Showing 252001 words to 255000 words out of 261165 words
Chapter 85 - Kwai Cikin Kaya Part 2 Hausa Novel Complete
a cikin idanunsu ƙarara Dad yace, “Munyi hakane domin rufe sirrinmu, dan bayan mun gama aikata abinda bokanyarmu tace ga Abdul-aziz sai kawai mukaci karo da Rahama da Bilkisu a bazata duk suna kallonmu ashe, duk da munsan asirin dake tattare damu bazai bari su iya komaiba a kanmu hakan bai hana hankalinmu mummunan tashi ba, a take muka aika ɗan aike wajen bokanya, mukuma mukabi ayarin masu kukan mutuwa da jimami. Kafin a gama kammala haɗa gawar Abdul-aziz muka sake samun ɗan saƙo daga bokanya akan bilkisu da Rahmah. andai rufe bakin Rahmah kamar yanda bokanya ta faɗa har abada bazata sake tuna abindama ta ganiba balle wani ma yaji daga gareta, Bilkisu kuwa babu yanda za'ai bakinta ya rufu sai dai ta haukace, hakan kuma bazai tabbata ba sai idan data farka za'a bata ruwan tsafin da bokanya ta aiko dashi. Musan mu bazai yuwu muyi hakaba, dan haka Nasir ya kawo dabarar zuwa ga Humaira (Mom) da Mama (Mama Atika) dan ya sakasu suyi mana wannan aikin ta hanyar daya dace tunda suma akwai nasu burin akan dukiyar Abdul-aziz........”
Kuka mama atika da Mom suka fashe dashi. mama Atika tace, “Wlhy ALLAH ne shaidarmu baku sanar mana akan hakan zakuyima Bilkisu asiri ba, Nasir ya samemu lokacin da aketa shirin fita da gawar Abdul-aziz, mukuma isowarmu kenanma babu jimawa. Yace muyi ƙoƙarin bama bilkisu ruwan maganin, ta hakane kawai zamu sami damar mallake duka dukiyar da Abdul-aziz ya tar.......” sai kuma ta kasa ƙarasawa ta fashe da matsanancin kuka. Uncle Nasir ya kalleta shima yana kukan,
“Ki ƙarasa mana mama, ai duk kece silar komai, kece kike mana huɗuba akan karmu yarda kowa ya fimu a ƴaƴan baba, kece kika saka ƙiyayyar Abdul-aziz a ranmu, a cewarki an auro uwarsa a bayan baya amma ɗanta yazo yafi kowa arziƙi a gidan harda ƴaƴanki, bayan kuma mune ya dace muyi wannan arziƙin saboda kece matar baba ta farko, mukuma mune ƴaƴan farko a gidan. A dalilin wannan huɗubar taki na jefa kaina a halaka, tun bana ɗaukar huɗubar Alhaji Ali da Alhaji Sadi har suka fara tasiri a raina, nidai burina kullum na wuce Abdul-aziz arziƙi dan na faranta miki rai. hakan yasa duk muguntar dasu Alhaji Sadi suka kawo shawarar a aikatama Abdul-aziz na dinga biye musu, har takai sunyi ƙokarin jawo Abdul-aziz cikin tafiyarmu, dan har wajen bokanya an kaisa da yaudarar zata bashi maganin sammune saboda magautan siyasa. Ko'a hakanma saida ya tirje, nine naita lallaɓarsa harya amince ya bimu, koda yaje yaga abinda muke nufin ɗorasa a take ya bijire mana ya kuma nuna ɓacin ransa mai tsanani akan hakan. Sai dai zukatanmu sun rigada sun bushe a lokacin. gani muke kamar zai tona mana asirine. dan haka muka gaza ƙyale rayuwarsa ta huta, duk wani burinsa na aikata alkairi ga talakawansa mun daƙilesa ta hanyar asiri da muzgunama rayuwarsa, kowane aiki munyi bake-bake a kansa tare da handame dukiyar da aka keɓe danyin ayyukan, daga ƙarshema bokanya ta bamu tabbacin jinin Abdul-aziz zai taimaki tafiyarmu, dan haka muyi amfani dashi, kafin hakan kuma dolene muyi fasiƙanci dashi. Jinin Abdul-aziz shine jini na farko da muka fara salwantarwa, dan da duk abinda zamuyi na tsafi da jinin dabbobi mukeyi. Amma nasarar da muka samu da jinin Abdul-aziz yasa burikanmu sake faɗaɗa, muka fara sadaukar da makusantanmu. Mama da humaira sune suka ɗurama Bilkisu maganin da bokanya ta bamu bisa taimakon Uwaisu, mukuma lokacin mun tafi bizne gawar Abdul-aziz.
Sanda muka dawo mun iske bilkisu cikin hauka tuburan, hakan ba ƙaramin daɗi yay manaba kuwa, dan asirinmu kam dai munsan ya rufu kenan. Ni na bada babbar ƴata kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana, na kuma bada na Mama (Mama Atika) sai dai bokanya tace ba'a lokacin take buƙatar Mama ba, dan tana hango zatai mana amfani sosai a tafiyarmu, haka na musanya jinin Mama dana Mama Suwaiba da Mama Maryam, na kuma haɗa da matata ta farko. Shima Alhaji Ali aka buƙaci ya kawo, shi a take ya bada na Mamansa da ƙanwarsa, da ɗansa na biyu, sai dai kuma nace bai isa ya bada na ƴar uwataba (Mom), wannan dalilin yasa ƙungiya tai masa lamuni akace ya bada na wata matar idan yanada ita, kokuma ya ƙara aure, sai kuma jinin ƴarsa babba mace shima. Hankalinsa ya tashi dan yana tsananin son Shahudah, a lokacinma batafi shekara huɗu da wata bakwai da haihuwaba, yayta roƙo da neman alfarma akan zai canja da wani. Da farko Bokanya bata amince ba, sai bayan kusan kwana biyu dayin hakan ta bashi umarni akan ya auri Rahmah, hakan shine kawai zai kawo sake rufuwar asirinmu, sannan idan Shahudah ta girma yay ƙoƙarin haɗata aure da Jawaad, nanma zamuci moriyar hakan, indai ya aikata haka ƴarsa zata tsira da matarsa, idan Rahmah da ta haihu sai ya bada duk abinda ta haifa madadin Shahudah. Da wannan shawara da umarni yay amfani, na shige masa gaba ya samu auren Rahma ta wajen mahaifinta, dan lokacin Mama Maryam ta rasu. Tabbas badan baƙin asirin da mukaima Rahma ba bazata taba yarda ta auri Ali ba, duk da kuwa abinda ya faru kusan shekara bakwai a lokacin, amma bata da wani zaɓi, dan ta ko'ina mun gama ƙulleta.
Kafin auren Rahma da Ali ya tattara su Humaira ya bar ƙasar dasu, wannan duk yana cikin dabarun karta tada hankalintane akan za'ai mata kishiya, shi kuma Ali yana matuƙar sonta bayason tashin hankalinta. Sai da ya maidasu da kusan wata biyar sannan akai bikin, lokacin Bilkisu ta gudu daga gida saboda asirin da muka kuma tafka mata aka kai gidan Alhaji Kokino, burinmu haukanta ya nisan tata da gida har abada koda ƙasar waje ne ma taje. Badan Ali nason Rahma ya aura ba. bayan bikinsa da Rahmah itama ya ɗauketa daga ƙasar ya maidata Ghana da zama duk a cikin shirinmu, sai dai kuma acan ɗin saita gamu da wata ƙawa data tsaya tsayin daka wajen taimakonta da addu'oi ganin kamar batama cikin hayyacinta a rayuwar aurenta da Ali. ba komai yaja hakanba sai ganin yanda Ali ke gallaza mata, bata taɓa yunƙurin barinsa ba ko faɗama ƴan uwanta, sai dai tai kukanta ta share hawaye. gashi tana zuwa ta samu ciki kuma. Ganin matarnan zata buɗe mana aiki ya sake ɗakkota ya maido ta nan ƙasar, inda mukai zaman dakon haihuwarta....” Kuka ya sarƙe Uncle Nasir ya kasa cigaba, sai Dad da shima ke kukanne ya cigaba da faɗin,
__________________
ZAFAFA 2021
_______________
Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
________________
“Tabbas na zalinci Rahama, dan a zamana da ita bata taɓa jin daɗiba koda na awa ɗaya, daga hantara sai ƙyara da gallazawa a tsakanina da ita. Bantaɓa bata ƴanci na matar aure ba. Abincima nakan batane tamkar wata dabbar da nake turka, kullum cikin roƙona take daban haƙuri amma ban taɓa saurarentaba, tunda cikinta ya cika watanni bakwai ta fahimci manufata a kansa sai hankalinta ya sake tashi, zuciyarta ta bushe, ta daina kuka akan dukkan gallazawar da nake mata, ta maida hankalinta wajen addu'oi akan ALLAH yakare mata cikinta, ƴan uwanta duk wanda yazo wajenta ko ƴan uwana roƙonta shine su tayata addu'a ta haihu lafiya. Daga randa na fahimci haka saina hana kowa shigowa gidan har ƴan uwana, na saka maigadin da babu wanda yake bari ya shiga saida izini na. Hakan ya ƙara saka Rahma a ƙunci da damuwa, nikam ko'a jikina ban taɓa jin tausayintaba, burina kawai ta haihu na samu cikar burina. A wannan halin cikinta ya cika watanni tara da wasu kwanaki, haihuwa kawai muke saurare, bana yarda nai tafiya mai nisa dan karta haihu bana nan, dama gashi na hana kowa shigowa gidan, na kuma ƙulle bakunansu da asiri har mahaifinta da ƴan uwanta. A wani dare ta farka da naƙuda, babu ko tausayi nazo kanta na tsaya, duk taimakon data buƙata naƙi yimata shi, haka taita wahala har wayewar gari bata haihunba, tunanin kar abinda zata haifamin ya mutu nayi asara ya sani shiryawa na nufi wajen bokanya ni da Nasiru, ko zamu samo wani taimakon da zamu bata ta haihu. Lokacin da muka dawo sai muka isketa ta haihu, sai dai babu ɗan sai ita kaɗai. Hankalinmu ya tashi, muka shiga mata tambaya sai tahau dariya da faɗin, “UBANGIJI baya zalinci ga kowa sai dai bawa ya zalunci kansa, jinin jinina yafi ƙarfinku azzalumai, ALLAH ya cire ƙwai a cikin ƙaya sai dai ku mutu, a yau kuma ALLAH ya tunatar dani duk abinda kuka binne akan yah Abdull, babu shakka kuma saina tona muku asiri, sai duniya tasan kuɗin su wanen........”
Wani wawan mari na ɗauke fuskarta da shi tare da buga kanta a bango har saida ta suma, kafin na shureta da ƙafa ta farfaɗo, a hakanma bakinta bai mutuba, gaya mana duk maganar da tazo bakinta takeyi, hakanne ya harzuƙamu muka kwasheta zuwa wajen bokanya. A can ɗinma bakinta bai mutunba, ta dinga faɗa mana jininta shine jini mafi tashin hankali da zamu salwantar, “Daga wannan ranar bazaku sake samun kwanciyar hankaliba azzalumai, insha ALLAHU wataran sai Ƙaddara ta haɗa Jini da jini sun addabi jininku, Jawaad da ɗiyar dana haifa da izinin UBANGIJIN al'arshi sune zasu zamewa rayuwarku barazana da tashin hankali tun anan duniya, kuma in ALLAH ya yarda sune sanadin tonuwar asirinku a duniya, waɗanan kwayayen guda biyu sai sun kunna wuta bisa kanku ku ƙayoyi kun ƙone ƙurmus kafin kuje ga UBANGIJI shima yay muku nasa hukuncin. Sai kun tuna wannan ranar da wannan furucin da izinin ALLAH. Daga yanzu ku zauna zaman saurare da cikar lokacin da ƘWAI zai fita a cikin ƘAYA ta inda bakuyi zato ko tsammani ba. Domin biyune zasu ɗau fansa tare da ɗunbin al'ummah”.
Wannan shine furucin Rahma na ƙarshe a garemu, muka aikata mata mummunan aiki tamkar yanda mukaima duk wanda muka salwantar. Duk da kuwa maganganunta sun shigemu, kuma tabbas sunyi tasiri a zukatanmu. Iya bincike bokanya tayi ko zata samo inda abinda Rahama ta haifa yake amma hakan ya gagara, abindama take gani jaririyar ta mutu, tun zukatanmu na rawa akan hakan har muka cire abin a ranmu muka cigaba da harkokin gabanmu, ciki harda aƙidar fyaɗe wa ƙananan yara domin amsar budurcinsu kawai kamar yanda bokanya ta sharɗanta mana. Rayuwa ta shuɗa, duniya ta samu a garemu, dan kuwa dukiya ta zauna ga kowanmu, duk abinda bokanya ta sharɗanta mana bi mukeyi, musamman ma ni da bana tsallake komai duk dan gudun kar bokanya tace na bada jinin mamana (Shahudah), haka kawai ALLAH ya jarabceni da matsanancin sonta fiye da suran ƴaƴana. gashi kuma bokanya tace min akwai nasarata tattare da ita, dama ƙungiya baki ɗaya, amma hakan bazai tabbata ba sai anyi aurensu da Jawaad. Da wannan damar mukai amfani wajen jan Jawaad jikinmu, duk da ita Humaira dai batasan ai nahin manufar ba, hankalinmu bai kwantaba har saida akai aurensu, sai dai kuma baiyi nisaba komai ya lalace, a lokacin mu kaɗai mukasan a irin tashin hankalin da muka tsinta kanmu, duk da daga baya bokanya tace mubarsu zatai wani aiki a kansu, amma a aura masa wata matar cikin ƴaƴan family ɗinsu, hakanma zai taimaka mana, sai dai sam Jawaad yaƙi hakan, mun buga ta kowanne fanni babu nasara, tun daga wannan lokacin komai na ƙungiyarmu ya ringa samun tangarɗa da ruɗani, ciki harda shigowar wani maharbi rayuwarmu, sai dai daga baya shi munyi maganinsa ta hanyar salwantar da rayuwar duka iyalansa dashi kansa. Ƙwatsam muna a wannan ruɗanin kuma sai ga Bilkisu ta shigo rayuwata a bazata, inda naci karo da ita a gidan ƴar uwata. Banyi sakaciba na ɗakkota, a washe gari kuma nakai sunanta ga bokanya kamar yanda mukeyi akan budurwar da duk muke buƙatar budurcinta, sai dai kuma Bilkisu sai tazo da banbanci ga sauran, dan bokanya tamin alƙawarin inhar na mallaki budurcin Bilkisu na cika dukkan sharuɗan ƙungiya, dukiyata zata sake haɓaka, zan kuma samu nutsuwa akan komaina. Tamin alƙawura da dama game da yarinyar, sai dai kuma komai bai yuwuba, dan yarinyar tana tattare da wasu sirruka da muka gaza ganewa har zuwa yau, ta zama sanadin rushewar abubuwa masu yawa a garemu ciki harda aurenta da Jawaad, tashin hankalin da muka fahimci yana tunkaromu a dalilinta yasa muka sadaukar da jininta ita da Jawaad.........”
__________________
ZAFAFA 2021
_______________
Masoya naku taurarinfa sun sake dawowa da sabon salo a 2021.
Hafsat miss xoxo🥰
KIBIYAR AJALI......!
(Sulke baya tareta saita gitta).😋🤗
Mamu gee🥰
MIN ƘALB!!😋🤗
Hafsat rano🥰
ABINDA KE CIKIN ZUCIYA...!!😋🤗
Safiyya huguma🥰 SIRAƊIN RAYUWA😋🤗
Bilyn Abdull🥰
SARAN ƁOYE🤗😋
Duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka👇🏻💃🏻
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
ACCOUNT NO 0812652655
ACCOUNT NAME- HAFSAT LAWAN GAMBO
BANK NAME: ACCESS BANK.
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
0903 234 5899
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
09033181070
Karku Bari ayi Babu ku domin wannnan salon na daban ne
SABUWAR SHEKARA
SABON SALO
TEAM#ZAFAFABIYAR🔥
________________
“Babban sirrin dake tattare da ita shine amincewar UBANGIJI game da furicin mahaifiyarta game daku”.
Wata murya ta bada amsa ga Dad a bazata. Gaba ɗaya falon suka juya suna kallon mai maganar cike da mamaki da al'ajabi. A bazata Bilkisu ta miƙe zaram tana share hawayenta, jikinta na wani irin tsuma da rawa tace, “Inna! Baba! Firdausi da gaske kune? Kodai gizon da kuka saba yiminne?”.
Fuskar Baba cike da murmushi yace, “Mune ƴata ba gizo muke miki ba, mune tsaye a gabanki bayan rabuwar ƙaddara ta tsahon shekaru, na godema UBANGIJI daya sake haɗamu Bilkisu, na godema ALLAH daya kawoni wannan ranar dazan sauke nauyin da ɗan uwana abokina ya ɗauramin tsahon shekaru”.
Da gudu Bilkisu ta nufesu ta rungume Inna da firdausi tana mai fashewa da matsanancin kuka, suma kuka suka sanya harda Baba. Mai martaba ne yay gyaran muryar da ta sakasu yin tsuru lokaci guda, cikin nutsuwa yace, “Su wanene ku? Mi kuma ya kawoku nan?”. Kafin a cikinsu wani ya samu damar bada amsa Jabeer dake bayansu tsaye yace, “Ranka ya daɗe suna tare da magana mai muhimmanci, tun da sassafe suke a gidan Jay suna jira dan suga matarsa, duk korar da maigadi yaymusu basu tafiba. Kasan yanayin da ake ciki, shinefa drivern sa ya kirani ya sanarmin, da naje bayanin da sukaiminne yasa na gamsu na kawosu nan”.
Umarnin ƙarasawa ciki aka basu, sai da suka zauna da mika gaisuwa Bilkisu na maƙale da inna sannan takawa ya bama baba damar yin bayani akan abinda ke tafe da su. Baba ya sauke nannauyan numfashi yana mai duban Bilkisu da Inna ke sharema hawaye, sai kuma ya duƙar da kansa ƙasa ya fara magana da rawar murya. “Sunana Abdullahi, babban amini ga malam Adamu makaho. Abotarmu ta farane tun lokacin daya kama haya a gidan da nake, tun muna iya gaisawa da mutunci sama-sama tsakanin iyalanmu har muka zama aminai, matanmu ma haka. Kamar yanda na daɗe ban samu haihuwa ba Adamu ma hakane, cikin hikimar ALLAH sai ga ciki a jikin matanmu kusan lokaci guda ni da shi. Matata itace ta fara haihuwar ɗiya mace, ga tanan (ya nuna Firdausi) dan dama ta riga matar Adamu samun ciki da kusan watanni biyu zuwa uku. Kamar yanda al'adarmu take matata ta tafi wankan jego ƙauye, bayan tafiyarta da kusan wata ɗaya matar Adamu ta wayi gari da naƙuda, hankalinmu ya tashi dan ba watan haihuwarta bane, a haka muka ɗauketa zuwa asibiti, ƴan kuɗin sana'arsa ya ƙundume ya miƙa akai mata duk abinda ya dace, sai dai daga ƙarshe likita yace sai an mata aiki, dan ɗan dake cikinta ya ruɓe, ma'ana yadai mutu ma, barinsa itama zai zamarwa tata rayuwar barazana. Hakan ba ƙaramin tada mana hankali ya sake yi ba, gashi ƴan kuɗaɗen hannunmu sun ƙare, kuma suna buƙatar kuɗi kafin su mata aiki. Adamu ya barni a asibiti ya hau acaɓa ya kaisa can anguwarsu gidan iyayensa dana sani, dukda dai ya sanarmin mahaifiyarsa aka haifa a gidan (Alokacin Adamu na gani da ido ɗaya fa) sai dai kuma bai wuce awa biyuba sai gashi ya dawo rai a ɓace alamar bai samo komaiba. A gabana ya labartama Asiya komai, dukda halin ciwo da take ciki saita kwantar masa da hankali, tace yaje wajen yayanta Alhaji Ali (Dad) tasan zai taimaka musu. Baiyi musubu ya jani muka tafi tare, gidane katafaren gaske mai ƙyau da gate, a lokacinma duk gidan da kaga gate to lallai maishi ya tara, munta ƙwanƙwasawa amma ba'a buɗe mana ba, Adamu ya tura ƙofar cikin haushi sai gata ta buɗe a bazata, sai da muka lalleƙa babu kowa sannan muka shige cikin gidan batare da tunanin komaiba. Munta sallama a ƙofa nanma dai bamuji motsin kowaba, sai wani irin nishi da gurnanin kuka. Babu tunanin komai Adamu ya nema cusa kansa, na riƙesa ina girgiza masa kai akan karya aikata haka, tunda ba gidanmu baneba, kuma akwai mace a ciki. Hankalinsa dake a tashe na halin da asiya ke a ciki yasa bai saurareniba, ya fisge hanunsa ya shige ciki babu ko sallama. Duk da a tsorace nake banida zaɓin daya wuce bin bayansa nima. Sanda muka shigo cikin falon sai mukaji kukan ya yawaita, gashi ana kukan ne da addu'ar fatan neman ɗauki daga ALLAH, Adamu