Showing 96001 words to 99000 words out of 261165 words
Chapter 33 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
tamjar yanda Jawaad ya yanke shawarar suyi kawai. Ya kuma kira Sir Ahmad ya sanar masa halin da ake ciki, hakama Alhaji Babba.
______________________
Tunda Jawaad ya kira Alhaji babba ya sanar masa inda zasuje da rokon a tayasu addu'a sai ya kasa zaune ya kasa tsaye, haka ya tara tsoffin anguwarsu sukai shawara akan subi makarantu yanzunan a dasa saukar Alkur'ani mai girma, tare da masallatai idan lokacin sallar zuhur yayi, ya kira Ummah babba da ƙarama ya umarcesu da yin abincin sadaka su bada a fitar a rabama mabuƙata.
lokacin dasu Jawaad ke cikin wancan mawuyacin halin addu'oin bayin ALLAH ne dana ƙananun yara keta riskarsu, tareda farin cikin mabuƙata da aketa rabama lafiyayyen abinci harda abin sha.
(Duk wanda yace ALLAH ya tsira wlhy, bawa saki kowa ka kama ALLAH shine shugaba mai kallon motsin kowa hatta da ƙwaron da idanu basa gani, mai bada kariya ga kowa ta inda bakai zatoba, mubar zagin shugabanni na duniya da suka zama wakilanmu akan san zuciyarmu, mubar ɗaukarsu matsayin waɗanda zasu bamu kariya ko farin cikin duniya domin suma mutanene tamjarmu, basu isa sanin abinda yake ɓoyeba sai wanda ALLAH yaso su sani, mu aje shirmen siyasa gefe muyima ƙasashenmu addu'a da shuwagabanninmu wannan shine nasararmu).
________________________
Su Jawaad sun isa da gawar Gimba ƙauyensu, inda helicopter ɗin da suke ciki ya sauka a filin makarantar primary ɗin dake gab da gidansu gimban, daga nanne aka ƙarasa da gawar bayan su Baba ƙaura sun fara isa gidansu Gimba sun isar da saƙo maiban tashin hankali.
Faɗa muku yanda abubuwa suka cabe a wannan lokaci abune mai wahala, dan matarsama suma tayi saida aka zuba mata ruwa, haka ƴan anguwa da danginsa sunata kuka dan gimba mutumne na mutane, sannan yanada son zuminci, duk alkairin da yake samu ga Jawaad bai yarda yaci shi kaɗaiba hatta da wanda ba nasabama ci suke shima.
Gimba shi kaɗaine ɗa namiji wajen iyayensa, babansa ya rasu tun suna yara, mahaifiyarsu itace taita ɗawainiya dasu har girma, sai ƙanwarta dake aure birni da bata gajiyawa da taimakonta da marayun ƴaƴanta har suka girma, yayi karatunsa har zuwa diploma saɓanin ƴan uwansa mata da ke tsayawa iyakar secondary ake musu aure, shine ɗa na farko, sa
i ƙannensa shida duk mata, huɗu sunyi aure harda zuri'a sai biyu na nan suna karatu, harma Jawaad ya ɗauka alƙawarin zuwa ya roƙa mahaifiyar su gimban dan suci gaba da jami'a idan sun kammala sakandiri ɗin da suke aji shida yanzu, a lokacin gimba yata murna dan dama burinsa kenan. Matar gimba ɗaya da yara uku duk maza, yaronsa na ƙarshe sunan Jawaad ya saka masa yana kiransa da suna yayana. Adalilin Hajiya Safara'u ƙanwar mahaifiyarsu dake zaune birni ya samu aiki a ƙarƙashin Jawaad, (zuwa gaba lokaci zai fiddo mana wacece Hajiya Safara'u).
Mahaifiyar Gimba mace mai haƙuri da sam batai kukaba saina zuci itace tace Jawaad ne zaima gimba wanka tare da ƙaninta mai suna Ibrahim wanda ya kasance dattijo ne sosai.
Su Jawaad suna can suna ƙimtsa gawar Gimba su Alhaji Babba suka iso kusan mota huɗu, harda jama'ar gidansu Jawaad wato kawunnansa.
Jawaad da kawu Ibrahim sun suturta gawar gimba tamkar yanda shari'a ta koyar, kafin mahaifiyarsa da ƴaƴansa harma da ƙannensa su shiga suyi sallama da gawar, daganan aka fito dashi domin miƙasa maƙwancinsa na gaskiya. Kuka sosai ya tashi a gidan maiban tashin hankali har aka fice da gawar daga gidan zuwa ƙofar gida inda su Alhaji babba da mutanen gari suka haɗu wajen sallatarta.
Masha ALLAH yayi jama'a kam har abin ya bama mutane mamaki, sai dai UBANGIJI shiyasan ajiyar da yay a wannan waje. (ALLAH ya gafartama gimba da iyayenmu da dukkan musulmai da suka rugamu tafiya😭🙏🏻).
Bayan an dawo daga kaisa su Jawaad basu tafiba, suna a cikin garin har gabanin magriba ana amsar gaisuwa dasu shi dasu Hafiz, Jabeer, Aliyu, sai Bilkisu. Sojojin da sukai musu rakkiya da Baba ƙaura sun wuce tun bayan da aka dawo daga binnesa. Rose ma lokacin da su Sir Ahmad zasu tafi dasu Alhaji babba bayan sallar la'asar Jay yace ta bisu. Bilkisu kuwa tana ciki tare da matar Gimba, batasan yaya akai sukasan ita matar Jawaad baceba, sai kawai ganitai anata nunata da faɗin itace matar ogan marigayi Gimba. Haka zasuyita jera mata addu'a da yabon halin Jawaad bisa ɗawainiya da taimakon da ƙauyen yake samu daga Jawaad ɗin ta dalilin gimba. Haka sukaita mata komai a girmame tamkar tafi kowa. Ita harma kunya ta komaji akan yanda suke matan.
Wajen ƙarfe shida saƙo ya iso mata akan ta fito inji boss zasu wuce. Haka ta tashi ta kimtsa jiki a saɓule dan ta amshi hijjab ɗin matar gimba ta saka tun ɗazun saɓanin da da take da baby hijjab kawai. Sunata mata godiya da addu'a, ƙannensa suka rakota har waje inda motar da zasu tafi take.
Sau ɗaya na kalli Boss na ɗauke idanuna saboda wani irin tausayi yake bani, na ƙaraso inda yake tsaye na gaishesu tare da sake musu gaisuwa, murya cike da damuwa ya amsa mani yana min nuni dana shiga motar daya buɗemin. Ni da shi da Jabeer ne a baya, ina jikin ƙofa yana tsakkiya Jabeer kuma a ƙarshe, sai Aliyu da zai ja motar Hafiz na gefensa. Haka muka wuce sunata mana addu'oin sauka gida lafiya.
Sosai Aliyu ke sharara gudu kasancewar garin yay wani irin ɗaurewar hadarin farkon damina mai cike da iska a ciki, babu mai magana a motar sai zancen zuci, cikin awa ɗaya da mintunan da bazasu gaza ashirin da bakwaiba muka iso cikin gari, zuwa lokacin garin ya sake yin duhu, gana hadari gana magriba, anata salloli a masallatai. Nayi zaton masarauta zasu kaini, sai naga an nufi gidansu Boss, koda mukazo gate sai yace basai Aliyu ya shiga da motarba bara mu sauka anan su wuce kar hadarinan ya riskesu..................✍
(Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka kashe ɗan fir'auna, miyasa suka kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba.)
dolene jiya kushiga ruɗani akan mutuwar ɗan fir'auna bayan farkon page na nuna bai mutuba, nima sai a Comments ɗinku na fahimci kuskuren danayi na koma na duba page ɗin, wlhy hankalina sam bai kaiba ko'a wajen editing, rayuwace abubuwa sunma ƙwaƙwale yawa, kana gabas tunaninka na yamma, amin afuwa ɗan fir'auna bai mutuba🤦🏻. anahin abinda naso sakawa a
wajen shine (Dolene koda zai halaka da izinin ALLAH sai ya gano suwaye suka so kashe ɗan fir'auna, miyasa sukaso kasheshi?, minene a binne da rayuwarsa da ɗan-fir'auna yaso sanar masa, yanaji a jikinsa masu son kisan ɗan fir'auna nada nasaba da abinda ya shafesa, minene shi? Wannan ne bai saniba).🤗🙏🏻
ALLAH ya gafartama iyayenmu😭🙏🏻.
[12/18/2020, 3:57 PM] HASNA✍🏻: +234 909 304 4460:
Page 31
...............“Muje”. Ya faɗa a hankali. Babu shiri nai azamar ɗago idanuna na kallesa, duk da ni yake kallo ban janyeba, cikin harɗewar harshe nace, “Anan zan... zan kwana?”. Tamkar baiji abinda naceba ya ɗauke kansa, dubansa yakai ga sararin samaniya daketa sake caƙuɗewa da duhu, batare da yace min uffanba ya raɓani ya nufi gate. Hawayen da nake maƙalewa suka silalomin a kumatu, a fili nace, ‘Dan ALLAH kar kaimin haka nidai’. Kamar yasan mi nake faɗe ya juyo yayinda ya buɗe ƙofar gate ɗin zai shige, “Karki bari na dawo na sameki a nan gurin”. Yafaɗa yana nunoni da ɗanyatsa alamar gargaɗi. Hannu nasa na share hawayen fuskar tawa kafin na taka nima zuwa gate ɗin. Maigadine kawai ke bin jam'i a bakin gate ɗin da yake anaji daga cikin gida. Ganin yayi tsaye yana kallon maigadin ne yasa nima naja na tsaya, sai da aka sallame sallar da dama zaman tahiyar ƙarshe suke. Kamar jira, ana yin sallama maigadi na miƙewa ya nufosa. Fuska a haɗe Jay ke kallon maigadi, baiko amsa gaisuwar da yake masaba da sannu dazuwa yace, “Ka bautama UBANGIJI tamkar kana ganinsa, dan idan kai baka ganinsa shi yana ganinka, MANZON ALLAH ya horemu da zuwa masallaci muyi sallah cikin jam'i, miyasa kai kafi zaɓar yinta kai kaɗai a cikin gida? Shin tsaron gate dan kar wani ya shigo yafi maka muhimmanci akan zuwa ka samo cikakkiyar ladar da mahaliccinka kaɗai ke badata? Daga yau ina mai baka shawara a kowanne lokacin salla ka kulle gate ɗin nan idan yazama dole saika zama mai tsaron mutanen cikin gidan kaje kai sallah cikin jam'i”. Kan maigadi a ƙasa yace, “Nagode sosai Alhaji, ALLAH ya saka da alkairi ya kareka kaima, ya ƙarin haƙuri?”. Cikin lumshe ido Jay yace, “Alhmdllh, abokinku ya tafi ya barmu”. Hawayene suka ziraro a fuskar maigadi, hakan yasa Jay yin gaba shima yana haɗiye abinda ya tokare maƙoshinsa.
Jiki a saɓule nabi bayansa mukabar maigadi na kuka, sai naji nima hawayen nawa na sake gangarowa, dukda bawani sanin gimba nai sosai ba mutuwarsa ta taɓani ainun, mutum mai fara'a dason mutane.
Yana gama buɗe ƙofar da keys ɗin daya ciro a aljihu iskar na tasowa, hakan yasa muka shige da sauri saboda irin mai ƙasarnan ce sosai, da sauri na maida ƙofar na rufe na jingina jikinta ina sauke numfashi da share fuskata da hijjab ɗin gudun kar wadda ta hau ta shigarmin ido.
Boss kam ya kunna fitilar falon saboda an kunna Gen..., a take haske ya gauraye ko ina, baice dani komaiba ya nufi sama abinsa. Tafiyarsa kawai zaka kalla zaka fuskanci yana cikin damuwa, dan a sanyaye yakeyinta. da kallo na bisa har saida ya ɓacemin, na sauke ajiyar zuciya ina lumshe idanuna, a ƙasan raina addu'a nake ALLAH yasa idan iskarnan ta lafa yace zai maidani Masarauta.
Tunda ya shiga bedroom ɗin sai ya shiga yatsina fuska, shaf yama manta ko gadonsa bai samu arziƙin gyaraba yau, duk yanda yake jinsa a matuƙar gajiye haka ya daure ya shiga kakkaɓe gadon, ya gyarashi tsaf kamar ba yanzu za'a kwanta a kansaba, fitowa yay ɗaukar tsintsiya, duk da sarai yaga Bilkisu dake tsaye jikin ƙofa har yanzu yay tamkar bai gantaba yaje ya ɗakko kwandon da kayan sharan ke ciki yazo ya sake hayewa sama.
Da kallo na bisa, haka kawai sai naga kamar bai daceba, dan da alama shara zaiyi da kansa, bayansa nabi jikina duk a saɓule, ga kaina namin wani irin ciwo ƙasa-ƙasa, ga yunwa dan rabona da abincin kirki tun breakfast ɗin safe, a garinsu marigayi fura kawai nasha rabin kofi itama sai da aka takuramin. Duk da sallamar da nayi bai ɗago daga abinda yakeba, nasan salon amsa sallamarsa a ciki-cikine hakan yasan ban damuba dan nasan dai ya amsani, nace, “Bara in share”. Kamar bazai kulani ba, sai kuma ya miƙamin tsintsiyar ya fice.
Ajiyar zuciya na sauke na cigaba da sharan a sake ganin ya fita saini kaɗai. Tsaf na kammala sannan na nufi toilet, shima dai yana buƙatar wankin dukda bawani datti yayba na tashin hankali, tsaf na gyarashi cike da ƙarfin hali. Ina fitowa daga bayin shima yana shigowa ɗakin, saurin ɗauke kaina nayi daga garesa saboda ganinsa a tuɓe babu riga sai dogon wando kawai da farar singlet yana waya, ya zauna a bakin gado
n yana cigaba da wayarsa, kusan mintuna biyu ya juyo inda nake tsaye, yatsunsa biyu ya murza sukai ƙara, hakan yasa na ɗago kaina garesa, alamar nazo yaymin. Ahankali na taka zuwa garesa, ya miƙamin wayar batare da yace komaiba ya bar wajen. Duk da bansan ko waneneba haka nai sallama, muryar Ummah naji ta amsamin, hakan yasa na gaisheta cike da girmamawa, itama daga can da kulawa ta amsamin tare da min ta'aziyya. Nai mata godiya Nabeelah ma ta amsa muka gaisa, sai aunty Batool itama, daga nan mukai sallama. Wayar na ajiye masa bakin gado na fita falo, Zama nai a kujera ina jiran ya fito naji hanlin da nake ciki, harga ALLAH bana fatan kwana a gidannan. Nai zurfi a tunani da jiran fitowarsa kira ya shigo wayata, gyara zama nai na cirota a aljihu, Amaturrahman ce, dan haka na ɗaga muka gaisa, daga can tace, “Mun jiki shirune, ca muke tun biyar zaki dawo?”. Ɗan murmushin ƙarfin hali nayi, kafin nai mata bayanin yanda zata iya fahimta, nakuma nuna mata cewar bamu dawoba muna ƙauyen su gimban sai dai gamu nan a hanyar dawowa” addu'ar isowa lafiya tai mana kafin mu yanke wayar. Na faɗama Amaturrahman hakane da tunanin idan boss ya fito zaiji tausayina ya maidani can a daren nan.
Jawaad daya samu yay wanka da ruwa mai ɗumi sosai sai yaɗanji daɗi da sauƙin nauyin jikinsa sai dai na zuciya, yay alwala ya fito, ƴan dube-dube ya hauyi sai dai babu ko alamarta a ɗakin, guntun tsaki yaja yana lumshe idanunsa, dan shi kaɗai yasan ya yakeji, ga yunwa ga gajiya ga damuwa, dan shi babuma abinda ya sakama cikin nasa bayan coffee da yasha a office sai ruwa da yayta sha a garin su Gimba. ita kanta tausayinta yakeji gashi bawani ƙarfine da itaba ta tashi daga ciwo shekaranjiya jiya. Wadrobe ɗinsa ya buɗe ya ɗauki jallabiya fara tas ya saka mata turare sannan yasa a jiki, harya shinfiɗa abin salla sai kuma ya kalli ƙofa, koya kirata bazai yuwu tajiba saboda iskar da ake a waje abun babu sauƙi, tamƙar zata ɗauke rufin kwano, danma duk Windows ɗin sashen a rufe suke shiyyasa sukejinta da sauƙi su.
“Ki taso kiyi wanka”. Ya faɗa kawai daga ƙofar ɗaki ya juya abinsa dan yasan zata iya jinsa daga inda take. Ba ƙaramin wintsilawa kayan cikina sukaiba lokacin da furucinsa ya isomin cikin dodon kunne, sai dai koda na ɗago tuni ya juya sai ƙamshinsa daya barmin. Rasama wane tunani zanyi nai, mi yake nufi da nazo nai wanka? ‘A toilet ɗinsa?’ na faɗa a fili kamar zanyi kuka. saukar ruwan sama babu zato ya sakani miƙewa zumbur dan naji tsoro wlhy, gashi da ƙarfi ya sauka dukda p.o.p hakan bai hanani jin ƙararsaba akan rufin, to nidai dama can akwai tsoro idan ana ruwa, nafi buƙatar naga mutane a kusa dani hankalina yafi kwanciya, balle wannan da ruwan ya kasance kaso biyu a cikin uku iskace ma, wani wal garin yayi na walƙiya, labulen Window'n da ba'a sakiba sai glass ɗin kawai aka rufe yasa naga tamkar inuwar mutum a wajen, jikina har rawa yake na tashi na nufi ɗakin boss da ɗan gudu-gudu sauri-sauri har ina neman faɗuwa, wayatama anan na barta saman kujera. Na maida ƙofar da ƙarfi na rufe ina rumtse idanu da sakin nishi mai ƙarfi, har yanzu ƙirjina sai wani ɓal-ɓal yake badawa.
Shidai Jay salla yake, amm duk da haka ya jiyo yanda Bilkisu ta rufe ƙofa da ƙarfi, koda ya idar bai juyi ya kalleta ba, ya miƙe domin kawo isha'i da yaga lokacinta yayi. “Sallarce bazakiyi ba komi kike nufi?”. Da sauri na buɗe ido ina kallon bayansa daya juyamin. Murya a raunane nace, “Ai idan naje gida duk zanyi fa?”. Cikin takaici Jay yace, “Ainan ɗin jejine ko? Karki bari na ɓata miki rai a darenan Miemaa, ƙyaƙy! tom”. Daga haka ya kabbara sallarsa.
Jin yanda yay maganar a kausashe na tabbar zai aikata duk abinda ya faɗa ɗin, haka na nufi toilet ɗin ina ƙunƙuni a raina, wannan wane irin abune haka, miyasa tunda anga hadarin baza'a kaini inda nakeba sai a wuto dani nan, nidai komai dare saina bar gidanan ehe. Da wannan ƙunƙunan a cikin rai na shiga bayin, ruwa mai zafi na haɗa dan jikina bala'in ciwo yakemin sosai, banga wani soso ba bayan nasa a bayin, haka na ɗauka nai wankan da shi ina maijin daɗin ruwan, sai da na kammala nai alwala sai kuma
naji ƙyanƙyamin maida kayan dana cire, to amma idan ba su ɗinba mizan saka? Nida bazan fita da tawul ba gaskiya, to idanma na ɗaura tawul inada kayan dazan saka ɗinne a ɗakin.........?
Wata irin ƙara na saki jikina na masifar rawa saboda ɗaga kan da zanyi idanuna sukai tozali da wata iriyar mummunar halitta baƙa ƙirin da jajayen idanu, jikinta dai zam maciji, amma kan bana maciji baneba...
A rikice Jawaad dake addu'a ya miƙe saboda jiyo ƙarar Bilkisu dake bayi, ALLAH ya sosa bata kulle ƙofarba, ya tura da ƙarfi babu ko neman izini ya shige, dai-dai bily tai baya zata faɗi saboda numfashinta daya ɗauke dan firgici, tallafota yay ta faɗo jikinsa, yayinda idanunsa kebin halittar dake silalawa ta Window zata fice da kallo. Sai da ta gama ficewa tsaf sannan ya maido kallonsa kan Bilkisu, saurin kauda idanunsa yayi dan babu komai a jikinta, ya jawo tawul dake ciƙin ƴar drawern glass na toilet ɗin ya yafa mata sanann ya ɗaukata cak batare da yace komaiba ya fita da ita. Saman gadonsa ya shimfiɗeta, dukda ya yafa mata tawul sai da ya sake jan bargo ya rufa mata har saman ƙirjinta, tsaye yay yana ƙarema fuskarta kallo tamkar maison gano amsar tambayoyin zuciyarsa akan fuskartata, tsahon mintuna kusan goma kafin yabar wajen ya koma toilet ɗin yana dube-dube, babu komai kam, sannan a mamakinsa Windown kaɗan ya ɗaga, hanyar da yabi baikai faɗin da halittarnan zata iya shiga da fitaba, ‘mikenan?’ ya tambayi kansa, dagacan gefen zuciyarsa ta bashi amsa da (Aljanu). “Aljanu!” ya maimaita akan laɓɓansa har sau biyu. “Hummm!” ya sake faɗa a fili yana ɗibar ruwa kaɗan a ƴar roba dake toilet ɗin ya fita. Iskar hadarin ta fara lafawa, sai ruwa da ake yaf-yaf na farkon damuna, dan daya fara da ƙarfi sai kuma ya koma ɗaf, sai kuma ɗan yaf-yaf, sai dai walƙiya da aketa faman yi harda cida mai ƙarfi lokaci-lokaci.