” ɗin ƙarshe sai yaji gaba ɗaya tsigar jikinsa ta tashi.
Ɗagoni yay a hankali na sake zama sosai a kujerar dining ɗin, ya riƙe fuskata a cikin tafukan hannunsa yana sharemin hawayen da babban yatsansa, muryarsa a shaƙe yace, “Miyasa kema kin iya rigima ne Miemaa?, aini Kin riga kin gamai min komai a rayuwa tunda kika zama sanadin haɗuwata da mahaifiyata”. Sake ɓata fuska nai alamar tahowar wani kukan, nace, “To dan ALLAH ka barni na cika ladana”. Murmushi ya ɗanyi mai ciwo yana sake turani cikin jikinsa, “Shike nan bar kukan haka, zanyi tunani daga nan zuwa safiyar da yace insha ALLAHU, ALLAH ya zaɓa mana abinda yafi alkairi”. “Amin” na faɗa ina murmushi.
Yau shine ya bani abincin da kansa, bayan mun kammala ya taimaka min muka tattare kwanikan zuwa kicin, ina wankewa yana ɗaurayewa har muka kammala sannan muka fito bayan na kammala tanadar abinda zan haɗa mana breakfast insha ALLAHU da safe. Yau kam bamuyi zaman wani aiki ba, brush kurum mukai da yin shirin barci muka kwanta. Babu jimawa barci yay awon gaba damu kuwa. Kusan ƙarfe uku na dare ya tadani, alwala mukai muka shiga yin nafilfili domin miƙa buƙatarmu wajen mahaliccin kowa da komai, mai rahama da ƙari ga bayinsa. Bamu sake kwanciya ba sai da mukai sallar asubahi, da yake a gida yayi shima muna idarwa ya jani muka haye gado, zanyi magana yasa tafin hannunsa ya rufemin baki ruf. Dole na haƙura muka kwanta, barci kuwa yay cak damu zuwa duniyarsa.
Bamu farkaba sai 8:11am, nice ma na fara farkawar, na waro idanu a waje dan ganin makarar da nake gudu dai ta tabbata, jawoni yay zai maida ya sake kwantarwa nace, “takwas fa ta wuce boss”. Buɗe idanunsa yayi yana ɓata fuska, da alama ba haka ya soba. Da ƙyar ya iya tashi muka shiga wanka tare, a gaggauce mukai muka fito, batare da mun tsaya neman abinci ba muka shirya, tea ɗin dana haɗa manama cayay muje masha a mota, shi dai maigadi ya miƙa masa nasa tare da kuɗi akan ya sayo bread mun makara yau. A motar kuwa muka sha tea ɗin abin dariya da tausayi (lol😂😜). Aiko yau ina rakasa office na fito dan ban kammala aikin jiyaba nima, a ƙofar office ɗin naci karo da rose, ko kallonta banyiba nai gaba abina, harna sauka ƙasa ina jiyo idanunta dake yawo a jikina, nidai ban fasa neman tsarin ALLAH da ga sharrinta ba harna ɓace abina.
Kusan sha biyu da wasu mintuna ya kirani akan idan anfito salla nazo na samesa. Amsa masa
nai da to ana idarwa kuwa can na nufa, shi kaɗaine a office ɗin yanata ayyuka, duk da da alama shima yanzu ya shigo ɗin, ban zaunaba har sai da ya bani izinin zama. Tasowa yay daga kujerarsa ya dawo ɗayar dake kallon wadda na zauna, ya kamo hannayena cikin nasa yana mai tsareni da idanunsa nan masu takurani. “Miemaa na amince kije gidan Alhaji kokino, amma da sharaɗi”. Cike da ɗoki nace, “Minene shaɗarin?”. “Sharaɗin shine kwana ɗaya kacal da yini biyu zakiyi, idan yayi tsaurine kikai biyu, sannan tare zamuyi aikin dan bazan taɓa barinki ki shiga wannan aikin mai haɗari ke kaɗai ba”. Rungumesa nai saboda jin daɗi, hannu biyu ya amsheni yana murmushi, nace, “Na yarda da duka sharaɗin, ALLAH ya bamu sa'a da nasara”. Yace, “Amin Beejay, yanzu zaki tashi Sadiq ya kaiki gida kiɗan shirya, shine zai kaiki inda zaku haɗu da baba, sai ya ƙarasa da ke”. “Wow da wuri haka?, insha ALLAHU zaka sameni fiye da yanda kai tunani, kaida kaitamin addu'a boss ɗinmu abin alfaharinmu”. Ɓata fuska yay cikin wasa yace, “ke da wa?”. Ganin yanda yay da fuska ya sakani ƙyaƙyƙyawa da dariya, “Ni kaɗai mana, sai su oga Jabeer ”. Hararata yay, “K nifa kibarma kirana da wani boss na gaji da ji”. Kunya naji sosai, dan haka na ɓoye fuskata a ƙirjinsa ina dariya.
★★★★
Duk yanda muka tsara hakance ta kasance, bayan sallar la'asar muka isa gidan Alhaji kokino, cikin shiri nake irin na ainahin garorin yaran nan na ƙauye da ko karatu basu taɓa samu ba, ga matarsa kam mun samu tarbar mutuntawa, ƴaƴan gidanne dai sai a hankali, dan gaba ɗaya halayensu baimin ba, sai wani famar min kallon banza suke, musamman mai son boss ɗin nan. Shiru nai na maƙure jikin kuje alamar tsorata ta baƙunta. Baba mai gadi da suka gama gaisawa da hajiya ya juyo ya kalleni, “K Larai! Baki iya gaisuwa bane? nifa banason wannan ɗabi'ar banzar kin sani”. Muryata na rawa nace, “Ina wuni hajiya, mun sameku lahiya?”. Dariya yaran suka bushe da ita duka falon, irin wai ƙauyancina ne ya basu dariyar. Ita dai hajiyar Murmushi tayi tana cigaba da kallona, tace, “Lafiya lau Larai, yasu mamar taku?”. “Lahiya lumi suke aradu hajiya, tace tana gaiheki”. Saboda dariya har ƙasa suke faɗuwa daga saman kujerun. A raina nace, ‘Wawaye kawai’.
Baba ne da yake ɗan murmushi shima yace, “Hajiya dama tazo daga ƙauye ne can anguwar tudun birji wajen ƴar uwar mahaifiyarta, to saita iske wai sunje suna ko ina, kuma sai jibi zasu dawo, shine nace data koma kuma ai wahala goma da ashirin tazo nan saita kwana idan suka dawo sai taje, ALLAH yasa dai ban wuce gona da iriba?”. “A'a Malam baka wuceba kam, ai kaga anyi zuminci tunda dama kaƙi kawo mana iyalanka shekara da shekaru, ni nagode sosai da wannan ziyara”. “Nima nagode hajiya, bara na koma bakin aiki to ga tanan”.
Ganin zai fita nai ƙwalƙwal da idanuna alamar kuka, “Kaka anan zaka barni?”. Juyowa yay da ɗan faɗa yana min daƙƙuwa, “Kinci gidanku Larai, nanɗin cin mutane ake bare kice za'a cinyeki? To idan hakan bai mikiba tashi ki kama hanyar ƙauye idan su Rakkiyar sun dawo sai ki dawo”. Baki na tura ina maƙe kafaɗa, “Ni alkur'an a'a”. “Ke kuma kika sani ja'ira kawai” ya faɗa yana ƙarasa ficewarsa. Yana fita suka fara jana da hira wai na basu labarin garinmu, nasan sosuke kawai su ringajin yanda nake magana suna dariya. Abinci aka kawomin, inaci ina basu labari kamar wata sakara, suko sai kwasar dariya sukeyi da zagina a kaikaice.
Haka na maida kaina ƴar cali-calin ƙarfi da yaji a gidan Alhaji kokino, sannan aiki duk dana gani zan tashi nayi kamar bansan ciwon kaina ba, bansan inajin kewar mijina ba sai da dare yayi nazo zan kwanta a tabarmar ɗakin masu aiki, hakan bai dameni ba, dan wannan ba sabo bane a gareni, kewar tasace dai kawai naji, sai tunani nake yanzu koshi mi yakeyi? Oho.
★★★★
Yanda Bily ke cikin kewa a gidan Alhaji kokino haka Jawaad yake a gidansa, tun da ya dawo daga wajen aiki duk sai yaga gidan yay masa wani faɗi da baƙi, yay zaune a babban falo yanata kallon sashenta, da ƙyar ya iya tashi yaje yay salla, koda ya dawo yaga zuciyarsa na ƙara ƙuntata sai ya fice daga gidan zuwa gidansu A
mina, baisan yawan zuwa gidan dan kar a fahimci akwai wani abu duk da yasan Dad baya a garin, sannan ma ƴan gidan hankalinsu baya aƙwance saboda rashin ganin Shahudah, shiko akan hakan yamaƙi zuwa ko family house ɗinsu tunda suka dawo, ya kuma kashe wayar da kowa zai iya samunsa.
A gidan su Amina ya ɗan rage kewa, maman yara tace ya kwantar da hankalinsa tanaji a ranta insha ALLAH bilkisu zata iya, dan a zuwan da sukayi jiya ta fahimci tana da hankali da wayo. Kai kawai Jawaad shi dai ya ɗaga, zuwa tara ya baro gidan, rasa mizaiyi yayi, haka dai ya koma gidan ransa duk a jagule. Tea kawai yasha yay shirin barci ya kwanta a ɗakinta, jin zuciyarsa ta sake ƙuntata ya ɗauki waya akan bara ya kirata ko muryarta yaji, sai da yaji switch up sannan ya tuna cewar bama ta tafi da waya ba. Tsaki ya buga yana jefar da wayar a kan gadon, waishi mima yasa ya barta taje ne?. haka yayta takaicinsa hardai daga ƙarshe ya sake ɗaukar wayar, Anuwar ya kira, bugu ɗaya kuwa ya ɗauka cike da ɗoki. Wannan kiran Anuwar shine ya rage masa kewar Bilkisu a ransa, sunsha hira sosai dai sai kusan ɗaya da rabi na dare sukai sallama, sai kawai yayo alwala ya hau salloli ma. Sai kusan uku ya kwanta sai barci.
WASHE GARI
Washe gari ma haka na tashi cikin ƴan aikin nan duk abinda sukeyi dani akayisa, babu wanda yace nabari a gidan, saima faɗa suke wai nafi masu aikin iya aiki. Nidai bance komaiba, sai lokacin da hajiya ke faɗa akan mai gyara mata ɗaki batayi da ƙyau ba, idan bazata iyaba a canja da wata. Murmushi nayi domin wata damace ni a gareni hakan, dan haka nai caraf nace ni bara na gyara mata yau. “A'a Larai, daga zuwa sai kita aiki? Aiba haka akeyiba”. “Lah hajiya karki damu, yo mufa mun saba alkur'an, dafa a ƙauyene da yanzu inacan ina sirhe, yo ni ina zan iya da wanga lalaci naku na mutan burni hajiya, ke dai bani aiki kiga aikin mata aradun ALLAH yanzu na ƙalƙale miki ɗaki ko fadar mai garin garinmu bata nuna masa fita ba”. Sunata dariyarsu niko na fuske abuna.
Zagewa nai naima ɗakin gyara na sosai, sai gashi hajiya na santi ita da yaran nata, aiko ranar na aikatu, dan ɗakunansu sukaita sakani na gyara musu suma yaran, duk da na gaji haka na daure dan fatana nidai a ƙarshe a turani ɗakin mai gidan, amma sai naji tsit. Washe gari babu wanda ya sakani wani aiki, har yamma, abin duk ya dameni inata addu'a da fatan samun hanyar da zan shiga ɗakin, dan a yinin da nai jiya na aiki nazarin gidan naitayi da hanyoyin cikinsa. Kusan ƙarfe huɗu da rabi ina zaune a can baya ni da ɗaya daga masu aikin gidan sai ga hajiya ta fito, sannu duk mukai mata da gaisheta dan duk yau ban gantaba bata yini a gida ba. Tace, “Larai Please zoki min wani ɗan aiki nan na dawo a makare”. “To” nace ina miƙewa, wani irin farin ciki ya kamani ganin mun nufi sama, inda nake da tabbacin turakar mai gidance anan. Fasalta muku yanda tsarin yakema ɓata lokacine, kowa ta ƙiyasta tsaruwarsa kawai. Kallona tai tana ɗan murmushi, “Larai nan zaki gyaramin, babu wata mai aiki dake shigowa ni nake gyarawa, to naje saloon da gyaran jiki sai yanzu na dawo gashi lokaci ya ƙure, kuma Alhaji nanda takwas na dare zai iso yayi tafiyane, na yarda da kene saboda kinada nutsuwa, dan ALLAH ki gyara komai ƙal kinji, ni kuma zanje mu ɗaura masa abinci”.
Farin cikin da ke cin raina na danne, na amsa mata da “Insha ALLAH hajiya zaki samu fiye da yanda kikeso” “Yauwa ƴar albarka nakuwa gode, bara na turo miki Laila ta tayaki. Ɗaf ɗokina ya gudu, kamar zanyi magana sai kuma nai shiru harta fice. aikin na fara ina tunanin yanda abin zai kasance, dan insha ALLAHU bazan fita daga ɗakin nanba yau sai da abun nan.
Laila ɗaya daga cikin yaran gidan ta shigo ko sallama babu, bataimin magana ba ta nema waje ta kwanta a cikin kujera tana danna waya, nima bance da ita komaiba na cigaba da aikin, tsaf na kammala falon na saka fresheners dana gani da turaren wuta, sannan na nufi bedroom ɗin. Ƙaton gaske ne shima kuma ya haɗu, sai dai gadon irin gajere ɗin nanne wanda babu yanda za'ai ka iya leƙa ƙarƙashin gado balle harka jawo abu. Wucewa nai toilet ina ƙullawa da kwancewa a raina
, gabana sai faɗuwa yake amma inata addu'a. Bayan na gama sai na ɗan fito falon dan naga mi laila keyi. Tsaye na taddata ta tashi, ta kalleni tana faɗin, “Nazo na baki bedsheet ko?”. Kaina na ɗaga mata alamar eh. Tare muka koma cikin ɗakin, ta buɗe haɗaɗiyar Wadrobe ɗin ta ciro zanin gado mai ƙyau ta ajiyemin a ledarsa. Murmushi kawai nai mata, a raina ina addu'ar ALLAH yasa ta fita, sai kawai naga ta ɗane sofa ta kwanta. Kaina na dafe ina cije leɓe, wannan itace damar da nake da ita ta ƙarshe, gashi kuma tana neman kufcemin. Jiki a sanyaye na fara yaye zanin gadon dake a gadon, na ajiyesa gefe suma filolin na fara cire rigarsu, harna gama na saka na wanda ta fiddomin, na ɗauki zanin gadon na fara shimfiɗawa, ina gab da gamawa akai kiran wayarta, gani nai ta tashi tana murmushi, ta kalle ni tana faɗin, “Larai banda aikin mugunta fa, ki tabbatar komai tsaf bara na amsa waya”. Kaina na ɗaga mata ina murmushi, ta zare keys ɗin duka drawer ɗin ɗakin ta fita da su, bakina na taɓe dan inda take bama tsaron ni bashine abin harina ba. Wata ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi jin ƙarar rufe ƙofa alamar tama fita daga falon. Ban ɓata lokaciba na yaye zanin gadon gaba ɗaya jikina na rawa, katifar na kama na ɗaga, bana ganin abinda ke ƙasan gadon saboda an saka kwali bisa katakon shimfiɗar gadon, maida katifar nai na ɗan fito falo na sake lalleƙawa, ganin babu kowa nai azamar dawowa na sake ɗagawa, shima kwalin ɗagashi nai, addu'a naketa yi a raina nidai, ina ɗaga kwalin wani hayaƙi ya taso ya bulemin ido, tari na farayi kamar zan mutu, na saka hannu na toshe bakina dan kar wani ya jiyoni, saurin maida katifar nai saboda jin kamar motsin tafiya, na cigaba da ƙoƙarin gyara gadon kamar dama shi nakeyi, hajiyace ta shigo, ɗagowa nai naimata murmushi, itama dai fuskarta da murmushin take faɗin, “Kai sannu da ƙoƙari larai, falon yayi ƙyau kuwa, an wanko bayi ko?”. “Eh na wanke hajiya, yanzu nan zan ƙarasa kawai”. “Yauwa to sannu da aiki kinji, ina Lailan?”. “Yanzun nan tafita inaga abu zata ɗakko”. “Okay